x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 27 - AGOLA free pages

  • 78001 words
  • 81000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
rashin jin ba'a magana sai ace yarinya ce, toh dai shawara ta anan sai ka haɗa da hakuri, kar kuma ka ce zaka kashe kan ka wajan kashe kudin a hidimar tarewan nan dan basu da godiya dan tun da tazo gidan nan a matsayin agola baka gani ba duk hakuri muke amma ko shi Daddyn na su basu gode masa" duk kallon ta suke da mamaki Sadeeq ya mike yace"Sai anjima" ko friends dinsa be jira ba ya fita suma duk suka mata sallama ta bi su da harara. Bayan Zahra ta shigo ta gaishe da su Anty Mairamah Ammi dake kallon ta tace "ki shiga tana dakin na ne" Zahra ta shiga ta karasa har inda Leena ke zaune ta hada kai da gwiwa tana sheshsheka Zahra tace "Haba ke kuwa Leena, sai kace baki san wanda aka aura Miki shi ba" Leena ta share hawayen ta, ta ɗago tana kallon wani direction Zahra tace "ke ma kin san Sadeeq be yi kama da wanda zai cutar da ke ba, wallahi dama hakura kikayi da kukan nan ki godewa Allah da yasa hakan ya faru, dan duk nan ba wanda zai ce yasan halin Muhammad ɗin 100% so Kinga bamu san bad side ɗin sa ba kuma dama ba'a zuwa neman aure da bad side, shi kuma wanda kika aura an san shi for more than years" Leena ko kallon Zahra ta ki yi. Hajiya da ta gama tsara tafiyar tana kallon Ammi tace "ina ga yana da kyau ace Khadija zata bi mu kar ta kullace mu tace ba'a sata a lamarin ba" Ammi bata so ba amma tunda Hajiya da kanta ne tayi magana yasa ta yi shiru, saboda kai Leena da za'a yasa su Anty Binta ba su mayar da kayan lefen a ranan ba. Bayan sallahn Magrib motoci ne jere a kofar gida Daddy, Jidda da su Anty Binta suka shirya Leena turare kuma sai kace da shi aka mata wanka Jiddah na kallon Leena tace "Leena wanan kukan kuma fah? Dan Allah ki daina nuna tsoron Ya Sadeeq har haka, nasha faɗa Miki Ya Sadeeq yana son ki amma kin ki yarda" Anty Binta ji take kamar ta ɗauke Leena da mari saboda takaici. Ammi barin gidan tayi dan ba zata iya ganin take up ɗin her very own daughter ba, Zahra tayi mata whisper a kunne "Please Leena ki daina wannan kukan, Jiddah ba zata ji dadi ba" Leena ko kula ta bata yi ba. Hajiya da ta koma sashen Mummy ta tsaya musu a kai sai ga Mummy da yaran ta suma sun fito duk sun yi kyau ma shaa Allah, Anty Binta da Mairamah sai hararan kasan ido suke mu su, anan parlorn Ammi Leena dake zaune cikin lafayan da aka rufe mata har fuska ta karasa ciki, Mummy ta fara magana "Leena zaman aure zaman hakuri ne, yi nayi bari na bari, duk muma da hakan aka fara" ta kama hannun Leena dake kara sautin kukan nata Jiddah nata kallon wulakancin rike Amarya da Ummu tayi, mota daya aka sa amarya da Mummy da Hajiya gaban motar kuma Zahra ne. Duk sai da sauran motocin suka tashi kafin na amarya ma ya tashi, ya SubhanAllah a daidai kofar gidan motocin sukayi parking, amma motar amarya har cikin compound ya shiga, dukkan su sai bin compound ɗin suke da kallo da mamaki sabar tsaruwan gidan basu tashi ruɗewa ba sai da suka shiga cikin parlorn wanda sai ka rantse wannan parlorn a kasar waje yake, Hassadan Mummy da yaranta ƙarara ya bayyana a kan fuskokin su, dan nan take annurin fuskar su ta ɗauke, Hajiya tace "wannan gida sai kace a Saudiya take" kowa nata fadin albarkacin bakin sa, Anty Binta da Jiddah suka kama hannun Leena suka kaita cikin bedroom ɗin da suke tunanin nata ne, bayan sun shiga Jiddah tayi ta aikin rarrashin Leena Anty Binta ta fara masifa tace "Shegiya sai kace wanda aka kawo ki gidan yankan kai" Jiddah tace "Easy Madam, ya zaki wani sa matar yayana a gaba ne?" ta rungume Leena dake zaune tana kallon Binta tace "ba zaki gane bane, tun asali ita da shi ba shiri suke ba kuma tsoron sa kamar take yi amma kuma haka nature ɗinsa yake dan yana mugun son ta" Zahra ta shigo dakin tana ma Leena magana a kunne, Anty Mairamah tana son shiga ciki amma bata son ta ba Mummy da ranar chance ɗin yin wani aika aika dan ido sosai ta sa musu Mummy wai zata buɗe dakin Sadeeq Anty Mairamah tace "A'a nan dakin mijin ta ne" Mummy tace "toh hanamu gani zakiyi?" ta murɗa handle din taji a kulle sannan ta dawo cikin parlorn ta zauna Anty Mairamah taji daɗin kulle wa da aka yi, Mummy bata taɓa jin tsanar da tayi wa Leena da Ammin ta ba irin na yau kawai controlling kanta take. Bayan Jiddah ta cire Wayan a kunnan ta tana kallon Binta tace "Toh kinji ango ko, wai mu fito a mayar da mu" anty Binta na dariya tace "mu tafi tun kafin ya shigo ya tsaya mana aka yana koran mu" Zahra tayi hugging Leena tayi mata magana a hankali duk suka mike Leena ta yaye mayafin kanta tana kallon jIdda tace "har dake ne anty Jiddah? Ai tare zamu kwana ba?" tace "Eh bari na raka su sai na dawo" bayan duk sun fita Mummy sai cika take tana bosewa, Niswa har da hawayen ta, Jiddah taje inda Sadeeq da Sultan sai few friends dinsa suke tsaye tana gaishe su sannan tace "Ya Sadeeq minti biyu mana" Sultan yace "Wallahi ki sashi a hanya Jiddah" ko kallon su be yi ba da kamar ba zai je ba sai kuma ya bi ta bayan sun ɗanyi nisa da su yana kallon ta alamar ita ya ke jiran ta fadi abinda zata ce tace"Ya Sadeeq kaga dai Leena yarinya ce, wannan halin ko'in kula in dan Allah ka canza, ka ga yanzu duk tunanin ta Wallahi baka son ta ne saboda yadda kake yi mata, please dont be harsh on her" yace "Kin gama min faɗan?" tayi ƴar dariya tace "wai ina gwada maka halinmu mu mata ne, kasan muna son caring" daga haka ya juya abinsa, jIddah ganin su Sultan sunyi hanyar gate ta bi bayan su da sauri dan kar a manta da ita. Sadeeq na shiga parlorn ya zauna nan kan sofa can kuma ya soso kanshi sai kuma ya mike, dakin da aka sa Leena nan ya wuce sai da ya tsaya for some minutes kafin ya iya ɗaurewa ya buɗe dakin ya shiga har sannan Leena na kuka jin an buɗe kofa ta daga kanta da sauri anan bakin kofa ta gansa ta mike tsaye da sauri tana kallon bayan sa hoping zata ga Jiddah at the same time tana share hawayen ta, tace "ina Anty jiddahn?" yace "Jiddah ai na aura da zaki ganta anan" nan da nan Leena ta fara wani sabon kukan yace "kin yi sallah ne?" Kai kawai ta girgiza masa daga haka ya juya ya fita, dakin da ke kusa da nata yasa key ya buɗe ya shiga sai bayan wajan 1 hour ya fito a dakin sa Ledan da ke kan center table ya ɗauka ya wuce ɗakin na ta ya buɗe da alama har tayi wanka ta canza kaya dan dogon hijab ne jikin ta ta takure a can edge din gado jin ya buɗe kofar, da sauri ta kulle idon ta ya karasa har cikin daki for the first time in her life taji yace "Leena!" yi tayi kamar bacci ta ke ya kuma cewa "Leena, wake up and grab something to eat, I know you didn't have dinner" Leena sabar mamakin sa bata san sanda ta mike ta zauna tana kallon sa ba sai kuma ta tuna ashe tayi pretending tana bacci ne da sauri ta sauke idon ta kasa ganin yadda yake kallon ta tace "I'm really not hungry" ya ajiye Ledan hannun sa akan stool ya juya yana kallon ta yace "Don't make me repeat myself, just come down and take the food" daga haka ya juya ya fita, itama mamakin yadda yayi magana take dama yana magana haka daga karshe ta mike ta sauka dama yunwa take ji, duba ledodin tayi na chips kawai ta ɗauka taci ta bar kazan a wajan. Washe gari da asuba bayan yayi alwala kafin ya tafi masallaci ya buɗe dakin ta da niyyar tashin ta sai yaga already tana toilet ma. tun da Leena ta idar da Sallah ta fara bacci, zuwa Sannan ta fara jin jikin ta Alhamdulillah. Kamar karfe 9 Sultan ya kira Sadeeq, Sadeeq da gama shirin sa kenan yana gaban dressing mirror ya daga kiran Sultan, ya ɗaga, Sultan yace "ina waje" daga haka ya katse kiran, bayan ya buɗe gate ya karasa inda Sultan yayi parking, mika masa hannun yayi bayan sun gaisa Sadeeq yace "ba zaka shigo bane?" Sultan yace "Wa ne ni, A'a abinci Mami ta aiko ni na kawo" daga haka ya sauka ya buɗe back seat ya fito da basket yana mika wa Sadeeq yace "toh Ango a gaishe min da Amarya" Sadeeq ko tanka sa be yi ba, ya wuce ciki Sultan na dariya ya shige motan sa. Bayan ya shiga ya ajiye basket ɗin a dinning room, dakin Leena ya wuce ya buɗe Leena da ke gaban dressing mirror tana shafa lotion iya towel ne ke jikin ta ganin ya buɗe kofar a ruɗe ta mike ta wuce bayan wardrobe da gudu, Sadeeq be san sanda murmushi ya kubuce masa ba, rabon da yayi wannan murmushi ba zai ce ba, ita kuma ta bata fuska tana kukunin taya zaina buɗe mata kofa ba tare da knocking ba, yace "Well, idan kin sa kayan ki fito muyi breakfast" bata amsa shi ba yana fita da gudu taje ta sawa kofar key tana jin haushin shigo mata da yayi, bayan ta gama ta zauna bakin gado tana tunani sake zuwa da yayi zai buɗe dakin yaji a kulle yayi knocking yasa a hankali ta karasa ta buɗe wani kallo yake mata hakan yasa ta sauke kanta kasa tace "ina kwana" be amsa mata ba sai gaba da yayi itama fitowan tayi daga dakin ta tsaya anan parlorn bayan ya zauna a dinning ya daga kai yana kallon ta yace "na zo na dauko ki ne?" ta fara tafiya a hankali, bayan ta zauna, gaba ɗaya gani tayi she's not comfortable da shi a wajan, shi da kansa yayi serving mu su ya tura mata plate ɗin ta gaban ta, da kyar take iya diba nan ma sai ta fake idon sa kafin zata kai bakin har ya gama bata ci yakai spoon hudu ba, bayan ya gama ya dawo kujeran dake gefen ta ya dauki abinci ya diba ya kai bakin ta ita kallon sa take da mamaki ya bata fuska yace "buɗe bakin ki?" ta fara girgiza masa kai tace "zan ci da kai na" kallon da ya mata ne yasa bata san sanda ta buɗe bakin ba, a haka har ya man feeding din ta.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_Ina matukar kaunar ku mutanen arziki, Nagode da ganin reactions din ku, comment dinku shike kara motivating ɗina, Allah bar kauna._

*I dedicate this to Layla and Rayyan's Fans*


32......
Nawaal da ke gefen sa sai basa labari take yi bata son barin sa shi kadai saboda kar ya samu chance ɗin tunani Abbah ne ya buɗe dakin Ummu na biye da shi a baya, Abbah handed him his ticket, passport, and travel papers, ensuring he had everything needed for the flight to Netherlands, godiya yayi wa Abba Nawaal tayi hugging ɗin sa tace "Ya MD, Have a nice journey, I wish I could take you to the airport, but I have lectures today" murmushi kawai ya mata Ummi na kallon sa cike da tausayin sa, gaba ɗaya gani take kamar ba Muhammad ɗin ta ba ne wannan. Mummy da ke zagaye parlorn ta, yau ko office ta gagara tafiya jiya haka ta kasa bacci gidan Leena gave her a sleepless night, tana zaune tun ɗazu tana jiran kiran aminiyarta da tayi ta kira wayan a kashe yasa ta tura mata message. Leena da ke waya da Ammi tace "Toh Ammi ki ce su Anty Binta su zo mana" Ammi tace "Ai su Binta sun yi tafiya, amma gobe za su zo" tayi shiru sai kuma tace "Toh na zo na ɗauki Ayaan ɗin?" Ammi tace "Naga kamar fa ba hankali gare ki ba, yanzu idan nace ki zo sai ki zo?" Leena ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Toh sai anjima Ammi" daga haka Ammi ta katse kiran. tun da tayi breakfast Ɗazu ta dawo dakin, ita kunyan Sadeeq ma ta fara ji, da ta tuna da shi, sai kuma tayi tagumi tana mamakin shi, toh dama haka ya ke ko dai ya canza ne, tana nan a haka har aka fara kiran Sallah tashi tayi ta wuce toilet, bayan ta idar da Sallah ta mike da sauri ta wuce dinning bata so idan ya dawo gidan yace zai bata da kansa, ta zuba abincin tana ci kawai taji an buɗe kofar parlorn kallon sa take har ya karasa cikin parlorn da sauri ta ɗauke  kanta, ya karasa dinning room din ya ajiye Ledan hannun sa,  idon sa a kanta ji tayi she's not comfortable yace "Okay, so you're eating already? You didn't wait for me to come back  so I can feed you?" ta ɗan kalle sa sai kuma tace "No, I'm just feeling hungry" yace "Then Why did you eat the rest of the breakfast? You should have waited for me. I would have brought us food" sai bata kuma ce masa komai ba, Ledan ya buɗe ya Ciro takeaway da ke ciki ya juye su a plate ya kai mata ɗayan gaban ta, ta ɗan kalle sa taga ita yake kallo da sauri ta ɗauke idon ta ta ɗauki wani plate ta rufe sai kuma ta mike wanting to leave the dinning area Sadeeq ya daga kansa yana kallon ta yace "Where are you going ?" tace "I'm satisfied" yace "Come back and finish your food" she frown her face tace "I'm telling you, I'm full" yace "Wait for me, let me finish eating. I've waited for you and even fed you, in the morning, now it's your turn to feed me so we can leave together" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta yace "I'm waiting for you" kuka zata fara masa yace "Okay, just wait for me, let me finish" ta koma ta zauna tana satan kallon yadda yake cin abincin is like da style ma yake ci, kusan duk sanda zata sata kallon sa sai taga shima ita yake kallo daga karshe ta daure taki kallon sa duk da jin idanun sa akan ta. Bayan ya gama ya mike itama tashi ta yi, tayi hanyar ɗakin ta yace "Wait, Are you not tired of sitting in the room? Why don't we take a walk around the compound? You're already wearing your veil, so let's go and see how it is" kallon sa kawai take ya tako har inda take ya kama hannun ta, ba ita ba hatta shi sai da yaji wani shock, kamar ta zare hannun ta amma be bata alama ba gaba daya jinta take wani iri a haka suka zaga cikin compound ɗin da kuma ɗakunan gidan, Lina didn't try to hide her joy, and she found herself savoring their stroll around the compound, feeling utterly relaxed in his presence, bayan sun dawo cikin parlorn still yana rike da ita akan sofa ya zauna kallon sa tayi sai kuma tayi murmushi ita ba zata iya zama kusa da shi ba, shima be san sanda yayi murmushin ba yace "zauna mana" da kyar ta iya zama yana kallon ta yace "Leena, Why didn't you love me?" ta sace kallon sa her eyes avoiding his tace "Did I say that?" yace "Yes, you said you wouldn't love me, kin tuna?" She corrected him, "I said I don't like you because you're often arrogant and you rarely talk to me, sometimes, even when I greet you, you didn't respond" yayi shiru yana kallon ta, ta cigaba "It's Only Uncle Sultan....." he cut her off, his voice raised in anger "Stopp!!! I don't want to hear it" tunawa da cewa tsawa ya mata da sauri yayi composing kansa, ya kai hannun sa fuskanta yana shafawa yace "I'm sorry Baby, I didn't mean to shout at you, it's just that I didn't want you to mention any other men's name" ta buɗe baki zata yi magana, He leaned in and kissed her deeply, their lips entwined in a romantic, French kiss, da sauri ya mike tsaye ya juya mata baya, ita kuma da sauri ta kifa kanta da sofan yace "it's almost Asr, kije kije kiyi sallah" daga haka ya fita, Leena taji hawaye na sauka mata, ta tashi gaba ɗaya jikin ta ba kwari ta wuce cikin dakin ta sai data jingina da kofa ta tsaya for almost 5 minutes, ta fara tunanin abubuwan da suka faru tun daga safe har zuwa sanda wannan incident ɗin ya faru, gaban mirror ta wuce tana kallon lips din ta, gani take kamar zata ga lips ɗinsa a jikin nata dan har sannan shock be gama barin ta ba, This was her first kiss in life, it was first time someone had kissed her so deeply, mamakin kanta take mai makon taji haushin sa sai kuma taji akasin haka, jin har an fara tada kabbara a masallaci yasa ta mike ta wuce toilet da thoughts kala da iri a ranta. Mummy da ke tsaye akan sa tace "Ba magana nake maka bane Rayyan? So ban isa da kai ba kake nufi?" yayi kasa da muryan sa yace "Mummy kwatakwata baki fahimta na" ya mike tsaye yace "Naji bari zanje yanzu" tace "Toh ko kai fah, kace ina gaishe su" bayan
End Ads