you, I do appreciate" daga haka ta koma inda su Ammi suke ta kalli Zahra dake mata Murmushi ta ɗauke kanta tayi kamar bata ganta ba, Zahra tayi hugging ɗin ta tace "Haba Leena, fushi zakiyi da Ni?" Leena tace "Sai yanzu zaki zo" Zahra na Murmushi tace "kin manta ranan last paper ɗin mu banda lafiya? Toh, ai har yanzu Ban gama warware wa ba beside nine ma ya kamata nayi fushi ko sau ɗaya baki taɓa zuwa in duba Ni ba" Leena tace "Wallahi na ɗauka ai kin warware ne" Ammi dake kallon su tace "toh kenan sai kiyi fushin Zahra, tunda bata san ta kira ki ba" Leena na kallon Ammi kamar zata yi kuka tace "Haba Ammi" Zahra dariya kawai tayi. Bayan sun koma. gida mutane suka dinga shigowa duk da de unguwar su ba wai unguwan da makwabci zai shiga ma makwabci bane amma idan Ammi taji wani abu takan shiga tace bari ta sauke hakkin makwabtaka, hakan yasa duk da ba wai tayi gayya bane anajin cewa Leena ce sai zuwa ake sai ka ɗauka Ammi ba ƴar Niger bace, waje ya kawatu na ban mamaki, Jidda tasa Leena ta sake wanka ta chanza kaya, sai ka rantse bikin ta akeyi, waya kare a kunnen ta tana waya da Muhammad Ammi ta shigo da niyar sanar da ita ta fito ta gaishe da ƴan unguwan su Babaajo da Nyaama na das sai ga Zahra ta shigo da gold a hannu tace ki "ki ɗan hakura da Wayan nan idan kin gama kyau sai ki kira shi ku yi tayi, Ni dai yanzu ba zan saka Miki gold ɗin nan" Ammi na kallon ta tace "Gold kuma? Gokd ɗin waye" Jidda tace "Au, be faɗa muku ba halan? Yayan ta Rayyan ne yace na kai mata tayi amfani da shi" Ammi tayi shiru tana kallon Leena da ta sauke idon ta kasa. abinci Chefs suka shigo da su ana raba wa mutane Kujeran da Leena ke zaune gefen ta Zahra ce, bayan anyi walima suka fara hotuna Jiddah ta kama hannun Leena tana tafiya da ita tace wa Ammi "bari yanzu zata dawo" haka nan Leena taji tsinkewan zuciya ita de tana bin Jiddah taga ba zata iya ba tace "Meya faru ne Anty Jidda?" sai da suka isa bakin gate Jidda ta sake ta tana gyara mata fuskanta ta buɗe gate ɗin su tana kallon Leena da murmushi a fuskan ta tace "toh Leena ki ɗan sake fuskan mana? Ko haka zaki fita?" Leena ta ɗan sake fuska Jiddah ta karasa fita amma hannun ta na rike dana Leena ta jawo ta waje kallon motar dake parke kofar gidan tayi and she saw him kallon sa take yi and froze, looking like a statue, she couldn't believe what she was seeing, was it really him? Yana murmushi ya karasa har inda take yasan tayi mamakin ganin sa ne yace "Yes, it's your baby, babe. I wanted to surprise you, so I decided to attend your graduation" Leena taji hawaye ya cika idon ta It wasn't until she saw him that she had realized just how much she missed him yana lekan fuskan ta yace "Baby! Kuka kuma? toh ko in koma ne?" Bata san sanda ta harare sa ba murmushi yayi yace "Congratulations on your secondary school and Qur'anic graduations, baby. You're incredibly talented more than anyone can imagine. I hope our babies will be just like you.'' ta ɗan kalli inda Jiddah take taga hankalin ta na kan waya sai sannan ta kalle shi tace "Thank you, I do appreciate, I can't hide" yace "shiitttt, don't stress yourself for me please" gani tayi yayi wa Jiddah maganan da ido sannan Jidda ta karaso inda suke tana kallon Leena tana murmushi ta zaga ta bayan ta to her surprise taga Jiddah ta rufe mata ido kuma sannan tana janta ji tayi son saya kuma ta gagara magana. Motar da ke gaban su aka yaye wa rigar motar da aka lulluɓe wani sabowar dalleliyar Bugatti Veyron ne ya bayyana gashi anyi decor ɗin jikin motar da Flowers and balloon sai sheki yake yi Muhammad ya cewa Jidda "take off your hand, Ma" Jidda ta cire tana murmushi, She stared at the car, then at her Muhammad, her expression a mix of surprise and confusion. Turning to Jidda, she seemed to ask silently, 'What's going on?" Jiddah ta mata alama da hannu i don't know, too. ta kuma juyawa side ɗin Muhammad keyn motar yake mika mata girgiza kai ta fara masa bata son tayi believing abinda ranta ke saka mata ya maso kusa da kunnan ta yace "Be Miki bane baby? toh ko a chanza Miki ne?" tace "Toh me zan yi da shi? Ka bari, wallahi Nagode, amma Ni yanzu me zan yi da mota?" jin shirun sa yasa ta ɗaga kai tana kallon sa gani tayi kamar ranshi ya ɓaci da hakan da tayi bata san sanya ta fashe da kuka ta karasa jikin motar tana kallo ba, Jidda a ranta take mamakin iko na Ubangiji, kamar ba ɗazu bane Mummy ta wulakan ta su akan mota.
Gaba ɗaya gidan da wanda suka zo suka ji labarin kyautar da Muhammad ya mata kowa yana jinjina kokarin sa lokacin har an shigar da motar cikin gida, Mummy ji tayi kamar ta ɗaura hannu aka ta dinga zunduma ihu haka take ji, hatta su Nisreen sai da ta basu tsoro gashi ko kallon ta sukayi sai ta fara sauke musu masifan dake cinta. Bayan Magrib, Rayyan suka shigo gidan tare ya masa sallama ya koma sashin su, gaba ɗaya ji yayi zuciyarsa ya masa nauyi Allah yana sani saboda Daddy yace su tafi sallah tare ne har ya iya haɗa hanya da Muhammad. A car park inda aka masa shinfiɗi ya zauna, yana jiran Leena ta fito dama suna zaune aka kira sallah Daddy yace ya bi Rayyan, bata ɗauki lokaci ba sai ga Leena ta fito tun daga nesa yake kallon ta, kanta a kasa ta karasa inda yake tace "bari na ɗan karbo sako a waje" yana kallon ta yace "Go ahead baby" ta tashi ta fita waje Sultan ta gani tsaye kallon cikin motar tayi taga Sadeeq, tace "Uncle Sultan shine baka zo ba ko?" yace "Haba little girl, ba gashi yanzu na zo ba?" ta koma side ɗin Sadeeq da ko sau ɗaya be kalle su ba tace "Uncle ina wuni" sai sannan ya kalle ta, ya gagara bata amsa sai gƴaɗa masa kai da tayi zata tafi ta jiyo Muryan sa "Har ya tafi kenan?" ta sauke kanta tace "Aa" ta koma gefen Sadeeq ciro abu yayi a bayar Motan ya mika mata taki karɓa tace "Menene kuma?" Yace"karɓa mana" tace "bayan duk abinda Mami da Amty Jiddah sukayi kuma sai ka sake bani, Allah Nagode" zai kama hannun ta ya danna mata tayi sauri ta karɓa ita gani take kamar zata takura mutane ne idan ta karɓa godiya ta musu ta wuce cikin gida.
Muhammad yace "kila idan na koma ba zaki sake gani na ba sai gobe bikin mu" Leena de taki ce masa komai ita mamakin yadda Muhammad yake son ta kawai take yi satan kallon sa tayi taga ashe ita yake kallo ta rufe fuskanta da hannayen ta tace "toh ka daina kallo na mana" yace "Ai wani abun ma baby sai an kawo min ke gida na, daga safe har dare kallon ki zan na yi"
Wajan pass 9pm Leena na kallon Ammi tace "Toh Ammi ke sai kina hawan motar mana, Ni me zanyi da shi, ji yadda kullum Mummy sai ta mana gori akan mota, ɗazu ta gama mana wulakanci akan mota sai kuma yanzu taga ikon Allah ai" Ammi tayi dariya tace "a wani garin kika taɓa ganin anyi haka? Ai mota taki ne Leena, so kike a kaiki Abuja babu motar ya ce an sayar?"
Bayan wasu kwana ki, bikin Leena sauran sati ɗaya kenan, amma har sannan Leena na zuwa makarantar koyan abinci, wanda kusan kullum sai ta haɗu da Malik saboda a unguwar yake da zama shi da iyayen sa kuma sukan gaisa amma kuma baya yarda ya mata ko wani yare sai larabci tunda ya fahimci tana ji, ta fito daga sashin su tana sanye da Hijab har kasa da nikab a fuskar ta zata fita taga Mummy da kawarta zasu fita Mummy tace "Eh wallahi, ai yarinyar yawo ta fara baki ganin ta ne a social media? Duk ta makalewa manyan gari shiyasa fah aka bata motar, ke kin taɓa gani an bawa budurwa mota kyauta, kema kinsa ba haka kawai za su bata ba" Fatima ta rike haɓa tace "Gashi ba karamin Mota bane wallahi! Chap lalle idon ta ya buɗe, Allah yasa ta iya zaman aure" Leena ko kallon su bata yi ba ta fita abinda and boiling inside her, taji ta sane Mummy with passion, ada takan bi umurnin Amminta ta gaishe ta amma yanzu ta daina tunda aka bata mota ta kara sanarta kuma duk wanda yazo gidan sai sun yi wannan maganar inda sabo ta saba ji amma ai kalmar da zafi sosai, anan bakin tutu ta hau taxi..
Hint the star at the corner please, ko baku son kuna motivating ɗina
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
25...........
Ammi na zaune tare da cousins ɗinta guda biyu, kana ganin yanayin su kasan ransu a mugun ɓace yake Ammi tayi kasa da murya tace "Ni dai kuyi hakuri har ku koma Niger dan Allah kar wanda ya tanka ta, neman magana kawai take yi, shiyasa take Abunda zaisa a tanka ta" Binta ta zauna tana girgiza kafa tace "Wallahi Dada sirbajo sai dai matan nan bata sake shiga harkar mu ba wallahi sai na gwada mata ni dangin fulani ne bata taɓa mu a kwana lafiya" Ammi tayi shiru tana kallon ta tama rasa me zata ce musu su fahimce ta Mairamah tace "Ah toh, wallahi ba zamu kyale ta ba, cin uban Shegiya zamu yi, hassada ce fal a cikin ta, kuma inda akayi decorn ko kusa da sashin ta ba'a kai ba amma ta fito ko kunyan ido bata ji ba zato ta wargaza wajan" Ammi sai binsu da ido take yi dan taga ran su ya ɓaci ba sauraron ta zasu yi ba, Binta na kallon Mairamah tace "Ke tashi mu fita karta ga kamar tsoron ta muke ji shiyasa muka shigo ciki" Mairamah ta mike tace "ai kuwa tayi kaɗan dan uban ta" Ammi na musu magana ko kulata ba suyi ba suka fice daga parlorn abun su. Yana zaune akan sofa hankalin sa gaba ɗaya na kan wayan da ke hannun sa a gefen sa kuma wata Dattijiwa ce da ba zata haura 53 years ba sai wasu ƴan mata guda biyu wanda ɗayan takai 28 dayan kuma tana 25, Duk maganar da Ummi take yi be ɗago ba Nimrah tace "Wallahi gaskiyar Ummi ne, ya za'ayi biki ace lami? atleast ko dinner ace ba za'ayi ba?" wani kallo ya mata ta ja bakin ta tayi shiru, Ummi tace "yanzu event ɗin karɓar lefen ma kar ayi kenan?" ya kalli Ummi sannan yace "Toh me amfanin hakan Ummi? Kawai akai akwati shikenan sai anyi wani shirmen?" Nawaal ta taɓe baki ta mayar da kallon ta wajen kanwar ta Nimrah tace "Ke Nimrah dama Allah Allah nake na dawo kasar nan ki bani labari wacece wanda Ya MD zai aura? Yanzu ya gama zagaye zagayen kenan?" Nimrah ta gyara zama tace "Ya Nawaal kenan! Kema kinsa Ya MD da taste, Leena sunan ta, She's not just fine, she's flawless wollah, yarinyar ta haɗu ta ko ina ne Famous ce ita fah, bari ki ganta" ta karasa maganar tana duba wayan ta mikawa Nawaal tayi ta karba tana kallo Nimrah ta kuma tace "Shine wai Ya MD ba zai kara mata gold a ciki ba" sai sannan ya kalle ta yace "Toh ki bani kuɗin mana" Nimrah tayi dariya Nawaal tace "ikon Allah, Ni kuma ban taɓa ganin pic ɗinta ko da a IG ne" Ummi da ke jin su tace "Shi ko bikin lami yake so ayi, ko me za'ayi yace A'a daga daura aure sai daura aure ko buɗan kai ma yace A'a ana dauko masa ita gidan sa za'a kai ta" Nawaal ta sake baki tana kallon sa tace "Toh ai da na sani da banzo ba, meye amfanin zuwan nawa toh tunda ba abinda za'ayi?" Sai sannan Muhammad ya kalle su, system ɗin sa dake chagy ya ɗauka ya bar parlorn Ummi tace "Ikon Allah!" Nawaal ta bisa da kallo tace "Shi kuma yaushe ya koma haka?". Dawowan Leena kenan tana sanye da Nikab a fuskar ta saboda gyaran jiki da ake mata ta gaida gatekeeper ya buɗe mata gate ɗin ta shiga kallon compound ɗin ta tsaya yi da kallo daga haka ta wuce ciki da sallama ta shiga parlorn Ammi dake kallon ta tace "ki samu ki ci abinci, saboda ku gama dilken kafin su karaso" Leena tayi jim sai kuma ta gyada ma Ammi kai gaishe da kannan Ammi tayi sannani ta wuce ɗakin ta dan ajiye jakkan ta, gaba ɗaya ta rasa me yasa ta nemi sukuni ta rasa meke damun ta ji take kamar bata da lafiya ta ajiye jakkan ta ta jona wayan ta a chargy ta yaye Nikab ɗin fuskan ta sai ga Binta ta biyo ta da abinci tana kallon ta "gashi" Leena ta karba tace "thank you Aunt Binta" nan bakin gadon ta ta zauna Binta na kallon ta tace "Leena lafiya dai ko?" Ga mamakin ta kawai taga hawaye na sauka idon ta tace "SubhanAllah me aka Miki?" ta karasa maganar tana zama gefen Leena, Leena tace "I'm just Scared!" tana kaiwa nan ta fashe da kuka Anty Binta ta jawo ta jikin ta ta rasa me zata ce mata tace "Scared of what?" Leena tace "i don't know, kawai ina jin zuciya ta na tsinkewa time to time" Binta na patting bayan ta tace "Hakuri zakiyi Leena, kuma kiyi ta addu'a daman hakan ya kan faru ba zaki samu peace of mind ba har sai an kaiki" Leena tayi shiru tana jinta dan gaba ɗaya taga ba ta ma fahimci inda ta dosa ba ne, bayan ta gama cin abinci me dilke ta shigo, yi mata kawai ake amma ita gaba ɗaya she's just spaced out bata ma san meke faruwa ba wayan ta ne ya fara ringing matar dake mata dilke ta kalle ta ganin da gaske fah she's Spaced out, tayi murmushi cike da tausaya mata tace "Leena toh ki ɗauka mana" sai sannan Leena táyi realizing ashe kiran ta ake yi ganin Muhammad ke kira yasa ta daga kiran ta kai kunne da sallama ɗauke a bakin ta, bayan ta gashe shi sai kuma tace "Toh, in shaa Allah" a haka suka yi sallama ta ajiye wayan a gefen ta Matar tace "Leena da zaki gane ki daina wannan Daydream ɗin, zaki jima kanki ciwo a banza, yanzu ƴan matan wannan zamanin basu ɗaga ma kansu hankali balle ma auren soyayya zakiyi kuma yana da kudi toh damuwar me zaki shiga har haka?" Leena ta kalli mata sai kuma taji hawaye na taruwa a idon ta wato kowa baya jin abinda take ji? Ita kadai ke ji kenan, ta runtse idon ta sosai. Mummy dake tsaye kan Rayyan tana kallon sa cike da tausayin yadda ya koma a ƴan cikin kwanakin nan tayi kasa da murya tace "Son, Dan Allah ka tashi kaci wani abun mana haka zaka ta zama ba abinci a cikin ka?" ya gyaɗa mata kai kawai daukan bowl ɗin pepper soup tayi ta sa spoon a ciki ta ɗeba ta kai masa makin sa girgiza mata kai yayi ya karba yana kallon ta yace "Mummy zanci amma dan Allah ki tafi ina son na samu hutu ne" tana kallon sa tace "amma ka tabbata zaka ci?" ya gyada mata kai daga haka ta mike ta fita ɗakin su Nisreen ta wuce ta samu Niswa na kwance tana danna waya Nisreen Kuma na bacci, Niswa ganin ta shigo yasa ta ajiye wayan a gefe Mummy ta karasa har bakin gadon su ta zauna Niswa tace "Sannu Mummy" Mummy tace "Nikam Niswa har yanzu naji baki kara ce min komai game da mutumin can ba?" Niswa ta yamutsa fuska ta mike ta zauna tace "Dan Allah Mummy ni ki kyale ni da zancen wannan mutumin" Mummy ta mata wani kallo tace "ban gane ba?" Niswa tace "Toh wai har nawa nake da za'a fara takura ni da maganan aure ne? Ko fah makarantar ban gama ba" Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Har nawa kike zaki ce? Toh dan Uwar ki Leena ba kanwar bayan ki ba ce? Kuma dan asara ace dan minister ne zai aure ta" tayi shiru sai kuma tayi murmushi tace "ayi mugani" Niswa ta kalle ta tace "Mummy, Leena daban, Ni daban, beside yanzu ina fara sa wannan damuwan a rai na sai ya hanani exams sannan na sama kaina damuwa" Mummy ta sake baki tana kallon ta da mamaki tace "Eh lalle kam kwarai, toh ni yanzu maganan wannan mutumin nake Miki" Niswa ta yamutsa fuska tace "Ni fah dan Allah Mummy ki raba ni da zancen wannan mutumin, dan ni rashin mutunci ma nayi masa, saboda Leena zata yi aure shikenan sai akawo min wani gaja, gaskiya Ni ba taste ɗina bane, ita kawar taki idan har Mutumin arziki ne zata yarda ta kawo mini shine? Ai saidai ta haɗa shi da ƴar ta Layla naga" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa ta mike tace "wallahi zaki sha mamaki na Niswa, ina ni kike wa tsiwa har haka? Toh ke idan banda rawan ido naga mutumin nan a NNPC yake aiki kuma gidan su suna da kudi na gani na fada" Niswa tace "Ni yanzu ba wannan ba, wallahi Mummy idan nace miki baki fahimtar abu sai ki ce min A'a, amma har yanzu kin kasa gane meke damun Ya Rayyan" Mummy na kallon ta tace "toh meke