x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 59 - AGOLA free pages

  • 174001 words
  • 177000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
na kallon Abdul-aziz yace "i think gobe zan tafi US" Abdul-aziz yace "Ban gane ba? Shine sai yanzu zaka sanar da Ni? Kila ko Mai martaba bai sani ba?" Ya numfasa sai kuma ya kama hanyar toilet yace "Eh, I have to go, almost a month banje naga Suhaif da Mamar sa" Abdul-aziz ya taɓe baki ya zauna yana danna wayarsa yana mamakin hali irin na 'yan biyun nasa. Duk suna zaune suna son ganin yadda plan ɗin su zai kasance Waziri yace "Gaskiya har yanzu muna wasa, dan ma taimakon da Allah yayi mana Abdallahn baya son Mulkin amma ai da tuni Mai martaba ya sauka ya  basa" Fulani ta ɗaura tace "Ni fah gani nake har yanzu muna ganganci da maganar nan bamu wani ɗaukar sa da muhimmanci ba amma idan ba haka ba ai da tuni an wuce wajan" Umma ta daura "Toh waya ce Hauwa'u n haka ta barsa? Kun taɓa ganin yaga laifin ta ko sau ɗaya? Kamar yadda kasan ita an halittota bata kuskure" ta karasa maganar tana jan tsaki, waziri yace "Ainihin mulkin nan a ɗakin mu yake, ba shi ya kamata ya gada ba, amma Mahaifin mu ya zaɓe sa tun kan ya mutu wai saboda shine yafi hankali" Fulani ta mike tace "ya kamata gobe ba jibi ba mu garzaya kauyen nan dole Mutumin nan yayi mana aiki cikin hanzari dan nagaji da zama da kuma kallon bakin ciki" Umma tace " Allah ya kaimu goben, sai mu ga ya ake ciki da farko tukun nan". Fulani tana tafiya cike da kasaita zata sashin ta, wata Dattijiwa daga cikin dattijen gidan da suke aiki ta fito rike da ruwa ta watsa, tsausayi yasa ruwan ya zuɓe a jikin Fulani, Matar ta sake baki tana kallon Fulani dan itama bata ɗauka tana tahowa ba, da sauri ta zuɓe kasa ta fara bata hakuri "Tuba nake Ran ki shi dade wallahi ban kula bane" Fulani ta sake baki tana kallon ta bata yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari, akan idon Hajiya Hauwa'u, ta sake baki tana kallon Fulani da mamaki dan a ƙalla matar ta haife ta koma tayi jika da ita, ta ɗaga hannu zata sake marin ta Hajiya Hauwa'u tace "Haba Fulani, ai zaki tausaya mata ko albarkacin tsufan ta, Dattijiwan tana duke kasa hawaye na sauka kan kuncin ta, a fusace Fulani tace"Ke babu ruwan ki, ki kama mutuncin ki kafin na gwada miki halina" Hajiya Hauwa'u ta bar wajan tana Allah wadare da halin Fulani.

Toh Ni dai naga kulawa, Alhamdulillah thank you guys, Amma ni nace muku nayi left ɗin channel ɗina😂🤦🏽‍♀️💔 naga sai kira ake ta min da lots DM wai nayi left, but Shaa Nagode da kula wa

A tayani Sharing saboda masu naima

#Jiddatulkhayr
08110615257*AGOLA (Behind the palace walls)*


*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Chapter 69

Hajiya Zainabu na zaune a ɗan karamin ɗakin, ga Fulani a gefen ta suna jiran jin mai Mutumin gaban su zai ce musu, Fulani tayi nisa cikin tunanin, tunanin da yanzu ita ce ainahin Fulani, amma aka hana a hannun Mai gidan ta zuwa kan Mai martaba Modibbo, wani tsaki taja a fili wanda hakan yasa Sarauniya Zainabu kallon ta, tace "Ya dai Fulani?" Ta kalli Mutumin dake gaban su sai kuma tace "Ni na kosa duk yadda za'a yi kawai ayi da Mutanen nan" ɗagowan Mutumin yasa suka Kalle sa suna jiran jin me zai ce, da muryan sa wanda babu daɗin saurara ya fara magana "Gaskiya Mai martaba Modibbo yana da babban lakani a jikin sa wanda idan har aka dage sai an masa wani abu toh gaskiya aiki na zai lalace sannan kuma ku kanku zaku iya rasa ran ku idan kuka masa, saboda tauraron sa na da karfi" suka kalli juna a take, Sarauniya Zainabu tace "Kinga tashi mu koma idan ya so sai muyi wani tunanin da ban amma banga ta rasa rai na ba, dan ban shirya mutuwa yanzu ba" Fulani ta mike duk jikin ta babu karfi. Gimbiya Indo na zaune tare da Mahaifin ta sai basa labari take, wanda kawai sai dai yayi murmushi ko kuma ya bita da eh ko A'a, waziri ne ya shigo, sai kirari yake ma Mai martaba, kallon sa ta dinga yi da mamaki kamar bashi ne wanda yake son ganin bayan Abban na ta ba, bayan fitan sa ta numfasa ta zuba wa Abba ido kamar mai raɗa tace "Abbah nasan baka yarda da kowa amma dan Allah ka sake kara rashin yardan ka da mutane ko da kuwa waye ne" Mai martaba yayi murmushi dan yasan daman yasan waziri ba son sa yake ba, sai kuma ya Kalle ta ya sakar mata murmushi, ita ma mayar masa tayi tana tunanin ko zata faɗa masa kudurin wasu daga cikin masarautar akan sa amma idan ta tuna harda Mahaifiyar ta sai jikin ta yayi sanyi. Sarauniya Hauwa'u ta shige part ɗin 'ya'yan na ta, Abdallah na haɗa kayan sa a box ga kuma Abdul-aziz yana zaune yana danna wayan sa, duk ɗaga kai suka yi suna kallon ta har ta karasa ciki ta zauna, duk suka gaishe ta tana kallon Abdallah tace "Kai kuma ina zuwa haka?" Yayi murmushi yace "Ummi US zan tafi" ta masa wani kallo tace "Da ban shigo ba ba zaka faɗa min ba kenan?" Ya sosa kansa yace "No Ummi, dama ina da niyyar yanzu na shigo na sanar da ke wallahi" tace "Hmmm, I can see" yayi murmushi yace "I think zan tafi na dawo da Amira, ta gama exams ɗin ta jiya so Kuma bana son ta haihu a can" tace "Ai dama shiru na maka taya Zaka ce ta haihu a US bayan ba wanin ta a can ɗin ba" ta kalli Abdul-aziz tace "Baba na Yarima" ya kalli Ummin sa sai kuma yayi murmushi, tace "Ya ake ciki ne? Ko dai baka ji me Mai martaba yace maka ba ne" ya ajiye wayan hannun sa yace "Dan Allah Ummi ku daina min maganar aure, duk sanda na shirya zan faɗa muku, ko kuma nace duk sanda lokaci na yayi" ta harare sa tace "Kai da mai Martaba ai, kuma kaji me yace maka, ace ɗan uwan ka da yake miskili ma ya fara tara iyalen amma kana nan kayi shiru ban jin ma kana da budurwa" yayi dariya, Abdallah ya mike yana kallon Ummi
yace "Bari naje na ma Mai martaba maganar tafiya na yanzu" Ummin ma mike wa tayi tana kallon sa tace "Gaskiya ya kama ta kam" daga haka ta fita, jakadiyar ta dake waje tana jiran ta dan basu shiga sashin su Yarima ko da wasa, ta fara bin bayan Ummi. Waziri wani irin kallo yake musu kamar zai dake su rai ɓace yace "Idan aka ce aiki ba zai yi akan shi Mai martaba ba toh akan yaran nasa kuma fah? Wannan wani irin shirme ne da rashin tunani Fisabilillah, daga anyi magana sai ku gwada a bar komai a hannun ku zaku yi handle while ba tunani gare ku ba" Fulani ta ja saki tana kallon Sarauniya Zainabu tace "Nifah tun kafin na gama processing maganar sa ta mike ta jani waje amma ku ma kun san ba wai rashin tunani ne da Ni ba" Yarima Usman ya ɗaura "A gani na ko, dama tun farko ba kan Mai martaba ya kamata ayi aiki ba, dama kan Yarima Mai shiru da kuma Yarima Jallube, su ya kamata ayi wa aiki, musamman Yarima Jallube yadda yake zakalkalewa a cikin Masarautar nan, yana gwada shine wanda zai gaje kujerar, dan gwamma shi Abdallah baya so, beside shi ba'a isa a masa dole ba" Hajiya Zainabu ta ɗaga kan ta tana kallon ɗan nata da irin nasa basirar, Waziri yace "ka kawo magana mai muhimmanci kuwa, sai dai shi Abdul-aziz na kallon mutane da daraja kamar ba kamar ɗan uwan nasa da yake kallon mu a matsayin ba kowa ba" Sarauniya Zainabu ta ɗaura "Dole zamu koma wa Mutumin nan, sai kuma mu faɗa masa yadda muke bukata". Yarima Abdallah ne da Yarima Abdul-aziz suka tun karo ɗakin Mahaifiyar su, Jakadan da suke ciki wata daga cikin su tace "Gasu Yarima Mai shiru suna karaso wa" hakan yasa duk suka mike suka fita, yayi daidai da lokacin da suka karaso, duk suka duke suna gaishe su, Yarima Abdul-aziz ne kaɗai ya ke amsa musu wanda tuni Abdallah ya shige cikin dakin Mahaifiyar na su, Ummi na kallon identical twins ɗin ta cike da sha'awa har suka karasa ciki, ta shafa kan su tace "Allah muku Albarka" duk suka amsa da 'Amin' Abdul-aziz yace "Yanzu zan kaisa Airport ne Ummi" ta numfasa tace "Allah ya kai ka Lafiya Abdallah, ya dawo da ku gida Lafiya" Abdallah ya rungume ta yace "Amin Ummi" tana kallon su tace "Ku cigaba da addu'a duk da Nima ina muku, kar kuyi wasa da daily Azkar ɗin ku, saboda shine garkuwar musulmi, dan haka nake so na sake tunatar da ku dan addu'a ne yasa har yanzu muke cikin gidan nan duk da yadda muke ganin tsanar mu a idon mutane, Kuma kowa ya san muguntan gidan sarauta, dan haka mu sake dagewa" duk suka amsa mata, ta cigaba da basu shawarwari kamar yadda ta saba daga haka ta musu addu'a, Abdallah ya mike shima Abdul-aziz ya mike suka nufi kofa dan gudun kar Abdallah yayi missing flight ɗin sa. Gimbiya Indo na zaune tana kallon jakadiyar ta Mai bata shawara wanda a kalla zata haife ta ko tayi jika da ita, tace "Kina ji, Ni har ga Allah bana bin bayan karya, maganar gaskiya lokacin da aka haifi su Yarima Abdallah ko auren Umman mu fah ba'a yi ba, toh na rasa gane dalilin da yasa basu son Yarima Abdallah ya gaje Masarautar nan, bayan shine ya dace da ya gaje" Jakadiyar ta ta numfasa tace "Allah kara miki tsawon rai Gimbiya, a kullum ina Alfahari da Allah yasa ke kika fahimci gaskiyar hakan, kuma Ni a gani na su waziri na wasa da hankalin Sarauniya Zainabu ne, dan suma ba zasu so a dauki Mulki a bawa Yarima Usman ba, bayan sun san Sarautar daga dakin su ya fito aka ba Mai martaba Modibbo, wallahi kamar suna using ɗin ta ne dan ta haka ne kadai zasu iya cimma Mai martaba da kuma su Yarima Mai shiru" Gimbiya Indo ta gyaɗa kai cike da fahimta tace "Amma ke kinsan dalilin barin Mulkin a hannunsu zuwa hannun Abba na?" Ta gyaɗa kai tace "kwarai kuwa, Kinga tun ina shekara goma nake cikin Masarautar nan, wanda yanzu wajan shekaru na Arba'in ina zaune a cikin ta, nasan ciki da wajan ta, nasan munafunka ta, tun ban san halin mutanan cikin ta ba har nayi karatun haddan ta, da suwa ke rayuwa a cikin ta" ta numfasa sai kuma ta ɗaura tace "Abun da yasa tsohon Mai martaba kafin rasuwar sa yace "baya kaunar bayan mutuwarsa a ba 'yan dakin su waziri Mulkin saboda a lokacin suna da mugun ta, ga su da bin Mata, sannan kuma suna shaye shaye, wanda hakan ya kusa taɓa musu ƙwaƙwalwa, tsohon Mai martaba yayi dogon rubutu wanda dattawan kasa suka sa hannu akai, yace ko bayan ransa Mulki a bawa Modibbo, wanda shi kaɗai ne a wajan mahaifiyar sa, su kuma su maza biyu ne da mata uku amma gaba ɗaya sun lalata rayuwar su saboda kudi ne kawai ke ruɗar su, wanda a lokacin hakan ya kawo babban rikici da kuma gaba wanda har sannan waziri da su fulani ke rike da abin a ransu har sannan, shi kuma dayan ɗan-uwan waziri, akan shaye shayen ya mutu, dan yayi ta ne ba kaɗan ba wanda har ya taɓa wasu daga cikin kayan cikin sa, an kai sa India a masa aiki toh acan ya mutu, wannan ne dalilin da yasa kika ga waziri ya rage sha saboda gudun haka, a lokacin Mahaifiyar su Yarima Mai shiru ta dage tukuru akan mijin ta da addu'a dan a lokacin ko wani Litinin da Alhamis zaki samu tana azumi, tayi riko da addini ba kaɗan ba, kuma takan tsaya akan mijin ta, har Allah yasa aka daura sa akan shugaban cin Masarautar wanda ta taka rawar gani a rayuwar Modibbo, bayan hawan sa da shekara guda Allah ya azurta ta da "yan biyu masu kama, wanda bayan sun girma ina tunanin a lokacin sun kusan shekara 6 a duniya Mai martaba ya kara aure, wato ya auri Mahiafiyar ku, toh tun daga lokacin ne su Fulani suka ja ta jiki dan kawai ganin sun haɗai kai dan ganin bayan Mai martaba da Sarauniya Hauwa'u , wanda tun a lokacin suka ware ta da 'ya'yan ta, hakan yasa Abdallah tasowa cikin shiru da miskilanci yadda yaga ana ma Mahiafiyar sa wanda hakan kuma ya bisa har girman sa sannan kuma ya kara tsanar Masarautar da kuma Sarautar wanda hakan yasa yayi aure da wuri a tunanin sa Mai martaba zai kyale sa yaje yayi rayuwar sa a waje sai kuma yaga ashe ba haka bane, ba kamar ɗan uwan sa da ba haka yake ba dan shi baya bari abu ya dame sa sannan kusan kullum yana fada da Mai martaba, wanda hakan yasa ya taso cikin son Mulki" Gimbiya Indo ta numfasa tace "Allah ya kyauta, amma gaskiya na fahimci wani abu daga maganar ki, tabbas suna using Mahaifiyata ce dan cinma burin su" Jakadiyar ta tace "Kwarai kuwa ran ki shi daɗe" Gimbiya Indo tace "Ki zauna kiyi tunanin nan da gobe dan Allah, saboda naga suna shirin tafiya gun boka akan su Yarima, kiyi tunanin me ya kamata muyi akai" Jakadiyar ta tace "In Shaa Allah zan zauna naga me ya kamata ayi" ta miƙe sai kuma ta dawo gaban ta ta duka tana mika mata bowl ɗin fruit, ta karɓa tana mata godiya. Da yamma Gimbiya Indo ta fito shan iska tare da wata jakadiyar ta, a hanya ta haɗu da Yarima Abdul-aziz da dawowan sa kenan daga Kai Abdallah airport, ta karasa wajan sa da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Hey! Yarima" shima murmushin ya mata yace "Sannu Gimbiya" tayi 'yar dariya jakadiyar ta ta gaishe sa ya amsa sannan ta bar wajan da sauri, Gimbiya Indo tace "Tun shekaran Jiya ban gan ka kai da Yarima ma" yayi murmushi yace "Sure! Ai ba'a ganin ki ne kwata kwata" tayi dariya tace "Ku dai" har zai yi gaba kamar mai nazari tayi saurin tsayar da shi tace "Um Yarima" ya juya yana kallonta tace "Please ko zaka bar gidan nan for the main time?" Ya gyara tsayuwar sa da kyau yana kallon ta, gaba ɗaya studying dinta yake yi, sai kuma yace "Why?" Tayi yake tace "It's Okay, kawai dai" hango Yarima Usman da tayi a gaba yasa tace "Bye!" Daga haka shima ya wuce yana nazarin maganar ta. Duk inda Yarima Usman yasa kafa dole mutane suke zuɓewa suna gaishe sa sabar yadda muguntan sa yake, kuma ko kallo basu ishe sa ba, direct ɗakin Umma ya wuce, kamar zai tashi sama yana huci yace "Umma me shegiyar nan take tare da Jallube?" Umma da ta fahimci me ke nufi tace "Ka ga Yarima ka daina kiran Kanwar ka da shegiya" ya zauna yana kallon ta yace "Yanzu fa shigo wa ta nagan su tsaye tare tana hango ni tayi maza tabar wajan shi kuma yayi sashin su" Umma tace "Ko ma mene ne kasan be wuce gaisuwa ce ya haɗa su ba, so ka dinga kyautata zato ma Kanwar ka" ya miƙe tsaye ba tare da ya sake ce uffan ba ya fita yana taku cike da kasaita. Mai martaba yana zaune a faɗa tare da fadawan sa ga kuma waziri na gefen sa, waziri ya ɗaga kan sa yana kallon Mai martaba jin furucin sa, sai kuma ya kalli dattawan Fadar, can kuma ya miƙe ya fita a fadar ba tare da ya sake tanka Mai martaba ba, Daya daga cikin dattawan Fadar yace "Gaskiya Mai martaba kai ne ka sake har Waziri ke abin da yaga dama, baka bari hukunci ya hau kansa" shirun da Mai martaba yayi yasa Mutumin ma shiru dan yasan kuma Mai martaba ba zai kuma cewa komai ba. Waziri kamar zai dake su yake magana yace "Ku tashi ku tafi, duk yadda za'ayi kawai ayi", Fulani ta ɗaura "Ka kwantar da hankalin ka, duk yadda za'ayi ba zamu bar wajan nan ba sai da kwakwaran nasara, dole komai ya tsaya a haka, Nima kai na nagaji" Gimbiya Indo ce ta shiga da sallama wani kallo da waziri ke mata yasa ta ɗauke kan ta, Fulani tace "Ɓace mana dan Allah Magana muke munafuka" ta kalli Umman ta taga ita take kallo, ta kalli Yarima Usman taga kallon da yake mata, ta taɓe baki ta fita ba tare da ta sake ce uffan ba, tana fita taja jakadiyar ta gefe ta tsaya tana kallon ta, tace "Yanzu na gansu duk suna tare, ina so dan Allah kisa ido ki gano min menene suke kullawa" jakadiyar ta rufe bakin ta da hannayen ta tace "Gimbiya ta ina zan iya wannan aikin? Ai gwara ke, yanzu ace suka kama Ni kinga abun ba zai yi kyau ba" Gimbiya Indo tace "Na fahimce ki, amma kiyi yadda zaki iya, sauran kuma Ni da kaina zan gano" tace "Toh Shikenan Gimbiya" daga haka tayi gaba jakadiyar na binta a baya


Share Fisabilillah


#Jiddatulkhayr
08110615256Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ItrejHWHeZ58WbKcxjeBpU?mode=ac_t

*AGOLA (Behind the palace walls)*



*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes



Chapter 70


Bayan Mutumin ya ɗago ya mika musu wani maganin a kulle cikin laidar gaban sa yace "Gashi, wannan maganin zaku tabbatar kun barbaɗa a kofar ɗakin su yadda idan suka fito zasu taka" Fulani ta karɓa da sauri tana washe baki, ya sake mika musu wani yace "wannan kuma zaku zuba a abin ci ne" ta karɓa tace "Toh" yace "ku tabbata sun ci abincin" ta gyaɗa masa kai, Hajiya Zainabu sai washe baki take, bayan ya gama basu maganin da yadda zasu yi amfani da su, Fulani
End Ads