x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 39 - AGOLA free pages

  • 114001 words
  • 117000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
juya mata, ta fara salati ba tare da ta shirya ba Anty Binta tace "shikenan tambayoyin naki? Ina sauri ne saboda abinci zan girka musu" inaa Jiddah ta faɗa tunanin da itama kanta bata san da shi ba, Anty Binta ta rabe ta ta wuce cikin gidan ba tare da ta sake bi ta kanta ba. Dakyar ta iya karasa har cikin gidan su, bayan ta shiga parlorn duk kallon ta suke suna jiran jin me take tafe da shi dakyar tace "Mami Leena ta haihu" Mami tayi shiru tana kallon ta sai sannan Sadeeq ya daga kan sa yana kallon ta Sultan yace "aina kika ji?" tace "daga gidan su nake yanzu haka suna asibiti ko sallamar su ba'a yi ba, kamar ma aiki aka mata" Sadeeq ya mike ba tare da ya sake kallon wani a parlorn ba ya fara haurawa sama, a hankali Jiddah tana kallon Sultan tace "Shikenan kuma yanzu ba matar sa bace?" Sultan bai bata amsar tambayar ta ba. Bayan yayi parking mashin ɗin sa ya sauka yayi knocking gate din gatekeeper ya buɗe kofar bayan sun gaisa Malik yace "an sallamo su kuwa?" yace "A'a, har yanzu basu dawo gida ba, kuma naji kamar kanwar mahaifiyar nata tace ba yau zasu dawo ba, dan ta haihu" ya gyada kai yace "Okay, Allah raya mana, ita kuma Allah bata lafiya, dama nazo naji ya jikin nata ne" Baba mai gadi yace "Ayyah, toh dai har sannan basu dawo ba" daga haka ya koma, sai sannan ma ya fara tunanin ace suna nan me ma zai ce ya kawo sa. Hajiya tayi ƙwafa tace "wallahi ni nasan maganin sa, daga shi har ita shegiyar matar nasa" sai maganganu take ba tare da ta damu cewa Rayyan na wajan ba, tana girgiza kafa tace "Allah maida mu gida, duk abinda zai faru ban damu ba" Anty Binta ta gyara zaman ta tace "amma toh ko Hajiya nace Daddyn bai san muna nan bane?" Hajiya ta fara masifa Ammi ta kalli Binta dan tasan da gangan ta sake tabo Hajiya, "kamar ya bai sani ba, baki da baki na masa magana amma yayi burus da Ni, saboda gani 'yar banza, wallahi daga shi har matar nasa su jira komawa ta gida" Rayyan ya sauke kansa kasa, Hajiya tace "Duk abin zai faru sai na barbade gidan da hayaki idan yaso duk abinda zai faru bai dame Ni ba" Rayyan ya mike Hajiya na kallon sa tace amma fah ba'a ma yaron hudu ba ba fah"


Idan naga reaction da dayawa zamu cigaba da samu update sau biyu a rana, amma idan naga babu reaction hakan na nuni cewa baku jin dadin labarin ne.

Jiddatul-khayr
08110615256
https://chat.whatsapp.com/K7dFXrl6zm1IG82QJyPjuV?mode=ac_c

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION


Chapter 45


___Rayyan ya da kata daga fitan da yayi niyya yana kallon Hajiya, Hajiya tace "Toh ai sai ka masa hudu ba ko Malam? tunda naga daga Sadik ɗin har uban naka ba mutunci suka gada ba" Rayyan ya tako har inda Hajiya ke zaune ya duka ya karbi Babyn yace "toh ai bansa sunan da za'a sa masa ba" Hajiya ta juya tana kallon Ammi dan jin me zata ce Leena tayi saurin cewa a sa masa "Abubakar" Rayyan ya tsaya kallon ta, Hajiya da Anty Binta suka sake baki suna kallon ta ta sauke kanta kasa, Hajiya tace"uban me shi Sadeeq din ya mike da kike son maida wa ɗan ki sunan sa?" Anty Binta tace "tun da kika zo kinji wani nasa ya zo ne, amma ke ga miji daɗi ko, duk wulakanci da ya miki baki daddara ba? Toh ki sani ba aure yanzu tsakanin ku, dan iddah ma kin fita" duk Ammi na kallon wani wajan amma bata tanka musu ba dan har sannan bata samu lokacin da tayi magana da 'yar nata ba, Leena tace "toh ai naga ba dan shi nace a sa masa sunan ba kawai dai I'm obsessed with the name" har sannan Rayyan idon sa na kan ta, Anty Binta tace "kar ki mayar da mu kanana mana, ya kamata ki cire sa a ranki dan yanzu kam babu wani abun da kika haɗa da shi" a hankali Leena dake juya tean gaban ta tace "Ni nasan har sannan ba yin kansa bane, dan ai tun daga farko ya nuna min so" tunawa da maganar Anty Binta na karshe wai yanzu ta fita a iddah kawai ta fara kuka duk kallon ta suke, su sun dauka saboda maganar sa masa Abubakar ɗin da tace ne ya sata kuka, Hajiya tace "kaga Rayyan sa masa Abubakar ɗin tunda kaga rashin kunya ƙarara take son nuna mana" Leena ta kifa kanta har sannan Rayyan na kallon ta a hankali yace "So kike ki jima kan ki wani ciwon?" Sai sannan Ammi tayi magana tace "Fama da kanta da take yi yanzu ai bai ishe ta ba sai kin kuma jin wani ciwon ko?" tayi shiru Rayyan yayi ma ɗan nata hudu ba duk da bai so ba ya mike ya kaiwa Hajiya Babyn daga haka ya fice, Hajiya ta kwantar da Babyn tayi tagumi tunani iri da kala ke yawa a zuciyan ta can ta daga kai ta kalli Leena da har bacci ya fara ɗaukan ta sai kuma ta sauke ajiyan zuciya. Mami dake kansa tun sanda suka kawo sa asibiti ita yanzu duk abin ya fara sata cikin ruɗani dan babu test da ba'a masa ba kuma ance lafiyar sa kalau, Jiddah ne ta kalli Mami tace "Ina ga fah kamata yayi kawai mu koma gida Mami, dan kinji duk result daya fito sai ace ba wani abun da ke damun sa" Mami ta sauke ajiyan zuciya tana kallon Sadeeq dake bacci. Layla bata tanka musu ba sai ma danna wayan ta da take yi, su kuma sai hira suke yi, Mummy sai maida zancen sakin da aka ma Leena take yi, Hajiya Fatima tace "Ai kadan suka fara gani" Niswa tace "Mummy ai baki ga yadda hankalin su ya tashi ba, daga gani har sannan yarinyar nan bata warke ba, shiyasa ko samun su na wuni a gida ba su yi" Hajiya Fatima da Mummy suka fara dariya sai sannan Layla ta sauke ganin ta daga kan wayan tana kallon Niswa tace "Toh ke yanzu uban wa yasa bakin ki a maganar su, kina yarinya sai shegen manyan ce, idan ke ce aka miki haka zaki ji dadi? ga dai aure gaban ki, ki natsune dai" Mummy ta sake baki tana kallon Layla Hajiya Fatima kuma tayi "Uhum, kai Layla" tana murmushi ta kare dan ita dama kamar tana shakkar 'yar nata ma, Mummy tace "Amma baki san wa ake magana akai ba ko Layla" ta mata magana in very calm way, Layla ta taɓe baki tace "Toh dama ku akwai wacca ta tsole muku ido ne bayan Leena?" Mummy tace "Toh ai itace wanda Rayyan ya kwallafa rai na hana sa nace ga ki nan sai an basa wata kuma" Niswa ta dinga hararan ta, Layla tace "Toh da kuka hana masa ita ya aure Ni, hakan yasa ya so Ni? Ba wannan bama yanzu a rashin tunani da kuka raba ta da auren ta ba hakan bane zai sa Rayyan ɗin yace zai koma mata a karo na biyu, ai wannan rashin tunani ne" daga Mummy har Maman ta shiru suka yi suna nazarin maganar ta, Layla har ranta bata so mutuwar auren Leena ba, Niwsa tace "kina magana da iyayen ki amma kamar kina magana da kannan ki fah?" Layla tace "Zo ki rufe min baki mara kunya" Hajiya Fatima tace "Haba Niswa, sai kace Layla sa'ar ki?" Mummy tana kallon Hajiya Fatima with shock, Hajiya Fatima ta kalli Mummy sai kuma tayi 'yar dariya tace "ina ga Layla na moody ne yau din" Niswa ta mike fuu tayi dakin su, dan bakin ciki Layla ta kama hanyar fita tana buɗe kofa taga Rayyan da saurin sa ya juya tace "Honey" jin muryan ta yasa ya jiyo yana kallon ta ta karasa wajan sa tace "shine rabon ka da gida tun jiya ko?" Kallon bayan ta yayi, yace "don't tell anyone kin ganni, anjima zan zo daukar ki, ki jira ni" ta gyada masa kai tana murmushi, daga haka ta kama hanyar garden, Rayyan har wani jiri yake ji, dakyar ya iya karasa gate yana tunani abin da ya gama ji, dakyar ya samu strength ɗin shiga Mota, how on earth could his mother be the one to cause a divorce? ya jingina da jikin motar yana jin zuciyar sa na kuna. Bayan sun dawo gida Mami dake zaune da wata sistern Baban su Sadeeq itama duk lamarin Sadeeq ya sata cikin ruɗani, Jiddah ce tayi Sallama, Mami ta daga kai tana kallon ta ta karasa cikin parlorn ta gaida Baabar ta sannan tana kallon Mami tace "Mami Ni da wani malami ne muka zo" Mami tace "ke da wani kuma?" ta gyada mata kai tace "zai shigo ne ya duba Ya Sadeeq" Mami tace "amma lafiya gare ki kuwa Jiddah?" Kanwar mahaifin su tace "Ai tayi tunani kuwa Mami" Sultan dake zaune a corridor ya fito yana kallon Jiddah yace "Yana ina, dear?" ta nuna masa waje ya karasa waje ya shigo da mutumin da yaki shiga da kyar dai ya samu ya lallaɓa sa, direct dakin da Sadeeq yake kwance suka wuce, Mami ta bi bayan su dan ita bata son irin haka, Malamin ya dinga kallon Sadeeq dake bacci ya juya yana kallon Sultan yace "Tabbas an masa illa, amma ba komai tunda lokaci bai kure ba, wannan rashin lafiyar ma kwantar da shi akayi" Jiddah tace "ya za ayi kenan?" Yace "Za'a warware komai, kawai dai an sa masa tsanar matar sa ne kamar yadda na fada miki tun kan mu zo, duk da ma yanzu wasu abubuwan sun warware kan su" Jiddah ta kalli Mami ta take bin sa da kallo, ya Ciro wasu haya ki da wasu itacuwa yana kallon Jiddah. Rayyan dake kwance a office ɗin sa har sannan bai daina tunanin da yake fama da shi ba, wayan sa ne ya fara ringing ya daga ganin Layla da kamar ba zai dauka ba sai kuma ya daga ya kai kunne tace "Honey, har Magrib ya gabato kuma baka zo ka ɗauke ni ba" sai sannan ya kalli agogon dake manne a office ɗin sa yace "Okay, on my way" ya katse kiran, sai daya fara biya ya duba Leena ya kuma tsaya musu abinda zasu bukata sannan, ya shiga dakin da Sallama Leena dake zaune ta ɗauke kanta ganin ya shigo bayan ya gashe su sannan Leena a hankali tace "ina wuni" yace "akwai wani abu dake damun ki" kai kawai ta girgiza masa yace "Kina kuka ko?" Hajiya tace "Ai dole ka tambaya, yanzu fah Shikenan bata da wani aiki face kuka wallahi ji nake kamar na daka shegiya" bai ce komai ba yace "barin tafi gida" Hajiya tace "Toh Ammi kina zaune ba zaki tashi ki bisa bane ko zaki tsaya jiran wannan motar hayan ne?" Ammi ta kalle sa tace "gida can zaka?" yace "Eh, Zanje daukan Layla" Ammi ta mike tana kallon Leena, Hajiya tayi saurin cewa yauwa Rayyan kama kanwar ka fada a matsayin ka na likita wai fa 'yar nan kafin ta bama jaririn nan Mama sai anyi da gaske, hakan ma tana yi kamar zata sake mana shi a kasa" Rayyan ya koma ciki dakin daga bakin kofar da yake yace "Leena, why don't you want to breastfeed your baby?" taki kallon sa kuma taki cewa komai yace "Don't you know how incredible good breast milk is for a baby?" ta ɗan bata rai ita fa kunyar sa take ji amma gani take kamar ba gane hakan yayi ba murmushi yayi yace "Please try your best to keep breastfeeding him, so he can grow up healthy and strong" daga haka ya ma su Hajiya sallama ya bawa Ammi waje ta fita sannan ya bi bayan ta. Hajiya Fatima tana kallon 'yar ta tace "ke ba zaki koma gida bane?" tace "Mun yi waya yace yana hanya yanzu zai karaso mu tafi" ta gyada kai tace "ki gaishe min da shi" tace "Toh" ta mayar da kanta kan abinda take a waya Mummy ta raka ta, bayan ta dawo ta samu Layla na kwance akan 3 seater, Mummy ko kallo bata ishe ta ba ta wuce ciki haka nan taji Layla ta fice mata arai, Layla ko daga kanta bata yi ba balle tasan da Mummy, Niswa ta fito ɗaukan system ɗin ta dake chargy a parlorn, ta harare Layla da bata ma san da fitowan ta ba ma. Rayyan yayi parking a kofar gidan sannan yace "Sai da safe Ammi" Ammi ta masa godiya ta wuce ciki, duk yadda Rayyan yaso ya samu Layla a waya amma gaba ɗaya ya kasa samun ta, ya sauka a motar yana shiga compound ɗin muryan Mummy da kawarta sai Niswa ne yaji ya fara echoing in his mind, dakyar ya karasa har kofar dakin su luckily ita kadai ce a parlorn, yayi karfin halin cewa "Ki fito mu tafi" Jin muryan sa Layla ta mike ta dau jakkan ta dama ta gama shiri shi take jira ko sallama bata ma su Mummy ba ta fita, ganin ba zai shiga ba hakan ya mata daɗi ba kadan ba tace "Dear mu tafi ko?" ya fara tafiya tana biye da shi a baya. Zuwa yanzu Sadeeq ya ji dama dama, Mami gani take abun kamar a mafarki ne, Jiddah tana girgiza kafa tace "Ai wallahi koma waye ne ya masa wannan bakin abun wallahi sai ya gani daga kansa har kan 'ya'ya da jikoki" Mami tace "Amma na hana ki ko Jiddah" Jiddah ta tashi tace "Mami sai dai fah kiyi hakuri dan wallahi har na gama biyan kudin da za'a min aiki" daga haka ta wuce ciki. Hajiya tace "inma zaki cire wannan tsohon mijin naki a rai gwara ki gaggauta cire sa kafin ki ja ma kan ki hawan jini, naga kaf dangin sa kin gansu anan ne?" Anty Binta ta gyara zama tace "Ah toh, gwara ma ki faɗa mata Hajiya, kila taji maganar ki dan naga kamar Ni ba fahimta na take ba". Niswa ta taɓe baki tace "Ai ni tun farko sai da na gwada bana son ta kwatakwata amma inaa gani kike ina kishi da Yaya na" Mummy ta sauke ajiyan zuciya tace "ban taba sanin haka halin ta yake ba, har Ni zata buda baki tace min haka?" Niswa tace "wai kuma a hakan dan ita kuke wahala ba, ai gashi tun kafin aje ko ina ta fara gwada miki halin ta, kuma Uwar ta bata yi magana ba sai ma dariya da tayi tana goyon bayan 'yarta" Mummy tana girgiza kafa dan bil hakki Layla ta bata mata rai tace "toh yaushe ta tafi kuma?" Niswa tace "Yaushe dama zata mana sallama". Bayan sallah isha'i Sultan ya shigo gidan dakin da Sadeeq yake ya karasa ya samu Mami da Jiddah ma suna dakin, yana kallon sa ya masa ya jiki Sadeeq ya amsa masa kawai, Mami ta mike ta fita ta musu alama da su biyo ta duk suka mike suka masa Allah karasa sauki, Anan parlorn suka haɗu da Mami suka zauna suna jinta Mami tace "Ni yanzu haka zamu zuba ido ba zamu duba yarinyar nan ba?" Sultan yace "Gaskiya ya kamata, da da hali ma ace harda Sadeeq din Mami" Jidda ta girgiza kai tace "Ina ga ba lallai sai da shi ba, zamu iya zuwa mu ɗin, dan yau fah wajan 3days kenan" Mami tace "Toh gobe sai ku shigo sai mu tafi asibitin" suka amsa da Amin Mami tayi murmushin takaici tace "haɗa ido da su ma kaɗai aiki ne". Duk suna zaune a ɗan karamin compound ɗin su suna shan iska suna hira gwanin ban sha'awa, Malik ya kalli mahaifin na sa jin abinda yace yayi murmushi yace "لا بأس يا أبي (it's nothing Abbah)" Abbah ya masa wani kallo cike da kaunar ɗan nasa yace "ستخبرني بالحقيقة بنفسك (You will tell me the truth yourself)" Malik yayi wani murmushi sai dai kuma bai ce komai ba Abbah yace "أين الفتاة التي حدثتني عنها؟ (Ina yarinyar da ka min maganan ta?)" Umma duk da ba wani larabci take ji sosai ba amma ta fahimci magana kamar na Leena Abbahn ya sako wa 'ɗan sa ta haɗe rai kamar bata san me dariya ba, Malik ya ɗan kalle ta sai kuma ya mayar da kallon sa ga Abbahn sa yace "هي موجودة، لكنني لم أتمكن من رؤيتها بعد، فقط أنا قلق وأريد أن أعرف حالها. (Tana nan Abbah, but I haven’t been able to see her yet, kawai na damu na san halin da take ciki ne" Umma ta mike tace "Ai sai kuyi ta yi" daga haka ta shige ciki, Abbah ya bita da kallo, Malik yayi shiru, shi ya rasa dalilin da yasa da zaran ya dauko maganar Leena Umma ke bata rai. Tun bayan da suka dawo gida kaya kawai ta canza ta wuce kitchen, haka nan taji tana farin ciki, ko dan yau ya kula ta ne bata sani ba, ta wuce dakin Rayyan tayi knocking sannan ta buɗe tana kallon yadda ya kura wa waje daya ido tasan daga gani tunani yake yi, ya juyo yana kallon ta tace "Am nace ko pasta zan daura? Ko kuma wanne zan girka" ya mike zaune daga kwancen da yake yi yace "No need, I'm full" ta dinga kallon sa kamar zata yi kuka sai kuma yace "Okay, ina tunanin pasta ɗin ma is okay" ta juya ta fita bata dau wani lokaci sosai ba ta gama girkin ta ta zuba a warmer ta ajiye a dinning sannan ta wuce toilet tayi wanka ta sa sleepwear ta feshe jikinta da different varieties of perfume har zata fita kuma sai ta tuna kanta ba hula kuma ya faɗa mata ya tsana rashin sa hula da take yi da sauri ta juya ta koma dakin ta dauki
End Ads