bi bayan ta tace "Ke Khadija abinda nake ji da gaske ne?" Mummy ta gyada mata kai trying hard not to cry, daga haka kawar ta tabar dakin, Mummy ta dinga kallon Niswa data ɗauke kai tana kallon wani waje amma yanzu babu hawaye ko kadan a fuskar ta, Mummy tace "Niswa faɗa min gaskiya ke ce? Ko Sharri ake son miki ko?" Niswa tace "Bayan kin ga abu kuma kike tambaya ta? me kike son na ce muku yanzu kuma?" Mummy ta ɗauke ta da mari, Niswa ta dafe kunci ta tace "wallahi Farouq sai na raba ka da farin cikin ka tunda Ni zaka ci amana" Mummy bata san sanda ta fara kuka ba tace "Wato Niswa abun da kike yi kenan? Kin ga irin rayuwar da kika je fa kanki a ciki ko?" Niswa ta mike ta wuce toilet dake cikin dakin Mummy tana toshe bakin ta saboda wani kukan daya zo mata. Hajiya ta sake baki tana kallon Daddy sai kuma ta kama Salati tace "wannan wani irin abun kunya ce Ya Allah, amma gaskiya Niswa bata kyau ta mana ba" Daddy dake kallon ta Camly but looking so disturbed yace "Hajiya dan Allah kar ki sanar da wani a cikin cousins dina, zasu je can suyi ta yawo da mune" Hajiya tace "ko min lalacewa ai ba zan sanar da su ba, kawai dai an fasa auren shikenan" daga haka tayi tagumi tana mamakin wannan lamarin. Anty Binta ta shiga dakin da gudun ta tace "Ammi, ke kina jin wai an fasa auren Niswa?" Layla da har bacci ya sake daukar ta ta mike da sauri, Leena dake rike da Babyn ta ta ɗaga kai tana kallon Anty Binta, Ammi tace "Binta kina da hankali kuwa? ya zaki zo kina magana wani iri mara dadin ji" Anty Binta tace "Wallahi ga magana ya karaɗa cikin gidan nan" Layla tayi wani murmushi without letting anyone notice sai kuma tace "Wallahi da gaske ne Ammi an fasa auren" Anty Binta ta gyada kai irin kinji ko, Ammi na kallon ta tace "Layla ke da kika wuni anan taya kika san an fasa?" Sai kuma yanzu tayi realizing, da sauri tace "Toh ai Ammi tun shigowa ta nan wallahi nake jin kishin kishin kawai dai nayi shiru ne" Ammi tayi tagumi tace "Allah ya kyauta, Allah sa hakan shine mafi alkhairi ya bata wani nagari" ba wanda yace Amin a cikin su. Duk yadda Mummy taso ɓoye abun nan amma haka magana yayi ta yawo wata Kanwar ta ne ta same Mummy a dakin ta tace "amma Aunty baki ganin dan zata auri me kudi ne yasa aka yi wani abun dan yace ya fasa auren ta?" Mummy bata ce mata komai ba, dan yanzu bata da bakin wani bayani, da ace ba'a turo da evidence bane sai ta iya rantse wa tace Ammi ne but yanzu kam tasan Niswa tayi disappointing ɗin ta sannan ta sata kunya irin wanda bata taɓa shiga ba. Kafin yamma gidan ya gama wase wa dan kowa ya tattara nashi da nashi ya kama gaban sa tunda taro ya kare dole yasa suka watse sai few cousins ɗin Daddy da ba'a garin suke ba suma kuma gobe zasu kama gaban su. Tun wannan lokaci da abun nan ya faru Rayyan ya kasa barin masallacin sai bayan da ya idar da sallan Asr sannan ya isa gidan dan kunya ma yake ji shiyasa yaki bari few friends din sa su yi noticing ɗin sa sannan ya kashe wayan sa, bayan yayi parking a kofar gidan na su, ya sauka ya shiga cikin gidan, abun ya dawo masa sabo fil a brain din sa, ɗan bin compound ɗin yayi da kallo ganin ba mutane yasa ya wuce part ɗin su, da sallama ya shiga kallo ɗaya yayi wa Nisreen dake parlorn idon ta yayi mugun ja kana gani kasan ba karamin kuka ta ci ba ya wuce ɗakin Mummy ya buɗe ya shiga ido hudu yayi da Niswa dake zaune akan resting chair tana kallon sa ta mike tsaye tana kallon sa, Rayyan ya karasa cikin dakin wani waya da ya gani wa wajan extension ya dauka, ganin haka yasa ta fara baya baya tana son ta samu hanya da zata gudu, Rayyan ya kamata yace "Mu zaki sa muji kunya? Uban waye wannan mutumin" Niswa tace "Yaya ka sake Ni dan Allah, wallahi Nima ban san shi ba" ya ɗauke ta da mari yace "Ni zaki ma karya? zaki buɗe baki kimin bayani ko sai na karya ki" ta fara kuka ya fara zane ta tana ihu da gudu Mummy ta shiga dakin ta ɗauke Rayyan da mari tace "Da uban me kuke so taji? fasa auren ta ko kuma da sata gaba da kuka yi?" Niswa ta ja gefe tana kuka dan ba kadan dukan ya shige ta ba, Rayyan ya sake baki yana kallon Mummy with shock yace "Mummy!" ta masa tsawa "ka fice min a daki" Rayyan ya sake bulalan hannun sa daga haka ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba, Niswa ta dinga kuka da gaske, Mummy tace "Dan uban ki zaki min shiru ko yaya?". Daddy tun bayan fitan Hajiya yaji kansa na masa mugun ciwo, ga ciwon da kirjin sa ya fara masa, ya rasa me guda ɗaya da zai mata ya huce haushi da takaicin ta daya ke ji. Layla ta gama cin abincin da Ammi ta zuba mata ta kai plate ɗin kitchen da kanta duk da har sannan tana ɗan fama da abdominal pain, daga haka ta fito ta wuce dakin sashin Mummy, bakowa a parlon hakan yasa ta karasa ciki ta zauna akan kujera tana tunanin toh ina suke kuma Nisreen ce ta fito daga dakin ta zata kitchen sai kuma ta tsaya tana kallon Layla tace "Anty Layla ina wuni" Layla tace "Lafiya kau, ina sauran mutanan?" Nisreen tace "Mummy na dakin Yaya ita da sister ɗin ta Anty Niswa kuma tana dakin Mummy i think" Layla tace "Okay" daga haka ta wuce kitchen ɗin bata dau lokaci ba sai gata ta fito ta wuce dakin su, bayan some minutes sai ga Niswa ta fito tana sanye da Hijab har kasa tasa facemask Layla tace "Hey brideyy!" Niswa ta ɗauke kanta ba tare da ta bi ta kanta ba zata fita Layla tace "Excuse me Amarya" Niswa ta juyo cike da confidence tace "Look! Bani da lokacin ki, so do your worst" Layla tace "Ohh really? Huh!" ta mike tsaye tace "I told you, it's a deal! you think I'm joking? You're playing with me Niswa, this is just the start, I'm telling you" Niswa ta tsaya kallon ta sai kuma ta fita a parlorn da saurin ta jin motsin kamar za'a fito daga kitchen, Layla ta taɓe baki ta koma ta zauna, Niswa ta dinga boye fuskar ta har ta karasa gate, bolt da tayi booking har ya karaso, da sauri ta wuce ta shiga ba tare da wani ya gan ta ba". Mummy na fitowa a ɗakin Rayyan tana kallon Layla dake zaune a Parlorn, Layla tace "Mummy ina wuni" a takaice tace "Lafiya" zata sake magana sai taga Mummy tayi gaba ta mike ta taɓe baki ta bar parlorn. Hajiya Fatima da suke Abuja sun kai wasu kayan tana gwadawa masu fixing in da zasu na arranging furnitures ɗin tayi receiving wannan message ɗin tayi jim dan ta rasa gane daga ina kuma aka samu wannan matsalar sai kuma tayi murmushi tace "Shegiya Hauwa, wato ke ma kin rama abin da aka ma 'yar ki kenan" duk da fasa auren da aka yi hakan be sa mai martaba sake biya musu kudin flight daga Abuja zuwa Kaduna ba ita da masu jere. Hajiya tayi sallama a parlorn Ammi, duk suka amsa mata, bayan ta shiga sai kuma ta zauna tayi tagumi tace "Sai kuma muka ji wannan mummunan labarin" Ammi tace "Eh wallahi, amma gaskiya basu kyauta ba" Hajiya ta hayyako mata tace"Basu kyauta ba kamar Yaya? Kin taɓa ganin gidan sarautar da zasu ba ɗan su gantalalliyar mata? Yarinya karama Kamar Niswa ace tasan ta sa harkan maza a gabanta, me Uban ya tare mata fisabilillah" Hajiya ta share hawayen daya gangaro mata tace "Ai abun kunya ne baki dayan mu, ace videon ta da wani katon saurayi yana yawo kuma ace tsirarar su fah" Ammi with shock take kallon Hajiya haka Leena data fito da niyyar gaishe ta.
I'm very sorry, wallahi ban wuni a gida bane, sai bayan sallahr isha'i na fara typing shiyasa nayi dare yau.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
___Mummy tabi ɗakin nata da kallo ganin bata ciki, ta kalli toilet da aka bar kofar a buɗe, tunanin ta ko tana dakin su ne, ta fita da kulle kofar dakin na ta zata dakin Rayyan ta tsaya kallon Nisreen data fito a dakin su, Mummy tace "Nisreen kima Niswa magana ta zo ta same mu a dakin Yayan ku" Nisreen tace "Ai tana dakin ki tun ɗa zu" Mummy tace "bangane ba? bata dakin ku kike nufi?" Nisreen ta gyada mata kai, Mummy ta wuce dakin su Nisreen ɗin bata ganta ba, ta leka har toilet nan ma bata nan, ta fito fuskar ta da alamar tambaya, Nisreen tace "Toh bata dakin ki?" Mummy tace "Eh" Nisreen tace "toh tana ina?" Mummy ta duba kitchen bata ganta anan ba ma, sai kawai taji hankalin ya yayi mugun tashi, ta zauna dirshen akan kujera tace "Yanzu kuma ina Niswa zata shiga?" Nisreen tace "A duba wayan ta idan babu toh bata nan" daga haka ta wuce dakin Mummy duk dube duben ta bata gani ba ta fito ta sami Mummy da tayi tagumi tace "Wallahi Mummy babu, dan na gwada kira ma ko zan ji ringing amma banji ba" Mummy ta wuce ta dauki wayan ta ta shiga kiran Niswa amma ko sau daya bata daga ba, daga nan kuma hankalin Mummy ya fara tashi sosai, Nisreen tana fita ta kitchen ɗin su zata duba ko tana backyard ne dan ta san Niswa da son zama a wajan taga babu kowa, Hajiya data fito daga dakin Ammi Nisreen ta tsaya har ta karaso kusa da backyard ɗin su zata wuce zuwa nata sashin tace "Hajiya Anty Niswa na sashin ki ne?" Hajiya tace "wata Niswan kuma? ba'a ganta bane?" Nisreen ta gyada mata kai tace "wallahi bata nan, duk mun duba ko ina shine nace ko ta karasa gidan ki ne" Hajiya ta buga uban Salati tace "Yanzu yarinyar nan har zata iya barin cikin gidan nan?" Daddy ya fito daga sashin sa zai tafi masallaci sallahr Magrib haka Rayyan ma daya fito daga garden Hajiya ta tsayar da Daddy da sauri tace "ina kuma Niswan zata je?" Daddy da rashin fahimta yace "bangane ba Hajiya?" Hajiya tace "Toh ga yar uwarta tace sama ko kasa ba'a ganta ba" Rayyan ya karasa inda suke yace "Menene kuma?" Daddy yace "Wato har zata iya barin gida? Toh taje ina?" Da sauri ya rike kansa dake sara masa Rayyan yayi saurin rike sa yace "Daddy ko zaka yi sallar a gida ne kawai?" yace "A'a zan iya tafiya" daga haka ya zare hannun Rayyan ya fara tafiya a hankali, Rayyan ya juya yana kallon Hajiya dake bin ɗan ta da kallon tausayi yace "Hajiya Niswa barin gidan tayi?" Hajiya ta nuna masa Nisreen tace "gata ka tambaye ta, suma neman ta suka yi suka rasa" daga haka ya juya ya bi bayan Daddy, zuciyar sa na kuna, yana tunanin kalar jarabawar da Allah ya musu na Uwa. Mummy tama kasa tashi a yanda take zaune sistern ta da friend din ta Maryam suna tsaye suma sun yi jigum tana mamakin ina toh zata je, Mummy ta mike itama backyard ta wuce ta duba ko zata ganta, ganin wajan wayam yasa ta wuce sashin Hajiya, rabon ta da sashin har ta manta, kamar wacca aka cirewa lakka haka take tafiya, ta shiga da sallama tabi wasu cousins ɗin mijin nata da kallo, dan tun da suka zo gidan bata taka ta je ta musu sannu da zuwa ba, ta ɗauke kanta ta wuce bedroom ɗin Hajiya, lokacin kuma ta idar da Sallah tana lazumi, Mummy ta duka gaban ta tace "Hajiya ko Niswa ta shigo nan ne?" Hajiya tace "kar dai har yanzu ba'a san inda take ba?" ta dinga kallon Hajiya tana mamakin har ta san da cewa ta bar gidan sai kuma ta gyada mata kai daga haka ta mike, Hajiya ma ta mike ta bi bayan ta. Bayan sun fito a masallaci Rayyan ya bi Daddy da sauri yace "Daddy" ya juya yana kallon sa har ya karaso inda yake a hankali yace "Daddy baka ganin Mummy tasan whereabouts ɗin Niswa ba?" Daddy bai ce masa komai ba amma har sannan yana kallon sa Rayyan ya kuma cewa "Abin da yasa nace haka, na shiga dana fara hukunta Niswa Mummy tace na ɓace mata daga ganin ta, me muke so Niswan taji da shi? shi yasa nake ga kamar tasan inda take" Daddy ya juya ya cigaba da tafiya Rayyan na bin sa a baya tunani kala da iri a ransa meanwhile kuma yana tunani hali irin na Mummy. Shigan su gidan sai ga su Mummy da Hajiya a compound ɗin zasu wuce sashin Mummyn dan yanzu Hajiya ta fara ganin abun Babba, ganin Daddy yasa Mummy zata wuce ba tare da ta sake kallon sa ba jin muryan sa ya doki kunnen ta ne yasa ta tsaya cak da yace "Ina Niswa, Khadija?" Mummy ta juya tana kallon sa sai kuma tace "Kaga Wallahi ban san inda yarinyar nan take ba, Nima haka na neme ta na rasa" Daddy ya tako har inda take tsaye yace "Ina tambayar ki ina Niswa?" ta girgiza masa kai tace "Nace maka ban san inda take ba ko?" saukan marin Daddy a fuskar ta yasa ta tsaya with shock tama gagara motsi ita ba zafin marin bane ya dame ta mamakin wai shine ya daga hannu ya mare ta? For the first time in her married life tace "ka mare Ni?" Strictly and in serious note yace "kin isa kice mana baki san inda Niswa take bane? Har zaki iya buɗan baki ki ce wani abu? Jiya ma ina ganin take taken ki nasan cewa duk abin da yarinyar nan take aikatawa da sanin ki, saboda ba uwar da 'yar ta zata aikata haka kuma ki nuna ɓacin ran ki ɗan na ɗauki mata ki, last thing da zan fada miki duk inda Niswa take wallahi kice mata ta dawo gida dan idan har ta sake ta kwana a waje toh a bakin auren ki" daga haka ya juya fuu ya wuce, Rayyan da kansa ke kasa shima ya wuce duk jikin sa yayi mugun sanyi, Hajiya kam Mamaki ma abun ya bata daga haka ta wuce, Mummy bata taɓa shiga tashin hankali ba irin na Wannan moment ɗin, tabar gidan nan? Inaaa ai ba zaiyu ba, daga haka ta wuce cikin gidan, dakin ta ta wuce direct ta dauki wayan ta hannunta na bari kuma hawaye na sauka kan kuncin ta ta shiga dialing numbern Niswa to her surprise taji wayan a kashe, bata san sanda tayi cilli da wayan ba.
A bangaren Niswa kuma bayan da Bolt yayi dropping dinta a daidai wani babban gida, ta sauka sannan ta nufi gate ɗin gidan gatekeeper ya buɗe mata ba tare da tambayar ta ba, dake ya santa dan ta saba zuwa gidan, tafiya take kamar zata tashi sama ba tare da knocking ba kawai ta buɗe kofar parlorn Luckily a bude ta samu kanta tsaye ta shiga ba kowa a parlorn tabi parlorn da kallo daga haka ta wuce bedroom ɗin dake parlorn ta buɗe ta shiga tsaye ta gansa a gaban mirror da alama daga wanka ya fito, ta tsaya ta kare masa kallo kamar yadda shi ma yake kallon ta sai dai shi kallon mamaki yake mata, ya karasa saka jallabiyan sa, Farouq na miji ne wanda ya gaji da haduwa wanda kyansa ke ruɗar mata, kuma yana da bala'in kudi wanda duk abin da kike so zai kashe miki, gashi da 6 parts da alamu yana gym, ɗaga mata gira ɗaya yayi da alamar tambaya, zuciyarta nata tafarfasa ta karasa har inda yake ba tare da tayi tunanin komai ba ta sauke masa mari, Farouq ya zuba mata idanu yana kallon ta da mamaki sai dai bai ce mata komai ba, ta fara kuka "Farouq me na maka da zaka tozarta Ni? Me ribar ka idan aka fasa aure na? Me zaka karu da shi? Wannan shine sakayyar yarda da kai da nayi? Shine sakayyar aminta da kai da nayi? har zaka so ka ga downfall dina Farouq?" ta karasa maganar hawaye na sauka kuncin ta ta dafe kujerar dressing mirror tana kallon sa har sannan fuskar sa expressionless ne balle ta fahimci what exactly yake ciki, sai sannan ya kalle ta a nitse kamar kullum yace "Niswa do you really think zan iya sa a fasa auren ki?" ta daga kai tana kallon sa dan ta san shi mutum ne straight forward, tace "Nude videos ɗin na da ka sake mana? and saboda kasan abun da zaka min kenan yasa kaki barin face ɗin ka ba?" sai sannan ya yamutsa fuska yace "Your nude videos? How?" tace "kana nufin baka sani ba zaka ce min ko Yaya? wa yasan ina zuwa gidan ka balle na bika hotel har yayi min video ba tare da na sani ba" yace "Look baby! ba yadda zan yi miki video, kin sanni kuma kin san wanene Ni, so! Ba zan miki karya ba" Niswa ta sulale kasa ta fara kuka na gaskiya ashe dazu bata yi kuka ba, tasan from heaven and earth Farouq idan yayi abu zai ce maka yayi ne without fear, amma sanin yace ba shi bane shine hankalin ta ya tashi fiye da na da, kuka da dinga sha, har sannan