x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 49 - AGOLA free pages

  • 144001 words
  • 147000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
murmushi ta ajiye wayan ta tana gaishe sa, Malik ya rasa menene but He really knows one thing for sure, sai yana tare da Leena ne kaɗai yake samun wata nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wata damuwar sa sai ya nema ya rasa and He always feels connected to Ammi so much because he experiences a peace that comes when he is in her presence, shiyasa baya yarda har ya zo gidan ba tare da ya gaishe ta ba, tamkar wata ɓarin shi yake jin ta, a hankali yace "Leena" ta zuba masa ido tana kallon sa, bayan sun ɗanyi hira yace "Toh kai ni wajan Ammi na na gaishe ta" tace "Okay" yana rike da Nawaf ya mike, tun da Mummy ta shigo da motar ta tayi parking idon ta na kansu, Malik ya kalle ta ganin kallon kurullan da take musu yasa a hankali ya juya yana kallon Leena da tun sau ɗaya ta kalle ta ta ɗauke kai yace "Who is she?" tace "Dan Allah kar ka sake kallon direction ɗin ta, Step Mum ɗin Ayaan ne" Malik ya dinga kallon ta da mamaki sai kuma yace "Toh ai dole zamu gaishe ta" tace "Ka gaishe ta amma banda ni" Malik ya sake juyawa yaga har sannan fuskar ta da mamaki karara yace "Good evening, Ma'am" da accent ɗin sa mai daɗi, ga mamakin sa yaga ta ɗauke kai ta wuce ciki kamar zata tashi sama, Leena na kallon sa tace "Na you sabi, ai sai da nace karka gaishe ta, toh kadan ma ka gani" daga haka suka wuce ciki dan gashe da Ammi da yace. Wannan ranan Mummy ta kasa bacci, fuskan Malik haka ya ta mata gizo, ga kuma wani bugawan da zuciyar ta yake yi idan ta tuna, wani zufa ne yake karyo mata idan har ta tuna cewa Leena zata sake aure kuma bata ga alama dai wannan jikin sa yasan wahala ba, sai ta mike zaune a razane. Layla ta raka mijin ta har bakin motar sa sai shagwaɓa take zuba masa, bayan ya shiga motar ta mika masa jakkan sa cike da shagwaba tace "kace ma Babyn kar yayi motsi ni kam" ya jawo ta sannan yayi kissing dogon cikin ta yace "Hey! Our very own unborn, yau kar ka buge Momman ka ko? tana jin zafi, idan zaka yi motsi kar kayi da karfi, Okay ɗan Albarka?" Layla ta turo baki tana kallon sa "wato ma yayi motsi zaka ce masa?" Yayi dariya yace "toh ai ya zama dole yayi motsi Baby, alamar yana lafiya kenan" ta sakar masa murmushi tace "A dawo lafiya" daga haka ta juya zuwa cikin gidan shi kuma ya wuce office. Mama dake zaune ita da yaran ta Ayrah da Baby, tana kallon su tace "Toh ai sai kuje mata weekend ɗin nan, idan kuma ta shiga watan haihuwar ta ke Baby sai ki koma gidan da zama tunda Ayrah aure zata yi, dan ma mijin na ta likita ne" Ayrah tayi dariya tace "Kai wallahi ban taɓa ganin wanda soyayya ya canza sa ba kamar Anty Layla, da a gidan nan ko kwano bata ɗauka da sunan aiki balle shara, hatta ɗakin ta fa sai dai nayi zuciya na gyara mata amma wai yanzu ita ce mai gudun housegirl wai zata na kallon mata miji" duk suka kwashe da dariya Mama tace "Amma ina bata kazan ta ko?" Baby tace "Chap, ai Mama idan kika je gidan Anty Layla banda kamshi da sheki babu abun da yake yi, kuma da kanta take yi" Mama tace "Dama iskanci ai guri ya samu" kamar daga sama suka jiyo muryan Mummy na doka sallama, Ayrah ta kalli Mama tace "Mama dan Allah kar ki kula ta, yanzu wani matsalar ta ne ya kawo ta" Baby ta taɓe baki tace "yau tasan da gidan nan kenan, ina ko sannu bata cewa Anty ba" Mummy ta sake doka sallama Mama ta taɓa Ayrah data amsa, Ayrah ta amsa, sai gashi ta shigo a birkice kamar wacca ta fito daga prison, su Ayrah suka gaishe ta daga haka suka mike zuwa ciki, Mama ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza wa, ta turo ɗan-kwalin kanta zuwa goshin ta tana kallon Mummy irin kallon rashin mutunci, Mummy tayi yake tace "Haba Aminiya ta" Mama tace "ki faɗa me ya kawo ki ki bar min gida Malama" Mummy tace "yanzu dan Allah akwai abinda har zai shiga tsakanin mu? Haba mana, so kike duk zumuncin mu ya watse?" Mama tace "kin gama?" Mummy ta zauna dirshen kasa tace "Dan Allah ba wannan ba, wallahi wata matsala nake ciki, ba matsala ba ma, matsalsalu ne suka min yawo, and I'm ready to spend ko nawa ne" Mama nan da nan ta sake fuska tace "Haba, ai ba wanda zai ji kanmu, kar ki damu komai ya wuce ai" Mummy tace "Nagode, wallahi kin san Shegiyar Leenan nan ta kawo wani gaye? Ina faɗa miki mutumin nan yayi mugun haduwa iya karshe, taya ina raye zan bar Leena da wannan mutumin" Mama tace "Sai me kuma?" Mummy ta gyara zama ta fara koro mata bayanai. Bayan tafiyar Mummy, Mama ta jawo wayar ta ta shiga kiran Layla, Layla dake kitchen tana dafa Lunch ta fito a kitchen ɗin tayi wajan wayan na ta da ɗan sauri, ganin Mama yasa ta ɗauka ta samu waje ta zauna, ko amsa gaisuwar ta Mama ba tayi ba tace "Layla kina jin surkuwar ki yanzu ta bar gida na" Layla ta sake baki tace "Toh uban me ya kawo ta? yanzu kila Leena tayi sabon saurayi ko kuma dan motar da aka tsayawa Ammi" Mama tayi 'yar dariya tace "Kin gama sanin halin matan nan" Layla tace "Allah yasa baki kula ta ba?, Ki cemin korar kare kika mata, please" Mama tace "kee, ai na kula ta, Malami na take son na kai ta" Layla tace "Mamaaa meyasa zaki kula ta dan Allah?" Mama tayi wani murmushi tace "Haba Layla, sai kace baki san wayee mahaifiyar ki ba? dama auren Ayrah ya tsaya min a rai, yanzu kinga zan samu na zare kuɗin gado da kujeru a jikin ta baki na alaikum" Layla tayi dariya tace "Kai wallahi Mummyn nan bata da wayo kwatakwata, haka fa Mama a jikin ta kika min kayan kitchen, dake ita tasa ran Malamai bata gane komai ba" a haka suka dinga hira Layla tunawa da tayi da girkin ta yasa ta yanke kiran ta wuce kitchen. Gaba daya Mummy ta rasa meke mata daɗi damuna ya sake cunkushe mata amma tun da ta samu Mama take jin ta at ease, dan ta lura Kawarta Amina bata kai Aminiyarta capacity ba, tana zaune a office ɗin ta tana cika wasu files sai ga kiran Mama ya shigo wayan ta da sauri ta ɗauka gudun kar ya yanke bayan sun gaisa Mama tace "Toh Mutumin nan yace ki turo da 100k kafin a fara aiki" Mummy tace "Toh turomin da account numbern da zan sa kuɗin a ciki" daga haka ta katse immediately sai ka text ɗin Mama da account numbern Ayrah, Mummy tayi forwarding wa Rayyan, ganin haka Rayyan dake zaune a office ɗin sa dan ya gama aikin sa na wannan ranan ya kira Mummy dan neman karin bayani game da Account details ɗin, da sauri tayi receiving bayan ya gaishe ta ta amsa tace "Kaga account details ɗin da na tura maka?" yace "Eh, Mummy" tace "yanzu nake son ka tura 100k ma account ɗin sai ka turomin da evidence of payment" yace "Toh Mummy, bari zuwa ko anjima zan tura" ta masa tsawa tace "Yanzu nake bukata Malam" yayi ɗan shiru sai kuma yace "kiyi hakuri, bari na tura yanzu ɗin to" daga haka ta katse kira ta mike ta fara tattara kayan ta zata wuce gida. Leena na kwance jikin Ammi tana karanta message ɗin Muhammad daya tura mata tun jiya sai yanzu ta buɗe, ta mikawa Ammi tace "Ammi ki kalli message ɗin Muhammad" Ammi ta karɓa ta gama karanta komai sai ta kalli Leena tace "Allah sarki, yana jin ba daɗi ne amma tunda har ya nemi yafiya kuma yace shi bada sanin sa bane kuma har kinyi aure ki yafe masa kawai" Leena ta mike daga jikin Ammi tace "Ammi Ni fah ban rike sa a rai ba" Ammi tace "Sure! Kawai kice masa komai ya wuce ai tuntuni" Leena ta gyaɗa mata kai ta shiga typing. Washe gari da yamma, Leena na zaune tare da Malik da yake bata labarin tana ta dariya dan ita har mamaki how nice He is take yi, Rayyan ya shigo ya same su a haka ya karasa suka gaisa da Malik, Leena ta kalle sa tace "Ina wuni Yaya, Anty Layla da jiki?" yace "Alhamdulillah" yana kallon Malik yace "Idan zaka tafi let me know, please" Malik na murmushi yace "In Shaa Allah" daga haka Rayyan ya wuce cikin gidan, bayan wasu mintuna Malik yace zai tafi hakan yasa Leena kiran Rayyan a waya yana ɗauka tace "Yaya yace zai tafi wai" yace "Okay, ce masa ina zuwa" daga haka ya katse kiran Leena na kallon sa tace "Barin shiga, Chat you later" yace "Okay, sister" daga haka ta shiga bayan ta hango Rayyan na taho wa. Sake gaisawa suka yi, Rayyan yace "Dama magana nake so muyi Malik idan har ba damuwa" Malik da accent ɗin sa yace "Okay, Babu damuwa ina ji" Rayyan yace "Naga kana yawan zuwa wajan Leena, and duk lokacin da kazo nakan ganta tana walwala sosai har da dariya ma, shine nake son dan Allah ka faɗamin me a tsakanin ku?" Malik yace "Nothing, sir. Kawai dai na ɗauke ta tamkar kanwa ta ce dan ina jinta sosai a jiki na, kuma ina tsananin tausayin ta dan tausayin nata ne ma yasa har muka shaku yanzu" Rayyan yace "So fah?" Malik yayi shiru Rayyan yace "Talk to me please, say out your mind?" A hankali Malik yace "Idan nace maka bana son ta nayi karya, da farko a matsayin sister na ɗauke ta amma daga baya komai ya juya har ina ji ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba" Rayyan ya rintse ido, yace "Why not ka faɗa mata?" Malik yayi murmushi yace "A'a, saboda kullum maganar ta ba zata sake aure a rayuwar ta ba, hakan yasa saboda kar na rasa ta na gwammaci nayi shiru" Rayyan yace "Zan mata magana" Malik ya kalle sa yace "A'a kar kayi, nasan yaudarar kai na nake yi, ba zan iya rike Leena ba, salary na bai taka kara ya karya ba sannan kuma Ni ke ɗauke da nawin iyaye na, ina jin abincin da Leena zata ci a wata har ya wuce salary ba, balle ma yanzu bani da kuɗin auren" Rayyan yace "Zan maka akwati da kuma Sadaki, and I promise you in shaa Allah bayan auren zan nema maka aiki" Malik speechless ya tsaya kallon Rayyan, Rayyan ya gyaɗa masa kai. Leena taji karan shigowan message wayan ta, zata karbi wayan a hannun Nawaf ya fara tsala mata ihu da kyar ta lallaɓa sa ta karɓe, ganin alert ɗin 300k tayi ta kalli Ammi tace "Ammi kin san nawa Sadeeq ya turo?" Ammi tace "sai kin faɗa" tace "300k fah, amma yana da hankali kuwa? Ko ce masa akayi Nawaf yana iya cinye 200k da yake turowa a baya ne" Ammi tayi murmushi tace "kila yanzu zai ce ai Nawaf ɗin na girma ne Shiyasa ya kara, amma Nawaf ɗin nawa yake ma ai ko 50k ne ba zai cinye ba" Leena ta taɓe baki Ammi tace "Inaga har da ke yake yi" Leena tace "A'a fah, dan ɗan sa yake yi" daga haka ta shiga typing ta tura masa message ta mika wa Nawaf wayan. Bayan isha'i kamar daga sama suka jiyo muryan Mami na sallama Ammi ta amsa mata, bayan ta shiga Nawaf yaje wajan ta da gudu yana murna, ɗaga sa sama tayi tana masa dariya kamar yadda shima yake mata, wanda ya kawo ta ne ya fara shiga da wasu kaya yana ajiye wa nan bakin kofar, kayan wasan yara ne birjik Mami ta tsayawa jikan ta, su keken yara, motar wasa and other stuff, Ammi ta tsaya kallon wanda ke shigo da kayan har sannan, can sai ga Leena ta fito sanye da hijabi ta karasa tana gaishe da Mami, Mami da fara'ar ta ta amsa tana tambayar ta ya hidima, kallon kayan da aka shigo da su tayi tace"Allah amfana Mami" Mami bata ce mata komai ba, Nawaf duk da bayi da wayo amma yasan cewa kayan na shine sai murna yake yana nuna wa Amma, daga haka Leena ta mike ta koma ciki, Ammi ta lura kamar har sannan Mami na jin kunyar ta dan haka yasa Ammi janta da hira, da zata tafi Ammi ta kwalawa Leena kira bayan ta fito tace "Mami zata tafi ne" Mami ta juyo tace "kinga na manta Jiddah fa ta haihu" Ammi tace "Ma Shaa Allah, me ta samu?" Leena tace "Allah sarki, ina jin yanzu bata da layi na ko nice banda nata dan yanzu bana ganin ko status ɗin ta ma" Mami na murmushi tace "Ta samu 'yarta, eh toh ina ji itace bata da naki dan kwanaki ta canza waya" Leena tace "Mami ki gaishe ta kafin naje" tace "In Shaa Allah" daga haka Leena ta koma ciki, Ammi kuma ta raka ta har gate. Tunda Malik ya koma gida maganganun Rayyan ne ya tsaya matsa a rai, at this point zai iya cewa be san me takamaima yake ji a ran sa ba, fargaba ne ko tsoron ratsa ta, ya jingina kansa a jikin wall ɗin ɗakin sa yana tunani dan haka ne ma yau da daddare ya gagara kiran ta dan bai san ko Rayyan ya tsanar mata ba.
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 58

Leena har ta kwanta sai kuma ta ja wayar ta kamar ta kira sa take ji dan ya saba da kiran na ta har zata yi dialing kuma sai ta fasa ta dinga kallon number sa daga karshe ta kashe wayar tayi addu'a ta kwanta.  Da safe bayan Malik ya gama shiri zai tafi inda yake koyarwa har zai fita Abba ya kira sa ya karasa ya duka a kan tabarman da yake kai yace "Me ke damun ka Malik?" Malik yayi shiru sai kuma ya buɗi baki a hankali ya shiga kora masa bayanan duk abin da ke faruwa har ya gama Abba bai katse sa ba sannan ya gyara zaman sa yace "Malik abin da zan faɗa maka anan shine ka rike mutuncin ka, duk da baka da shi, sannan ba wai zan raba ka da yarinyar bace, A'a kawai dai ya kamata kasan hakan zai iya zama maka abin gori wata rana" Malik ya kalli Abban sa yace "Abbah nima na san da hakan amma shi ina da tabbacin ba zai sanar da ita ba, sannan ina tsoron na ratsa ta, kuma yayi min Alƙawarin zai sama mini aiki, balle ma ai na gama haɗa akwatin kawai dai na san ita ba irin kayan ya dace da ita ba ne, kuma bana neman taimakon sa, Allah zai buɗa min ta wata hanyar" Abbah yayi shiru yana kallon Malik dan yasan at this point Malik ba zai taɓa fahimtar sa ba yace "Shikenan Malik, zan taya ka da addu'a idan har da Alkhairi Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah raba ku cikin ruwan sanyi" a hankali yace "Amin". Tun safe Leena ta gama shirin ta na zuwa wani taro da za'a a yi cikin garin Kaduna kuma itace guest of honor, har ta gama shiri bata kalli kiran Malik ba balle ko text ɗin sa which is unusual dan bai saba mata haka ba ta ɗauki jakkan ta ta wuce parlor ta sami Ammi na kallon Sunnah Tv tace "Ammi na tafi, idan Nawaf ya tashi akwai sauran cake ɗin sa" Ammi tace "dama ba da shi zaki je ba?" ta marairace mata tace "Haba Ammi, Kinsan fah mutane da yawa zasu zo idan na tafi da shi kuma ban isa na hana sa zuwa gun mutane ba" Ammi ta gyada kai tace "Allah bada sa'a" ta amsa da Amin ta wuce parking space, ko da ta shiga Mota sai ta gagara tada motar haka nan, gani take ko ta masa laifi ne, ta ciro wayar ta a jakka tayi dialing numbern sa har ya gama ringing bai ɗauka ba, tayi shiru tana tunanin yadda suka rabu Jiya, da sauri ta ware ido tunawa da Rayyan yace yana son ganin sa toh ko yace masa ya daina zuwa ne? Nan da nan taji haushin Rayyan duk da bata da sure akan hakan, a hankali tayi addu'a sannan ta tada motar ta bar gidan. Niswa ta tsaya kallon sa sai kuma a hankali tace "Dan Allah Farouq kayi accepting maganar Mummy tunda karin auren shine burin ta" wani kallo ya wurga mata yace "Toh sai ki sa na kara auren tunda banda niyya" tayi shiru tana kallon sa ita har cikin ranta take son ya kara auren ko dan ta samu sauki a wajan mahaifiyar sa dan yanzu laifin ma ya dawo kanta cewa itace ta hana sa kara aure, ya mike tsaye yace "I think barin Kaduna zamu yi tunda har ta sa mu a gaba har haka" ta tsaya kallon sa da mamaki sai dai bata ce komai ba ya kama hanyar fita tace "Toh dan Allah na tafi gida yau ɗin?" ya juya ya mata kallo daya yace "ki bari sai gobe" ta fashe da kuka dan ta lura idan ta shine ko shekara zata yi ba tare da gida ba hakan ya ke so, ya koma yana kallon ta sai kuma yace "Shikenan, dagaske yau kam nayi miki alkawari gobe zaki tafi" ta share hawayen ta tace "Toh ka rantse" ya shafa kansa bai san sanda yayi murmushi ba yace "Alright, Na rantse" ta gyada masa
End Ads