x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 34 - AGOLA free pages

  • 99001 words
  • 102000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Layla zata yi magana ta katse kiran. Leena ta fito daga dakin ta tana sanye da simple gown, Farida da ke mopping parlorn ta daga kai tana murmushi tace "ina kwana anty Leena" Leena ta sakar mata murmushi tace "Sannu da aiki! Kin tashi lafiya?" tace "Lafiya kalau" Leena zata kitchen tace "Ga can breakfast ɗin a kan dinning, idan baki son shi kuma sai na kara dafa miki wani" Leena tayi shiru jin har breakfast ta gama gani take kamar wahala take sa ta, daga ganin Farida kasan bata saba wahala ba, tace "Amma Farida aikin be yi yawa ba? Wallahi da kin bari" Farida tayi dariya tace "Karki damu" Leena ta karasa dinning tana buɗe kulolin, jin aroman yasa ta fara jin amai da sauri ta rufe, ta ɗan saci kallon Farida sai kuma ta wuce kitchen dan bata son sata wani aikin. Kwana biyun nan har Leena ta fara warware wa, Mami takan shigo ta duba saboda Sadeeq ya koma aiki. Da yamma suna zaune a parlorn daga ita har Farida ba me cewa komai, Faridan kam ma chatting take yi, Leena kuma tana zaune ta kurawa Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi ta ke yi ba, Knocking gate aka fara Farida ta kalle ta tace "Anty Leena kamar sallama ake yi fah" Leena tace "Toh ko zaki duba mana waye ne" ta ajiya wayar na ta akan kujera taje ta buɗe, Hajiya tace "Ina ta sallama, ko bacci kuke yi ne?" Farida ta gaishe ta ta bata hanya ta shiga tace "Muna can ciki ne", Leena na Murmushi ganin Hajiya Bayan sun gaisa tace "Hajiya ya su Ammi na" Hajiya tace "Ai Ni bansan abinda take yi ba, ko su a Niger ɗin haka suke Oho? Ace yarinya ba lafiya wai ita ba zata iya zuwa ba" Hajiya ta karasa maganar cikin takaici Leena ta sauke kan ta kasa ganin kallon da Hajiya take mata, Hajiya tace "Ashe dai gwara da nazo da guziri na" ta dauki Baggo bag ɗin da ta zo da shi ta mika mata tace "Gashi sai kiyi ta fama" Leena ta karba ta turo baki taki cewa komai, ta kuma satan kallon Hajiya taga ita still take kallon, Leena kawai ta tsargu da kallon da Hajiya ke mata  Bayan Farida ta kawo ma Hajiya ruwa, Hajiya ta mike tace "A'a ba zama ya kawo ni ba kawai naga jikin Leena ne na koma" tana kallon Leena tace "Toh Allah ya raba lafiya, naga ma laulayin duk ya ranar da ke, kin wani zabge, toh duk abinda kike son ci kawai ki bugo waya ki faɗa" Leena tayi kasa ta murya tace "Nagode" har Hajiya ta fita sai kuma ta dawo tace "kina ji za'a kawo lefen Niswa ma" Leena tace "Toh Allah ya nuna mana rai da lafiya" Hajiya tace "Amin Amin, baki gan shi ba kuwa suma familyn su masu kuɗi ne" Leena bata kuma cewa komai ba, daga haka ta mata sallama. Leena har cikin ran ta tayi farin ciki wa Niswa, dan tasan kila idan tayi aure zata fita a rayuwar ta.Bayan kwana biyu Leena ta shirya Sadeeq ya kaita gida wuni, bayan yayi dropping dinta yace "ana Asr zan zo ɗaukan ki" ta gyada masa kai ta sauka sai gyara hijab ɗin jikin ta take yi har ta shiga cikin gidan, ta buɗe kofar parlorn Ayan dake zaune ya mike yace "Addah ke ce" da gudu yayi kanta muryan Ammi suka ji a bayan su tace "kar ki fari ya faɗa jikin naki fa" Ina har karasa ya rungume ta suka karasa cikin parlorn Ammi tace "so kike ya Miki rauni? ai sai ki hana sa" Leena tayi murmushi tana gyara hijab ɗin jikin ta, har yamma Leena na bacci sai da Sadeeq ya zo ɗaukan ta tukun ta tashi ta wuce dakin Hajiya zata mata sallama ta haɗu a Mummy ta gaishe ta Mummy tace "Ikon Allah, wato ku amaran zamani har gida kuke zuwa ɗan nuna cewa kuna da ciki?" Leena ta tsaya kallon ta tace "Toh a haifar da dan mana" daga haka ta wuce Leena jikin ta yayi sanyi dan ita ta gagara fahimtar wannan kalmar Mummyn. Bayan an kawo gaisuwar Niswa Mummy kamar ta tashi sama dan murna dan kowa sai da yayi mamakin kayan lefen da aka kawo mata, akwatina set 10 kuma babu kaya mai arha a ciki, videon karban lefen sai trading yake ta yi, Mummy da ahalinta kuwa ba'a cewa komai, har bakin mota Mummy ta raka Hajiya Fatima da sai dariya suke yi, Hajiya Fatima tace toh sai mun karasa a waya kawai, duk yadda ake ciki zaki ji, Mummy na Murmushi ta koma cikin gidan bayan sunyi sallama. Bayan wasu watanni, har anyi bikin Jiddah da Sultan wanda su ma suke zaune a cikin garin Kaduna. Ranan Alhamis da safe tun da suka tashi suke ta shirye shiryen zuwan Sadeeq daga aiki, bayan sun gama hada komai sun kai dinning Leena ta wuce dakin ta dan yin wanka, bayan ta fito a shigar ta me kyau duk da bakon yanayin da take ji amma haka nan ta daure, ta karasa cikin parlorn ta zauna dan bata son barin Farida ita kaɗai, Farida ta daga kai ta zuba mata idanu sabar yadda tayi kyau, can tace "Anty Leena ina ga zan wuce gidan Mami fah, Kinga sai na kwana mata idan ya so jibi sai na wuce Abujan, kuma yana da kyau na leka Anty Jiddah ma" Leena tayi shiru dan sai taji ba daɗi tace "Ba zaki kara mana wasu kwanakin ba?" Farida tayi murmushi tace "Kinga da ba dan admission dinmu bane ya fito da wallahi sai kin haihu zan koma" Leena tace "Wallahi sai duk naji wani iri, Toh Allah yasa ku fara a sa'a" ta amsa da Amin, still kallon Leenan take yi sai kuma tace "Anty Leena kinyi kyau sosai, Ma Shaa Allah" murmushi kawai Leena ta mata. Karan buɗe gate da suka ji yasa suka fahimci ya dawo, Sadeeq na gaba Sultan na baya suka shiga parlorn, Kallo ɗaya Sadeeq ya musu ya wuce dakin sa Sultan ya bisa da kallo haka Leena ma dan wannan ba halin sa bane tun da sukayi aure, bata ɗauke ido ba har ya shiga dakin sai sannan ta mayar da kallon ta kan Sultan tace "Sannun ku da zuwa, ina wuni" gaba ɗaya abinda Sadeeq yayi bai masa dadi ba ya ɗauke kansa yace "Lafiya Leena, ya jikin kuma?" tace "Alhamdulillah" kallon ta yake yi ganin hankalin ta baya kansa sai satan kofar dakin Sadeeq take yi da ido yasa ya mike yace "Leena I think zan wuce" Farida ma ta da ji wani iri ganin yadda Leena tayi ta rawan kafa dan zai zo harda su lalle da kitso duk da cikin ta ya tsufa a haka ta juri zaman, ta mike tana kallon Yayan nata tace "Ya Sultan bari kawai na bi ka sai kayi dropping ɗina gidan Mami" yace"dan kin ganni sai kuma kice zaki tafi? Kuma naga ko sallama da Sadeeq baku yi ba" tace "I know, yanzu zan masa sallama, dama kuma ina da niyyar tafiya ai saboda jibi zan koma Abuja, saboda screening din my" yace "Alright, ki gama sai ki same ni a mota" daga haka yama Leena sallama tace ya gaida Anty Jidda. Bayan Farida ta fito da akwatin ta Leena ta shiga dakin ta ta ɗauki siyayyan da tayi mata, da kyar ta karba, ta tsaya kofar dakin Sadeeq tace "Ya Sadeeq, I'm going" ya fito fuskar nan ta sa a tamke yake tace "Dama zan tafi ne" yace "I have your acc details zaki ji sako na" tayi godiya sannan ta karasa parlorn Leena na faking murmushi ta raka ta har bakin motar Sultan. Bayan ta dawo ta buɗe dakin Sadeeq ta shiga baya dakin amma tana jin alamar karan ruwa a toilet hakan yasa ta fahimci yana toilet din, ta zauna bakin gado tana jiran fitowar sa, tunda Sadeeq ya fito daga toilet kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana tsane ruwan kansa da dan karamin towel ya karasa jikin mirror, har sannan Leena na binsa da idanu Allah ya gani ɗaurewa kawai take yi dan ji tayi kamar zata yi kuka idan ma wani abun tayi masa ai sai ya faɗa mata amma sai ya share ta, ta mike ta fara tafiya inda yake da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Welcome back home, honey" wani kallo ya watsa mata yace "Excuse me, I want to wear my clothes" Leena ta sake baki tana kallon sa expression dinta ya koma shock tsawan da ya daka mata ne yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye ya fara sauka a fuskan ta, dakyar ta wuce dakin ta ta zauna tana share hawayen da yaki tsaya mata. Layla ta fito rike da plate ɗin abinci a hannun ta kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tayi har zata wuce shi sai kuma ta dawo parlorn ta tsaya a gaban sa tace "Amma ai kaji abinda Mummy tace ai" be tanka ta ba yi yayi kamar be sanda wata a wajan ba ta kuma cewa "Wai wannan wani irin wulakanci ne? Wallahi na gaji da halayyan ka Rayyan, na gaji" daga haka ta fashe da kuka ta zauna kasan carpet sai sannan Rayyan ya ture system ɗin da ke gefen sa, harga Allah halayyan ta ne baya so, dan ya san pure love take masa, yace "ke ko da yaushe kuka?" tana sheshsheka tace "Ko sau daya baka taɓa ɗauka na a matsayin matar ka ba, kullum kallon waccan aka cusa maka ita kake min" yace "Layla" ta lalle sa yace "Ba ke bace bana so, halaiyan ki ne bana so, duk abinda na hanaki bakya bari, ko sau nawa zan hana ki fita toh sai kin fita sallah kuma sai nayi da gaske kike tashi kiyi, a haka ne kike so na so ki?" ta ɗauke kanta dan shi kullum ana fara magana sai ya kawo wannan zancen, ita kawai zata tsanar da Mummy halin da take ciki ne, duk yadda Rayyan yayi ta mata magana haka nan ta share sa daga karshe ma barin wajan tayi. Gaba daya haka Leena ta wuni bata da wani walwala, dan tun dazu Sadeeq ko leko ta be yi ba, balle ya san ya take ko ɗan da ke cikin ta, ta kyar ta mike ta daura alwala tazo ta gabatar da Isha'i, jin ba zata iya jure wannan sabon yanayin nasa ba ne yasa ta wuce dakin sa ko knocking bata yi ba ta buɗe ta same sa yana kwance kan gado yana kallon wani wajan Leena ta karasa har gaban sa zata durkusa nan kasa yayi saurin mikewa yace "daka ta" ta tsaya kallon sa ta buɗe baki za tayi magana yace mata "Out!" ta girgiza masa kai tace "i can't" ya sake mata wani tsawan a karo na biyu yace "I said out!" Wannan karan Leena ta gama taorata da lamarin sa dan wannan ba Sadeeq dinta bane tace "At least ka saurare ni mana Uncle" a harzike ya mike ya daka mata tsawa yace "har zan baki doka zaki tsaya min akai ki kiyi?" tace "But.." to her surprise ko bari ta karasa maganar be bari tayi ba ya sauke mata wani lafiyayyar mari a fuska, Leena ta dinga kallon sa ya kuma daga hannu zai mare ta ta ja baya tana kallon sa hawaye na tsintiri a fuskan ta, ta fita dakyar take iya ɗaga kafa. yunwan da take ji ne ya farkar da ita daga bacci daya fara ɗaukan ta kallon agogon tayi taga ashe ma dare baiyi ba dan 11pm ne ma ta sauka daga kan gadon a hankali da kyar take iya tafiya sabar yadda kafafun ta suka kumbura, tana fita a dakin ta ta gansa kwance kan resting chair ta ɗauke kanta ta ta karasa dinning buɗe kulolin wajen tayi taga ko taɓa abinci da ta kashe kanta wajan yi be yi ba, hawaye taji sun fara zuba a fuskan ta ta sa hannu ta share ta debi wanda zata iya ci sauran kuma ta sa a fridge, bayan ta fito a kitchen wannan karan baya parlorn jiki a sanyaye ta wuce dakin ta, wannan daren haka Leena ta yi shi ba tare da ta rintsa ba, dan bacci ma yaki ɗaukan ta, tana ta forcing kanta dan bata son tunani tunanin da take yi saboda tasan illar hakan. Bayan ta idar da sallar asuba tayi morning azkar ɗinta ta mike ta wuce kitchen ta fara hada masa breakfast bata dau lokaci ba ta kammala ta jera a dinning, ganin ya fito ya sa ta karasa cikin parlor ta duka tace "Good morning" Sadeeq dake gyaran neck tie ɗinsa ya daga kai yana kallon ta dan shi bai san tana wajan ba ma, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, Leena ta tace "Dan Allah idan da wani abun da na maka ka fada min amma ka tausaya wa condition dina" ko kallon ta be yi ba ya dauki briefcase dinsa Leena tace "Toh ko da ba zaka min magana ba ga breakfast din ka is ready" haka ya fita ba tare da ya ko kalle ta ba. Leena tana tsaye a wajan kamar wata gunki, ta fashe da kuka ta zauna nan kasa sai da tayi mai isar ta sannan ta mike, ita yanzu ba abin ta faɗa wa Ammi bane hankalin ta ya tashi. tana cikin bacci taji an buga kofar da karfi ta farka a ɗan raza ne ta mike zaune tana kallon sa strictly yace "sakwara zaki girka min" Leena tace "toh" daga haka ta sauka akan gadon shi kuma ya wuce ya fita bayan ta shiga kitchen ganin garin ya kare yasa ta fito ta same sa a parlorn yana kallon Tv ta karasa har gaban sa ta duka tace "Babu garin fa ya kare" a takaice yace "sai kuma a gidan babu doya ko?" ta dinga kallon sa dan ita bata jin zata iya girka shi idan ba garin bane wani kallo da yake mata yasa ta mike ta wuce kitchen ɗin zata iya rantse wa wannan ba Sadeeq dinta bane, dan abinda zai sa ta wahala akai duk ya hanata ta girki ma da kyar ya yarda take dafa indomie, sai data bata lokaci tana girki, bayan ta fito ta ajiye a kulolin a dinning, sai gashi ya bude kofar parlorn ya shiga ya bari a bude tana kallon sa tace "Na gama" tsawa ya mata yace "Sai yanzu? Ke wacca irin mahaukaciya ce?" Sultan dake biye da shi a baya ya tsaya speechless baki a bude yana kallon Sadeeq, a ɗan harsige yace "Sadeeq are you alright?" Sadeeq yaja tsaki ya wuce daki, Sultan ya dinga kallon Leena data sunkuyar da kanta.

Please hint the star at the corner.
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧

*HAUWA JIBRIN SULAIMAN*
*Jiddatul-khayr*✍🏼

*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION*


*Chapter 40*


Jiddah tace "ina jin ka dear" Sultan yayi shiru yana kallon waje daya Jiddah ta kura masa ido, ya gyara zaman sa yace "Jiddah, bana tunanin Leena tana jin dadin auren ta" Jiddah ta masa wani kallon tace "bangane ba?" yace "Ranan da nayi dropping Sadeeq a gidan sa Leena ta fito da niyyan tarban sa but unfortunately Sadeeq ko kallon ta be yi ba ya wuce ciki, and can you imagine Jiya a gaba na yake mata ihu kuma yake kiran ta da jahila" Jiddah ta sake baki tana kallon sa sai kuma ta girgiza kai tace "bana tunanin Ya Sadeeq zai aikata haka" Sultan yace "ya zanna faɗa miki abinda idanuwa na suka gane min kice A'a" tayi shiru amma still kana kallonta kasan she was totally confused yace "Please zaki je gidan, ki sa ido dan lura da halin da take ciki, inma ya kama You can even ask her, ko dan condition dinta" Jiddah ta gyada masa kai, duk sai take ji ba lafiya ba hakanan. Zuwa yanzu Leena ta gama tsare wa da lamarin Sadeeq har bata son haduwa da shi, ita yanzu damuwar ta ma idan labour ya kamata cikin dare ya zata yi gashi bata son ɗagawa Ammi hankali. Jiddah ta shiga parlorn su da sallama Mami dake zaune tana cika wani files na wajan aiki ta daga kai tana kallon ta har ta karasa cikin parlorn bayan sun gaisa, can Mami ta daga idon ta akan system ɗin gaban ta tana kallon Jiddah tace "An samu waccan za'a kaiwa Leena?" Jiddah tace "A'a ai waɗannan kin ce sunyi yara sai dai dattijiwa" Mami tace "Sure, na fi son Dattijiwa saboda abubuwa da yawa" Jiddah tace "zan kara mata magana muji me ake ciki" Mami tace "Toh shikenan, Nima nayi kwana biyu ban leka Leenan ba wallahi" Jiddah tace "Nima zan je can na duba ta anjima" daga haka ta bar Mami anan parlorn ta wuce dakin ta bata dade ba ta fito tace "Mami barin tafi" Mami tace "Dama ba wuni kika zo min ba?" Jiddah tayi dariya tace "zan dawo gobe, yanzun ma gidan Ya Sadeeq zani na biyo nan" bata kai ga karasa rufe baki ba sai ga Sadeeq ya shigo parlorn da sallama, ya gaida Mami ciki ciki ko amsa gaisuwar Jiddah be yi ba ya wuce sama, Leena ta bisa da kallo. Knocking da Jiddah ta dinga yi yasa Leena farkawa a bacci, da kyar ta mike ta fita compound ɗin, bayan ta buɗe taga ashe Jiddah ne, ta kirkiri murmushi ta masa mata baya ta shiga, bayan sun shiga parlorn suka gaisa Leena ta mike tace "barin kawo miki ruwa" Jiddah tace "No, daga gidan Mami nake yanzu ma zan koma gida" Leena ta wuce tace "Eh, duk da haka" daga haka ta wuce kitchen ta dauko mata ruwa, Jiddah sai kallon ta take yi ganin yadda Leena ta koma wani iri ba walwala tattare da ita, Jiddah tace "Leena" Leena ta kalle ta Jiddah ta koma kusa da ita tace "Meke damun ki, Please? Leena ta girgiza kai tana murmushi tace "Bakomai fah"
End Ads