x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 64 - AGOLA free pages

  • 189001 words
  • 192000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
Bayan kwana biyu Daddy suka bar wannan gidan suka koma sabon gidan sa wanda Daddy yace Ammi zata cigaba da rikon Nisreen a wajan ta..

Wait.. har sannan baku following Wattpad acc dina? Oops..
*AGOLA (Behind the palace walls)*



*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Chapter 75

After some months.. Mummy ta fito compound rike da makullin motar ta Layla dake rike da hannun Leena zata kai ta gun driver ya kai ta school saboda Rayyan cikin dare an kira sa a asibitin da yake aiki, tayi clashing da Mummy wanda ta yi hanyar gun motar ta ba tare da tace mata uffan ba dan har sannan tana riƙe da ita a rai akan bata ko amshi Leena a matsayin jika ba, Layla ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki, driver ya karasa wajan ta da sauri yana gaishe ta, ta amsa masa sannan ta basa Leena wanda yanzu take play class, daga haka ta juya cikin gidan, Mummy ta kasa tada motar sabar yadda Layla ke bata mamaki wato ita zata iya kin gaisar wa? Tafi minti uku zaune cikin motar tana mamakin ta, sai yanzu ta fahimci ashe ba rashin haduwa suke ba avoiding haduwa da ita Laylan ke yi, tayi ƙwafa ta tada motar ta ta bar gidan tana ayyana a ranta ko ya Rayyan zai yi gobe zata bar masa gida, ai tana da aiki balle a wulakanta ta. Bayan ta isa gun aiki taga kusan kowa ita yake kallo sai dai bata bi ta kansu ba ta haura second floor ta wuce office ɗin ta sai dai da ta buɗe taga wata mata ce zaune akan office chair ɗin ta tace "Excuse me, what are you doing in my office?" Matar tana taunan chewing gum tace "I'm sorry to say, this used to be your office before, but now it’s mine, you can check the door, you'll see your name is no longer on it" Mummy ta juya tana kallon sunan 'Deborah Elijah' dake manne instead of her name 'Khadija Yusuf' haka kawai ta fara jin zuba ta san idan za'a kori ma'aikatan su mostly haka ake musu but bata son tayi believing hakan, ta dake tana kallon Matar tace "But how come?" Matar ta mata wani kallo irin ta dame ta ɗin nan ta yamutsa fuska tace "There’s your system over there, you can take it, because it won’t be of any use here anymore please" Mummy jiki a sanyaye ta karasa ciki ta ɗauki System ɗin ta kunna tana duba ciki taga Cloud din Ma'aikatan an cire sannan duk wani file da docs duk sun cire ta dauki abin ta ba tare da ta sake bin kan wannan matar ba ta bar office ɗin anan stairs ta haɗu da wata tace "Hello, Ma'am! Oga Murtala yace na kira ki" ta mata wani kallo sai kuma ta wuce office ɗin nasa, ko sallama babu a bakin ta ta shiga ya ɗaga kansa daga system ɗin gaban sa yana kallon ta yace "Mrs Khadija, we're So.." ta katse sa tace "I don’t want any explanations, just tell me what is happening" hakan yasa ya miƙa mata wani envelope, ta karɓa kamar da faɗa, sannan ta ciro papern ciki, heading ɗin ta fara karantawa bata kai ga duba contents ɗin ba kawai ta rufe ta miƙe daga haka ta bar office ɗin nasa ta sauka, wajan motar ta ta wuce ta shiga, ta kai minti 10 tana tunani, can ta ɗauki wayar ta ta shiga kiran Hajiya Amina har ya katse bata ɗauka ba daga haka kawai ta tada motar ta bar haraban wajan. A daidai kofar gidan Hajiya Amina tayi parking dan yanzu bata da wani abu da yayi saura mata kuma, bayan ta parka motar ta shiga cikin gidan da ko gate babu, plastan gidan ma ya sufa wanda yasa pantin gogewa, ta samu wata 'yarta tana fifita wutar gawayi a sakar gidan ga kuma robar koko a gabanta da alama tana son ruwan kan wutan ne ya tafasa ta kaɗa kunun, ta ɗaga kai tana kallon Mummy sai kuma ta cigaba da fifita wutar ta, Mummy kamar zata ɗura mata a'shar sai kuma ta tsaisaita kanta tace "Ke ina Amina take?" Yarinyar ta taɓe baki tace "Ba tana ciki ba" daga haka Mummy ta wuce cikin parlorn nasu da sallama a bakin ta, Hajiya Amina ta fito daga dakin ta da sauri tana "kamar Muryar Hajiya Khadija fa nake ji?" Ganin Mummy yasa tayi turus a bakin kofar ɗakin nata, Mummy tace "Wallahi nice, kin ganni da sassafe ko? Ai matsala nake ciki wlhi, so yanzu zamu gun Malamin nan" Hajiya Amina ta karasa cikin parlorn da sauri tana kallon Mummy ta haɗe hannayen ta biyu tace alamar roki tace "Dan Allah Khadija ki rufamin asiri ki fita min a gida" Mummy with shock take kallon ta, ta sake cewa "Dan Allah ki rufawa tawa auren asiri kar ya mutu ki bar min gida kafin miji na ya ganki" Mummy tace "Ni zaki kora Amina?" Hajiya Amina tace "Gwara ke fa, ko yau da aka sake ki kina cikin gatan ki, ga kina aiki kuma ɗanki yana da kuɗi, Ni fah yau aka sake Ni kauye zani, Kuma Kinga ina daraja aure na" Mummy was frozen tana kallon ta, Hajiya Amina ta sake haɗe hannayen ta tace "Uwar Miji na bata son alaka ta da ke sannan Miji na yamin warning, Ni kuma harga Allah ina daraja Uwar sa balle tasa a sake Ni, dan haka ki fita kafin su dawo su tarar da ke a cikin gidan nan in shiga uku" Shamsiyya dake dama kunun a sakar gidan nasu tace "Mama toh ga Abbah da Kaka sun dawo daga asibitin" Hajiya Amina ta zaro ido tayi bakin kofar ta ɗaga labulayen tana ma Mummy tsawa tace "Wai ba zaki bar min gida bane? Yau naga jaraba, sai kace baki da zuciya" Kaka da Mijin Hajiya Amina da har sun karaso cikin gidan, Kaka tace "Wai meke faruwa ne Amina?" Hajiya Amina ta juya tana kallon Kaka tace "Kaka wannan Matar ne ta dawo min gida" Mijin ta without second thought yaje ya ɗauke ta da mari yace "Amina shine zaki gayyato min ita" Hajiya Amina na rike da kuncin ta,ta duka kan kafafun ta ta fara masa hakuri, Kaka ta fara masifa tace "Kai wani irin mutum ne? Baka ji shigowar mu tana kan korar ta ba? Shine zaka kama ka mare matar ka sabo da wata banza can, Matar dake min biyayya zaka mara akan ido na?" sai kuma ya ɗago ta yace "I'm sorry, Amma nace bana son sake ganin ta anan ko" Shamsiyya tace "Wallahi tun ɗazu Mama ke korar ta amma ta ki tafiya" Mummy ta share hawayen daya zubo mata wanda bata san hawayen menene ba tace "Nagode Amina, ba sai kinmin korar kare ba zan fita na bar miki gida, amma duniya da fadi kije zaki gani" Hajiya Amina tayi shewa tace "Kece ai wanda za'a cewa kije zaki gani, Dan Allah karki sake tako min gida don ni ina jin Maganar Miji na sannan ban raina Uwar sa ba, kuma ban ma wani Mugunta ba balle kice zan gani" Mummy har ta karasa jikin motar ta spaced out, wannan karan sai da ta ɗauki more than 10 mins tana zaune ba tare da tasan mema take aikatawa ba. Farida ta fito daga kitchen riƙe da lunch box sai kuma wani plate dake dauke da brown yam da ketchup, anan parlorn ta ajiye tace "Sweetheart" Nawaf ya fito daure da towel a jikin sa, ta zaunar da shi kan cushion ta dauki cosmetics box ɗin sa, ta shafa masa lotion dinsa ta dauko masa well ironed uniform dinsa ta saka masa sai kuma ta feshe sa da turare, Murmushi ya mata tayi kissing forehead ɗin sa tace "Kayi sauri ka gama breakfast din ka barin ɗauko hijab sai na kai ka school ko?" Bata fuska yayi tace "What?" Yace "Kinsa ketchup kuma" tace "baka so ne?" Ya gyaɗa mata kai, ta ɗauka ta kai dinning ta rufe sannan ta kawo masa wanda ta ajiye zata ci, ta mika masa ya karba yana murmushi, daga haka ta wuce dakin ta bata dade ba sai gata ta fito rike da car key a hannun ta tace "Tashi na kaika kar kayi latti by boy, idan yaso sai kayi breakfast ɗin naka a motar" ya miƙe yana kallon ta yace "Aunty kowa fa yana tafiya school da siblings ɗin sa amma ni ni kaɗai nake zuwa" tayi murmushi ta shafa cikin ta da yanzu ya girma tana kallon sa tace "Soon kai ma zaka samu kani ko kanwa ko?" Ya gyaɗa mata kai daga haka ta fita da shi, a school gate tayi dropping ɗin sa amma kamar kullum ya fara mata shagwaɓa wai har class room dinsa zata kai sa hakan yasa ta sauka tana rike da hannun sa suka wuce cikin School ɗin. Banka ɗa kofar parlorn tayi ta shiga ciki tana "Wayyoooooo! I'm exhausted" Malik dake kitchen yana stir frying chicken spaghetti ya fito da sauri sai kuma ya tsaya kallon Leena da tayi rashe rashe a kasan tiles da tsohon cikin ta wanda haihuwa Yau ko gobe sai kuma ya fara dariya yace "Lafiya Wifey?" Tace "Ina lafiya anan, Exams ɗin yau yadda kasan ban karanta from cover to cover ba, hmm dakyar fah na samu na fidda kai na" Yace "Sorry, gaskiya su daina wahalar min da Mata ko nakai su ƙara" tace "Yanzu ka dawo daga Office?" Yace "Nope, nakai 40 mins shiyasa har na daura abinci" tace "Dan Allah jeka duba idan ya kusa karasawa ka debo min kawai, yunwa nake ji" ya miƙe ya wuce kitchen bai wani ɗauki time ba sai gashi ya fito rike da plate sai kamshi abinci ke zubawa, Leena ta karba tace "Kash, anya baka fini iya girki ba?" Yayi dariya yace "Duk a cikin yunwan ne?" Bayan taci da yawa sai kuma ta juya tana kallon sa tace "Ka yi waya da Abbah?" Yace "Eh dazu mun yi" tace "Me yace maka?" Yace "Ba wani abu mu kayi magana akai ba, kawai ya taimaye ko da akwai wata matsalar ne" tace "Ina ga toh bai faɗa maka ba, amma Granny fah?" Yace "A'a gaskiya bamu yi wata magana da ita ba" ta sha ruwan dake gefen ta tace "Wai dama cewa tayi ina gama exams zan koma Yola acan wai zan haihu" Malik yayi shiru sai kuma yace "Ashe tare kuwa zamu koma" tayi 'yar dariya tace "Kai ka sani kuma" daga haka wayan ta ya fara ringing, ta kallin sunan Farida a screen ɗin tasan Nawaf ne dan duk sanda taga Sadeeq ko Farida tasan Nawaf ne hakan yasa ta daga tasa wayan a speaker tace "Sweetheart" yace "Ammah" tace "Na'am" yace "Yaushe zaki zo gidan Ammi?" tace "Na kusa" yace "Haka fah kullum kike cewa" tace "Toh menene?" Yace "Toh ai mun kusa fara Exams ne ina so idan zan je gidan ta hutu kema zaki zo" tayi shiru sai kuma tace "I will speak to your Abbah akan kazo min hutu idan other Daddyn ka yazo Kaduna sai kuzo Yola tare ko?" Yace "Promise Ammah" tayi dariya tace "I Promised" daga haka ya miƙa wa Farida bayan sun gaisa daga haka tayi ending call ɗin. Ammi tayi parking motar ta a compound ɗin, zuwan ta daga aiki kenan gashi har yamma tayi kuma dole tama Daddy dinner, bayan tayi parking ta sauka, a Parlorn ta samu Nisreen tana ma Ayaan wani lesson, duk suka ɗaga kai suka gaishe ta, Ammi tace "Daddyn ku ya dawo kuwa?" Nisreen tace "Aa bai dawo ba" daga haka ta wuce dakin ta, sallahr Asr tayi tana idar wa tayi evening zikr ɗinta sannan ta miƙe ta fito parlorn sai ga Hajiya na doka sallama bayan ta shigo tana mika ma Mummy robar hannun ta tace "Kinga Kindirmo me kyau na sama mana" Ammi ta karɓa tana Godiya tace "A fridge zan sa yayi sanyi, Ko Nisreen na baku zaku sha naku yanzu?" Tace "A'a Ammi ki bari yayi sanyin"  bayan tasa a fridge ta dawo cikin parlorn tana kallon Nisreen tace "Nisreen taso muje mu daura dinner" Hajiya ta rike haɓa tace "Wai ke baki gajjiya ne? Yanzu fah zuwan ki amma zaki wani shiga kitchen ai jiki da jini ma yana son Hutu" Ammi tayi murmushi Hajiya tace "Gashi kinki yarda a kawo miki 'yar aiki ni kuma wannan abu da mamaki yake" Ammi na murmushi tace "Toh aikin ai ba yawa suke da shi ba" Hajiya ta taɓe baki daga haka ta bar parlorn. Mummy tun da ta dawo cikin gidan ta rasa meke mata daɗi, abin da Hajiya Amina ta mata ba kaɗan ba ya kona mata rai, da ta tuna sai ta fashe da kuka, ta tuna sanda suka sha haduwa da Hajiya ba tare da sun gaishe ta ba dan da farko Hajiya Amina na gaishe ta Mummy tace akan wani dalili sai Hajiya Amina tace da gaskiyar ki, taya ma za'a haɗa ki gida ɗaya da ita duk abin da kika mata ai ita ta zaja ma kanta, kawai ta hana ki sakat da mijin ki? ta tuna yanzu babu ko sisi a wajan ta dan duk abin da take dashi ta bawa Hajiya Amina ta kai mata wajan Malam gashi yanzu tayi two zero, kawai ta sake fashewa da wani sabon kuka kamar yarinya karama, kuma ko da wasa Matan Rayyan basu shiga sabgar ta dan gwara Hasna takan gaishe ta amma itama daga nan Shikenan, ta sake rushewar da kuka tunawa da yadda Hajiya Amina ke yi da Mijin ta harma da surkar ta, wai Miji ya mare ta amma ta duka tana basa hakuri? amma da yanzu itace da tuni sun daurata akan wata hanyar, at this point bata ma san me take ji ba, hakan yasa ta wuce toilet ta wanke fuskan ta, da zama ita kadai banda damuwa babu abin da zai kara mata daga haka ta wuce pain parlorn gidan. Hasna na kama wa Leena kai ga Layla kuma zaune a kan one sitter suna labarin wani littafi suka ji an buɗe kofar parlorn duk suka ɗaga kai suna kallon Mummy da mamaki har ta karasa ta zauna, bayan duk sun gaishe ta a takaice kamar wanda ake musu dole, sai kuma Layla ta miƙe ta wuce ciki, can Hasna tana karasa kama wa Leena kai itama ta miƙe ta bar parlorn, tana kallon Leena dake wasa da Babyn ta zata ɗauki yarinya kawai ta tsala ihu daga haka ta gudu zuwa dakin Layla, Mummy tayi tagumi hawaye na zuba daga idon ta, ta miƙe taji wani jiri ne ke shirin ɗibar ta, ta kai hannu zata dafa kujerar kawai taji ta a kasa timmm, yayi daidai da buɗewar Rayyan ya shigo parlorn, da sauri yayi kanta yana kwala Mata kira amma ko motsi bata yi....



Wait... Wai har sannan baku following Wattpad acc dina? Idan na zo da sabon littafi ya zaku sani? Or baku ji dadin AGOLA bane?
*AGOLA (Behind the palace walls)*


*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Hello darlings! Alhamdulillah, I'm feeling a lot better now. I truly appreciate your care and kind wishes, Love yah


Chapter 76

Farouq na tsaye jikin motar sa after every secs sai ya duba agogon hannun sa sai kuma ya kalli entrance ɗin main parlorn, can sai ga Niswa da Zahra sun fito, ganin su yasa ya buɗe booth suka sa kayan hannun su a ciki, Niswa ta wuce front seat ta buɗe ta shiga, Zahra kuma ta shiga back seat, ya zaga ya shiga mazaunan driver yana kallon su yace "Bayan kun gama shiri amma fitowa ya gagare ku? Kun fa san zan wuce Office" Zahra tace "Karasa shiryawa ne muka tsaya yi" Ya ɗan kalli Niswa da gaba ɗaya she's not herself, daga haka ya tada motar, driver ya buɗe musu gate ya fita, a daidai asibitin da Rayyan ke aiki ya parka motar, yana kallon Niswa yace "Hey!" Ta ɗan kalle sa yace "Ki kwantar da hankalin ki zata samu sauki In Shaa Allah" ta gyaɗa masa kai yace "Zan shigo ɗan anjima idan na cika wani file a office ko?" Tace "Allah ya kaimu" Ya sakar mata murmushi daga haka itama ta sauka wanda tuni har Zahra ta sauke basket dake bayan motar, ganin haka yasa bai sauka ba, su kuma suka wuce zuwa inda Mummy ke kwance, bayan sun shiga dakin da aka yi admitting ɗin ta, suka same ta kwance ga kuma Rayyan dake gefen ta da alama yana lallaɓa ta ne ta saka wani abu a cikin ta amma fir taki, wanda ko an saka mata ɗin ma haka zai zubo saboda bakin a karkace ya ke, Bayan duk sun gaishe ta Niswa taji hawaye na taruwa a idon ta ganin yadda Mummy ta koma a cikin kwana biyun nan, she can't believe wai Mahaifiyar ta ce kwance da shanyeyen gefe guda, ga bakin ta ya karkace, tana ta motsa bakin nata kamar tana son tama Niswan magana hakan yasa Zahra miƙe wa tace "Anty Niswa barin duba wata friend ɗina da ba lafiya" Niswa ta gyaɗa mata kai sanin kawaicin Zahra ne, Niswa ta karasa jikin gadon tana kallon Mummy ta sake fashewa da kuka, Rayyan ya mata wani kallon yace "Ke tashi ki fita idan kuka zaki na yi, baki san sake daga mata hankali kike yi ba" Niswa ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Yaushe zata samu sauki Yaya?" Yace "Idan be yi ba i think zamu fita da ita ne for better result" tana kuka tace "Do so dan Allah" ya gyaɗa mata kai, ga Mummy da hawaye ke zuba ta motsa bakin ta ta fara magana, Rayyan yace "Ki kai kunnen ki wajan bakin ta magana take son miki" hakan yasa tayi yadda yace da kyar Mummy ta furta mata "Niswa Mutuwa zan yi" Niswa ta ja kanta tana toshe bakin ta tana girgiza mata kai ta cigaba "dan Allah ku yafe min
End Ads