Rayyan ne taga ya kira ta dawo ta zauna kan sallayan wani kiran ne ya shigo taji bata da wani interest ɗin magana da shi yanzu zata yi silencing wayan taga ashe Muhammad ne kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta kai kunne sallama yayi ta amsa tace "good evening!" tana ji ya sauke ajiyan zuciya yace "Baby How have you been?" tace "I'm doing great" yace "Alhamdulillah! yanzu naji hankali na ya ɗan kwanta, Baby. I'm so disturbed kwana biyun nan, a office sai da aka ban pass na kwana biyu wai naje na huta sabon yadda nake treating Kowa kamar su suka hana ni magana da ke baby" sai kuma taji ba daɗi abinda ta masa yawan ci yana kira bata kusa ne amma bata taɓa bin kiran back ba, tayi kokari dan kar ya gane tana cikin damuwa tace "I'm so sorry, exams nake yi bana zama a gida ne shiyasa, and ya wanci kuma yanzu da wuri nake bacci, amma da ko text sai na maka" yace "No, no, no, baby don't street yourself for me please, me na kuma bayani, tunda you're fine, I'm glad" tayi shiru shima shirun yayi sai yace "toh barin barki Kiyi baccin ko" tace "thank you". gani take kamar gari ba zai waye mata ba, ta rasa ya zata yi dama idan ta shiga damuwa ɗakin Ammi ne comfort zone ɗinta, ta shiga rubutawa Ammi sako tana rubutawa tana hawaye a haka ta gama rubuta mata tayi sending, ta saba idan da ne Ammi zata leko ta tace kinyi addu'a? Kinsa maganin sauro? Kinyi this and that amma yau ko motsin Ammi bata ji ba tasan ran ta ya ɓaci sosai ne.
Do hints the star at the corner, please.
Thank you, and Happy reading!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
22......
Tun da ta idar da sallar asuba tana nan kan sallayan ta gagara tashi saboda wani ciwo da kanta ya keyi, ta san da abaya ne toh tabbas da warhaka kam Ammi tazo ta duba ko tayi Sallah asuba amma yau Ammi ko ta kanta bata bi ba, tana nan kwance har taji dawowan Daddy daga masallaci. Daddy yace da Ayaan "toh je Ammi ta shirya ka ko" ya gƴada masa kai Ammi ta fito jin muryan sa ta gaishe sa ya masa yace "ina Leena? Jiya ta kawo min IVn su nace zan nema ta kuma na sha'afa" Ammi tace "waya san mata" yana kallon ta yace "bangane ba?" tace "ban san ko tana sashin Hajiya ba ne" Leena ta daure ta fito tana kallon Daddy ta gaishe shi be amsa ba, sai kallon ta da yake yi yace "Me yake damun ki?" daga haka Ammi ta kama hannun Ayaan tace "mu je na shirya ka ko" Leena ta sauke idon ta kasa ganin kallon da Daddy yake mata kamar wani me son gano wani abu ta tace "Babu kawai na kwana da ciwon kai ne" Daddy ya mike yace "barin ma Ya'yan ku magana kafin ya fita sai ya duba ki" ta gƴaɗa masa kai kawai yace "Nawa kike bukata na waliman ki?" tayi shiru yace "ko bakiyi list ba ne?" tace "Eh" yace "toh ki bari idan kika ji sauki sai ki rubuta Kiyi totally sai ki faɗa min amount ɗin" tace "Toh, Nagode Daddy" daga haka ya wuce sashin Uwar gidan sa. Leena har sannan tana tsaye a wajan ta gagara motsi daga karshe dai tabi Ammi kitchen ta tsaya a bakin kofa tace "Ammi dan Allah Kiyi hakuri" Ammi bata juyo ba tace "Wani abu ya faru ne?" Leena tayi shiru bata ce komai ba kuma bata bar bakin kofar ba sai sannan Ammi ta juyo ta kalle ta tace "Niger ɗin ne baki son komawa?" Leena ta girgiza kai sabbin hawaye suka ka fara sintiri a fuskar ta tace "Wallahi ba dan shi bane Ammi, damuwa ta yadda kika share ni ne, idan har komawa ta can ɗin zai saki farin ciki toh barin ki komawan ba" ta kare maganar tana me fashewa da kuka Ammi struggles to hold back tears bata juyo ba amma Chak ta tsaya da aikin da take yi tana jin kukan Leena har zuciyar ta She can't fake her feelings, her love for her daughter surpasses everything. She feels her pain deeply, and as someone who values the best for her child, she wants to protect her from getting hurt by Mummy. That's why she's setting boundaries between her and Rayyan. Leena's passions become hers, and above all, she adores her daughter.
Daddy yana shiga yaga Niswa na kwance kan 3 seater tana chatting ganin sa yasa ta tashi ta zauna ta gaishe shi ya amsa yace "yau ba lectures ne Niswa?" Kai ta gƴada tace "Dama lectures daya gare ni kuma lecturern ba zai zo ba" yace "Okay" Rayyan ne ya shigo ya gaishe da Daddy, Daddy ya amsa yace "yauwa dama Leena bata jin dadi ne so kafin ka fita ka duba ta" akan kunnan Mummy da ta fito wanda har ta gama shirin tafiya, Rayyan na kallon Daddy yace "Daddy me yake damun ta ne?" yace "Ta tashi ne da ciwon kai" wuff Mummy tace "Duk garin nan babu asibiti ne da sai Rayyan zai duba ta?" Daddy yace "ke Meyasa kullum baki son zaman lafiya?, shi Rayyan ɗin laifi ne idan ya duba ta, idan su Niswa ne zaki hana shi duba su ne?" tace "toh ai su ba ɗaya suke ba, taya ma zaka fara haɗa wata shegiyar agola da yaran gida" Daddy yayi murmushi yace "Ke musulma ce Khadija, ya kamata kisan cewa itama yarinyar bada son ta ta zama hakan ba, kamata yayi ki godewa Allah daya barni Kuma ya barki akan ƴaƴan ki, dan dukkan mu ba dabaran mu bane" bata son su fara samun issues da safen nan saboda yanzu burin ta ta samu tayi tafiyar da ke gaban ta, ta wuce dan yi breakfast. Ammi tace "Toh na haɗa Miki tea ne?" ta girgiza kai tace "zan ci wannan ɗin" Sallamar Rayyan suka ji daga bakin kofa Ammi ta ɗaga kai tana kallon kofar sai kuma ta amsa masa tace "shigo mana Rayyan" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta Rayyan da ya shiga parlorn ba zai iya tuna When last ya shigo ba, hakan yasa yaji nawin Ammi sosai, kunya kawai yaji ya kamasa Ammi dake dinning room ita da Leena ta tashi ta karasa cikin parlorn ya gaishe ta kansa a kasa ta amsa tana tambayar sa ya karfin jikin yace "alhamdulillah, dama Daddy ne yace nazo na duba Leena kafin na fita aiki" Ammi tace "Okay" ta mayar da duban ta kan Leena tace "Leena ki karaso ga Rayyan zai duba ki wai" daga haka ta wuce dakin ta Leena ta karasa cikin parlorn idon ta a kasa tace "Good morning" be amsa mata ba yace "What's wrong with you?" he asked, touching her forehead to check her temperature tace "Ba fah komai ba ne, It's just a slight headache, and I'm feeling okay now" yace "But your temperature is high" tayi shiru yace "Leena!" sai sannan ta kalle sa yace "Mene ne?" tace "bakomai dagaske, kan da sauki wallahi" yace "bari toh zan kawo Miki magani kafin na fita" tace "Thank you". Leena na shan magani ta kwanta sai bacci, bacci da bata samu tayi in peace jiya ba shine yanzu ta samu. Rayyan yana kallon Mummy da ta fito da wani ɗan babban jakka a hannun ta ya tashi ya je zai karba jakkan tace "A'a ka bari ba sai ka wahala ba" kallon Mummyn nasa ya ke yace "Toh barin kai ki airport sai na wuce aiki" da sauri ta kalle sa tace "A'a yi wuce War ka zan hau bolt" yace "bolt kuma Mummy? kuma fa ai ba abinda zanyi yanzu" tace "aikin fah?" yace "kin san yau zanyi resuming so ba lalle su ɗauka zan yi resuming yau ɗin ba" ya karasa maganar zai karɓa jakkan hannunta yana cewa "barin kai ki kawai" ta hatsalo masa tace "Toh sannu uba na, ina ce maka A'a kana son takura ni, toh ba zanje ba, shikenan" da mamaki yake kallon Mummy toh yanzu kuma me yayi zafi a maganar sa, ita da ko da wasa bata yarda ta shiga bolt amma yau kuma tace bolt zata hau, komawa da baya yayi yace "I'm sorry, Amma ba wai da wani manufa na fada hakan ba, Allah tsare hanya ya dawo da ku lafiya" tace "Amin" daga haka ta fita, Rayyan ya tsaya jim sai kuma ya fita. Me adaidaita tsawu ya tsaya a bakin tashar, Mummy ta sauka ta mika masa kuɗin sa, gate ɗin tasha ta karasa ta tsaya ta ciro wayan ta tana kiran Aminiyarta bugu biyu ta ɗauka tace "Nima gani nan karaso wa" bayan ta kashe ko minti biyar ba'a yi ba sai ga me napep ya tsaya ta sauko ta mika masa kudin sa sannan ta karasa wajan da kawarta take tana dariyar Mugunta tace "Shegiya da yanzu wani aikin kirki ne cewa zakiyi yayi safe amma wai harda rigani zuwa" ta karasa maganar cikin shekiyan ci Mummy tayi dariya tace "baki san yadda nake gagara bacci bane gashi kullum waye wan gari sai naji kamar nayi hauka idan na tuna bikin na matsowa kusa" shiga cikin tashar suka yi, wajan motar wani kauye suka karasa. Leena na farkawa taja wayan ta da niyyar ganin karfe nawa ne text ɗin Muhammad taci karo da shi murmushi tayi sannan ta tashi, yanzu ta ɗanji dama dama ko dan yadda Ammi ta sauko ne oho, sauka tayi a gadon ta gyara ɗakin sannan ta wuce ban daki tayi wanka ta chanza kaya ta ɗauki wayan nata tana sake karanta sakon sa replying ɗinsa back tayi sannan ta jona wayan a chargy ta fita zuwa parlor ganin Daddy tayi da Ammi suna zaune daga gani soyayya suke sha abin su zata wuce Daddy yace "ya jikin naki dai Daughter" kanta a kasa tace "Alhamduida da sauki yanzu" Ammi na kallon ta cike da tausayi harga Allah duk duniya ba wnada take so fiye da Leena, hakan da take mata kuma so ne ba wai taki ta bane, itama ta san ba zata taɓa iya mayar da ita Niger ba tana kallon ta tace "Toh ki sake breakfast ɗin mana ai yanzu zaki iya yi tunda jikin da sauki" ta gƴada mata kai tace "barin je na gaishe da Hajiya kar tace yau naki leko ta dama jiya munyi faɗa" Daddy na dariya yace "kinyi list ɗin ne?" tace "A'a" yace "Dama me da me zaki buka ne?" tace "Dama ɗinki zanyi na ranan, da wanda zan sa a wajan taron da kuma.wanda zansa a gida, sai memo, sai kuma masu deco da zasu zo gida suyi" Daddy yace "okay, In sha Allah zuwa anjima zan Miki transfer, tace "Toh, Nagode Daddy, Allah kara buɗi" yace "Amin" daga haka ta wuce ɗakin Hajiya tana shiga taga Hajiya na yagan kaza nan da Nan har ta manta da wani damuwan da ke damu ta tace "Kai wallahi, Allah yana so" Hajiya ta kalle ta tace "ke kuma me haka" ta zauna dirshen a gaban Hajiya tace "toh ban nawa mana" Hajiya tace "dama baki je jarabawar bane? da ban ganki da safe ba" tace "na tashi ba lafiya ne sai da Yaya yamin allura tukun" duk maganan da tayi tana kallon cikin plate ɗin hannu Hajiya, Hajiya ta ɗauki fuka fiki ta mika mata Leena ta ɓata rai ganin abin da take bata bayan ga manyan soka a ciki Hajiya tace "idan ba zaki karba ba wallahi zaki rasa" Leena tace "toh bayan kadan kika bani ai wannan ba abinda zai min" Leena ta fake idon Hajiya ta ɗauke cinya da gudu ta kama hanyar fita Hajiya ta sake baki tana kallon ta Leena bata tsaya ba sai a kofar ɗakin su dan tasan tana shiga Ammi taga yana yin ta zata mata faɗa dan ta hana ta gudu sai da ta huta sannan tayi sallama ta shiga bata ga Daddy a parlorn ba Ammi kadai ta samu ta wuce dinning ta bubbuɗe kulolin tace "Ammi ai toh Banga fry egg ba" Ammi tace "idan har ba hannun ki ciwo ya ke yi ba toh ki shiga ki soya" Leena kamar zata yi kuka ta kama hanyar kitchen Ammi ta sake baki tana kallon ta tace "Sannu Leena, girki da ba'a sa ki ba kin iya yi ba tare da kin ɓata fuska ba amma na cikin ki shine zaki min kuka?" tana kallon Ammi sai kuma ta shige kitchen ɗin Ammi tace "Allah kaimu bayan waliman ki , lokacin ba boko balle islamiyya ke zaki fara abincin gidan nan safe, rana da dare sai dai ki mutu dan ni hannu na zan cire" ta leko tana kallon Ammi tace "Ammi ai catering school ya kamata fah ki kaini amma anan ai ba lalle nayi me kyau ba Kinga ko can koya mana za'ayi " Ammi yi tayi kamar bata san tana yi ba. Bayan Leena ta fito a toilet zata yi sallahn azahar jin karan message yasa ta ɗauki wayan ganin alert ɗin kuɗin da ya shiga take zaro ido tayi tana kallon amount ɗin da sauri ta wuce dakin Ammi tana kwala mata kira Ammi ta fito da sauri tace "ke lafiya ?" Leena tace "yanzu alert ɗin Daddy ya shigo min 1Mil fah ya samun" Ammi tayi shiru tace "Toh Allah Ubangijin ya biya sa da gidan Aljanna" Leena tace "Amin ya Rabbi" sai sannan ta fara tsalle tace "Ammi kimin ordern kayan mana sai gobe na kai ɗinki Kinga ba lokaci fah" Ammi tace "toh naji" daga haka ta shige ɗakin ta ta zauna a bakin gado tana mamaki mutun irin Daddy ko da wasa bayagwada cewa ita ɗin ba ƴar sa bace, sannan baya banbanta ta da ƴaƴan sa wajan saya musu kayan sa wa, uwa uba duk lokacin da Leena tayi kokarin a makaranta sai ya tsaya mata gift ya bar ƴaƴan cikin sa, bata manta cewa Leena ita ta fara rike waya a 'ya'yan gidan lokacin da tayi kokari a SS1 ɗin ta ya tambaye me zai bata a matsayin gift tace waya hakan yasa Mummy ta kara tsanar ta, toh Meyasa ba zata kwantar da hankalin ta a gidan ba, me zai sa ba zata so uwar sa ba, dubi yadda mahaifiyar sa ta ɗauke ta da ƴarta fiye da yadda take son uwar gidan sa, share hawayen daya gangaro mata tayi ta tashi ta hau kan sallaya dama sallah zata yi Leena ta kwala mata kira. Leena bayan ta gama long appreciation and prayer message da zata turawa Daddy sake karantawa tayi taga yayi daidai sannan ta tura masa, shiga call log tayi searching numbern sa ta yi tayi dialing be ɗaga ba hakan yasa ta ajiye wayan tayi sallah.
Leena ita kaɗai take dariya kamar mahaukaciya, da ta tuna abin da tama Hajiya sai ta fashe da dariya, Ammi ne ta kwala mata kira ta sauri ta amsa ta je, Ammi tace "kin sanar da Muhammad kuwa?" Leena ta girgiza kai Ammi tace "ya kamata ki sanar da shi, sai ki kuma ki je ki kaiwa Mami ma invitation card ɗin" Leena tace "toh Ammi". Da yamma Leena zata gidan Mami ta fita kenan ta haɗu da Hajiya a compound Leena ta ɗauke kai Hajiya tace "Ai na zama abokiyar wasan ki ne na ke gani Leena" Leena taki cewa komai ta fita. Bayan mai gadi ya buɗe mata gate tace "Mami na ciki?" yace "Eh duk suna ciki" Leena ta shiga a compound taga Sadeeq na waya kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuma ya bita da kallo...
https://www.wattpad.com/1547254859?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=jiddatulkhayr
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
23........
Daidai entrance ta ga Sultan da Jidda suna dariya alama dai labari ɗayan su yake ba wa ɗaya, da gudu Leena ta karasa tayi hugging ɗin Jidda, Jiddah tayi hugging ɗinta back tace "sweetheart" Leena na dariya "yaushe kika zo Aunt" Jidda tace "ai ke gaɓa ɗaya baki kirki yanzu kin manta da mu ne ai" Leena tace "Wallahi da gaske makaranta ke boye ni, exams nake fama da shi" ta juya tana kallon Sultan daya zuba mata ido tana dariya tace "Uncle Sultan, ina wuni" yace "ai na ɗauka saboda Kinga Jidda kin manta da ni" tace "Haba ai ban isa ba" tana kallon Jidda dake murmushi tace "Anty, Mami na ciki?" Mami tace "Eh tana ciki" Leena ta wuce cikin parlorn da Sallah. Sai da Leena ta shiga parlorn kafin Sadeeq ya ɗauke idon sa akan ta. Leena ta gaishe da Mami, tana mika mata IV ɗin tace "Dama sauka zanyi next week, kuma a gida za'a min waliman na school graduation ɗina, za'a haɗa ne" Mami tace "Ma shaa Allah, Allah ya nuna mana Leena, Allah sa anyi na tsoron Allah ne" tun kan Leena ga kai ga cewa Amin sai ga Sultan da Jidda sun shigo Jiddah tace "Amarya Leena, sorry gulma muke yi da Ya Sultan yasa na manta da cewa Amarya ce ashe" Leena taki cewa komai Mami tace "Za'ayi saukan Leena fa next week" ta kare maganar tana mikawa Jidda IVn ta, karɓa ta gani ta mika ma Sultan suka mata Allah sanya Alkhairi, bayan Mami ta shiga cikin ɗakin ta, Leena tace "Anty Jiddah ina zaki taimaka min wajan prep ko?" Jidda tace "why not, me plan ɗin ki?". Leena ta fita compound da niyyar amsa wayan Muhammad akan zata ce masa bata gida sai ganin mutum tayi akan ta da sauri ta ɗaga kai tana kallon sa da mamaki ta sauke idon ta kasa tayi tace "Good evening" be amsa mata ba sai ma tambayar daya je fa mata "Why did you choose to get married now, Leena?" Leena, keep an eye on him, kallon cikin idon ta ya ke yi alamar yana jiran amsa, ji tayi ba zata jura haɗa ido da shi ba ta sauke idon ta kasa, har Muhammad ya sake kira Leena ta gagara picking