ta fito haka nan dai take yi, tana komawa bangaren ta taji wayan ta na ringing da ɗan gudun ta, ta karasa ta ɗauki wayan ta wuce dakin ta sai da tasa key sannan tayi picking tace "ya ake ciki yanzu?" shima wanda ya kira ta yace "Wallahi Hajiya ina faɗa Miki har yanzu ko mutun daya daga ɓangaren angon ba'a gani ba, Alhajin naki ma naga damuwa ƙarara a fuskan sa" Mummy tayi wani buɗa ta katse kiran tana jin wani farin ciki mara misaltuwa, da sauri ta shiga kiran aminiyarta tana dauka tace"Ke de halin da ake ciki yanzu Babu ango balle mutanen sa". Jiddah dake ma Leena magana sai ga kiran Sultan ya shigo, ɗauka tayi tana sauraron abun da ke cewa da sauri ta kalli Leena sai kuma ta mike ta wuce jikin wardrobe Leena ta bita da kallo zuciyan ta na bugawa haka nan taji wannan kiran ba Alkhairi bace Jiddah tace "Ya Sultan, Do whatever you can to save a life, please" daga haka ta katse kiran tana kallon Leena cike da tausayi Leena ta mike tana kallon ta tace "An fasa auren ko?" Jiddah tace "A'a fah, wani irin magana ne wannan kuma Leena?" Zahra da ta sake baki tana kallon Leena speechless jin me tace, Jiddah ta karasa har inda take tace "Ina zuwa Leena, Zahra please ki tsaya da ita" Jiddah na fita sashin Hajiya tayi ta shiga da sallama ta gaishe da bakin da suka zo ta karasa inda Mami ke zaune ta duka tace "Mami idan ba damuwa ina son magana da ke amma mu ɗan fita" Mami na kallon ta tace "Lafiya ?" tace "Muje Mami" daga haka Mami ta mike. Sultan dake tsaye yana rike da hannun Ayaan gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi amma yana hoping hakan zai zama Alkhairi wa each other. Yayan Daddy yace "kana ganin hakan ba matsala?" yace "ba wanda zai ja idan har an daura auren beside shi Rayyan ɗin saboda ita yarinyar yaki aure, itama yarinyar tana son sai" ya girgiza masa kai yace "wannan ba hujja bace, kama ta yayi ace ko da zaka daura auren na su ya zama na da consent ɗin iyayen su mata, musamman ita uwar yarinyar kar tayi tunanin dan ba kaine ka haife yarinyar ba shiyasa kace haka" Daddy yayi shiru shi yasan ba za'a samu matsala ba ta wajan ta amma idan har tayi tunanin hakan fah? Yayan nasa ya daura da cewa "Idan har zaka bi ta nawa shawarar yana da kyau ace uwar nata tasan da halin da ake ciki sannan" Daddy yace "wallahi idan har ta Sirbajo ne toh ba zata taɓa cewa zaɓi na be yi ba" yace "toh shikenan, ka fini sanin halin ta ai" suka karasa cikin masallaci akan za'a daura auren Leena da Rayyan. Limamin masallaci ya ɗaga kai yana kallon Daddy yace "ina shaidar gwajin su?" Daddy yana kallon sa da rashin fahimta Yayan sa yace "takardar test na asibiti zaka basu" Daddy ya dafe kai yace "ainahin wanda za'a daura auren sun fasa shine yanzu za'a daura auren da yayanta ne" Limamin ya girgiza kai yace "sai dai kayi hakuri Alhaji, amma mu bamu daura aure sai da takardar shaidar asibiti" Daddy ya dafe kansa Yayan nasa na kallon sa yace "kaje gida kasa suyi test din yanzu Ni kuma Nasan dabaran da zanyi da baki kaga sai a rufe maganar akan ba'a kawo test bane" Daddy ya mike ya fita daga cikin masallacin duk ranshi a ɓace ya shiga Mota ya kama hanyar gida. Ammi ta sake baki tana kallon Mami dake mata magana sai kuma ta mayar da kallon ta kan Jiddah she's just speechless har wani zazzaɓi zazzaɓi ta fara ji. Binta ta ja Mairamah waje tace "ke baki ji kishin kishin da ke tashi bane? Wallahi ina tsoron Shegiyar matan can" nan ta faɗa mata maganar da ke yawo amma kowa kasa kasa yake magana Mairamah ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta kama hannunta zuwa balconyn Ammi da niyar gulma nan suka ga Ammi, Jiddah da Mami na magana kasa kasa reaction din Ammi ya tabbatar musu da abinda ke ransu haka ne, shigowan Daddy gidan yasa duk suka zuba masa ido suna kallon sa Ammi ta mike tsaye bata kara gaskata hakan ba sai data ga babu annuri tattare da shi, ya karasa har inda suke tsaye yace "Sirbajo ina son ganin ki yanzu ke da Leena a parlor na" wani sanyi Ammi ta fara ji me rasa jiki ta kalli Mami sannan ta karasa cikin parlor ko takan Mutane dake parlorn bata bi ba ta wuce ɗakin ta. Daddy na shiga parlorn sa kawai kan kujera ya samu ya sauna ya jingina da kansa lumshe idon sa yayi yana tunani ganin wannan ba mafita ba ne ya buɗe ido ya dauki wayan shi ya kira Hajiya yace ta ɗan zo sashin shi akwai Magana, ya kira Mummy sannan ya kira Rayyan yace shima yana son ganin sa. Mummy tana murmushi ta buɗe dakin su Niswa tace "ku, ku taso Daddyn ku na kira na, ina ga auren Agolan da aka fasa ne zai sanar dani" Niswa ta dirko daga kan gadon tace "An fasa Mummyyyy?" bata san sanda tayi maganar da karfi tana rike haɓa Mummy tace "toh dama shi sa'ar tane? Ai sai dai ta samu irin yaran shago da ake biya dubu sha biyar a wata" Niswa tayi wani salle tace "buri na ya kusa cika". Ammi da Leena suka yi sallama a parlorn ya basu izinin suka shiga ba su kai ga zama ba sai ga Yayan Daddy Usmanu shima ya dawo gidan ya shigo, ganin yanayin Daddy yasa Leena ta sake jin hankalin ta yayi mummunan tashi fiye da na da kana ganin ta kasan tayi karama ma wannan tashin hankali Daddy dake kallon yanayin ta yace "Leena kinyi waya da Muhammad ne?" da kyar ta iya girgiza masa kai, shi ya ɗauka ma sunyi waya ne ganin yadda ta wani fita hayyacin ta yace "Okay, je ki kwanta ki huta ko? Naga kamar kin gaji" ya karasa maganar yana faking mata Murmushi Yayan nasa ma sai kallonta yake cike da tausayin ta, tana son tace masa A'a amma ta gagara kawai ta mike ji take kamar zata fadi ta buɗe kofar anan kuma ta haɗu da su Mummy da yaran ta mata zasu shiga dakin suma Mummy na Murmushi tace "Amarya ba kya lefi ko kin kashe ɗan masu gidan ne" Nisreen ta masa mata tun da ita ta riga su fita tana kallon ta, Niswa tace "Amaryar Muhammadu ba" ta kare maganar tana dariya ko kula su bata yi ba balle tasan me suke nufi ita nata damuwan daban ne yanzu, su Mummy suka karasa ciki sai can ga Hajiya ta shigo da sallama ganin kowa na Zazzau ne yasa ta kasa karasa cikin parlorn tana bin kowa da kallo tace "Anya lafiya kuwa?" Daddy yace "kiyi hakuri Hajiya ki karaso zaki ji koma menene" Rayyan ne yayi sallama a bayan ta ta juya ta kalle sa sai kuma ta karasa cikin parlorn shima Rayyan ɗin haka yayi sai da ya bi parlorn da kallo yana hoping everything is fine sannan ya karasa ya zauna wajan ƙafafun Daddy ya gaishe da su. Gyaran Murya Yayan Daddy yayi wanda yake cousin dinsa, Hajiya ta zuba masa ido tana son jin Meyasa aka tara su, yayi musu sallama bayan su amsa ya fara magana a hankali cike da tunatar da su kowani musulmi yana tafiya ne akan gadan zaren kaddarar sa ne kuma ba wanda zai kauce, Hajiya tace "Kai Usmanu! faɗa mana kawai meya faru dan mu mun gaji zuciyan mu ta samu salaman bugawa da take yi" yace "Toh Hajiya" "Dama abinda ya faru shine, wannan yaron da yake neman ƴarmu da aure Allah ya ƙaddara ashe ba mijin ta bane, shine yasa yanzu shida dangin sa sunce an fasa auren" Hajiya ta dafe kirji ta mike tace "An fasa auren?" Ammi ta zuba masa ido tana kallon sa dama ta san abinda zai ce kenan tunda Mami ta mata magana Rayyan da sauri shima ya ɗaga kai yana kallon Uncle ɗin nasa Mummy tace "Toh fah, to ko sunji wani mugun abu ne akan ta shiyasa suka fasa?" tun furucin farko da Yayan sa yayi Daddy yake kallon reaction din Mummy yasan da zafi a fasa auren ɗanka, duk suka maida kallon su wajan Mummy sabar mamakin jin furucin ta Hajiya tace "Ai kaf gidan nan ba wanda ke da hali me kyau sama da ita Leenan, yarinyar da kowa yake so saboda hankalin ta? Shine zaki wani kawo maganar banza ana jimami" Daddy ya daura dacewa "Tun a masallacin naso na aura mata aure da zaɓi na amma sai kuma suka ce suna son ganin shadar asibiti shiyasa ba'a daura ba" Daga Ammi har Mummy suka zuba masa ido Hajiya tace "toh waye kuma zaka ɗaura mata auren da shi?" yace "Rayyan zan aura mata" Hajiya tace"Alhamdulillah" Rayyan ya tsunkuyar da kansa, wani zabura daga Mummy har Ammi suka yi, duk lokacin daya suka mike suna kallo sa Mummy tace "Wallahi ba'a isa a ɗaurawa ɗana wancan ƴar iskan yarinyar ba, akan wannan maganar sai dai duk abinda zai faru ya faru" Ammi tace "Ki kwantar da hankalin ki, Nima ba zan taɓa yarda na bari ina numfashi a doran kasa a ɗaura wa 'ƴa ta wani daga zuriyar ki ba" Daddy ya daka musu tsawa yace "Muna magana in peacefully way zaku tara mana mutane ne?" Ammi ta zauna tana girgiza kafa tace "Wallahi da ko ace an ɗaura auren sai inda karfina ya kare wajan sai ya sake min 'ya, kuma ba zan taba bari ta tare a gidan sa ba, dan 'ya ta ba zata taɓa shiga gidan da aka tsane ta tun tana ƴar karama ake musguna mata ake mata mugunta iri da kala ba, gidan da ko tarbiyya be ishe su bane zan kai 'ya ta, kuma ace na iya bacci, inaaaa! Never" tunda ta fara magana kowa ya sake baki yana kallon ta dan Ammi ba mutum bace me son hayani ko magana ba Mummy kuwa hararanta ta dinga wasa mata Yaya Usmanu kuwa gyada kai yayi dan yasan ba lalle iyayen su yarda ba abinda kuma kenan yake son Daddy ya gane, Daddy yace "kenan ban isa da ku bane da ba zan yanke hukunci a bi kai a zauna ba? Sirbajo harda ke, ke da nake ma ganin kina da hankali, baki ja in ja da Ni ba kaman Khadija ba, daman Ni ba damuwa ta da ra'ayin ta ba saboda Rayyan ɗa na ne, amma Leena kar Kiga kaman ina nuna Miki fin karfi ne a kanta" Ammi tace "tunda har ka iya gane cewa bana cewa A'a dinka Eh, kuma bana cewa Eh dinka A'a Tohm ka sani wannan babban lamari ne da yasa nace A'a wannan lokacin, dan wallahi a shirye nake da na bar gidan ka akan wannan maganar, ita Khadijan naga Uwa ce kuma tana da tasiri akan ɗanta haka zasu ta juya min ƴa yadda suke so, ina har Rayyan ta hana shi gaishe Ni balle yayiwa Leena magana, kuma ina da tabbacin itace ta hana sa dan da can ba haka yake ba kaga kuwa zai yi ta mata biyayyar uwa ni kuma ana kashe min 'ya, har kai kanka ba sai da tasa ka cire Leena a makarantar da 'ya'yan ta suke ba saboda kiyayyan da suke mata, wani kalan abu ne yaranta basu ma Leena ba, ina har driver ta hana sa ɗaukan ƴaƴana a mota, sai yanzu ne za'a zo min wai na bari 'yata ta shiga wannan gida, inaaaa never!" Duk akayi shiru ana kallon ta ganin yadda tayi spark bana kaɗan ba Mummy nata murmushi dan hakan ya mata daɗi tasan atleast idan ita tace bata so Daddy zai iya hakura Hajiya tace "Tohm maganar gaskiya anan shine kar muce zamu tauye mata hakkin ta ɗan gaskiya ta kawo hujja me karfi, kuma kowa yasan yadda bata magana amma tunda yau ta buɗe baki tayi ya kamata musan wannan wani lamari ne na daban kuma tana da gaskiya ko nice iyakan abinda zan ma ƴata tilo, duba da yadda Leena ta dinga wahala a cikin gidan nan na kyara da tsangoma harda ma gori, Nima yanzu gaskiya bana goyan bayan auren yanzu, Allah ba kowa rabon sa" Hajiya tayi wani murmushi tace"akwai lauje cikin naɗi" tunawa da tayi sanda Mummy tace mata karta bari ayi auren Leena yanzu, Daddy yayi shiru alamun hakan me masa ba Ammi ta daura da cewa "Tunda wannan ya fasa akwai wanda yake son ta, kuma Mahaifiyar sa da ƴan uwan sa suna sonta yanzu haka sun tausaya mata suna neman a basu auren ta a yau din dan su a shirye suke" da sauri Mummy ta ɗaga kai tana kallon ta zuciyan ta na bugawa Rayyan tunda ya runtse ido be buɗe ba Daddy shima shirun yayi yana kallon ta, Yaya Usmanu ne yace "aina shi yaron ya ke?" Ammi tace "harda ɗan uwan sa wajan ɗaura auren ɗazu yanzu haka mahaifiyar sa tana daki na ita da kanwar sa" Yana kallon Daddy yace "toh kawai su je suyi test yanzu" Ammi tace "akwai test din da Leena tayi, Tohm shima mahaifiyar tasa tace shima akwai wanda yayi lokacin da wacca zai aura ta mutu" yace "Ma Shaa Allah, shi da waliyyi nasa mu hadu a masallaci ki sanar da su" Ammi ta mike tace "yanzu ma kuwa?" Daddy har sannan ya rasa me zai ce gaba ɗaya ya zama out of words Hajiya tace "A'a tunda har ƴan uwan sa na son yarinyar ai da sauki, yanzu tun kafin a fara yawo da mu a cikin unguwa kawai ku samu ku koma masallaci a daura mata aure dan na gane wanda Amin ke magana akan sa" daga haka Ammi ta fita sai yanzu ta tuna ashe dazu har zazzaɓi ta fara ji amma yanzu duk ta neme su ta rasa taji ta at very ease ysnzu. Bayan Ammi ta sanar ma Mami, Mami tace "bari Sultan ya ma kanin mahaifin su magana dama neighbors dinmu ne, su ma sai su tafi tare da Sultan din" Ammi tace "Tohm shikenan" Mami nata godiya Ammi tace "haba ai mune da godiya, ai rufa mana asiri kuka yi" daga haka ta wuce". A bakin kofar kitchen taga kannan nata ta karasa dan yadda suka damu atleast ta kwantar musu da hankali tayi kasa da murya tace "za'a daura auren da wani yanzu in shaa Allah" Anty Binta tace "karde wannan Rayyan ɗin ne?" Ammi tace "sai na yarda? Toh ai baku san me ba ai intention ɗin Daddy nasu kenan na gwada musu inaa, shine aka hakura" suka ce hauka kike zaki yarda Mairamah tace "ku daina ganin laifin yaron ma, itace tayi wani abunta shiyasa yaron yace ya fasa auren yanzu" Ammi ta juya ta fita ta barsu a nan wajan suna kuskura ɗin su. Aka daura auren Leena da angon ta Sadeeq akan sadaki Naira dubu dari biyar, jama'a suka shaida.......
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
29.....
Bayan Rayyan ya koma daki, ba zai iya fada exactly meya ke ji ba, ga wani sabon zazzaɓi daya rufe shi, wani sanyi me rasa kashi yake ji, da kyar ya isa shiga toilet yayi alwala duk da sanyi da yake ji haka nan ya daure ya dauro ta, bayan ya fito ya shinfida sallaya yayi raka'a biyu sanda zai fara addu'a hawaye kawai ya ji yake sintiri a fuskar sa, yanzu kam yasan cewa tayi masa nisa ba zai iya cigaba da kallon ta kuma ya daina jin abinda yake ji akan ta ba gwara ya roki Allah ya yaye masa son da yake mata. Duk halin nan da ake ciki daga Leena har Sadeeq ba wanda ke da labari a cikin su. Ammi ta shiga dakin ta da cup din tea da abincin da ta zuba a plate bata bi takan mutane da ke falon ba ta wuce su, har inda Leena take ta karasa ta zauna tana mika mata abinci, Leena ta girgiza mata kai tace "Ammi banda appetite, kuma ma bana jin yunwa ba zan iya ci ba" Ammi ta bata rai tace "Zaki karɓa ki ci ne ko zaki tsaya cewa baki da wani appetite, naga ga tea nan zai ɗan sa kici abincin" ta karba ita hankalin ta ma baya jikin ta taga gidan yayi shiru kuma har sannan ba wanda ya mata bayani kuma haka nan take jin ba lafiya ba, da kyar take iya tura abincin daga karshe ma kawai tean tasha sai ga Anty Binta ta shigo tana "Alhamdulillah, an daura Ammi" Ammi ta daga kai tana kallon Binta sai kuma tace "Allah ba su zaman lafiya" tace "Amin" Leena ta ajiye Cup ɗin hannunta ta gagara daga kai. Muhammad a mummunar zabure ya tashi Ummi da ta shigo da niyyar rage masa Acn saboda tsanyi da garin ya ɗauka ta tsaya kallon sa daga bakin kofar, rike kansa yayi yana addu'a Ummi ta karasa ciki da sauri tace "Lafiya son?" yace "Ummi kaina kamar zai fasha, ki rike min kimin addu'a, Ummi Abbahn su je an ɗaura auren?" Ummi ta fita da sauri ta wuce dakin Abbah tace "Dear, Muhammad fah ya rike kansa duk ya fice hayyacin sa wai kansa na masa ciwo, ko za'a kaisa asibiti" Abbah ya mike yace "Duk yadda kuka ga yayi, it's Okayy" daga haka ya kama hanyar bedroom dinsa Ummi tasha gaban sa tace "ban gane ba? Haba nace maka yaro yana cewa kan sa zai fasha" sai sannan ya juyo yana kallon ta yace "Put yourself in their shoes, Allah kadai yasan wani hali suke ciki, ace hours to your wedding kawai a tura maka text dan wulakanci for that matter wai an fasa aure? Imagine fah, ni yanzu da kike gani na cire hannun na a lamarin MD" Ummi ta fara kuka tace"Wannan wani kalan abu