x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 50 - AGOLA free pages

  • 147001 words
  • 150000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
ka daga haka ya fita. Leena ta dawo gidan a gajiye lis, dan tana sallah taci abinci ta hau bacci, ringing ɗin wayan ta ya katse mata baccin, ta ɗauki wayan tana kallo mai kira sannan tayi picking tace "Hello Yaya" yace "Bacci kike yi?" tace "No, na farka ai" yace "Ina son ganin ki idan ba damuwa" tayi jim sai kuma ta mike tace "Okay, when?" yace "Yanzu, come and meet me ina garden ne" ta miƙe zaune tana murza ido daga haka ta wuce toilet ta wanke fuskan ta sannan ta sanya hijab ta fito Ammi tace "ina zuwa kuma?" Tace "Yaya ne ke kira na, ina Nawaf Ammi?" Ammi tace "yana ɗakin Hajiya" Leena ta gƴaɗa kai daga haka ta fita. Tana kallon sa tace "Ina wuni" yace "Lafiya Maman Nawaf" ta ɗan kalle sa sai kuma bata ce komai ba yace "magana nake so muyi amma ina son ki bani hankalin ki kuma ki fahimci ni" tace "Okay". With shock Leena take kallon Yayan ta jin maganar da ya mata, sai dai kuma taji ta gagara jin haushin Malik ta kalli sa tace "A'a Yaya gaskiya Ni yanzu bani da ra'ayin aure" yace "ko kuma ki ce baki son sa saboda ba zai iya rike ki ba" ta tsaya kallon sa dan maganar ya ɓata mata rai tace "Yaya sai aka ce maka Nima ina cikin Matan da kuɗi ya dame su?" Yace "Toh abin da shi Malik ɗin zai ɗauka, beside na masa alkawari zamu nema masa aiki mai kyau, kuma idan har nayi wa Daddy magana ma ke ma kin san ba zaiki samar masa wani aikin ba" Leena ta girgiza kai tace "Ni yanzu babu wani aure a gaba na dan haka yayi hakuri kawai" Rayyan yace "Okay, na faɗa masa cewa kin ce baki son sa? Ya kuma daina zuwa? Sannan ya nemi wacca zata so sa kawai ya aura dan ke kin ki accepting ɗin sa?" Leena ta sake baki tana kallon sa da mamaki sai kuma ta ɗauke kai tana tunani, Rayyan yayi murmushi yace "kuma kin san Daddy ba zai yarda ya barki ki cigaba da zama ba aure ba, Ni kuma zan faɗa masa kince ba zaki sake aure ba" Leena ta ɗan kalle sa sai kuma ta ɗauke kai tana kokarin mai da hawayen ta, dan da gaske Sadeeq yayi breaking heart ɗin ta bata taɓa expecting za su rabu ba balle har ta shiryawa zuwan ranan. Mummy na kallon Rayyan da ya gama gaishe ta zai mike tace "zauna za muyi magana" ya koma ya zauna yace "Ina ji Mummy" ta yi regretting face tace "Nasan abubuwan da nayi a baya ban kyauta maka ba, sannan ace abun da kake so wai ni na kasa so? Shine dan haka yanzu nake baka umurni da ka auri Leena dan tana bani tausayi ainun" with shock yake kallon Mummy sai kuma ya girgiza kai yace "No Mummy, na daɗe da cire Leena a rai na tun kafin tayi aure na cire ta dan nasan ba zaki taɓa goyon bayan na aure ta ba balle har Ammi ta yarda" ta daure fuska tace "Umurni nake baka Rayyan" ya tsaya kallon ta da mamaki tace "Or else wallahi ka saki Layla, saki uku kuma" ya ja baya with shock yake kallon ta yace "Mummy na sake Layla fa kike cewa?" tace "Umurnin nawa zaka kauce? Idan nace kuma a watan nan nake son ka auri Leena ko ka saki Layla idan har ka ki ɗaya daga ciki sai na tsine maka" zufa ne ya fara karyo masa be san meya kawo sa gidan nan ba yau, bayi da wani Alternative, yaso ya boye mata amma ganin zai shafi rayuwar sa yasa a hankali ya buɗe baki yace "Mummy ba wai auren Leenan bane ba zan yi ba, na riga da na ma wanda yake zuwa alkawarin zan ba sa" Mummy ta tamke fuska tana kallon sa da mamaki yace "Idan na aure ta kuma ban masa adalci ba, zai ɗauka saboda basu da kuɗi ne yasa muka masa hakan" nan da nan Mummy ta sake fuska tace "bangane basu da kuɗi ba?" Ya gyaɗa mata kai yace "Eh, yaron basu da kuɗi dan a makarantar wani private school yake koyarwa sannan shi yake dauke da nawin iyayen sa which salaryn sa bai wuce 20k ba" Mummy tace "kaji ka dai da wata magana, toh kai waya faɗa maka hakan, sannan kana kallon sa kaga ba karamin mutum bane duba da yadda skin ɗin sa yake sheki nikam naga har kama da Leenan ma yake min" yace "Tun dana ga ya dake da zuwa yasa na gano gidan su bayan nayi bincike akan sa sannan na masa tayin auren ta dan mutumin kirki ne kawai dan basu da arziki ne, shima ya gwada min yana son ta har na mata magana akai ita ma" Mummy tace "Je ka zamu yi magana" daga haka ya sauke ajiyan zuciya ya fita, Mummy ta kira wani mai bada Flowers ɗin su ruwa yana zuwa ya duka yace "gani Hajiya" tace "Harisu wani aiki zan saka idan zaka iya" ya daga kai ya kalle ta yace "Hajiya zan iya da yardan Allah" ta gyaɗa kai tace "Harisu, akwai wani da yake zuwa wajen Leena, ina so ka samun ido akan sa ida ya zo sannan ka bisa a baya ba tare da yasan kana bin nasa ba har kasan ina ne gidan su sannan waye shi, kuma suna da kudi ko babu" yace "Toh Hajiya" Mummy tace "idan har kayi hakan, sannan ba tare da ka sanar da wani ba, kuma ka samo min bayanai nan da nake nema na maka alkawarin zan ninka maka salaryn ka har na tsawon shekara ɗaya, daga dubu 20 zuwa dubu 40" da sauri ya daga kai yana kallon yace "Toh..toh.. Nagode sosaiii Hajiya, kar ki damu zaki samu bayanan da kike so" daga haka ta juya ta bar sa nan tsaye, bayan Mummy ta shiga ita kaɗai take ta murmushi ai dama tun farko mijin da take ta wa Leena fatan ta aura kenan, idan ko har haka ne bata damu da kyau ɗin sa ba yaje can ya aure ta talauci ya kashe su. Leena tayi shiru tana ta mamakin maganganun Rayyan dan ba kaɗan ba maganar ya dake ta, taya ma Malik zai ce yana son ta? Amma sai kuma ta samu kanta da rashin jin haushin sa, har Ammi tayi noticing ɗin ta tace "Leena tunanin me kike tun ɗazu? Da sauri Leena ta kalli Ammi sai kuma tace "Babu komai Ammi" Ammi tace "Okay, ashe ma kin fara ɓoye min abu ko?" Leena ta girgiza kai ta zauna ta fara narrating ma Ammi duk yadda suka yi da Rayyan, Ammi tace "Toh me a maganar nasa da har zaki ɗaga hankalin ki kina wasu tunani?" Leena tace "Toh Ammi ni nace masa ina son sa da har zai masa magana?" Ammi tayi murmushi tace "Toh yanzu wa zaki raina wa hankali kice ba son sa kike ba? Duk zuwan da yake kusan kullum da wayan da kuke yi shima duk cikin kiyayya ne?" Leena tayi shiru tana kallon wani wajan Ammi tace "Rayyan yayi min daidai, ko dan kina ganin Daddyn ku ya zuba miki ido bai ce komai bane? Tun yaushe mutumin nan yake shigo mishi gida amma ya kauda kan sa yanzu kuma kice ba son sa kike ba sai kuma a zuba muku ido sai yayi ta zuwa ke kuma kiyi ta fita kuna hira?" Leena ta sauke kan ta kasa tana wasa da fingers ɗinta daga haka Ammi ta mike ba tare da ta kara ce mata komai ba ta wuce dakin ta. Daran ranan haka Leena ta kasa bacci, maganganun Ammi da Rayyan ya dinga zuwa mata, ta rasa ya zata yi ta kauda tunanin nan amma ta kasa, kuma haushin Malik take ji da rashin kiran ta da baiyi ba through out ranan, ta jawo wayan ta ta kalli karfe 12pm ta ja tsuka ta rufe kanta da duvet dan ta samu bacci amma sai ta kasa, tayi ta juye juye daga karshe kawai ta sake jawo wayan ta ta rintse ido tayi dialing numbern sa yana ringing har ya katse bai ɗauka ba ta ja tsuka ta ajiye wayan, kawai taji wayan ta ya fara ringing da sauri ta ɗaga tana kallon sunan sa dake kan screen ɗin bata ɗaga ba har ya yanke, ya sake kira ta ɗauka takai kunne yayi sallama ta amsa masa daga haka tayi shiru, shima shirun yayi a hankali yace "Leena" tace "Shine ko kira babu?" Yace "I'm sorry, just that.." ta katse sa "Sorry for what? Don't tell me aiki kake or something else" yayi shiru ita ma shirun tayi can ya daure yace "I don't know ko Rayyan ya miki magana?" Tace "that's the reason ka daina kira na?" Yace "No, kawai dai ina fargaba ne" tace "Fargaba for what? Ka faɗa min, shi ne ba zaka iya faɗa min ba sai Yaya? So you don't trust the comfortability I have for you? Ba zaka iya approaching ɗina ba? Well duk lokacin da ka shirya then, Is left for you" daga haka ta katse kiran tayi shiru tana tunanin abubuwan da ta faɗa masa sai taji she really sounds dull ta taɓe baki daga haka bacci ya ɗauke ta. A bangaren Malik kuwa mamaki ma hana sa bacci yayi daga karshe ya shiga rubuta mata long message ya tura mata. Washe gari Ammi ta gama shirin ta cikin laffaya ga Nawaf ma da ta gama shirya sa tana zaune daga parlorn tace "Yanzu Leena tun ɗazu shine kika kasa shiryawa? Ba fa ke kika shirya Nawaf ba balle kice min kin tsaya shirya sa ne" tace Ammi gani fitowa fah" ba'a ɗau lokaci ba sai ga Leena ta fito tana sanye da Atamfa da Veil, Ammi tayi hanyar kofa da Nawaf a hannun ta, Nawaf ya juya yana kallon Leena yace "Amma come with us" ta tsaya ta rufe ko ina sannan ta bi su a baya da sauri, suna shiga compound ɗin su Mami suka ga Sadeeq na tsaye waya kare a kunnen sa, kallo ɗaya Leena ta masa ta ɗauke ka, ya sauke waya a kunnen sa  ya karasa inda suke ya ɗan duka yace "Ina wuni, Ammi" Ammi ta tsaya su gaisa, a takaice Leena tace masa "Ina wuni" daga haka ta wuce ciki ta bar su Ammi da suka tsaya gaisawa, ganin kallon yaron yake yasa Ammi tace "Nawaf je gun Daddyn ka ko?" daga haka Ammi ta bi bayan Leena, daga yaron yayi ya ɗaura sa kan bayan motar sa yana kallon sa cike da so da kauna yace "Ka Sanni?" Nawaf yana ta babbaka masa dariya kamar ya san sa, kissing ɗin sa yayi shima yana masa dariyar. Mami tace "yau kuma ina Baba na?" Ammi tace "yana wajan Baban sa a waje" Leena sai kallon jaririn Jiddah take. Har suka fito Sadeeq na rike da Nawaf suna ta shirmen su, Mami ta kalle sa tace "Toh zasu tafi, Malam" Ammi tace "A'a bar su idan sun gama hirar ai sai ya kawo sa" da sauri Sadeeq yace "Toh Shikenan Ammi" Leena dake baya ita da Jiddah a hankali yace "Leena" ta tsaya tana kallon sa yace "Thank you" tace "For?" sai kuma yayi diverting maganan yace "ya maganan school ɗin ki?" tace "Ban fara ba tukun, Maybe nayi Jamb this year" yace "Success, but please kar ki canza mind" kai kawai ta gyaɗa masa daga haka ta fita ba tare da ta sake kallon su ba, Nawaf yace "Amma bye".
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧



Wattpad @Jiddatulkhayr
Instagram @Jiddatulkhayr writes


Young talented writers association (YOTA)


Chapter 59


Sa'adutu, Murjanatu, Aisha bint Sa'id, Daddy's princess, Noor and Co. I dedicate this page to you guys.


Kwana biyun da suka wuce Ammi ta sa Leena a gaba, gashi gaba ɗaya tunanin ta ya tsaya cak, ta rasa exactly me zata yi, ga Malik da ya sata gaba, she thought haɗuwan ta da Sadeeq zai sa ya mata maganar komawan ta gidan sa but bata ga alamar hakan ba, ga kashin zuga da Ammi ta saka mata akan idan bata tsaida ɗaya ba zata sa Daddy ya mata magana, dan haka ta dage da addu'a kawai. Ta fito tana sanye da Jilbab, hannun ta ɗaya riƙe da hand bag ɗayan kuma tana rike da Nawaf, suna tafiya zuwa parking space, Nawaf ya cire hannun sa a nata bata kula sa ba ta cigaba ta tafiya, gate ɗin aka buɗe ta ɗan daga kanta ganin wanene, ga mamakin ta ta kalli Niswa ne, ta ɗauke kai ba tare da ta sake kallon wajan ba, ta buɗe kofar motar zata shiga kawai ta tsinci muryar Niswa "Hey! Leena" Leena ta daka ta da shiga motar ta juya sai kuma taga Niswan na mata murmushi kuma tana tun karo ta, hakan yasa itama ta sake fuska tace "Sannu, Anty Niswa" tana murmushi tace "Kina nan Lafiya, ya Babyn ki?" Ware ido tayi ganin Nawaf tace "Ohh, wow, has my little baby grown this much" ta ajiye jakkan ta a bayan motar Leena ta duka ta ɗauke shi tana kallon sa tayi kissing ɗin sa, ya fara mata murmushi ta sauke sa tana kallon Leena tace "Is like fita zaku yi ko?" Leena tace "Eh" tace "Toh sai kun dawo" daga haka ta wuce zuwa dakin su. Da sauri Umma ta dakar da Abbah tana kallon sa cike da mamaki tace "Inaa! Ai ba zai taɓa yuwa ba, gwara ma ya canza ra'ayin sa akan yarinyar nan" Abbah da mamaki yake kallon ta, ta mike daga kan tabarman da take tace "wallahi ba zan taɓa lamuntan Malik ya auri wannan yarinyar ba, ba zan taɓa yarda ba, toh shi me zai yi da bazawara? Ko yanzu sai na fito masa da mata wallahi, budurwa ma kuwa" Abbah ma ya mike yace "Toh ki sani tunda yace yana son ta shikenan, sannan da kike maganar bazawara ina son ki san cewa fiyayyan halitta da bazawara ya fara, dan haka baki isa haramta masa ita ba" daga haka ya wuce ya bar gidan dan yanzu masifar Umman ya fara gajiya da shi. Mummy ta zuba wa Niswa ido ganin yadda ta rame kamar ba ita ba tace "Niswa kina cin abincin kuwa?" Niswa tayi murmushi tace "Eh, Mummy" Mummy tace "Har yanzu zaman naku ba daɗi ne?" ta girgiza kai tace "Ni fah bani da matsala da shi, kawai dai baya son nace zan fita, matsala ta yanzu kuma da gidan su ne, amma shi kam bayi da matsala" Mummy tayi shiru tana kallon 'yar na ta yadda ta koma ba wannan tsaurin ta koma wani shiru shiru da ita. Da yamma Niswa ta shiga sashin Hajiya, Hajiya ta sake baki tana kallon Niswa da mamaki, Niswa ta gashe da Hajiya, Hajiya ta amsa tana kallon yadda gaba ɗaya ta bar Niswan da ta sani a baya, ta kara mata nasiha daga haka ta mata sallama.  Leena na ba Ammi labari gani tayi Ammin na sha mata kamshi saboda maganar nan, murmushi kawai tayi, ta yi kamar bata ma fahimci me Ammin ke nufi ba, sallaman Niswa suka jiyo, Ammi ta amsa mata bayan ta shiga ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa mata, tace "Ashe har Babyn ya girma, nikam girman sa ya ban mamaki" Ammi tayi dariya tace "kila dan baki ganin sa ne" Leena ta lura tun shigowan ta take kallon ta sai dai bata ɗaga ido da niyyar kallon ta ba sai taga kallon nata take a hankali tace "Leena kin kara kyau, kuma kinyi kiɓa, Ma Shaa Allah" Leena tace "Kai Anty Niswa" murmushi kawai ta yi, Ammi nata mamakin ta dan a da kam ko kallo Ammin bata ishe ta ba balle gaisuwa, ta mike tana kallon Ammi tace "Zan tafi, Ammi" Ammi ta mike tace "Ki tsaya ina zuwa" daga haka ta shige dakin ta bata daɗe ba sai gashi ta fito rike da laida, tace "Ga shi kin zo bani da komai sai turare ne" tana murmushi tama Ammi godiya daga haka ta fita Ammi ta kalli Leena tace "Ki raka ta ko da gate mana" Leena tace "Kamar site ɗin Daddy zata fa". Daddy ba karamin jin dadin sauyin Niswa ba yaji sai dai yaji wani iri ganin yadda ta lalace. Mummy ta fito daga backyard zata ɗaki da sauri Harisu yace "Hajiya" Mummy ta bi compound ɗin da kallo ganin ba kowa yasa ta tsaya har ya karasa, ya duka yana gaishe ta, ta dakatar da shi tace "Bani amsar sako na kawai" yace "Okay.. Dama na bibiye sa ne, har unguwar su naje nasan gidan su, sannan yaron gaskiya basu da kuɗi dan ɗan karamin gida ne gare su, ga kuma shi ke ɗauke da nawin iyayen sa, bayan haka kuma 'yan unguwar sai zagin sa suke ganin yadda suke fama da bakin talauci amma sai yana saka kaya mai kyau akan ya ci ma cikin sa wanda wasu suke ganin kamar yaudarar 'yan mata yake yi" tace "kana da tabbacin abinda kake faɗa?" Yace "kwarai ma kuwa Hajiya, har gidan su fa nace miki naje, kuna naga shigan sa gidan, wallahi ba ma zaki yarda a gidan yake ba Shiyasa mutanen unguwar suka ce yaudara gare sa" Mummy tayi wani murmushi tace "Nagode da wannan sakon" ganin zata juya ta shiga yayi saurin tsayar da ita bayan ta tsaya yace "Hajiya kuma duk sanda zai zo gidan nan ma machine yake zuwa" tace "Naji, ka saurari sako na" daga haka ta shige ciki, hamdalah ta fara yi, ita at this point zata iya hakura da ta cusawa Layla bakin ciki gwara kawai ya auri Leena da yaudaran. Malik ya shiga cikin gidan na su da sallama a bakin sa, Umma kaɗai ya gani zaune a ɗan sakar gidan na su, da ɗan karamin radiyo tana saurara, Kallon Malik da tayi yasa ta kashe radiyon, Malik ya karasa har inda take zaune ya zauna yana
End Ads