x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 60 - AGOLA free pages

  • 177001 words
  • 180000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads
tace "Ina za'a juye tunanin su ne?" Yace "Masarautar ma gaba ki ɗaya zasu tsane ta ba zasu yarda ace zasu mulke ta ba balle har ya kai ga ace ance za'a naɗa su" Fulani ta karɓa tana murmushi tace "Toh Godiya muke" daga haka suka fita, bayan sun koma Masarautar, suna cikin shiga sai ga Mai martaba ya fito zashi masallaci, kallo ɗaya yama Sarauniya Zainabu dake tare da su Fulani, wanda har sai da ta sha jinin jikin ta, yana mamaki hali irin na Zainabu, wato har zata iya haɗa kai da makiyan sa? Har zata iya haɗa kai da wanda basu kaunar sa. Washe gari kamar yadda suka saba haka suka sake haɗa kai, Sarauniya Zainabu tace "Yanzu yadda za'a bar baɗa musu a kofar ɗakin ne da kuma a cikin abinci shine babbar matsalar" Waziri yace "ku bani ni nasan yadda zan barbaɗa da daddare, sai ku kusan yadda zaku haɗa kai da masu haɗa mu su abinci" Fulani ta mika masa laidar tace "Hakan yayi, idan aka sa musu kusan asuba ka ga dole zasu sallahr asuba kuma zasu taka" yace "Eh dama shine duk lissafi na". Kamar yadda suka tsara haka nan ya faru, dan tun karfe biyu da rabi na dare Waziri ya fita, yana tafi a hankali har ya karasa bakin kofar ɗakin su Yarima, ya zazzaga sannan ya bar wajan ya koma ya kwanta. Da asuba Yarima Abdul-aziz ya fito za shi masallaci, ya buɗe kofar sai yaji kamar jiri kawai sai ya fara addu'a sannan ya sauka ya wuce masallaci bayan yaji kamar jirin ya bar sa. Da safe Gimbiya Indo ta tsaya a kofar sashin Yarima, bayan ta kira sa a waya ya bata izinin shiga, ta shiga yana zaune a parlorn na sa yana sipping tea har ta karasa ta zauna bai ɗago ya ganta ba, sai da tace "Hey, big bro" sai sannan ya ajiye tea din hannun sa yana kallon ta da murmushi yace "Hey you" tace "Ina Yarima?" Yace "Baya nan ai" ta gyaɗa ka sai kuma tace "Zamu iya magana ?" Ya gyara zaman sa yana kallon ta yace "Why not?" Tace "Please duk abin da za'a kawo maka ko daga wajan jakadai ko daga wajan wane ne please idan ba Ummi bane kar ka ci" wani murmushi da beyi shirin yi bane ya suɓuce masa yace "Alright, Lil sis" ta mike tace "Thats all, bye" ya bita da kallo yace "Thank you". Mai martaba na zaune a fada ga waziri a gefen sa sai sauran dattawan fada, Waziri na kallon Mai martaba yace "Allah ya taimaka ka, amma ya kwana biyu bana kallon su Yarima" a takaice wani dokari yace "Ai basu nan" waziri ya Kalle sa da sauri yace "Ban gane basu nan ba?" Yace "Eh basu nan, sun tafi US kaman" waziri yaji wani zufa na keto masa wato duk abin suke shiri akan su basu nan ma kenan. Bayan kwana biyu Abdul-aziz ne yayi parking motar sa ya sauka ya karasa cikin airport din, tun bai karasa ba ya hango Abdallah wanda yake ɗauke da Suhaif ga kuma Matar sa Amira a gefen sa da dogon cikin ta, Suhaif na hango Abdul-aziz ya fara tsala ihu wanda hakan yasa Abdallah sauke sa, da gudu yayi wajan da Abdul-aziz yake shima ya duka yaron ya shige jikin sa yayi hugging ɗin sa so tight yana dariya kamar yadda yaron ma yake dariya ya mike tsaye da shi a jikin sa, har suka karaso wajan sa, Abdallah ya sakar ma dan uwan nasa murmushi shima ya mayar masa yana kallon Amira yace "Sannu Amira" tana murmushi tace "Ina wuni" yace "Lafiya ya jikin ki?" Tace "Da sauki" ya juya yana kallon Abdallah, Abdallah ya ɗaga masa gira ɗaya sama yace "Yes kayi missing ɗina ne kake damu na da kira?" Abdul-aziz yace "Ban sani ba" Abdallah yayi dariya. Bayan isan su Masarautar hanyar dakin Sarauniya Hauwa'u suka nufa, tun da Abdallah ya hango Waziri ya Ciro wayan sa ya kara a kunnen sa kamar me waya har suka zo inda yake, Abdul-aziz ne kaɗai da Amira suka gaishe sa. Suhaif yayi kan Hajiya Hauwa'u da gudu yana cewa "Granny" ta duka ta rungume sa, manna masa kiss tayi a forehead ɗin sa tana masa dariya kamar yadda shima yake mata, bayan sun zauna suka gaishe ta, ta kalli Amira da ta kumbura, tace "Shiga ciki ki huta ko" Amira ta mike tana murmushi ta wuce ciki, Abdallah ya dinga kallon Ummi sai dai kuma ya kasa cewa komai, dan shi ba haka ya so ba, Abdul-aziz ya kunshe dariyar sa dan ya fahimci me Abdallah ke nufi. Waziri yana zaga ɗakin ransa yayi mugun ɓaci yace "Har ni Abdallah zai iya share wa saboda ya gama raina ni? Ni ne wai zai kalla ba tare da ya gaishe ni ba?" Hajiya Zainabu ta ɗora "Ina ji gwara kai ma da ni, dan wallahi nikam kallon banza ma yake mun, sometimes kam ma gani nake kamar hararata ma yake yi" Fulani ta Kalle ta tace "Ya kuka yi da masu sharan part ɗin na su?" Tace "Hmm baki san me ba? Cewa suka yi wai babu wanda yake kai musu abinci sai Mahaifiyar su, dan haka ba lallai su samu access da abincin su ba" Fulani tace "Me wuyar ai yanzu Shikenan, tunda har yanzu dukkan su suna gidan". Waziri na tsaye da Yarima Usman sai wani wanda suke aika, suna magana, Waziri yayi sensing kamar da mutum a bayan su, hakan yasa ya ɗan juya, daidai da wanda yake bayan na su jikin zana zai gudu, Waziri yace "Daka ta" Mutumin ya juyo ya zuɓe kasa saboda ba wanda bai san Mugunta Waziri ba ya fara basa hakuri, Waziri ya taka har inda Mutumin yake ya wanke sa da mafi yace "Waya aiko ka?" Ya fara magana cike da shakkar Waziri duk da ya girme sa a shekararu yace "Ka gafarce Ni, nazo wucewa ne sai kuma nagan ku tsaye shine zan koma kai kuma ka juyo" Waziri ya sake ɗauke sa da mari yace "Har zan tambaye ka kace zaka min karya? Ba zaka faɗa min wanda ya aiko ka bane?" Ya fara girgiza masa kai, Wani murmushi ne Yarima Usman yayi yace "Waziri ka daina ba hannun ka wahala a jikin kaskantaccen Mutumin nan, a kira masu horo" ai kuwa nan da nan Mutumin ya ruɗe dan ya san muguntar su, ya fara kuka yana masa magiya, Amma tuni Yarima Usman ya aika a aiko da masu horo, basu ga girman Mutumin nan ba haka suka sa aka miƙe sa aka fara zabga masa sumagiya. Mai martaba ya fito akan zai wuce ciki dan Alwala ya wuce Masallaci, tun daga nesa yaga dukan da ake ma wannan Mutumin, fuskar Mai martaba yayi mugun ja sabar yadda ransa yayi dubu ya ɓaci, dan abu na farko da ya tsana shine yadda ake duka a Masarautar, ganin yadda Mai martaba yake tafiya yasa kowa matsawa gefe, duk sun duka kasa, Mai martaba yana isa wajan, masu horo ganin Mai martaba yasa suka sake wannan Mutumin da sauri, wani kallo ya watsa musu wanda hakan yasa suka zuɓe kasa suna basa hakuri, ya juya yama waziri kallo ɗaya sannan yama Yarima Usman wanda ya dukar da kansa kasa yace "Tuba nake Abbah" Calmly Mai martaba yana kallon Mutumin da ya dukar da kansa hawaye na sauka fuskar sa yace "Tashi ka tafi" Mutumin ya miƙe yana godiya wa Mai martaba, Waziri ya juya yana kallon Mai martaba cike da takaicin irin wato shi bai isa yasa ayi hukuncin nan ba, daga haka Mai martaba ya cigaba da tafiya, waziri ya ja tsuka shima ya bar wajan. Ko sati da zuwan Amira daga US bata yi ba ta haifi ɗan ta Suhail. Bayan wasu kwanaki, har sannan Waziri da tawagar sa sun gagara cin nasara akan Yarima Abdallah da Abdul-aziz, duk yadda suka yi musu barbaɗe da kuma haɗa baki har a ɗakin su masu musu gyara sun zuba amma Jiya iya yau, daga karshe suka canza wajan boka kuma har sannan abu ɗaya ake ciki, ta ɓangaren Mai martaba kuwa ko da wasa bai fasa maganar Abdallah zai hau Mulkin ba, dan a cewar sa Abdul-aziz nada saukin hali toh ba zai iya da wannan Masarautar ba dan gwara Abdallah bayi da sauki ko kaɗan, sannan baya shakkar faɗar gaskiya, hakan yasa su Waziri sake haɗa dantse amma har sannan sun kasa ganin bayan su, har a fura suka sa magani aka kai fada lokacin da Mai martaba yace yana bukatar ganin su Yarima dan za'a tura su training amma Gimbiya Indo ta san yadda tayi ta canza wannan fura da Nonon, wanda hakan yasa suka sha kuma akan idon waziri kuma suka ga ba abin da ya same su. Kamar kullum Gimbiya Indo na zaune tare da Jakadiyar ta, tana shan fruits sannan tana sauraran abin da Jakadiyar ke faɗa mata, ta ajiye Apple ɗin hannun ta tana kallon Jakadiyar tace "Kina ji ko? Wallahi Mutanen nan ba zasu taɓa canzawa ba, duk abin da suke shukawa sai na lallaɓa na ɓata amma Kinga basu daddara ba, at least zuwa yanzu ya kamata su hakura saboda basu ganin Result amma inaa basu ji basu gani" Jakadiyar ta tace "Amma Gimbiya baki tsoron ranan da zasu kama ki?" Ta daga kafaɗa alamar she don't care, tace "Inma suka kama Ni, tun kafin su ɗau mataki zan sanar da Mai martaba, ba shikenan?" Jakadiyar ta ta numfasa tace "Yanzu toh ya zaki yi?" Tace "Naji yau zasu fita cikin dare, saboda wai Mai martaba ya fara ganin fitar sun yana yawa, shine nake son na sa masu saka musu ido dan ina da tabbacin bai wuce wajan boka zasu ba" Jakadiyar ta gyada kai tace "Amma Gimbiya kiyi da hankali saboda ina jin tsoro, musamman wanda zaki sa aiki kar suje suyi yadda za'a gane kamar na wannan Dattijon kwanaki baya can" tayi murmushi tace "Wannan ya saba min aiki kuma ba'a taɓa kama sa ba, dan kowa yana masa kallon wanda hankali bai gama isar sa ba shi yasa basu kama sa" tace "Toh Allah ya bamu Sa'a" tace "Amin". Kamar yadda Gimbiya Indo ta fahimci cewa suna da fita cikin dare hakan kuwa ya faru, dan wajajen sha ɗaya suka fake ido suka fita, tana tsaye a garden tana kallon su amma ba wanda ya lura da ita, daga haka tayi murmushi ta wuce cikin gidan. Bayan sun isa duk suka tsaya suna kallon Bokan da Mamaki, yace "Tabbas basu sha wannan Nono da Furar ba, dole an canza ne ko kuma ba'a sa maganin a ciki ba" suka kalli juna, Fulani tace "Toh yanzu ya zamu yi, fin shekaru muna abu ɗaya yaki ci yaƙi cinye wa" yace "Wannan karan zaku sha mamaki" Hajiya Zainabu tace "Toh ba yadda za'a yi a tura su can duniya inda ba zasu kara tunawa da Masarautar ba ma" ya kalle ta yace "Bari mu duba mugani" ya gama kar kaɗe kar kaɗen sa sai kuma ya Kalle su, yace "Za'a musu kurciya idan har haka ne, amma dole wa Mutum ɗaya za'a yi a cikin su, dan ba zai yi a yiwa dukkan su ba" Fulani da Hajiya Zainabu suka kalli juna, Hajiya Zainabu tace "A yi wa Abdallah tunda shine mara kunyar ko?" Fulani ta girgiza kai tace "Matsala ta dake baki da tunani ne wata sa'in, Idan har aka kora Abdallah definitely Abdul-aziz zai hau kan kujerar Mulkin musamman da ya kasance yana son Mulkin, Amma idan Abdul-aziz ne ya bar Masarautar toh tabbas ba wanda zai matsa ma Abdallah akan lallai sai ya hau kan kujerar" Hajiya Zainabu ta gyaɗa kai cike da gamsuwa, Dan haka suka bada sunan Abdul-aziz. Basu suka koma Masarautar ba sai kusan karfe 4am, hakan ma suna yin ɗarɗar dan kar wani ya gansu suka wuce sashin su. Washe gari, bayan su Yarima sun dawo a sallah La'asar ko abinci basu ci ba yaga Yarima Abdul-aziz dake rike da Suhail a jikin sa Suhaif kuma na gefe yana wasa, ya kalli Abdallah na haɗa kayan sa a box, ya sake baki yana kallon sa, yace "Ban gane ba?" Abdallah yace "What?" Yace "Ban sani ba, naga kana haɗa kayan ka ne a box, kuma nasan ba gidan ka zaka tafi ba tinda Amira na nan tare da Ummi" ya ɗan Kalle sa sai kuma ya tsosa kai yace "kasan me? I'm sorry tafiya ne ta kama ni, so zaka kaini airport please" Abdul-aziz ya harare sa yace "ka nemo mai kai ka ɗan I'm not your driver da zaka na sani aiki ba tare da na shirya ba" Abdallah yayi murmushi dan yasan hakan zata faru yace "Haba mana, please" Abdul-aziz da Suhail ke jikin sa ya miƙe tsaye yace "Dagaske nake, ba inda zan kai ka" zai fita Abdallah yayi saurin tare hanya yace "Me hakan ne wai" a haka dai ya samu yayi convincing ɗin sa har ya yarda, bayan sun fito a part din su za su je ma Ummi da Amira sallama suka haɗu da Gimbiya Indo ta fito zata garden, ta karasa wajan su tana gaishe su, ciki ciki Abdallah ya amsa mata kamar wanda ake masa dole, Abdul-aziz ne ya sake mata fuska suka gaisa. Bayan Abdul-aziz yayi dropping ɗan uwan sa a airport, Abdallah ya rungume ɗan uwan sa haka nan yake ji wani iri a jikin sa kamar wani abu zai same shi ko kuma ɗan uwan na sa, ya kalli Abdul-aziz sai kuma ya ɗauke idon sa yana kallon wani waje yace "Yarima Abdul-aziz ina jin wani iri ko ba zan dawo bane?" Abdul-aziz ya harare sa yace "ban gane ba?" Yayi murmushi yace "idan har ban dawo ba, please ka kulamin da Family na" Abdul-aziz yace "Just pray Amma ba wani abu da zai faru sai Alkhairi" a haka ya rungume ɗan uwan nasa sannan suka rabu.https://wa.me/2347047721483
Ga dama ta samu ina yan çıkın jihar Bauchi state da kewaye muna bada rent din kayan Amare ah farashi mai sauki wannan rayuwar dai kowa yasan ynx lissafi akeyi kiyi rent cikin aminci ba ruwanki da AJIYAR kaya bayan biki 🥰 muna bada rent din duk wani kayan amarya abunda ya fara daga kayan amarya , shoe and bag , bridal luxury beads , saki, Ashooke, Rawsilk, sego dadai sauransu ga number dinmu what’s app or call 07047721483, 07030318069

*AGOLA (Behind the palace walls)*




*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes



Chapter 71

Tun da Yarima Abdul-aziz ya dawo gida yake jin shi kamar mara lafiya hakan yasa ya wuce ɗakin Ummi ya zauna, fitowar Ummi daga bedroom ɗinta ta tsaya kallon sa tace "Lafiyar ka amma?" Ya kirkiri murmushi yace "Lafiya Ummi, kawai dai ina jina kamar mara lafiya ne" ta karasa inda yake ta taɓa jikin sa taji babu zafi tace "Ga jikin naka kuma babu zafi, bari a kira Family Doctor" yace "No Ummi, lafiya na Klau fah" Amira ta fito rike da Suhail, ya miƙe ya karɓe sa yana ma yaron dariya, ta gaishe sa ya amsa daga haka ya wuce sashin su. Washe gari tunda aka yi zama a fada idon Waziri na kan Abdul-aziz, wanda har Mai martaba duk da ba magana yake a fada ba sai da yace "Yarima Lafiya?" Abdul-aziz yace "Abbah bakomai" ya gyaɗa masa kai. Kamar yadda ko da yaushe Suhail na hannu Yarima Abdul-aziz yau ma hakan take, bayan ya dawo daga sallahr Magrib har zai shiga ɗakin sa sai ga wani kurciya tazo ta saman ɗakin sa, ya ɗaga kai yana kallon wannan kurciyan sai kuma ta miƙe ta fara tafiya shima kawai ya fasa shiga ɗakin nasa ya fara bi duk inda wannan kurciyan ke tafiya, wasu daga jakadan da dogaran gidan suna gaishe sa amma bai ma amsa ba hakan ya basu mamaki, kana ganin sa kasan ba lafiya bane, a haka Yarima Abdul-aziz ya bar gidan sarauta tare da Suhail dake hannun sa wanda barin sa Masarautar ta girgiza Mutanen da ke cikin Masarautar da har wanda suke wajan ta dan kowa yasan Yarima Abdul-aziz da saukin hali gashi da taimakon marayu da marasa karfi, Ummi da Amira haukane kadai basu yi ba Sabar tashin hankali, Abdallah kuma babu wanda ya kaishi shiga tashin hankali dan yama gagara rike kansa. Waziri da tawagar sa suna zaune Waziri ya kwashe da wani dariya yace "Yanzu ai sai su nemo sa tunda zasu san inda yake" Sarauniya Zainabu ta ɗaura "Ai sai kunga yadda Uwar tasa ta fice a hayyacin ta kamar wata ƙwarangwal haka ta koma, shi kuma sarakan marasa kunya ido ya rai na fata ai" Fulani tace "Ai har sannan bamu tsare ba dan yanzu wasan zai fara, tass sai mun karasa da su, sannan sai munga bayan su" Yarima Usman dake sauraron su ya numfasa yace "Amma yanzu kuna ganin Mai martaba zai iya bani sarautar?" Wani kallo Waziri ya jefa masa sai kuma bece komai ba, Sarauniya Zainabu tace "Ai dole ma, tunda kaga yanzu nasara ta fara tafiya, kasan komai zai dawo da sauki" ya gyada kai yana murmushi. Gimbiya Indo ta share hawayen ta tana kallon jakadiyar nata tace "Wallahi wannan sharrin su ne, sun samu sun tsalwantar da rayuwar Yarima" ta karasa maganar tana kuka mai tsuma jiki, Jakadiyar ta ita dai sai bata hakuri take dan bata da wani abun da zata iya cewa a halin yanzu. Har wajan wata guda babu Yarima babu labarin sa wanda hakan ya sake gigitar da Masarautar gaba ɗaya...... Granny ta numfasa tana share hawayen fuskan ta wanda yanzu abun yake sake zuwa mata sabo fil, gaba ɗaya parlorn sun girgiza da wannan labarin, a hankali Granny tace "Shikenan tun daga nan kuma bamu sake samu ko da labarin Yarima ba balle kuma shi Suhail dake tare da shi, bayan ɓacewar Yarima sai kuma Yarima Babba ya soma jinya kamar zai mutu wanda duk an cire rai, sai dai da akwai wata rana da Gimbiya Indo ta fadawa Mai martaba abin da
End Ads