kalle ta Zahra tace "Ahtoh gwara ta baki amsa" Leena tace "banda yaya ni, ban ma san shi ba" yarinyar tace "Ikon Allah" ta kalli ƴar uwan ta da mamaki tace "ke baki ga kamar nasu ba?" tace "ai ban ganta ba sai da kikayi magana, wallahi sai ka rantse shine a hijab badan shi ɗin Babba bane" ta kare maganar tana dariya. Dawowan Daddy yayi daidai dana Rayyan, tare suka karasa har sashen su Rayyan, ya zauna akan cushion yace "Yima Maman ku magana" daga haka Rayyan ya shiga mata magana suka fito tare tana kallon sa ta zauna kujeran dake opposite ɗin sa tace "Gani" yayi gyaran murya yace "Dama nace barin sanar Miki anjima in shaa Allah za'a kawo goron tambayar Leena" Mummy da Rayyan har haɗa baki suka yi wajan cewa 'goron Leena? Daddy yace "in shaa Allah" Rayyan ya fara jin kansa na juya masa ɗakin ma gaba ɗaya gani yayi ya masa duhu, haka zalika wajan Mummy wanda har yanzu shock ɗin bai barta ba, ta gagara magana Daddy na kallon Rayyan yace "Anjima zaka je ɗauko su" daga haka Mummy ta tashi ta wuce ciki wanda ko kaɗan ba zata iya faɗin exactly me take ji ba, Rayyan ya dafa kansa da hannu bibbiyu Daddy yace "Lafiya Rayyan? Sai sannan ya ɗaga kansa ya kalli Daddy da jajayan idon sa Daddy yace "Are you Alright?" ya gyaɗa masa kai daga haka ya tashi ya fita a parlorn Daddy ya bishi da kallo, ba inda Rayyan ya tsaya sai part ɗin Hajiya har zai shiga kuma sai ya fasa ya koma part ɗinsu, zai shiga sai yaga Daddy zai fito yaja baya saida Daddy ya fito sannan ya shiga, ɗakin sa ya wuce yana shiga yasa key nan wajan ya tsulale tsabar yadda yake ji garin na juya masa. Bayan Leena sun fito a taxi suka kama hanyar shiga cikin mall ɗin Zahra sai zuba take Leena hankalin ta kwatakwata baya gurun hankalin ta ya tafi can wani duniyar daban tana gaba Zahra na biye da ita a baya a daidai Entrance door Leena taji tayi karo da mutun da sauri taja baya ta ɗaga kanta da niyyar Bama wanda ta bige hakuri, Hakurin nata makalewa yayi daidai lokacin da taji wani bugun zuciya shima hakan ne a gurin sa sun ɗauki some secs a haka suna starring each other, Maganar Zahra ce ya dawo da su daga duniyar shock da suka faɗa tace "Leena are you, Okay" sai sannan Leena ta bashi hanya bata san sanda tace "Sorry" ba, Zahra ta zaro ido dan ganin sa da tayi awajan, shi kuma ya sauka ya ci-gaba da tafiyan sa as gentle as he is. Zahra tace "Mukam Leena ko dai gamo yau muka yi ne?" Leena har sannan tana ɓari tace "Dan Allah mubar maganan nan" Zahra ta taɓe baki, har suka gama sayyayan da za suyi Leena kwatakwata bata da nutsuwa. Mummy da take ta kiran Fatima bata ɗaukawa hakan yasa tayi ji fa da watan nata ta rasa meke mata daɗi a duniyar toh ina ma zata yanzu?, zama tayi a bakin gado tayi nisa a tunanin da take. Ammi da kawarta Zainab ba abinda suka mance basu haɗa musu naci ko na sha ba Zainab tace "Ai kuwa rahama na Ubangiji duk kin ka da mutun Idan Allah ya bashi ba yadda zakayi" Ammi tace "Allah kyauta kawai ya shiryar damu". Daddy ya dinga kiran Rayyan baya ɗauka hakan ya bawa Daddy haushi yana kallon Amininsa yace "Ni Rayyan zai sa naji kunya? taya zan sa driver kaɗai yaje ɗauko su, ai sai su ga kamar ban karrama su ba" Aminin nasa yace "barin kira Farouq idan yana nan kawai sai su tafi tare da naka driver ɗin" daga haka ya fara dialing Numbern ɗan nasa. Mummy dai na zaune inda take tun ɗazu, ringing ɗin wayan ta taji a wajan da ta yar da shi da sauri ta karasa ganin Fatima yasa ta ɗauka ta kai kunne muryan ta na shaking tace "Fatima na mutu na lalace, ke da kika ce min zaki zo har yanzu shiru? Toh wallahi yanzu za'a kawo gaisuwar yarinyar nan" tace "Kiyi hakuri gani nan na kusa karasowa" daga haka ta katse kiran tana share zufan da yake gangaro mata a fuska. Leena na kwance sai waya take da Muhammad, Zahra na gefen ta tana game daga karshe ajiye wayar tayi a gefe tana kallon shagwaba da Leena take zuba masa, Zahra ta gyaɗa mata kai tace "Shegiya kika ce min baki son sa" tayi mata maganar kamar raɗa Leena ta harare ta ta ɗauke kai taci gaba da wayan ta, Hajiya ta doka sallama Ammi da Anty zainab suka amsa ta karasa cikin parlorn tana ma Ammi godiyan kayan daɗin da ta kawo mata, Ammi tace "Wallahi bakomai Hajiya, Hajiya tace "ina Linan take ne wai?" Ammi tace "tana ɗakin ta" daga haka ta wuce ɗakin Leena Hajiya ta sake baki tana kallon Leena, Leena kuma ganin Hajiya yas ta tashi daga kwance da take yi ta cire wayan a kunnen ta tana turo baki Hajiya tace "Eh lalle kam, yaran yanzu Allah ba kunya gare ku ba, mu fa lokacin mu idan aka ce za'a kawo gaisuwar mu toh guduwa muke bamu tsayawa, ko runfa bamu haɗawa da iyayen mu" Leena ta turo maku tace "toh ai ku naga lokacin ku daban muma daban" tana karasa maganar ta wuce toilet da gudu tabar Hajiya baki buɗe Zahra banda dariya ba abinda take yi, Hajiya ta fito parlor tace "Tabbas yau Lina ta faɗa min magana" Anty Zahra ta fara dariya tace "toh ai Hajiya gaskiya ta faɗa" ta karasa maganar tana dariya daga haka Hajiya ta fita tana cewa "ai zaki zo daki na". Motoci da suka amsa motoci kusan goma ajere suka shigo layin su Leena banda motocin securities da suke biye da su, Nan cikin layin suka samu waje sukayi parking karan jiniya ya cika unguwar aminin Daddy ne ya fita har kofar gidan ya shigo da su direct parlorn Daddy wasu daga cikin securities suka sauke akwati set biyu suka shigo da su amma basu shigar ɗakin Daddy ba nan bakin kofar parlorn suka bari, bayan sunyi gaisuwa nan suka fara bayanin game da zuwan su. Fatima ta karasa layin amma ganin motoci sun cika layi ba wajan shiga yasa ta tsaya ta kira Mummy, Mummy da ta tsaya tana leke ta jikin windown dakin ta taji karan kira ta ɗauka da sauri Fatima tace "gani na shigo amma layin naku ba wajan parking fah, me yake faruwa ne a unguwar" Mummy with cracking voice tace "ke de ki bari, wallahi wanda suka kawo gaisuwar yarinyar nan ne, na shiga uku na nikam" Fatima ta gwalo ido tace "tab wallahi wannan ba kananun mutane bane, barin karaso da kafa kawai" daga haka tayi parking. Hajiya dake compound ta sake baki ta koma ciki tana kabbara. Sun so asa bikin nan da 3 weeks Daddy yace "Duba da yadda kuka ce yarinyar ba zata zauna a garin nan ba, kuma kunga tana kan SSCE ne, gashi zata yi saukan Haddah nan da 3 weeks ɗin, gama exams ɗinta ma zai kai wannan lokacin why not asa bikin nan da 5 weeks". Anty Zahra tasa securities ɗin suka karasa da abincin cikin parlorn Daddy. Fatima ta shiga parlorn da sallama Mummy ta fito da sauri Fatima tana kallon Mummy tace "Kambala'iiiii, toh da kyar ace ba ɗan gwamna ƴar nan zata aura ba, Kinga cikin unguwan nan kuwa? Kai kilama shugaban kasa ne" ta karasa magana tana rike haɓa sai kuma tace "Lalle da kyar idan ba abunda nake tunanin bane, chap shiyasa naga Daddyn su Rayyan ɗin ya kuma gƴara gida nan" Mummy tace "Yanzu meye mafita? Wallahi ina faɗa Miki zuciyata kamar zata bugu, na rasa inda zansa raina, Abu ɗaya kawai na sani, da rai na bazan taɓa bari ayi auren nan ba" Fatima tayi dariya tace "Kinsan ko hauka kike baki isa hana wannan auren ba ko? Dan idan kuɗi ne daga gani ba zaki taɓa hada mijin ki da su ba" Mummy tayi shiru Fatima tace "Mafita ɗaya ne, idan har zaki yarda" Mummy tace "idan har za'a fasa I'm ready". Anty Zainab tace "Kai sirbajo aina Leena ta haɗu da wannan mutumin?" Ammi tace "tafiyan ta Abuja yin wannan poem ɗin ne fa ta haɗu da shi acan" Anty zainab tace "Allah mai iko, toh Allah tabbatar mana da Alkhairin sa". Duk suka fito a parlorn kowa da annuri a fuskan sa Har bakin mota Daddy ya raka su, bayan sun jiyo sun kama hanya Aminin Daddy yace "Nima barin tafi ba sai na koma ciki ba" duk yadda Daddy yaso ya dawo ciki amma yaki yace "toh ai Abunda ya kawo mu mun gama" haka Daddy ya kyale sa shima ya juya". Leena da ta fito ɗaukan ruwa tana jikin fridge jin muryan Daddy na magana yasa ta sunkuya da sauri, Daddy na kallon Sirbajo yace "Ku fito sai ku ga kayan, kuyi yadda za'ayi da su". Hajiya ta gwalo ido tana kabbar tace "Tabbas Allah yaga marai cin Lina, ji goro sai kace wanda zamu buɗe Sufamaket?". Dakyar Fatima ta lallaɓa Mummy akan suzo su ga kaya ko da na second ne kar ace suna hassada tunda Daddy da kansa yayi magana. Bayan sun karasa Mummy ta kasa yarda da abinda idon ta ke gani Fatima banda gyada kai ba abin da take yi duk sun kasa magana Hajiya tace "ikon Allah kalli yadda harda akwati set biyu kuma wai duk acikin goron tambaya? Chap ai a wannan marran sai dai ɗan ministan kam? take Mummy da Fatima suka kalli juna Mummy taji kamar ba zata iya tsayuwa ba, take ta juya ta kama hanyar ɗakin ta, ganin garin ma take yana juya mata, Fatima tayi yake tace "Eh lalle yarinya kam tayi goshi" daga haka ta juya itama. Hajiya ta taɓe baki. Sai can Magrib Anty zainab ta tafi, Zahra ma sai kusan Magrib ta tafi Ammi ta bata kuɗin mota ta ɗeba mata snacks ta haɗa mata da turare da sabulu. Bayan Daddy ya dawo daga Magrib yaga be ga Rayyan ba ya shiga parlorn Mummy ya haɗu da Niswa yace "Ina yayan ku?" tace "Bangan sa ba tun ɗazu" ɗakin sa ya karasa ya tura kofan yaji a kulle Mummy da ta fito daga kitchen Daddy ya kale ta yace "ina Rayyan?" tace "Rabo na da shi tun da rana" daga haka ya juya ya fita. Mummy ta zauna nan kujera tayi tagumi ta rasa yadda zata sa ranta taji daɗi da ta tuna Shawarar Fatima sai yaji dama dama Niswa ta kalle ta tace "Mummy baki da lafiya ne?" Mummy ta juya tace "Dan uwar ki ki tashi ki ban waje kafin ranki ya ɓaci" tsimsim Niswa ta tashi, ɗakin su ta wuce taga Nisreen na Assignment, Nisreen tace "Anty Niswa, me yake damun Mummy?" tace "Nima ina zan sani? ba tare muka dawo gidan nan muka same ta haka ba?" daga haka ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Rayyan har ya katse be ɗauka ba ta kuma dialing still ba amsa ta ajiye wayan. Ammi dake kallon Leena tace "Toh me na kukan?" tana share hawayen ta tace "Ammi toh Meyasa za'a sa 5 weeks? Kuma ba'a Kaduna zan zauna ba, Ni kuma Ammi bana son nayi nisa dake?" Ammi tace "Naga a Abujan ma ga Antyn ki Jiddah, ai atleast akwai wanda kika sani kuma naga gasu Sadeeq duk sun ɗauke ki a matsayin kanwa ko bana kusa dake zasu taimake ki idan taimakon kike nema beside ma Allah ba zai sa hakan ma ya faru ba tunda kina addu'a kuma nima ina Miki" ta gyada kai sai kuma tace "Ammi toh maganar 5 weeks ɗin kice a ɗaga asa 1 year" ta karasa maganar tana fashewa da kuka Ammi ta dinga kallon ta sai kuma tace "wallahi abin naki iskanci ne, anan idan har Muhammad be kira ba hankalin ki tashi yake kin dinga kumbure kumbure da duba waya akai akai amma yanzu dan iskanci shine zaki sani a gaba kina min Kuka" wayan Leena dake gefe ne ya fara ringing ta goge Hawayen ta ta jawo wayan dan ganin waye ne ke kiran, ganin Muhammad ne yasa ta tashi ta bar Ammi a wajan Ammi ta sake baki tana kallon ikon Allah. Hajiya da take ta jira shigowar Rayyan ta basa labari har ta gaji, ganin har 11pm yayi tasan ba zai shigo ba daga haka ta kulle kofar ta ta wuce ciki. Muhammad haka ya dinga rarrashin Leena har ta sake tama manta da wani 5weeks suka dinga zuba soyayya har wajan 12am sai sannan Muhammad yace "baby" tace "Uhm" yace "it's already late, ki kwanta kinji?" Leena bata so hakan ba amma sai tace "toh"....
*AGOLA (Behind the palace walls )*🫧
18......
Bayan an idar da Sallah Asuba Daddy be ga Rayyan a masallaci ba yana dawowa gida ya wuce sashin Hajiya ya gaishe ta, sashin Ammi ya wuce bayan ya duba lafiyar su sannan ya wuce sashin Uwar gidan sa bayan sun Gaisa yana kallon ta yace "baki da Lafiya ne?" ta ɗauke idon ta akan sa tace "Lafiya na kalau" ya gyaɗa kai yace "it's okay, yauwa ina Rayyan ne?" Sai sannan Mummy ta tuna da Rayyan ma tace "baku haɗu a matsallaci ba ne?" yace "Ai rabo na da Rayyan tun juya da azahar ban sake sa shi a ido ba" Niswa dake kitchen ta fito tace "Daddy tun jiya nake kiran sa bai ɗauka ba kuma be kirani back ba" Daddy yace "duba min ɗakin sa" Niswa ta karasa kofar Rayyan tayi knocking sannan ta murɗa handle ɗin taji a kulle tace "Daddy ɗakin nasa fa a kulle ya ke" Daddy yayi shiru sai kuma ya ciro wayan sa a aljihun gaban rigar sa yayi dialing numbern Rayyan har ya katse be ɗauka ba ya kuma dialing Rayyan dake fama da kansa ko buɗe ido idan yayi sai yaji kamar kansa zai rabe ya samu dakyar ya iya picking call ɗin, Camly Daddy yace "Ina kake Rayyan?" Rayyan yayi maganar amma baya fitowa sosai Daddy yasa wayan a handsfree yace "Me kace?" da kyar ya iya buɗan baki yace "Ina ɗaki na" ya kare maganar da kyar yake iya sauke numfashi, ba Daddy ba hatta Mummy jin muryan Sultan sai da hankalin su yayi Mummunan tashi Daddy na kallon ta yace "Ba shi da Lafiya ne?" tuni har ta mike tace "Wallahi ban sani ba" Daddy shima ya mike tuni Niswa da hankalin ta ya tashi har ta isa bakin kofar ɗakin sa Daddy ya gwada buɗewa yaji a kulle yace "Rayyan zo ka buɗe kofar mans" Mummy za tayi magana yace "kiyi shiru" sai kusan 2 minutes Sannan Rayyan ya iya daurewa ya sauko da rarrafe ya karasa bakin Kofar ya buɗe sannan ya matsa gefe Mummy kamar zata tura Daddy ta riga sa shiga ihu ta kwala tana rufe bakin ta da hannayen ta tana kallon Rayyan hakan yasa Daddy ya shiga cikin dakin da sauri yana kallon Rayyan daya kwanta nan kasa ya taɓa jikin sa yaji da zafi be ce komai ba ya fita a ɗakin asibitin da Rayyan yake aiki ya kira Mummy ta durkusa kansa Niswa ta fara kuka ta fice a ɗakin ba zata iya juran ganin yayan ta a haka ba Mummy ta ɗago sa ta rungume sa hawaye na sauka fuskar ta tace "Rayyan kashe kanka za kayi da ba zaka sanar mana baka da Lafiya ba?" After some minutes sai ga Ambulance ya karasa gidan some of his colleagues ne suka shigo suka ɗauke shi aka fita da shi Daddy ya shiga nasa mota ya bi su abaya Mummy ta koma cikin gida taji gaskiya ba zata iya zama ba fita tayi ta ɗauki motar ta ta kama hanya itama. Leena ta fito a kitchen ɗin Hajiya tace "toh ai naga kazan kaɗan ya rage ai" Hajiya tace "Kinga ajiye min abuna, ki kira shi Muhammad ɗin sai ya turo Miki wani, dama hakuri kawai zan yi na baki" Leena tace "Toh ai zan yi managing ɗinsa na dafa indomie ne" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace"ki godewa Allah wallahi, daya baki miji ɗan minista saboda ni tunda can nake cewa me rike ki sai Alhaji, addu'a tane ya biki" wayan Hajiya ya fara ringing Hajiya ta ɗauka ta kai kunne daga ɗayan ɓangare Daddy ya sanar mata suna asibiti anyi admitting Rayyan Hajiya tace "ikon Allah dama Rayyan ɗin bai da lafiya ne?" Bayan sun gama waya Leena ta karasa cikin parlorn tana kallon Hajiya tace "Hajiya Yaya ne bai da lafiya? Meya same sa? kuma tun yaushe?" Hajiya tace "kina fah ji yanzu baban ku ya kira Ni yake sanar dani amma ji yadda kike jero min tambayoyi" Leena tayi shiru tana kallon ta Hajiya tace "Allah sarki ashe shiyasa jiya be shigo ya gaishe Ni ba, har ina cewa zan basa labarin wanda suka kawo gaisuwar ki" Leena ta tashi jiki a tsanyaye tace "toh Allah bashi lafiya" Hajiya tace "Amin" daga haka Leena ta koma part ɗin su. Ammi na kallon ta tace "yanzu kazan Hajiyan sai da kika raba ta da ita?" Leena tace "wannan fa gas chicken ne, Ammi" sai kuma ta zauna tana kallon Ammi tace "Ammi ashe ya Rain bashi da Lafiya" Ammi tace "Allah basa lafiya" Leena tace "Ammi an yi admitting ɗinsa fa" Ammi tace "toh" Leena tace "toh kuma Ammi?" Ammi tace "toh nine zan yaye masa ciwon? Ko baki ji nace Allah basa lafiya bane?" Ammi ta kare maganar da ɗan tsawa Leena ta tashi tsimsim ta wuce kitchen. Hajiya ta doka sallama a kofar parlorn su Ammi, Ammi ta amsa Hajiya ta shiga ciki tana kallon Ammi tace "Yau Lina na da makaranta ne?" Ammi tace "A'a yau bata da shi" Hajiya tace "toh ina so tarakani ne asibiti zan kaiwa Riyan breakfast "Ammi tace