hula ta saka, dakin sa ta wuce, tayi knocking sannan ta shiga still yadda ta barsa dazu haka nan yake tace "Amma babe kana lafiya?" ya juya yana kallon ta murmushi ta masa atleast yau ya sauko, tace "Abincin fah is ready" ya nuna mata wajan shi yace "Ki zo za muyi magana ne" da sauri Layla ta karasa tana murmushi, kallon ta yake yi sai kuma yace "I'm begging you Layla, kar ki boye min komai" ta gyada masa kai tace "Wlhi gaskiya zan fada maka, Menene?".
____Yayi shiru yana kallon ta ta marairace masa tace "I'm all ears, please" yace "I don't want you to hide anything from me about what's going on, I know you know about it" ta gyara zama tana masa dirty look tace "Promise me that if I tell you the truth, you'll start loving me" gyada mata kai yayi har sannan tana kallon sa yace "I've made a promise" ta kwanta a jikin sa tana wasa da fingers ɗinta a hankali tace "Everything you heard is true, dan nasan kaji komai" shirun da taji yayi ne yasa ta daga kanta tana kallon sa yace "Layla ki faɗa min duk abin da ban sani ba" ta sauke idon ta kasa dan ita har cikin ranta taji haushin kashe wa Leena aure da suka yi dan ba ta so Rayyan yace zai koma mata a karo na biyu, tayi shiru tana tunani tajiyo muryan sa yace "Layla" ta sake kallon sa yace "Ina jinki" ita fah She didn't bother to reveal their secret, a hankali tace "duk planning ɗin Mummy ne da Mama, duk wani abu da ke faruwa if It's not normal toh definitely suna da hannu" Rayyan yayi shiru da bai cire rai da jin hakan ba, tunawa da Hajiya da ta basa magani yayi, lokaci guda ya tuna lokacin da ko laifin Layla ya daina gani, ya sauke ajiyan zuciya dan tunawa da alkawarin da yama Laylan, ya san zai iya canza ta tunda har tana son sa kuma zata na fada masa duk wani next move din su, ai it's enough hakan kuma, tausayin Leena yake ji da mijin ta har cikin ran sa dan tun day one yaga soyayyar Leena a idon sa, tace "Zauwji" ya kalle ta tace "Dan Allah ka fara so na" yace "ai ina son ki" ta girgiza masa kai tace "Wallahi baka yi" yace "ba wai ke bane bana so, kawai halayyar ki ne bana so, kuma idan na hanaki abu bakya bari" kallon sa take tace "Wallahi ina bari, kuma ai kai ya kamata ka canza Ni" yace "Meyasa kika zubar da ciki?" jin tambayar sa tayi har ƙwaƙwalwar kanta ta sauke kanta da sauri dan bata taɓa expecting zai fahimci hakan ba tunawa da shi likita ne sai kuma jikin ta yayi sanyi tace "ba yin kaina bane, Mummy ce tace zan tsufa da wuri, and I regret my action" Rayyan kallon ta yake ba kiftawa, gani yake kamar kawai mahaifiyar sa haifan sa tayi ba tare da tana son shi ba, yasan son da yake nunawa Leena ya sa aka tsane ta, ganin yanayin Layla yace "Muje kar abinci ya huce" ta sauka daga jikin sa tana jin hawaye na sauka kan kuncin ta, Rayyan ya jawo ta jikin sa yace "C'mon, kuka kuma?" Shi tun lokacin da yake mata wannan kallon ya fahimci hakan amma da ke baya son ta sai yaji abin bai dame sa ba, yana rike da ita suka wuce dinning. Washe gari tun kafin karfe 8am housegirl ɗin Mami da ita kanta Mamin sun gama hada breakfast da zasu kai ma Leena asibiti, harda su kai da ƙafan Sa da suka dafa, Mami ta wuce dakin ta dan yi wanka, bata dau lokaci ba ta fito tana mitan har sannan su Jiddah basu karaso ba, fita tayi a dakin ta wuce dakin Jiddah tana kallon kanwar late husband dinta ta shiga dakin ta zauna tace "Hajiya ko zaki shirya ne kafin yaran su karaso, dan Ni na gama shiryawa" ta mike akan darduman da take ta ninke tace "Toh shikenan barin shiga wanka yanzu" Mami ta fita a daki zata shiga dakin ta sai taji sallamar su Sultan ta koma cikin parlorn bayan sun gaishe ta suna tambayar jikin Sadeeq Mami tace "Ni wallahi gaba ɗaya abin mamaki yake bani, yanzu fah haka kamar ba shi ba ya warke tass, sai dai matsalar sa tunanin da yasa a gaba ne" Jiddah tace "ba dole ba, ai cuta kam an cuce sa wallahi" Sultan yace "amma kinyi magana da shi Mami?" Mami ta girgiza kai kawai, Sultan yace "ya kamata kuwa, saboda maganar da zai fada miki ma kaɗai zai iya healing ɗin sa" Mami tace "Haka ne" daga haka Sultan ya mike yace "barin duba sa" Jiddah ma ta mike ta bi bayan sa, Mami ta sauke ajiyan zuciya ta wuce dakin ta, bayan sun shiga Sadeeq take zaune kan dadduman yana karatun Alqur'ani ya sallame ya ajiye Qur'anin ya ju ya yana kallon su suka gaishe sa suna masa ya jiki a takaice yace "Alhamdulillah" Jiddah yace "amma idan ka warware zaka duba Leenan ko?" Sadeeq yayi murmushin takaici yace "A'a" Jiddah tace "A'a kuma?" kai kawai ya gyada mata ta kalli Sultan da sauri sai kuma ta sake mayar da kallon ta ga Sadeeq da har ya ninke darduman ya koma kan resting chair dake dakin sa, Sultan yace "amma ya kama ta kuwa, atleast ai ɗan ka ne, hakan bai kamata ba" Sadeeq yace "A tunanin ka zan iya sake hada ido da ita ne? When I think that there's no marriage between us now, it really hurts me a lot, wallahi ji nake kamar na ɓace kawai sabar raɗaɗi" Sultan yace "ban gane ba? Kamar ya ba aure tsakanin ku?" Sadeeq ya kalle sa yace "ko baka ji ance ta haihu bane?" yace "Toh hakura zaka yi da ita ko me kake nufi?" ya girgiza kan sa yace "i can still remember yadda na sake ta, tana kuka asking for help Amma ko a jiki na" yayi shiru for some seconds sannan ya cigaba "I don't know what the future holds, but I'm praying for the best" daga Jiddah har Sultan sai da suka ji tausayin sa na ratsa su, duk da cewa ba halin sa bane, Mami ne ta buɗe kofar dakin tace "Toh sai ku fito ko? Ku ake jira" duk suka mike jiki a sanyaye Mami na kallon Sadeeq tace "zaka bukaci wani abu kafin mu dawo?" Ya girgiza mata kai yana kallon Jiddah yace "kiyi min kissing Babyn on my behalf" Jiddah taji kwalla ya taru mata da sauri ta fita dan zata iya fashe wa da kuka Sultan ma duk sai yaji ba daɗi, Mami ta dinga kallon ɗan nata cike da tausayi daga haka ta juya ta bi bayan su Jiddah da har sun fita. Ammi ta dinga kallon Daddy da har sannan yaki ce mata komai, tace "Magana fah nake maka" yace "and so?" ta sake baki tana kallon sa daga haka kawai ta mike ba tare da ta sake kula sa ba, bayan ta isa bakin gate tana kallon gatekeeper tace "Sannu Baba" yace "yauwa Hajiya, kin fito kenan, ya me jiki kuma?" tace "Alhamdulillah" yace "ina wannan mutumin da ya kawo ta ranan?" Ammi tace "wani mutum kuma?" yace "wanda dai ya kawo ta gida ranan, toh kusan kullum sai ya zo wai yana son sanin ya jikin nata Ni kuma nace wallahi ban sani ba amma har sannan baku dawo gida ba" Ammi tace "Ayyah, jiki kam da sauki kawai dai sun rike ta ne saboda aiki da aka mata" yace "Allah kara lafiya" suna magana Mummy tazo fita daga gidan da motar ta ita da Niswa tayi horn mai gadi ya buɗe musu gate Ammi ta matsa gefe har suka fita kuma ba wanda yace mata kala itama bata damu ba kamar a baya idan ba su mata magana ba sai tayi ta damun kan ta, bayan ya rufe gate tace "Dama fah driver nake nema, yayi nisa ne?" Yace ai "tun daya kai Ayaan makaranta ya wuce ɗakin sa yana bacci" Ammi tace "dan yi masa magana mana asibiti zai kai Ni" da sauri mai gadi yayi sashin su don kira mata driver ita kuma ta wuce cikin gida da dauko basket ɗin da ta gama hada musu breakfast tana mamakin Daddy har sannan, yanzu tama daina hawa motar gidan sai dai ta hau motar da akama Leena gift, bayan ta fito ta samu har ya wuce parking space yana warming motar ta karasa wajan ya karɓe kayan hannun ta yasa a bayan motar yana gaishe ta. Bayan sun isa asibitin Jiddah ta ciro wayan ta dan kiran Binta taji suna ta ina amma sai bata ga numbern ta ba tana kallon Mami tace "Mami wallahi banga numbern ta ba, toh ko da me nayi saving Oho" Sultan ya Ciro wayan sa ya kira Rayyan buga daya Rayyan ya dauka bayan sun gaisa yace "Dan Allah ko zaka iya fada mana inda Leena ke kwance?" yace "Okay" bayan ya faɗa masa suka sauka Mami sai sannan ta kara jin nauyin su, duk tafiya suke jiki a sanyaye. Hajiya sai faman banbami take wa Leena, Anty Binta tace "Toh ba zaki ba sa bane?" tana share hawayen ta ta ɗauki babyn Anty Binta na tsaye a kanta, ta lulluɓe jikin ta da Babban veil sannan ta fara breastfeeding Babyn, Hajiya tace "Da ke haka aka miki ai ba zaki ganu ba" bata sake cewa kowa komai ba, knocking ɗin kofar da akayi ne yasa suka juya suna kallon kofar Hajiya tace "a bude yake" Jiddah tayi karfi halin buɗe wa ta shiga da sallama su Mami na biye da su a baya, Leena kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta nan da nan taji hawaye na taruwa a idon ta kamar yadda Hajiya ke kallon su haka anty Binta ma, bayan sun Zazzauna Kanwar mahaifinsu ne ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa a dakile tana kallon wani wajan, suma duk suka gaishe ta amma ba wadda ta sake wa fuska, Anty Binta ta gaishe su suna tambayar ta ya me jiki, a hankali Leena ta gaishe da Mami da Baabar su Sadeeq, Mami ta amsa tana tambayar ta ya jiki, tace da sauki, bayan sun gaisa da su Sultan suma duk ya jikin suka mata, haka nan Leena bata ji dadin reaction din Hajiya ba, Mami kuma tayi farin cikin rashin Ammi da basu yi ba dan ji take kamar ba zata iya haɗa ido da ita ba, Anty Binta ta mike ta karasa wajan Leena, Leena ta gyara jikin ta sannan ta mika mata Baby, ta karba ta kaiwa su Mami, Mami ta dinga kallon fuskan Babyn taji hawaye ya cika mata ido ganin Babyn take yi kamar sanda ta haifi Sadeeq haka sak ya ke shima, ta masa addu'a ta mika wa Sultan shima kallon kyakkyawan fuskan Babyn yake yi, Baabar su ta karba tana addu'a, a hankali Jiddah ta karba itama tana kare wa Babyn kallo, kuma duk babu mai cewa komai, Sultan na kallon Anty Binta yace "An masa hudu ba ne?" Caraf Hajiya ta bada amsa "Toh kai sai aka ce maka ba'ayi ba sai ka yarda?" Ba Leena ba har anty Binta taji ba daɗi Sultan yayi murmushi kawai yace "me sunan Babyn?" kafin anty Binta tayi magana Hajiya ta kuma riga ta "Toh ita dai Linan wai Abubakar za'a kuma saka masa" ta karasa maganar tana tagumi dan ita wannan lamarin na bata mamaki, duk sai da jikin su yayi sanyi jin wai an sawa Babyn Abubakar, Ammi ne ta buɗe kofar dakin da sallama, Mami taji kamar ta nitse, ranan da ta roki Ammi wai a daura auren da ɗan ta Sadeeq wannan scene ɗin ne ya dawo mata sai kuma taji jikin ta ya kara sanyi, Ammi ta gwada kamar ba komai duk da sakin 'ƴarta da akayi ya mata ciwo ba kadan ba, amma ta dake suka gaisa cikin mutunci Ammi ta ajiye musu basket ɗin hannun ta tana kallon Binta tace "ki hada mata breakfast din Binta" Mami ta kalli Jiddah tace "Kinga mun manta namu basket ɗin a mota kawo Babyn kije ki dauko" Mami ta karba tana kare masa kallo ba'a dau lokaci ba sai gata ta dawo, Jiddah ta dinga taba Mami da kafa dan tayi bayani amma Mami tayi kamar bata gane ba, can tana kallon Binta tace "sister Binta ko zamu iya magana?" da sauri Hajiya ta mayar da kallon ta ga Binta tana son kallon reaction din ta, Binta ta mike suka fita a dakin, Jiddah ta mata bayanin duk abinda da ya faru, jikin Binta yayi sanyi har ta kasa magana, bayan sun koma ɗakin asibitin, Mami na kallon Jiddah ta mika wa Anty Binta babyn suka mike suka musu sallama. Bayan fitan su Hajiya tace "ji wani jaraba kuma, sun zo su tayar mata da hankali ne?" Ammi ta sauke ajiyar Zuciya tace "ai dama ya kamata su zo Hajiya, tunda yanzu maganar lafiya ake" Hajiya tace "Toh dama ke me kika sani Hauwa? Ina haka kike ko da yaushe baki canzawa jiya iya yau, shiyasa kishiyar ki ta samu galaba akan ki" Ammi kawai tayi murmushi dan ko Hauwa da Hajiya ta kira tasan ranta ya ɓaci ne, anty Binta tace "Toh ai baku san me Kanwar nasa ta ce min ba" sai kuma ta juya ta kalli Leena dake cin abincin gaban ta a hankali. Bayan kwana biyu, babu irin siyayyan da Mami da yaran ta suka mance ba suyi wa Leena da jaririn ta ba, har hakan ya sa Hajiya ta ɗan sauko, a bangaren Rayyan ma kuwa ba'a barsa a baya ba dan shima ya taka rawar gani ba kadan ba, har sannan kuma Sadeeq ya kasa zuwa ganin Baby duk da kuwa san da yake ya sa Babyn a idon sa, bikin Niswa kuwa saura kwana goma, Mummy kuma har sannan bata zo ko da sau daya ta duba Leena da jiki ba hakan yasa Hajiya kara tsanar ta. Yau tun safe Anty Binta ta mayar da wasu kayan da suke amfani a asibiti gida, dan yau za'a sallame su, bayan Rayyan yayi parking motar sa Layla ta buɗe kofar ta sauka shima saukan yayi, bayan sun shiga dakin da sallama duk suka amsa masa ya gaishe da su Hajiya suka amsa yace "Ammi ina Leenan?" Ammi tace "tana toilet ne" yace "ayyah" Layla ta gaishe da su Hajiya, Hajiya na kallon Rayyan tace "Dama ai yana da kyau kana shigo da ita pamili dan ta san mu, muma mu santa, amma kullum bata shiga cikin mu kamar matar ɓoye" Layla murmushi kawai tayi Ammi ta mika mata Babyn ta karba tana kare masa kallo kawai taji hawaye ya cika mata ido lokacin daya kuma taji son Babyn har cikin zuciyar ta, sai yanzu taji haushin zubar da cikin da ta yi, Anty Binta ta buɗe kofar toilet ta fito Leena na biye da ita a baya, Leena ta gaishe da Rayyan, tana kallon Layla dake kallon Babyn hannun ta with passion tace "Ina wuni" Layla ta kalle ta tace "Lafiya, ya jikin kuma" tace "Alhamdulillah" bayan fitan Rayyan ba'a dau lokaci sosai ba sai gashi ya dawo yana kallon Ammi yace "An sallame ta yanzu". Bayan yayi parking motar a kofar gidan su duk suka sauka har sannan Layla na rike da Babyn Anty Binta ta so karba amma Ammi ganin yadda Laylan take makale da Babyn yasa tace a bar mata kawai, bayan sun shiga compound ɗin, Niswa data fito daga sashin Daddy ta sake baki tana kallon su da mamaki, har parlorn Ammi suka karasa, Ammi tace "Layla ko a baki Babyn ne?" Murmushi kawai tayi, Ammi tace "Allah baki ke ma" a hankali tace "Amin" Hajiya ta mike ta wuce zuwa sashin ta, Rayyan ya mike yana ganin Leena yace "ki dai tabbatar kina shan magani" a hankali tace "Tohm, Nagode" ya mike ya fita. Niswa na shiga parlorn bata ga Mummy ba ta wuce dakin ta ta buɗe, da sauri Mummy dake rike da wani abu a hannun ta ta mayar da hannun nata baya tana son ganin wanene tace "Sai ki shigo min dakin ba sallama?" Niswa tace "Mummy kin san me na gani yanzu?" Mummy tace "Meya faru?" tace "Wallahi Ya Rayyan da Layla na gani suna raka su Leena sashin su,