x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - AGOLA free pages

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 196927 words
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

HAUWA JIBRIN SULAIMAN (Jiddatul-khayr writes)
Assalamu Alaikum! Mutanen Arziki!

A warm welcome back to my page! After a long hiatus, wallahi nayi missing dinku, well, I'm thrilled to return with a new story that I've been eager to share with you. Introducing "Agola Behind the Palace Walls," Book 1 of a compelling series.

Wannan lokacin! This time around, I'm excited to share my story in three languages: Hausa, English, and Arabic.

I trust that my avid readers will enjoy this story as much as my previous ones. Please dive in, read, and share your thoughtssssss.

Amma kunsan ina kwadayin feedback? Sure! Your feedback and votes mean everything to me. I hope you'll support me on this journey!

Any highlights of mistakes are most welcome - don't hesitate to message me. Thank youuu!"

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_By Jiddatul-khayr_


~Book 1~
Prologue
Alhamdu Lillah
Hello everyone, as you may know, I'm Leena Abbah, a young climate change advocate, so today I'd like to talk about.... Wafce wayan akayi da sauri Leena ta juya tana kallon Ammin ta with a frown face, Ammi tace "Waya ta ce abun wasan ki ko Leena? ba dama na ajiye waya sai kin dauka kin cika min waya with unnecessary pics and vids, right?" Leena says, "Mummy, these aren't unnecessary pictures and videos. Check out, they're meaningful" kawai ta fashe da kuka Abba ne ya fito daga dakin sa kafin yace komai Leena ta tashi taje da gudu ta fada jikin sa, he's patting her back comfortingly while looking at Ammi yace "Ammi yanzu Kuma me maman tawa ta miki dan Allah? Ke ko tausayin ta baki ji sai kiyi ta sata kuka?" Ammi tace "Bata da aiki sai daukan min waya tana wasa dashi" Leena tace "Abbah, ba wasa ba fah nake yi dashi I want to share something important with everyone" Abbah ya kama hannunta ya jata zuwa kan kujera, Ammi tace "Ai ga Abban naki sai ya baki nasa ai, danni banda lokacin ku" Abbah yace "tace message take son sharing muga video din" Ammi tace "Tuni na goge ai" Leena tasa ihu ta fara kuka tuni Ammi ta fice daga parlorn dakyar Abbah ya lallashe ta ya bata nashi wayar. The next day, Ammi na bakin murhu tana fifita wutan gawayin da yaki kamawa, ganin wutan ya ɗan fara kamawa yasa ta daura ruwan zafi da zata ma Leena wanka, Leena na kwance a daki tana rubutun waken baka a diary dinta Ammi ta ke leko tace "Leena har yanzu baki tashi kinyi brush din ba? Leena ta tashi da sauri tace "yanzu zanyi" Ammi tace "Let me repeat myself again zaki sha mamaki" daga haka ta koma wajen murhun ta ganin ko ruwan ya danyi zafi, Ammi na fita Leena ta wuce toilet din dakin ta brush tayi kamar yadda Ammi tayi instructing dinta, Ammi ta juye ruwan acikin wani bucket ta wuce da shi cikin gida da niyyar yima Leena wanka, karo ta kusan ci da Abbah da ya fito ganin ko ta gama shirya Leena, ta ja baya da sauri tace "I'm sorry ai ban ganka ba" yace "kin gama kuwa?" Yana magana yana duba agogon dake makale a jikin bango Ammi tace "Haba Abbah kasan fa yau mun makkara yanzu zan mata wanka sai inje na karasa abun breakfast din" yace "Okay, I think zan fita naje na tsiyo mata ko da bread da madara ne, sai ki hada mata tea kar tayi latti ne" Ammi ta tsaya sakake tana kallon Abbah tace "Haba Abu Leena, da wani kudin kuma zaka tsiyan mata? Ba gwara ka tsiya mana kayan miya ba?" yace "Yanzu ma bata lokaci muke kar yarinya ta makkara" yana gama fadan haka ya wuce ya fita ita kuma ta wuce ciki ta samu already Leena ta cire sleeping dress dinta tace "Biyo NI" tana gama mata wanka ta sa mata uniform, already Abbah har ya dawo ya hada mata tea suna fitowa suka gansa zaune yana fifita mata da gudu Leena taje ta fada jikin sa tana dariya tace "Good morning Abbah na" shafa kanta yayi yace "Morning my little Angel, hope you had a restful night?" ta girgiza masa kai tana murmushi yace "why?" Tace "because I slept late last night, ina ta karatu ne Abbah" yace "Okay, have your breakfast, and hurry up! You're going to be late" tace "Okay" tuni Ammi tayi fi cewar ta, ta koma kan girkin ta, tana cikin je fa ɗanwake sai ga Abbah ya fito rike da hannun Leena yace "Sirbajo mun tafi" tace "Adawo lafiya" Leena taje tayi kissing Ammi tace "Bye Ammi" Ammi tace "Ayi karatu lafiya, okay dear?" Leena tace "Okay Ammi na", Leena na murmushi ta karasa inda Abban ta yake ya tada machine din sa, sannan ya daura ta akai sai suka fita. Da yamma bayan Abbah ya dauko Leena daga islamiyya da gudu ta shiga parlor Ammi ta daka mata tsawa tace "Nace miki ki daina wannan guje gujen naki times without number Amma bakiji ko?" Abbah da ya shigo ya  kama hannun Leena yace "Haba Sirbajo, ke idan ba kiga kin sa ƴarnan kuka ba ba kijin dadi ne, Haba mana" Ammi tace "Gudun da take yi ne banso idan ta fadi taji ciwo kuma fa?" Abba yace "hakan ma ba zai faru ba" Leena ta cire hannun ta ana Abbah taje ta zauna a gefen Ammi tace "I'm sorry Ammi, I promise not to do it again kinji? Toh ki daina fushi dani" Ammi ta jawo ta jikinta tace "I know you're a good girl kuma ba zaki kara ba, so yanzu tashi muje in miki waka sai Abbah ki ya kaiki gidan Mami" juyawa tayi taga Abban ta na kallon su With so much love and adoration itama murmushin tayi Ammi ta kama hannunta suka wuce dakin ta. Bayan ta shirya ta fito da kayan ta a hannun Ammi, Ammi na kallon Abbah tace "Abban Leena gashi na shirya ta kar kuyi magrib ne a hanya" Abba yace haka ne kuma, ya karba jakkan dake hannun Ammi, Ammi tace "ku gaishe min da Mami, da su Nyaama, Babaajo" ta gyaɗa kai tana murmushin Abbah ya kama hannunta suka fita. Wani Babban gida dake unguwar kinkinau suka isa, kana ganin gidan kasan ba karamin gida bane suna isa kofar gidan mai gadin gidan ya leko ganin su ya fara murmushi yana buɗe musu gate din tun kafin Abbah ya karasa packing din machine dinsa Leena ke kokarin sauka sai da mai gadin gidan yaje da sauri ya sauke ta kana ganin ta kasan tana cikin murna tace "Babaajo I miss you so much, it's been almost a month since we saw each other" ya kai mata duka da wasa yace "idan ba zaka daina min wannan yaren ka ɗin ba to karka sake min magana" yayi magana with his fulani accent Leena ta kwashe da dariya tace "Toh ai Ni bana miji bane" ganin Abbah ya karasa packing dinsa ya maida hankali sa gunsa Abbah ya gashe sa da ladabi ya amsa yana tambayar sa Ammi, Abba yace "tana lafiya tace agaishe ku ma" yace "Ayyah muna amsawa" daga haka Abbah ya wuce cikin main gidan,  Matar me gadin ne ta leko tana cewa "Me gidan kamar Muryar lina nake jiyowa" da gudu Leena taje ta rungume ta tace "Nyaama nayi missing dinku". Abbah daya shiga cikin gidan ya samu Mami a parlorn gidan tana yankawa Alhaji fruit da ladabi ya gaishe ta itama ta amsa masa cikin kulawa yace "Mami ya jikin Alhajin!" tace "yanzu dai da sauki, Alhamdulillah" yace "Allah kara masa lafiya" tace "Amin" tace "ina Leena din?" yace "ta tsaya wajan su Baabajo" Mami tayi murmushi tace "tohm tashi ka shiga ka duba shi" Abbah ya mike yayi dakin Alhaji, Mami ta kira me aikin ta tace ta dauka kayan Leena da Abbah ya shigo da shi ta kai mata dakin ta. bayan Abbah ya fito yace ma Babaajo "Baba barin gaisa da Mama" Babaajo yace "toh barin mishi magana" daga haka Babaajo ya leka ɗan kurkurin dakin su yace "Ka fito yaron can zai gaishe ka" Nyaama ta yafa gyallen ta suka fito tare da Leena bayan sun gaisa Leena tace "Abban Bye bye" Abbah yace "be a good girl, okay?" ta gyaɗa masa kanta sannan tayi cikin gidan da gudu tana shiga parlorn taga Mami a parlor da gudu taje tayi hugging dinta Mami tace "Lalalala kyaryani zakiyi Leena?" Leena na dariya tace "i just miss you ne Mami naa. Bayan some months, Leena da gaba daya tunda taji Abban ta zaiyi tafiya jikin ta ya mutu tana kallon Abbahn nata tace "Abbah na dan Allah kar kayi tafiyan nan, bana son ka tafi ka barni kaji? Abbah na kallon ta yana murmushi yace "In shaa Allah, bazan daɗe ba kinji? Aiki na samu zanje interview, Kinga sai in mayar dake makaranta mai tsada kije kiyi ta debate ko" tace "amma nikam inajin dadin yanda muke hakama Abbah" Ammi tace "dare yayi, tashi na kaiki daki ki kwanta" a haka Ammi ta kaita ta mata addu'a sannan ta kashe mata wuta ta fito, wannan daren Leena ta gagara bacci sai daga karshe bacci ya dauke ta nan ma ta rinƙa mafarkai marasa dadi. Da safe bayan Abbah ya gama shirin tafiya Leena ta ringa kuka wai karya tafi ya kamo hannunta yace "Leena is just because of you zan tafi, inason na cika miki burin ki, ko dagaske baki so zama Climate change dinne?" tace "Abbah na fasa yanzu idan har ba zaka tafi ba" Ammi ma da jikin ta yayi sanyi ta kamo hannunta tace "just pray for your daddy, okay?" ta gyaɗa kanta Abbah ya shafa kanta yace "Allah Ubangiji ga iyale na, ka kare min su kada ka bari su shiga kunci, ka daukaka min Leena ka cika mata burin ta" ba wanda ya iya cewa Ammi suka raka sa bakin kofa suna mai masa addu'a Leena na masa bye bye ,ya tare mai adaidai ta ya shiga. Ammi bata taɓa shiga cikin tashin hankali ba kamar yadda ta shiga yanzu, dukda Leena yarinya ce Amma hakan bashi ya hanata fahimtar sakon da aka isar Musu ba.



Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧

~Book 1~
Chapter 1

Alhamdu Lillah

Wani Babban layi ne dake unguwar Rimi low cost, duk gidajen da ke layin babu mai karamar gida, gidaje ne nagani na fada wanda sai ka ɗauka ba'a cikin garin Kaduna kake ba Abuja ne, wani Babban gida ne a farkon layin wanda fadan kyansa da tsaruwan sa bata lokaci ne, wani babban mota ne ya shigo street din daidai wannan kofan gidan ya tsaya yana horn mai gadi nake ban daki da sauri ya fito dan muɗe gate din yana buɗe wa motar ta shiga cikin gidan tayi parking, ashe kyan gidan bakomai bane ta waje, Babban gida ne mai Apartment biyu dake kallon juna sai kuma wani part dake tsakiyar su amma ta baya yake, motar da tayi parking ne yaran cikin suka bude motar suka sauka driver ya bude bayan motar kowa ta cire lunch box dinta da school bag, biyu daga cikin ƴan matan suka wuce part din da ke hannun hagu dayan yarinyar kuma ta wuce na hannun dama da gudunta, kofar parlorn ta buɗe ta shiga ciki with a smile on her face ta wuce dakin maman ta tana cewa "Mummy, you girl is back" ta murɗa kofar taji a kulle she frowned, ta wuce kitchen tana cewa "Mummy, where are you?" Nanma taga shima a kulle Her face scrunched up in a frown, and tears started streaming down her cheeks, Nan bakin kofar kitchen din ta zauna tana ta sheshsheka, yunwa kuma take ji sosai, dakin ta ta wuce hoping shi ba'a kulle yake ba, tana buɗe wa taga a buɗe yake ta shiga ciki ta cire uniform dinta, zata aje school bag dinta ta hango an ajiye mata gongonin madara ga sugar cube, ga lots of cornflakes sannan ga Golden morn, haka yasa ta fahimci kila Ammin ta tayi tafiye ne ta barta tace "Ammi, why do you travel and leave me here alone?" kuka ta ringa yi daga karshe ta tashi ta wuce karamin part din, da sallama ta shiga parlorn taga Hajiya na zaune tana cin abinci tace "Hajiya , where's my Mummy?" Hajiya tace "A'a ni idan ba zaki min hausa yanda zan gane ba toh kiyi ta kanki" zaman dirshen tayi a gaban Hajiya tace "toh ina mamana?" tace "Eh lalle kam, kamar maman taki bata koya miki sallama da gaisuwa ba ko? Sai karyan yaran da ba naki ba gaki ƴar gold" kamar zata yi kuka tace "toh ai na manta ne" Hajiya tace "Sarai dama ƴar nan kina jin Hausa sai karyar baki ji" Leena da ta gaji da jin surutun Hajiya kawai ta ja bakin ta tayi shiru sai kuma ta fara kuka Hajiya tace "dan Allah karki cika min kunne ki kurman tar dani, tho Ammin ki dai tafiya Niger tayi anyi musu rasuwa" tace "Tace miki ranan da zata zo?" tace "kinga ni kar kizo nan kin takura Ni" Leena tace "toh ni yunwa fa nake ji" tace "tashi kije dakin su mama riyan a zuba miki" Leena ta kyaɓa baki tace "bayan kin san ko naje sai dai Mummy ta dake ni amma baza ta ban ba ai" Hajiya tace "ton ga can raguwar nawa ki dauko na zuba miki" ta wuce kitchen ta dauko kwano sannan ta kawo kular wa Hajiya, Hajiya ta buɗe ta zuba mata Leena sai kallon ta take yi Hajiya ta mika mata tace gashi" Leena tace "Toh, ai baki sa min nama ba, kuma bana cin abinci sai da Nama" Hajiya ta rike haba tace "iyyeee, Lalle ƴar nan Ammin ki ta koya miki mugun hali, wato ɗan naman da aka samin kika sawa ido ko?" Hajiya na mita ta saka mata nama yanka daya ta koma gefe tacin abincin ta, Sallama akayi duk suka daga kai suna kallon kofar Rayyan ne ya shigo Leena na murmushi tace "Welcome back ya Rain" yace "Little angel" kamar zata yi kuka tace, "ya Rain you see, My mom went on a trip and left me here alone" Rayyan yace "You are not here alone, I'm here with you, okay?" Leena ta gyaɗa masa kai sannan ya sauka akan cushion ya hau kan carpet sannan ya gaishe da Hajiya da ta suke fuska tace "ai na zata wajan ta kawai ka zo riyan" yana murmushi ya bata hakuri amma dake Hajiya tasan riyan nata ne, na tsiyo mata kayan kwalaman yasa tace "toh yana iya da kai, ai ba'a shiga sakanin jika da kaka" Leena ne ta tashi zata mayar da sauran abincin da ta rage kitchen Hajiya tace "kai ƴarnan akwai ki da barna kin san ba zaki gama bane kika sa na juye miki abincin harda nama na" ta karasa maganar tana me rike haɓa ta juya tana kallon Rayyan tace "Riyan kana jina ko? Ƴar nan haka wai ita bata cin abinci sai da nama haka tasa na juye mata shine kuma yanzu zata wani rage min sauran abinci" tana karasa magana Leena na fitowa a kitchen Rayyan yace "sai hakuri Hajiya Leena yarinya ce" tace
End Ads