x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 177

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Ta miƙe tare da ficewa daga room ɗin tana ƙoƙarin goge hawayen fuskar ta....



Nasreen da Tasleem ne suke zaune a bakin gado sun jeru kamar masu karɓan gaisuwa, a hankali Nasreen take motsa lips ɗin ta tana yiwa Tasleem nasiha akan ƙin bin umarnin mahaifiyarsu,

"Tasleem kin san uwa uwace koda ita ɗin mahaukaciya ce balle mun samu uwa jajirtacciya kuma mai kula akan ƴaƴanta, tana matuƙar ƙaunar mu meyasa baza mu bi umarnin ta ba? meyasa baza mu mata biyayya a matsayinta na uwa ba? mu kaɗai ta haifa ƴan uku babu namiji a saman mu da ƙasan mu, mai yasa baza mu zamo mata jajirtattun jaruman triplets ba...."

Tasleem lumshe ido tayi tare da faɗin "please it's okay! shin a yanzu bama mata biyayya ne ko bama bin umarnin ta?..."

Nasreen ta ce "bakya tsoron ta sannan bakya bin umarnin ta..."

Tasleem murmushi ta sau idonta na kallon gefe guda ta ce "meyasa kika yi wannan tunani akaina ?..."

Nasreen ta ce "abinda ya faru yau ke da Mommy, a gaban baƙon ta kika rufe ido kamar ba mahaifiyar ki ba, kina sa'in sa da ita akan abinda bai kai ya kawo ba, just ki durƙusa ki gaishe da baƙon ta shine problem haba Tasleem, ana sara ana duba bakin Gatari mana, mata mai mutunci mai daraja mai kima a idon kowa amma ta kasa samun wannan darajar da mutunci a idonki, I think ko wani kika ga yana cin mutuncin mahaifiyar ki sai yanda ƙarfin ki ya ƙare balle ke da kan ki..."

Wani irin tsawa Tasleem ta dararawa Nasreen har sai da Nasreen ta toshe kunnuwanta, haka Tasleem ta miƙe tsaye tana faɗin "ke kin kasa fahimtata shin waye zai fahimci halin da nake ciki? waye zan gaya wa damuwata? duk babu domin kuma bakin ku ɗaya da mahaifiyata wacce ta kasa bamu lokacin ta, muhawara, shawara, damuwa duk mun kasa sanar mata saboda tsoron da ta dasa wa zuciyoyin mu, gani take idan ta zauna da mu tasan matsalolin mu zata cutu ne, har yau mommy bata taɓa yi mun abinda nake so ba taya itama zata samu abinda take so a wurina? Nasreen babu wacce zata fahimci halin da nake ciki, akwai wani sirri a jikina wanda idan mungu ya raɓe ni ƙiyayyarsa ta zaunu kenan a cikin zuciya ta, ina jin ƙamshin mungu a ko ina yake, duk wanda yake cikin ƙungiyar mugunta zan sa ni idan na kalli cikin ƙwayar idanuwansa, Allah ya bani baiwar gano haka wanda babu tsafin da zai kawar mun da wannan baiwar da Allah ya bani, mommy tana daga cikin mungwayen faɗin duniya domin naji hakan a jikina..."

A ruɗe Nasreen ta miƙe tsaye tana faɗin "Tasleem ki dakata haka, shin kin taɓa ganin ta aikata wani abinda ba dai dai ba?..."

Tasleem ta ce "ko ban gani ba amma naji hakan a jikina..."

A tsawa ce Nasreen ta ce "Zancen banza kawai..."
tana kuka tana girgiza kai ganin bata da ta cewa ne yasa ta fice daga ɗakin,
Tasleem bin bakin ƙofar tayi da kallo tana mamakin kanta yanda take jin wasu abubuwa a jikin ta, ta kasa yadda da abinda take ji akan mahaifiyar ta amma wasu lokuta takan yadda da haka, haka take ta wannan tunanin har ta nemi wuri ta zauna...

Nasreen bayan fitar ta a falo ta tsaya sai kai kawo take ta kasa samun nutsuwa, maganganun Tasleem ne suke yawo mata a kai, bata taɓa tunanin Tasleem tana da ƙwarin gwiwar da zata furta waɗannan maganganu, tana cikin wannan halin taji an da fa kafaɗarta, a zabure Nasreen ta juyo tana kallon wacce take bayan ta, idonta akan Madam Nablah ta ce "Mom daman ke ce?..."

Madam Nablah murmushi ta sau tare da faɗin "maganar zucin mai kike?..."

Nasreen ta ce "Mom ba komai..."

"Kin tabbata?..."
A cewar Madam Nablah..
Jinjina kai Nasreen tayi alamar eh.

Madam Nablah ta ce "zuwa nan da anjuma kaɗan ku je supermarket ku zazzaɓi kayan da zaku yi hidimar shagalin bikin ku, kayan ɗaurin Aure kuma nasa ayi mun ordersu daga can London da kayan furnitures..."

Nasreen cikin rashin fahimta ta ce "Mom wani irin kaya zamu zaɓo bayan kayan sakawa da furnitures, kuma naji kina maganar biki tin yanzu shin yaushe ne?..."

"Sai na nema wa Tasleem abokin haɗi kafin na yanke rana...." a cewar Madam Nablah, sannan ta nufi waje tana faɗin "zan fita saina dawo..."

Nasreen a hankali take lumshe idanuwanta domin jin maganar take kamar a cikin mafarki...

Juyawar da zata yi kwatsam ta tarar da Abeesh yana sauƙo wa daga saman upstairs kan sa a ƙasi, itama ganin sa yasa tayi saurin juya bayanta tana ƙarƙame da idonta, domin yanzu ba ƙaramin kunyar sa take ba,
tsaya wa ya yi ata bayanta yana so yayi magana amma yana tunanin shin wacece a cikin su,
A hankali ya furta "My Juju?..." (Tasleem)

A hankali ta girgiza kai alamar ba ita bace still bata juyo ba, ya kuma cewa "my Sis?..." (Asmeen)

Ta sake girgiza kai alamar a'a.

Murmushi ya sau domin shima tin tinin ya gane Nasreen ce tin sauƙowar sa, domin ko wacce ya karanci halayen ta, ɗaukar takarda da biro ya yi bayan ya gama rubutun sa ya ajiye akan table ɗin falo sannan ya wuce ta gefenta idonsa akan kyakkyawar fuskar ta ga idonta a lumshe bata son haɗa ido da shi, shima kuma hakane yana jin nauyin ta haka ya fice daga falon daman wurin aiki zai tafi, Nasreen tana jin ya ta da mota sai a lokacin ta buɗe eyes ɗin ta tana sakin nannauyar numfashi, ta juya kenam idonta ya sauƙa akan takardar da yayi rubutu a ciki, sai da ta ɗau tsawon mintuna kafin tasa hannu ta ɗauki letter tare da buɗe wa, abinda ta fara karantawa shine rubutun saman takardar

"Amincin Allah ya ƙara tabbata ga wannan baiwar Allah mai ɗauke da kyakkyawar murmushi akan fuskar ta, ina fatan kin tashi cikin wadataccen lafiya,
Dokar hana kaimun abinci sai ke ya fara aiki yau, amma baki kai mun ba kin bar ni da yunwa Allah yasa kar murmushin fuskar ki ta ɗauke wuta akaina saboda wannan dalilin, bazan taɓa ƙin ki ba sarauniya amma ban san taki zuciyar ba, idan har kin amince da ni ina mai baki haƙuri akan cewa ban iya soyayya ba, sannan tsoron soyayya nake,
Bissalam...."

Bayan Nasreen ta kammala karantawa tsabar farin ciki bata san lokacin da ta hau saman kujera ta faɗo ƙasin carpet ba, ta rungumi letter akan ƙirjinta sosai tana hamdala, haka ta rufe idanuwanta sosai tana jero addu'o'in farin ciki da warkewar zuciya, cikin farin ciki ta fara buɗe eyes ɗin ta ganin Asmeen a tsaye ta zuba mata ido ne yasa Nasreen miƙe wa ta nufi wurin ta tana faɗin "Asmeen sai yanzu kika dawo? kodai ansha ruwan soyayya ne..."

Asmeen itama murmushi tasau tare da faɗin "ina taya ki murnar samun abinda kike so ƴar uwa..."
tasa hannu ta rungume ta, Asmeen hawaye ne kawai suke zubo mata na baƙin cikin halin da ta tsinci kanta na rashin dace da masoyin gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah..."

Nasreen jin kukan Asmeen ne yasa ta ɗago da ita tana faɗin "lafiya kuwa Asmeen? meya faru dake? dan Allah ki sanar mun Please..."

Nasreen itama hawaye ne suka cicciko mata ganin a halin da ƴar uwar ta take ciki ga kuma idanuwanta sun yi jawur tsabar kukan da tasha kafin ta bar part ɗin Shaprees....

Asmeen ganin yanda Nasreen ta ruɗe lokaci guda yasa ta wayince tana murmushin ya ƙe ta ce "No no no please my Sister..."

Nasreen ta ce "to meyasa kike kuka?..."

Asmeen tana murmushi ta juyar da harshe yaren su tana faɗin
"Meri pati mere liye bohot pyaar karta Hai, aur main bhi use apne dil ki dhadkan se pyaar karti hoon...."

Nasreen cikin kuka ta ce "idan har hakane meyasa kike kuka? ni ban yarda da ke ba..."

Asmeen riƙe hannunta tayi ta ce "Nahe! Nahe!! Nahe!!! Kukan farin ciki nake..."

Itama Nasreen murmushi ta sau tare da ƙara rungumar juna cikin kulawa...


The Soldier Amaar Junaid: yana zaune a ƙerarren gidan wanda ya mallaka bayan dawowar sa daga ƙasar Bangladesh country in south Asia, Sojan ƙasar Bangladesh bayan ɓatar da shi da akayi a cikin ruwa tsawon shekaru Ashirin, ba tare da sanin yanda iyayensa suke ba.

Takaitaccen tarihin Amaar Junaid.
Shi ɗin ɗan nan ƙasar Nigeria ne ɗan haifaffen garin Maiduguri, su biyu iyayen su suka haifa shine babban ɗa a wurin iyayen sa sai ƙaninsa mai suna Abeesh wanda mahaifiyar su ta rasu a haihuwar Abeesh, tin daga lokacin mahaifinsu ya cigaba da kula da su, duk wata tarbiyya da ilimin boko da Islam sun samu a wurin mahaifinsu,
Akwai wani ƙanin mahaifinsu Amaar wato Alhaji Ahmed Tajiddeen ya buƙaci a bashi ƙaramin yaron Yayansa wato Abeesh kasancewa shine ƙarami, zai fi samun kulawa a hannun mace wacce zata zamo masa tamkar Uwa, daga lokacin Alhaji Ahmed ya damƙawa matar sa Madam Nablah Abeesh a hannunta domin a lokacin bata samu haihuwa ba, kuma Madam Nablah a lokacin mutumiyar kirki ce ga sanin darajar mutane, ita ta cigaba da kula da Abeesh ta mayar shi tamkar ita ta haife shi, shi kuma Amaar baya buƙatar zama a wurin kowa sai a gun mahaifinsa amma yakan je gidan da ƙaninsa yake kullum domin dubo shi, mahaifinsu kuma bai ƙara Aure ba haka yake zaune....

Bayan wasu ƴan shekaru itama Madam Nablah Allah ya azurtata da samun yara mata ƴan uku tin daga lokacin aka rasa tunanin Madam Nablah, ƙwaƙwalwarta ta sauya zuwa munguwar ƙwaƙwalwar da bata tunanin komai sai na cutarwa, ta faɗa cikin wani ƙungiyar da bata san da zaman sa ba, ganinta kawai tayi a ciki anan aka bata umarnin ta kawo jinin mijinta idan har tana son ta zama sarauniyar gagara duniya, hakan kuwa akayi sai jin labarin mutuwar mijinta akayi lokaci guda, Mahaifinsu Amaar kuwa bayan ya fahimci halin da ake ciki ya buƙaci ɗan sa Abeesh amma Madam Nablah fur ta ƙi amince wa daga ƙarshe ma ɓoye Abeesh tayi yanda ba wanda zai ƙara ganinsa...

Amaar Junaid ya kasance mai matuƙar ƙaunar ƙaramin ƙaninsa Abeesh, daga lokacin shima ya daina ganin Abeesh, ya damu sosai amma sai dai akwai wacce take ɗebe masa kewa,
Ɗiyar ƙanin mahaifinsu wato ɗaya daga cikin triplets, sun yi matuƙar shaƙuwa sosai, triplets tin suna yara ba'a iya banbance su amma Amaar Junaid yana iya gane gwanar sa wato Tasleem, a makaranta basa rabuwa haka a gida, a baya yana yawan zuwa gidan Madam Nablah saboda ƙaninsa Abeesh yanzu kuma da ya daina ganinsa sai yake zuwa saboda Tasleem, duk wannan shaƙuwar da suka yi akan idon Madam Nablah suke, kwata kwata bata jin Amaar a ranta tin daga lokacin da wannan matsalar ya faru da ita taji an dasa mata ƙiyayyar Amaar, ta tsane shi sosai ji take kamar ta kashe shi, idan Madam Nablah taji tana son aiwatar da abu a ranta takan aiwatar da shi ne cikin sauƙi ba tare da ta takura kanta ba...

Wata rana Amaar yana gidan Madam Nablah yana wasa a filin ball dake other site shi da Tasleem,
A lokacin Amaar yana shekara 10 ita kuma Tasleem ko wacce tanada shekara biyar biyar a duniya,
Su na cikin wasan su sai ga Madam Nablah a filin wasan, dai dai lokacin da Amaar ya wurgo wa Tasleem ball a lokacin Madam Nablah ta cabke tana masa wani irin kallo na ƙiyayya,
Tasleem ce ta tsaya a gaban ta tana faɗin "Mom ki bamu kwallon mana..."

Amaar yana dariya ya ce "A'a Tasleem itama Mommy tana so zata yi wasa damu..."

Idon Tasleem akan fuskar Madam Nablah ta ce "Mom meyasa kike fushi to kuma idonki akan Amaar ɗina..."

Madam Nablah sakin murmushin yaƙe tayi sannan ta durƙusa ƙasi tana shafa fuskar Tasleem tare da faɗin "My beauty Tasleem inaso ki ara mun Amaar ɗinki zai rakani wani wuri yanzu zamu dawo..."

Tasleem hannu tasa tana toshe hancin ta tare da faɗin "Mom meyasa duk turaren da kika saka kike warin jini ne?..."

Madam Nablah a ruɗe ta zaro manya-manyan idanuwanta cike da tashin hankali ta ce "jini kuma Tasleem aina?..."

Tasleem ta ce "eh kina warin jini shiyasa bana son zama a kusa da ke, kuma ina mafarkin ki kina cin ɗanyen naman mutum, kuma kina zama namomin daji...."

Madam Nablah rufe idanuwanta tayi sosai tana girgiza kai ta ce "ki daina faɗin haka kin san mafarki ba gaskiya bane, kina addu'a..."

Tasleem murmushi tasau a lokacin ta ce "TOH Mommy, amma ina zaki je da Amaar? nima zan bi ku..."

Madam Nablah ta ce "a'a jira mu yanzu zamu dawo..."

Ta miƙe tsaye idonta akan Amaar ta ce "ka je ka shiga mota bari na ɗauko key..."

Daga nan ta wuce,
Tasleem kamar zata yi kuka ta ce "Amaar baza ku tafi dani ba koh?..."

End Ads