— mahaifinku yana can ƙasan gidan Mahaifiyata, an tsare shi shekaru ashirin da suka gabata. Nasha ganinsa a cikin mafarki na amma ban taɓa tunanin shi bane, sai wata rana da na bi bayan Mommy a ɓoye har zuwa yanda yake amma tsoro ya hanani faɗa. Madam Nablah bata ma san cewa na sani ba."
Amaar gaba ɗaya ya rikice haka yake fitar da numfashi daƙer yana faɗin
"Na... na dade ina mafarkin wannan abun nima. Kuma yanzu ke kike sanar mun cewa gaskiya ne?"
Ya girgiza kai ya ce
"Ya kamata na je yanzu. Wannan na nufin rayuwarmu na cikin haɗari...."
Tasleem ta riƙe hannun Amaar sosai, tace:
“Zamuyi wannan tafiyar tare, ni kaɗai ce nasan yanda yake kuma sai da ni ku samu hasken hanya..."
Amaar yana zubda hawaye haka yasa hannu ya rungumo Tasleem jikinsa tare da sumbatarta ta ko ina tsabar tsananin farin ciki, haka yake jin ƙaunarta yana ƙara shige cikin zuciyar sa....
Abeesh yana zaune a falo shi kaɗai sai murmushi yake ta zuba wa, a wannan yayin Nasreen tazo ta same shi cike da mamaki itama ta zauna kusa da shi idonta akan fuskar sa wacce ta gagara gane ma'anar wannan murmushin...
Abeesh a ruɗe ya juya yana fuskantar Nasreen tsabar farin ciki bai san lokacin da ya rungume ta sosai a jikinsa ba yana faɗin "wannan ranar nake jira daman, gaskiya ta bayyana, bazan iya faɗan a yanda mahaifin mu yake ba amma muddin wani ya sanar a yanda yake kuma ake ƙoƙarin ceto shi to tabbas zan ji hakan a jikina, Nasreen gaskiya ta bayyana, daman nasan mahaifina yana raye domin akan idona akan ɗaure shi a cikin wani duhun ɗakin ƙasa amma bazan iya bayyana hakan a zahiri ba, an kurmantar dani ta yanda bazan taɓa faɗan gaskiyan abinda na gani ba amma hakan bai sa na manta ba, saboda ƙarfin addu'a dana riƙe....."
Yana bayani cikin hawaye da nuna farin cikin, itama Nasreen hawayen take tana share masa hawayen sa da tafin hannunta...
Ta gefe guda kuma Amaar da Tasleem ne suke tsaye wanda tin farkon maganar Abeesh suke tsaye suna riƙe da hannun juna, daga Amaar har Tasleem duk kowa hawaye yake, Amaar ba ƙaramin tausayawa ƙaninsa yayi ba...
Abeesh yana ganin su ya taso da sauri ya tsaya a gaban Tasleem yana hawaye ya ce "my Juju nagode sosai, ta sanadiyar ki yanzu bakina ya buɗe wurin faɗan gaskiya akan zaluncin da aka yiwa mahaifina....
Yana girgiza kai yasa hannu ya rungumeta yana kuka, itama tana kuka tana rarrashin sa....
Amaar ya ce "a yanzu zamu je wurin da mahaifin mu yake zamu ceto shi daga hannun hallaka...
Abeesh ya ce "ina tare da kai Yaya, tare zamu wannan tafiyar..."
Tasleem ta kalli Nasreen ta ce "ki zauna mana anan nasan Mommy bata nan a halin yanzu, idan har ta dawo kafin mu fito ki riƙe mana ita please..."
Nasreen ta ce "yanzu ina zaku nufa?..."
Tasleem ta ce "dole ta ɗakin ta zamu shiga domin nan ne kawai hanya mafi sauƙi...."
Nasreen ta ce "ki mallaki key ɗin ɗakin ta ne?..."
Tasleem girgiza kai tayi sannan ta ce "ban mallaka ba amma yanzu zan gado yanda key ɗin yake..."
Ta lumshe idanuwanta cikin lokaci ƙanƙani ta buɗe tana faɗin "ba da key ake buɗe ɗakin ba, sai da jinin jikinta ɗakin yake buɗuwa amma kar ku damu jinin mu ɗaya da ita, zanyi amfani da jini na...."
Daga nan suke nufi room ɗin Madam Nablah, suna zuwa Tasleem tasa reza a hannun ta sai ga jini ya ɗiga akan ƙofar ɗakin, sai da ƙofar ta shanye jinin kafin ta karɓi jinin a matsayin mai mallakar ta, sai ga ƙofa ta buɗu da kanta, a take suka yi saurin shiga, ɗaki kamar aljannar duniya domin ba ƙaramin tsaruwa ya yi ba sai dai ko wani ɓangare da ajiyar tsafi a jiki mai ado da kwalliya....
Tasleem kai tsaye ta nufi wani ƙaton photon mahaifinta wanda ta nan ne ƙofar take, Amaar da Abeesh kallon photon suka yi sun san cewa photon mahaifin su Tasleem ne domin da wayon su ya mutu, gani suka yi Tasleem ta rufe ido tare da wasu karatun yaren aljanu kamar yanda taga Mommynta tayi domin bata manta wannan sirrin ba, gani suka yi photon ya rabe biyu sai ga wani ƙofa nan ma ƙofar ta buɗu, cike da mamaki Amaar ya ce "kenan ana amfani da wannan photon wurin tsafi?...."
Tasleem ta kalle shi cikin damuwa sannan ta ce "al'amarin Mommy ba sauƙi...."
A haka suka kutsa ciki da addu'o'i a bakin su, baƙin duhu ne a wurin ko gaban su basa iya gani,
Tasleem rufe ido tayi tare da furta wata kalma ta haske sai ga sumar gashin ta wanda yake a kwance har gadon baya ya bayyana da wani irin haske, haske mai sheƙi wannan ya haska ko ina na wurin, haka suke kallon wurin kamar hasken rana, Amaar murmushi kawai yayi domin kaɗan daga cikin baiwar haske,
Abeesh kam gaba ɗaya ya cika da mamaki ganin yanda Tasleem ta koma, sumar gashin ta ya koma fari tass kamar furfura sannan ya bayyanar da haske, a ruɗe ya furta kema tsafi gare ki?..."
Tasleem tayi murmushi sannan ta ce "ba tsafi ba, baiwa ce ta haske..."
Amaar ya dafa kafaɗarsa ya ce "ita ɗin sarauniyar Haske ce kar ka damu da hakan...."
Shima Abeesh murmushi ya yi suka cigaba da tafiya, sai da suka yi tafiya mai nisan gaske har sun zo dab da wurin suka tarar da wani ƙofar ƙarfe anyi katanga da wurin da Mahaifin su Amaar yake, wanda babu bil'adama da zata tsallake wannan ƙofar....
Cike da mamaki Tasleem ta ce "yanzu kuma? amma lokacin da nazo nan babu wannan ƙofar...."
Amaar ya ce "ta gane cewa akwai wanda yasan da wurin shiyasa ta kafa tsaro..."
Abeesh ya ce "yanzu taya zamu ratsa nan wurin?...."
Amaar ya kalli Tasleem sannan ya ce "kiyi amfani da ƙarfin ikonki ki sama mana hanyar wuce wa...."
Tasleem gaba ɗaya ta rikice ta soma faɗin "ban san ta yanda zan fara ba..."
Amaar ya ce "Tasleem zaki iya, kiyi ƙoƙarin ganin cewa zaki iya, ke fa sarauniyar Haske ne kar ki karaya da wuri haka...."
Tasleem cikin ƙwarin gwiwa ta rufe idanu ta fara motsi da lips ɗin ta alamun akwai abinda take faɗi a cikin zuciyar ta, wani haske ne ya bayyana a cikin tafin hannunta lokaci guda ta da fa jikin ƙofar da hannaye masu ɗauke da haske, nan ta fara ƙoƙarin tura wannan ƙofa da ƙarfin haske, gaba ɗaya haske ne ya mamaye ƙofar...
Ta jikin ƙofar suka ji murya na tashi a rikice ana faɗin:
“Kuna son sanin gaskiya? Toh ku ji: Amaar ba irin mutumin da kuke tunani bane. Kuma Tasleem... ke 'yar wanda ke jini da Madam Nablah ba wai jinin haske ba. Idan gaskiya ta fito, ƙaunar da kuke yiwa juna zata koma ƙiyayya.”
Tasleem ta tsayar da abinda take ta kalli Amaar tare da faɗin
“Me ake nufi? kenan har yanzu haske bai gama karɓata ba saboda ni jinin Madam Nablah ce? sannan wani irin gaskiya in ta fito soyayyar mu zata koma ƙiyasta?..."
Amaar girgiza kai ya yi sannan ya ce "wannan kalmar ɗorata akai akayi domin a tsoratar da mu amma soyayya da aka ginata ta hanyar gaskiya bata taɓa komawa ƙiyayya, ke Sarauniyar Haske ne bakida wani alaƙa da duhu..."
Amaar ya kalli jikin ƙofar cikin ƙwarin guiwa ya ce
“Komai gaskiya ce, zamu fuskance ta....."
★★★★★
A gefe guda kuwa, Shaprees yana cikin mawuyacin hali. Ruhinsa na cike da damuwa da rikicewa. Ganin mahaifin wani dattijo (mahaifin su Amaar) cikin gilashin asiri ya jefa shi cikin rudani.
Shaprees yana zaune a wurin da yake gudanar da sirrin sa yana kallon cikin wuta ya ce:
“Madam Nablah ta ɓoye gaskiya. Wannan ba dai-dai bane. Wannan tsoho… yana da alaƙa da hasken da Sophia ta ke kira.”
Zuciyarsa ce ta fara ɓallewa daga duhun da Madam Nablah ta jefa shi ciki. A hankali, harshen soyayya da gaskiya ya fara haskaka cikin zuciyarsa.
Shaprees a hankali ya furta:
“Asmeen ba zata cancanci wannan hukunci ba... kuma Sophia ba zata so haka ba.”
★★★★
Madam Nablah kuwa, tana zaune a cikin ɗakin tsafinta, ta fara jin karfi yana kubucewa daga jikinta. Ta juya cikin madubi, amma madubin ya fara hayaƙi.
Madam Nablah a rikice ta furta:
"Wani yana shirin tono sirri... wani yana tasowa daga ƙasa?"
Sai wani baƙon haske ya fito daga madubi. Fuskar Abul Abeesh ne. ta tintsire da dariya amma cikin zuciyarta ta fara jin tsoro da faduwar gaba.
Madam Nablah a ruɗe ta miƙe tsaye tana faɗin:
“Bai kamata ka rayu ba! Na tsare ka da tsafin da babu wanda zai iya warwarewa! Amma a yanzu ana shirin ruguza wannan tsaron da ƙarfin haske shin waye wannan mai ƙarfin ikon shiga makomata?....."
Sai wani murya daga cikin madubi ya furta:
“Idan haske ya haɗu da gaskiya, komai na duhu zai fāɗi...”
Madam Nablah ta firgita. Ta fahimta cewa hasken da take ƙoƙarin hana wa shi ya fara fitowa. Kuma wannan haske, ba daga waje yake ba — daga cikin waɗanda ta cuta da hannunta ne.....
*NEXT PAGE.....*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
35 to 36
Tasleem da ƙarfin tsafin hasken ta take ƙoƙarin buɗe ƙofar nan, cikin ɗaga murya da azaba take faɗin "Ya Amaar ku taimaka mun..."
Amaar da Abeesh hannu suka sa zasu ture ƙofar, ba shiri suka ja da baya tare da yarfe hannayen su sakamakon wutar ƙuna da suka ji, ƙofar ta ƙone musu hannu, Abeesh tsabar azaba sai da ya durƙusa, Amaar ya ce "wannan ƙofar da wuta aka ƙirƙire shi, Tasleem ta ce "na ƙirƙiri haske don ƙofar ta buɗu amma na riƙe hasken ne da ƙarfina, ƙarfina ya kusan ƙarewada zaran na sake komai zai koma baya..."
Amaar ya ce "a'a Tasleem ki ƙara daure wa naga ƙofar tana motsi..."
Tasleem kamar zata yi ihu ta ce "to ku taya ni manaaaa...."
Amaar ya ce "taya zamu taya ki alhalin bamu da ƙarfin ikon tsafi..."
Tasleem ta sake furta "Da addu'ar bakin ka zaka taimaka mun, nasan zai mana amfani..."
Amaar da Abeesh riƙe hannun juna suka yi tare da jero addu'o'i, da ayatul kursiyu......
Abul Abeesh yana ɗaure akan kujera ba abinda ya canza masa, kullum a haka, da baƙar hula yanda akayi rufe masa fuska da shi, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi saɓanin tiririn wutar da yake shaƙa akoda yaushe, a cikin ransa yake faɗin "tabbas haske na kusanta na, sanyi da iska mai daɗi na ratsa tsatson jikina, alkhairi na kusanta na, ina ji a jikina ƴaƴana suna kusa da ni...."
Haka yake ta maganar zuci haɗe da murmushi.....
Ya buɗe idonsa a hankali. Bayan shekaru ashirin a cikin duhu da shiru, ya fara jin haske yana ƙoƙarin shiga zuciyarsa. Numfashinsa yana zurfi, ya furta
"Yarona... Armaan...da Abeesh su kusan iso gareni...."
A sama kuwa, Amaar, Tasleem, Abeesh, suna ƙoƙarin buɗe ƙofar da ƙarfin Addu'ar su Amaar da kuma ƙarfin hasken Tasleem.
Amaar yana duban Tasleem ya ce
"Za mu buɗe ƙofar ƙasa — zan ga mahaifina da idona, idan har na same shi a cikin wani mummunan hali wallahi saina ɗau mummunan fansa nima...."
Tasleem ta duƙar da kai cikin takaici da jin kunyar kasancewar ita ɗiyar Madam Nablah ce tana motsi da lips ta ce
"Na tsorata. Amma yanzu zuciyata ta fi ƙarfin tsoro. Ina son a yi adalci."..
Abeesh yana kallon Amaar ya ce
"Yanzu ne lokacin da zamu kawo ƙarshen tsafin da ya hana mu ganin gaskiya..."
★★★★★
A bangaren Asmeen, zuciyarta na ci gaba da jagulewa. Wani wuri a zuciyarta na ƙara yi mata kira — kiran da take ji daga can cikin zuciyar Shaprees. A daren jiya, ta gan shi yana kukan ɓoyayyen sirri.
Asmeen a zuciyarta ta furta:
“Shaprees yana ɓoye wani abu… amma me yasa ni nake jin zuciyarsa na kiran taimako? Shin zuciyarsa ba ta duhu gaba ɗaya ba ne...?”
Ta miƙe sannan ta nufi ɗakin Shaprees. A lokacin kuwa, Shaprees yana kallon wani guntun hoto da ke ɗauke da Sophia — matar da ya rasa.
Shaprees a hankali ya furta
“Idan na auri Asmeen, zan iya mayar da Sophia? Ko kuwa zan jefa kaina cikin wani sabon duhu?”
Ya tambayi zuciyarsa a dai-dai lokacin da Asmeen ta turo ƙofa,
Jin turowar ƙofa yasa ya kalli bakin ƙofar kamar daman a tsarge yake, idonta da nashi suka haɗu.
Asmeen idon ta akan sa yanzu ko tsoronsa ta daina ji, ta ce
"Shaprees… ba zan iya aure ba tare da na san gaskiyar zuciyarka ba. Me kake ɓoyewa...?"
Shaprees ya juya a hankali, kamar mai shirin furta wani abu mai nauyi ya ce
"Zan sanar miki amma ba yanzu ba, akwai lokaci...."
★★★★★
A bangaren Madam Nablah, abubuwa sun fara fita daga hannunta. Madubin sihirinta ya ƙi nuna mata abin da ke faruwa a ƙasa. Garkuwarta na dusashewa.
Madam Nablah a firgice ta ce
"Na sha maganin komai... me ke faruwa yanzu?"
Sai kuma wani ɗumi ya shiga ɗakin. Wata murya daga baya ta furta:
“Yanzu lokaci ya yi… ki fuskanci abin da kika ɓoye.”
Madam Nablah ta juyo da sauri — Shaprees ne tsaye a bakin ƙofa, idonsa yana haskakawa da ƙarfin da ba ta saba gani ba.
Ya kuma cewa
“Na gano gaskiya. Kuma ba zan ci gaba da aikinki ba. Wani sabon haske ya fara haskaka cikin zuciyata.”
Madam Nablah cike da mamaki take bin Shaprees da kallo, a ɗan ruɗe ta ce
"Kasan me kake faɗa kuwa Shaprees? ka fa karɓi tsafin wuta da kuma yarjejeniya, ZULQARNAIN ba'a jayayya da shi sannan ba'a karya masa alƙawari....."
Shaprees juyawa ya yi ba tare da ya bata amsa ba....
Madam Nablah haka take huci kamar wata zakanniya har idanuwanta sun canza zuwa ja kamar garwashi...
A ƙasan ƙasa ƙofar da aka ɓoye Abul Abeesh, sun yi nasarar buɗe ƙofar wuta daƙer, sannan suka buɗe murfin gidan ƙasan Amaar ne ya fara shiga kafin Abeesh sai Tasleem wacce ta biyo bayan su jiki a sanyaye...
Ganin mutum a zaune kan kujera a ɗaure ga baƙar hula a rufe da fuskar sa, Amaar da sauri ya nufi wurin sa tare da durƙusawa yasa hannu ya buɗe masa fuska, Abul Abeesh wanda gashin gemun sa yake cike da furfura, tsabar azaba da ganin duhu akoda yaushe har idanuwansa sun ƙanƙance, hatta girar sa saida ya koma fari na furfura,
Idanunsa suka haɗu da na Amaar da Abeesh, lokaci guda ya fashe da kuka.
Duk da kamannin ƴaƴan nasan sun canza daga yanda ya san su tin yarinta, ya ji a jikinsa cewa zasu dawo gare shi domin Abul Abeesh asalin malamin kimiyya ne....
Abul Abeesh da hawaye akan fuskar sa shaɓe-shaɓe ya ce
"Yara naa… kun girma."
Amaar da Abeesh haka suka rungumi mahaifinsu cike da damuwa suna kuka, tare da faɗin "Abul! Abul!! Abul!!!..."
Amaar yana kuka ya ce "Abul! ka yafe mun, ban san kana cikin wannan kogon hallakar ba, mun kasa maka amfanin komai