x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 32 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 93001 words
  • 96000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 207

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
da Amaar. Wannan shine kuskurenki. Zanyi maganinki.”........

New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

43 to 44



Dare Ya Sauƙa....
Wani irin shiru ne ya rufe gidan, bayan walimar biki da dukkan shagulgulan da suka yi yau. Gidan ya koma cikin natsuwa, hasken fitilu masu launin rawaya na ratsa dakuna da falo cikin salo. Kowane yanki yana ɗauke da ɗan ƙamshi na turaren bikin da aka yayyafa.
A cikin wannan natsuwa, akwai abubuwan da zuciya ke ɓoye wa— abubuwan da zasu fara bayyana a daren nan...


---

Abeesh & Nasreen – Daren Da ya fi ko wanne Sanyaya Zuciya

Abeesh yana sanye cikin fararen kayan barci marasa nauyi, yana zaune gefen gado ya yi shiru, fuskarsa cike da tunani. Sai ga ƙofa ta buɗu, Amaar ne ya shigo da murmushi a fuskarsa.

“Kai Ango, yau rana ce, kar ka bari komai ya dagula maka lissafi. Ka manta da jiya, ka kalli gaba.”



Abeesh ya ɗago kai ya kalleshi da ɗan murmushi sannan ya ce

“Yaya... nagode. Ban san yadda zan fara ba.”



Amaar ya dafa kafaɗarsa Ya ce

“Da soyayya ake farawa. Ka nutsu, ka saurareta. Zuciyarta na da taushi fiye da yadda kake tunani.”



Sai ya miƙe ya fice, ya bar masa dakin.

Bayan ƴan mintuna, ƙofar ɗakin ta sake buɗewa a hankali. Nasreen ne ta shigo cikin kayan bacci tana sanye da dogon hijab har ƙasi kanta a ƙasa kamar sabuwar amarya. Hawayen da tasha a cikin zuciyarta sun gama goge fuskar ta, sai siririn murmushi da yake bayyana cikin salo..

Abeesh ya miƙe yana kallonta. Ba tare da ya ce komai ba, ya matso kusa ya kamo hannunta.
A hankali ya furta

“Nasreen...”



Ta ɗago idonta da ɗan kukan da ya rage, muryar ta na rawa take faɗin

“Ya Abeesh... kayi haƙuri da duk laifin da na maka. Duk da abubuwan da suka faru, zuciyata bata daina ƙaunarka ba.”



Sai ta durƙusa a gabansa tana kuka ta ce

“Na yi kuskure... amma nayi nadama. Kuma zan yi iyakar ƙoƙarina don zama matarka mai daraja.”


Abeesh ya riƙo hannunta, tare da ɗago ta Ya ce

“Na jima ina fushi da ke, Nasreen. Amma wallahi, zuciyata ta fara sabo da ke tun kafin ki nemi gafara. Na ji yarda, na kuma ji soyayya. Amma...”



Ya tsaya yana kallonta daga bisani ya ƙara sa da cewa

“Catrina na damuna. Ban san me ke faruwa da ni ba. Kamar wani iko ne ke jan zuciyata gareta...”



Nasreen ta dafa kirjinsa tare da faɗin

“Zan tsaya tare da kai. Mu fuskanci komai tare.”



Suka rungume juna cikin shiru tare da kewar juna da kuma ƙarfin soyayya....

Jin knocking ƙofa suka ji, a lokacin Nasreen ta je ta buɗe, murmushi Nasreen tayi ganin Tasleem riƙe da kulolin abinci da kayan marmari,
Tasleem ta ce "Amarya bakya laifi da duk kan alamu kina cikin shauƙin soyayya, ga wannan yau na makara ban kammala girki da wuri ba....

Nasreen ta karɓa tare da yi mata sannu da aiki, daga baya ta rufe ɗakin.....


Daren ya lulluɓe garin da natsuwa, hasken wata na sauƙa cikin ɗakin da Abeesh da Nasreen ke zaune, soyayya na yawo a tsakanin numfashinsu. Bayan sun cin abinci,
sun yi wasa da dariya mai daɗi...


Nasreen na sanye da rigar bacci mai launin shudi mai laushi ta miƙe tare da ta nufi jikin mirror tana feshe jikinta da turaren ‘lily’ wanda Abeesh ke matuƙar so. Idanunta cike da annuri, murmushi na launin so yana bayyana a fuskarta. Tana kallon mijinta da wata irin sha'awar da ke bayyana muradin zuciyarta.

Abeesh ya taso ya zo yanda take tsaye a gaban mirror kusa da ita, ya kamo hannunta, yana jin yadda jikinta ke rawa da raɗaɗin soyayya. Sun kalli juna tamkar zuciyarsu na magana da harshe ɗaya.

"Abeesh…" ta ce cikin ƙasa da murya, kamar mafarki.

"Na'am, Nasreen?" ya amsa yana shafar gefen kumatunta.

"Na ji kamar wannan rana ta fi kowacce muhimmanci... so nake mu bayyana yadda muke ƙaunar juna fiye da kowane lokaci." ta furta hakan cikin shagwaɓa...

Ya lankwasar da kansa, yana kallonta cikin kulawa Ya ce

"Zuciyata da taki sun jima da haɗuwa tun kafin mu sani, Kuma wannan daren, zan mayar da ke sarauniya a gado na da zuciyaa ta,

Rungumar juna suka yi cike da natsuwa da kulawa, Ƙamshin jikinta ya saka shi jin wata irin salama, zuciyarsa ta sauka cikin lumana. Ya sumbace ta a goshi, a kumatu, sannan ya janyota jikinsa, yana jin yadda numfashinsu ke haɗuwa cikin ɗumi da so.

Iska mai daɗi ne yake ratsa su, suka ci gaba da kusanci – da hannu, da ido, da zuciya. Kalaman soyayya na sauƙa a kunnen juna, hannaye na yawo cikin natsuwa da ƙauna.

A cikin dare, suka zamo tamkar ruhu guda biyu da suka haɗu, suka bayyana jin daɗi, aminci, da soyayya ba tare da ko da ƙaramar kalma ba. Wannan dare ne na soyayya mai tsarki.....

Hasken ɗakin suka kashe, daga nan hankali ya gushe, sai surutai da ba'a sanin mai suke faɗi, sun koma wata duniya da ban.....




Shaprees & Asmeen – Daren Auren su..

Shaprees ya shiga daƙin Asmeen da natsuwa. Ya riga da yacire kayan bikin, ya koma cikin shigar dare (kayan bacci) yana kallonta cikin wani kallo mai taushi.
Asmeen tana gefen gado, tana ƙoƙarin kau da kai saboda karayar zuciyarta — bata yarda da shi ba har yanzu.

Shaprees ya zauna a gefenta ba tare da ya matsa kusa ba Ya ce

“Asmeen, bana son matsa miki. Na san ba kya sona, kuma bana buƙatar ki Amince dani yanzu. Amma ina so ki sani — ni ba Shaprees ɗin da kika ji labari bane, ko kika gani Ni sabon mutum ne.”



Asmeen ta kalle shi, ta ce cikin sanyin murya

“Kamar yadda ka ce, bana jin zan iya yarda da kai a daren nan. Amma ba na nufin zan zama uwargida marar biyayya”



Shaprees ya ɗan murmusa sannan ya ce

“Kin nuna min girmamawa da fadakarwa fiye da ƙiyayya. Wannan yana nufin akwai fatan alkhairi”


Daga nan ya kwanta a kujerar ɗakin dake gefe da gadon yana faɗin

“Zan kwana a nan gefen. Idan kina buƙatar wani abu sai ki sanar mun, Amma sai abinda kika yanke tukun.....”



Asmeen ta kalle shi da mamaki. Wani sanyi ya shiga ranta, amma sai ta boye ta furta

“Na gode da karramawa, Shaprees.”


Shaprees ya kwanta akan kujera, ya juya bayan sa
A cikin zuciyarsa yana addu’a yana faɗin

"Ya Allah ka ƙarfafa ni, ka bani damar gyara kuskure na, ka sa wannan mata ta fahimce ni."


Dab da Asuba misalin ƙarfe 4 Abeesh da Nasreen na kwance domin a daren yau basu samu yin bacci ba, iskar sanyi mai ɗauke da ƙamshin furanni tana kadawa a jikin labulen taga, tana zagaya dakin da hasken fitilar bango na haskaka da launin zinariya mai salo. Abeesh da Nasreen, cikin shauƙin su, suna kwance a saman gadon da aka ƙawatar da farin zanen siliki da fure-fure masu ɗaukar ido.

Nasreen na kwance a gefen shi, kanta a saman kafadarsa, yana shafa gashinta da hannunsa cikin natsuwa kamar yana karanta wani sirrin soyayya da babu wanda zai iya fassara shi sai zuciyarsu biyu. Idanunta suna lumshe ba domin tana bacci ba, sai don tana jin daɗin lumshewa cikin annashuwa.

Abeesh ya ɗan ɗaga kanta ya kalli fuskar da ya saba kallo tun farko da suka fara haɗuwa, amma a yau ya sake kallonta da sabuwar fahimta. Fuskar Nasreen na cike da lumana, cike da aminci da kwanciyar hankali wanda ya shige shi gaba ɗaya.

"Nasreen," ya kira da ɗan ƙaramin murya.

"Na'am," ta amsa ba tare da buɗe ido ba.

Sannan ya ce

"Ina ji kamar duk duniya ba ta da wani ɗanɗano idan baki cikin rayuwata."

Sai ta murmusa, ta buɗe idonta a hankali

"To ni fa na rasa inda zan sa kaina da kalaman ka,"
ta ce tana juya fuskarta gare shi, tana kallon idanunsa da ke cike da gaskiya.

Abeesh ya kama tafin hannunta, yana murzasu a hankali sannan ya dafa kirjinta da lallausar hannunsa Ya ce

, "Wannan zuciyar shine mafakina."

Cikin jin daɗi, ta sanya kanta a kirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa daidai da nata. Daga nan suka fara tattaunawa da kalmomin da basu da sarkakiya: game da gobe, game da mafarkinsu, game da iyali da fatan cika rayuwa da farin ciki.

Suna kwance cikin farin ciki har zuwa lokacin ƙiran sallar asuba..
Sun ci gaba da musayar kalmomi masu daɗi, musayar kallon da ke furta: na kamu da ƙaunar ki, musayar dariya da shiru wanda ke nuni da gamsuwa da kusanci.

Kafin nan sun riga sun zana hoton da ba zai goge ba a cikin zuciyarsu—na daren farko da suka kasance ba ma’aurata kawai ba, sai ma abokan amana na gaskiya da gaskiya...

Daga nan Abeesh ya tashi da niyyar ɗauro alwala, ya shige toilet sai da ya yi wanka sannan ya ɗauro alwala yana fito wa ya sanya jallabiyar sa, sai da ya sumbaci Nasreen akan goshin kafin ya fita zuwa masallaci,
Itama yunƙurawa tayi ta tashi da niyyar yin wanka da Sallah.....

★★★★★

Washegari da safe, hasken safiya yana kadawa cikin ɗakin Nasreen da Abeesh. Wata irin nutsuwa ce ke zagaye tsakanin su, babu hayaniya, babu kalamai da yawa. Abeesh yana kwance yana kallon Nasreen wacce ke zaune tana gyara gashinta. Fuskar ta na sakewa da murmushi mai taushi—na farin ciki da kwanciyar hankali, kodayake akwai ɗan fargaba a cikin zuciyarta. Ita kanta bata san dalilin hakan ba—zuciyarta kamar tana hasashen wani abu.
Ita har ta manta da wata Catrina....

Abeesh ya miƙe daga gado, yana ƙara kusanto ta.

Ya ce

“Nasreen… na gode da jiya. Soyayyarki ta sake sabunta min zuciyata.”



Ta juya da murmushi mai sauƙi Ta ce

“Ni ma nagode da yanda ka rungume ni da haƙuri. Ina fatan soyayyarmu zata ƙarfafa.”



Sai ya rungumeta a hankali. Amma a cikin ransa — akwai sanyi da zafi. Ya kan ji Catrina tana taso masa a zuciya kamar ƙamshi mai dāɗi da cike da ruɗani. Yana jin yana ƙaunar Nasreen, amma wataƙila ƙaunar Catrina ya fara shigarsa da wata hikima ta daban.


A Ɓangaren Shapreen da Asmeen..

Washe da safe rana na bayyana daga tsakiyar gajimare...

A cikin gidan aurenta, Asmeen na zauna a gefen tagar dakin, tana kallon yadda rana ke dukan lemar ganyen itatuwa. Shaprees na zaune gefenta, yana duba wata tsohuwar takarda da ke ɗauke da bayani akan wasu kalmomin sihiri. Amma daga gefe, idanunsa na kallon Asmeen cikin sirri—wani kallo mai cike da ɓoyayyen buri da damuwa.

"Asmeen…" ya furta.

Ta juyo da ɗan murmushin dole, wanda bai kai zuciyarta ba. "Na’am?" ta furta cikin sassanyar murya

Shaprees ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "Kin kyauta da kika amince ki zama matata. Zan baki kulawa yanda ya kamata Ko da ba soyayya ce ta kawo mu nan ba… zan so ki, in har lokaci ya bani dama."

Asmeen ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce "Ka san ba don raina ya so ba na shiga wannan aure. Amma zan yi ƙoƙarin zama yadda ya kamata…"

Shaprees ya ɗaga mata hannu kamar yana hana ta ƙarasa maganar, ya ce

"Bana son ki tilastawa kanki. Amma idan wata rana zuciyarki ta buɗe, zan san hakan..."

Sai ya miƙe, ya bar dakin cikin natsuwa, amma zuciyar sa tana matuƙar masa zafi —zafin rashin samun kulawa daga wadda zuciyarsa ke so, kodayake manufarsa ta farko na boye a cikin ɗumbin sirri.....

******* Catrina kuwa a wannan ranar kwata-kwata bata fito falo ba, tana kwance a ɗakin ta tsananin soyayyar Abeesh ya hanata sake wa, daga wasa abu yana shirin zamo gaskiya, bata san ya akayi tayi wannan saken ba domin ba soyayya ne ya kawo ta ba....

Bayan Sallar Isha'i kowa ya ci ya sha...
Sannan kowa ya koma room ɗin sa, Ɓangaren Abeesh part guda ne a babban falon gidan, wanda kana hawa upstairs room biyu ne suka kasu biyu, room one akwai wani falo ɗan madaidaici a ciki sannan a wuce bedroom nan ne site ɗin Abeesh, other room kuma nan ne room ɗin Nasreen, kowa da room ɗin sa sai dare ake haɗuwa a room ɗaya...

Cikin Dakin Abeesh...

Abeesh na zaune kusa da taga yana kallon sararin sama. Yana cikin tunani mai zurfi. Zuciyarsa ba ta huta ba tun daga daren farko da Nasreen. Duk da cewa yana ƙoƙarin mantawa da komai, akwai murya a zuciyarsa da ke kiran wani suna — Catrina...
Yana cikin wannan tunanin yaji
Sautin ƙwanƙwasa ƙofa, kallon bakin ƙofar ya yi sannan ya ce

“Shigo...”


Catrina ce ta shigo cikin natsuwa, sanye da riga ruwan toka mai launin lu’ulu’u irin shigar sarauta. Gashinta a nade yana sheƙi kamar zinariya a cikin duhu. Fuskar ta na ɗauke da murmushin da yake rikita zuciya,

“Na san wannan lokacin bai dace naxo ba,”
in ji Catrina tana takowa cikin ɗakin da siririyar murya, ta cigaba da faɗin
“amma sai na ji bazan iya barin dare ya wuce ba tare da na ganka ba.”


Abeesh ya kalleta, bai ce komai ba, Sai dai yana jin wani sanyi na ratsa jikin sa, kamar ana shafawa da furanni masu ƙamshi. Murmushi ta ƙara yi, ta zauna a gefen shi.

“Kayi sanyi, ko zaka iya sanar mun yanda ka kasance da Nasreen?”
ta faɗa cikin lallausan salo.

Kallo ɗaya ya yi mata sannan ya ce

“Kada ki kawo batun Nasreen, Catrina.” Ya faɗa a nutse, ba da ƙarfi ba, ba da rauni ba.


Ta ce

“Shin na kawo naka ne? ba nata ba? Ka sani Abeesh Kana cikin zuciyata fiye da yanda nake fatan,
Abeesh… ka daɗe kana cikin ruɗani. Ka ƙi yarda da zuciyar ka.”


Ta miƙa hannu tana shafar hannunsa. Kamar kankara ne ke narkewa cikin wuta. Abeesh ya janye hannun ba tare da ƙarfi ba. Ya kalleta a karon farko, idanunsa na ɗauke da haɗuwar soyayya da fargaba.

Ya ce

“Ki tafi, Catrina. Kafin na rasa gaskiya. Na haƙura da soyayyar Nasreen kafin, amma yanzu… Ina ƙoƙarin gyara wa, Kar ki sa in dawo baya.”


Catrina ta ce

“Gyara?” ta faɗa da ɗan dariya mai cike da sarkakiya. “Kana son gyara soyayya da macen da ta mare ka saboda mahaifiyarta? Wacce ta bar ka cikin duhu lokacin da kake buƙata? Kuma yanzu kake neman haƙura saboda tsoron zuciyarka?”


Abeesh ya runtse ido. Cikin ɗumi,
ta matsa kusa da shi, muryarta na shigewa cikin kunnensa a hankali ta furta

“Ka riga ka zabe ni a zuciyarka, Abeesh. Ko da za ka zauna da ita, sai dai jikinta. Amma zuciyarka... tawa ce.”


Sai ya buɗe idonsa ya dube ta.
A can cikin zuciyar sa — yana jin gaskiyarta. Amma har yanzu yana jin laifine hakan, da kuma cin Amanar wacce yake so..

Girgiza kai ya yi tare da faɗin

“Catrina... ki gaya min gaskiya. Wacece ke? Me kike so daga gare ni?”


ta yi murmushi a taƙaice sannan ta ce

“Ni? Ni ƙaunarka nake so. Kuma kai kanka ka sani.”


Ta miƙa hannu, ta dafa ƙirjin sa — inda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
Ta ce

“Zuciyarka tana furta sunana fiye da yanda harshenka ke iya furtawa...”


---

A Wurin Nasreen...

A ɗakin Nasreen, tana kwance da ido a buɗe. Bata jin bacci. Bata jin kwanciyar hankali. Zuciyarta tana bugawa tamkar akwai wanda ke shirin kwance mata farin ciki. Ta miƙe tsaye, tare da sanya hijabi, zuciyarta na cewa “Ina jin wani abu ba daidai ba.”...

Sai ta fice daga ɗakin a hankali — zuciyarta na kiran sunan Abeesh.


Nasreen ta tsaya a gaban ƙofar ɗakin Abeesh, zuciyarta na tsalle kamar ana harbi da kibiya a cikin zuciyar ta, Hannunta na rawa, amma ba tsoro bane, kishin so ne — kishi da fargaba, da son sanin me ke faruwa.

A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin...

Abeesh yana zaune a gefen gado, Catrina kuwa na zaune akan cinyar shi, hannunta a kan ƙirjin sa yayin da ɗayan hannu yake zagaye ta bayan wuyansa suna sumbatar juna cikin salo da ƙwarewa, cikin fitar hayyaci Abeesh haka yake cakurkuɗa mata sumar gashi tare da shashshafa ta ko ina, har ta saman nonuwan ta, idanuwansa a lumshe, shaƙar ƙamshin turaren ta na ƙara jefa shi cikin wata duniya da ban, haka yake shocking lips ɗin ta kamar wanda ya samu lollipop....

Idanun Nasreen ne suka cika da hawaye lokaci guda, Ta tsaya a bakin ƙofar ba tare da sun lura da ita ba. Amma Catrina, kamar ta
End Ads