hango wani inuwa a bayanta ta jikin bango, ta juya a hankali. Da ganin Nasreen, murmushi ya bayyana a fuskarta, ba na jin kunya ba, sai na cin nasara,
A hankali ta juyar da kanta bakin ƙofa yayin da shi kuma yake ƙara danne kansa a cikin rigar ta yana sumbatar saman nonuwan ta....
“Oh... Nasreen.” Ta faɗa da muryar kwantar da hankali, amma a cikin zuciyar ta tana farin ciki da wannan lokacin...
“Kiyi hakuri, bamu san kina nan ba...”
Nasreen ba ƙaramin rikicewa tayi ba, nufan cikin ɗakin tayi da sauri, zuciyarta na harbawa.
Abeesh kuwa da sauri ya ɗago kansa a ruɗe yana kallon Nasreen, a ruɗe ya miƙe tsaye cikin firgici, ya janye Catrina daga jikinsa yana kallon Nasreen cike da fargaba.
Muryar sa ne ta fara rawa yana faɗin
“Nasreen, ba yadda kike tunani bane—”..
A rikice Nasreen ta ce
“Shiru! Ka riga ka gama min,” ta ce cikin kuka mai raɗaɗi sannan ta cigaba da faɗin “Na farka cikin dare don in roƙe ka gafara gaba ɗaya, ka nuna mun cewa ka yafe mun amma yanzu sai na same ka da ita — ita! Wacce ban ma san ko ita wacece ba!”...
Bata ƙara sa maganar ba ta fashe da kuka..
Catrina ta matsa kusa da Nasreen, tana kallonta da wani irin murmushi da yake ƙara jefa zuciya cikin matsin lamba.
Ta ce
“Ya kamata ki saba da hakan, Nasreen. Idan kina da kyakkyawan dutse a hannunki, mutanen duniya za su so su karɓe shi. Kuma ni... na fi dacewa da wannan dutse.”
Nasreen ta juya, ta dube Catrina da wani irin kallo mai ƙayatarwa. Sai ta matso kusa da ita ta ce da ƙarfi:
“Ke baƙuwa ce a gidan nan. Kuma baƙuwar da bata san mutunci ba, komai yana da iyaka! Kinyi nasarar cusa kanki a zuciyar mijina — amma wallahi ba zaki iya karɓar sa gaba ɗaya ba. Sai na nemi mafita. Domin wannan soyayya tawa ce — kuma ni ce na cancanta da ita!”
Abeesh ya matso, ya riƙo hannun Nasreen. Idanunsa cike da damuwa ya ce
“Ki saurare ni, Nasreen... na rasa kaina ne na cikin ɗan lokaci. Ina ƙoƙarin mantawa da ɓacin ran da kika sanya mun Amma zuciyata ta kasa jurewa ruɗanin da ke kewaye da ni...”
“Na yafe maka, Abeesh,” ta faɗa cikin hawaye. “Amma ban yafe mata ba. Kuma sai na gano ita wacece!”
Catrina ta zura hannayen ta cikin sumar gashinta, ta juya kamar mai cike da ƙwarin gwiwa tana faɗin
“To ku ci gaba da soyayya idan zaku iya. Amma ku sani — wanda ya fara shan ruwan ni’ima daga tabkin duhu, ba zai iya sha daga rijiyar haske ba.”
Sai ta juya cikin natsuwa ta fice daga ɗakin — tana barin ƙamshi mai ɓoye ɓoye, da murya mai zurfi da ba kowa ke fahimtarta ba...
---
Shaprees da Asmeen...
Shaprees yana zaune kusa da Asmeen a ɗakin su. Cikin nutsuwa, ya ke kokarin kawo zaman lafiya da soyayya. Bai motsa da son rai ba. Bai nemi kusanci ba. Sai dai yana nuna kulawa ta gaskiya.
Yana kallon ta cikin kulawa ya ce
“Na san kina jin tsoro, amma ina rokanki, ki bar ni na zama aboki a gare ki. Komai ya girmi lokaci. Ni ba duhu bane kamar yanda kike tsammani.”
Asmeen ta juya daga kallonsa. Amma zuciyarta na tafasa da tambayoyi — Shaprees ya canza? Ko kuwa wata dabara ce sabuwa?...
A wannan lokacin haka Shaprees ya gama surutan sa amma ko sau ɗaya bata kula shi ba sannan bata bashi haɗin kai don su zamo cikakkun ma'aurata ba, duk da bai tilasta mata akan ta amince da shi ba....
---
A cikin ɗaki Amaar na zaune akan katafaren gadon sa yayin da
Tasleem take kwance a cinyar sa tana sharar hawaye. Amaar na shafa kanta yana rarrashi a hankali yake furta
“Muna raye ne don mu jarrabtu, Kin ga fa ko Abeesh da Nasreen ba su da sauƙi — amma soyayya na tsira daga ruɗani idan aka dage da addu'a da gaskiya akan ci ribar sa...”
Tasleem ta ɗaga kai ta ce:
“In dai kai ne a kusa da ni, ko da duniya ta ƙi yarda da mu, ni bazan taɓa fasa ka ba…”
Sun juma suna tattaunawa akan batun soyayyar su, da bata da wata mafita......
Washegari da safe, hasken safiya ya leƙa cikin gidan Madam Nablah, amma zuciyoyin da ke cikinsa ba su samu nutsuwa ba. Duk da anyi bikin daɗi da annashuwa, gidan ya shiga wani hali na ruɗanin soyayya da ba a iya kwatanta shi da komai sai da guguwa.
Abeesh da Nasreen...
Abeesh ya fito daga ɗakinsa da kyar, idanunsa ja, fuskarsa cike da gajiya da ruɗani. A daddafe ya shiga falo, yana jin zuciyarsa kamar tana nauyi. Yana kokarin mantawa da abin da ya faru da Catrina daren jiya, amma... sautin muryarta, kamshin jikinta, da idanuwanta masu sanyi suna binsa kamar inuwa.
Nasreen kuwa ta rufe kanta a ɗaki. Tana kuka, tana addu’a, tana shan wahalar ganin mijinta na soyayya da wata da ba ta san komai game da ita ba. Amma ko da ta dage da addu’a, zuciyar Abeesh tuni ta samu wani rami da Catrina ta cusa kanta a ciki. yana jin haushin hakan, sai dai ba zai iya fitar da ita ba.
---
A ɗakin Catrina...
Catrina tana zaune a gaban madubi, tana kwalliya. Fuskar ta ɗauke da shu'umemmen murmushi, amma zuciyarta na ɗauke da ƙaƙƙarfan nufi — zata ci gaba da shiga jikinsa har ya daina jin komai ga Nasreen. Ta shafa wani turare wanda ke janyo hankalin maza, wani sihiri ne da ta ɗora don ƙara ruɗa Abeesh. Tana murmushi, tana furta cikin ƙasan harshen ta:
“Zan bar Nasreen da sunanta... Amma zuciyar mijinta, mallakina ce.”
---
Asmeen da Shaprees...
Asmeen tana kwance a gado, tana kallon Shaprees wanda ya tayar da sallar lafula. Da kyar take iya jure halayensa na kirki da nutsuwa — sabon Shaprees daban ne da wanda aka ce mata mungu ne.
Yana idar da salla, ya juyo yana kallonta da murmushi mai sauƙi Ya ce
“Kiyi hakuri da ni, Asmeen. Ina sane da cewa kinyi aure da wani da ba ki so ba. Amma zan zama amini a gareki... kafin in nemi zama masoyi.”
Asmeen ta saki wani numfashi mai zafi. Zuciyarta na rikicewa — ta fuskanci gaskiya tana tsoron ta fallasa zuciyarta.
---
★★★★★★★
Tasleem tana zaune a ɗakin girki, tana gyara kayan karin kumallo. Idanunta na ɗauke da hawaye, sai dai tana ɓoye su. Zuciyarta na raɗaɗin jin kishiyar soyayya a cikin gidan da mahaifiyarta ta haifar da rikici a cikinsa.
Amaar ya shigo cikin natsuwa, ya tsaya yana kallonta. Yana ganin yadda damuwa ke ɓoye a fuskarta duk da murmushin ƙarya da take ƙoƙarin sakarwa.
Ya ce
“Tasleem, Na san kin gaji da wannan rayuwar ƙyama. Amma ki sani... ba laifinki bane. Ki dage da addu’a, domin soyayyarmu za ta sami haske—duk da duhun da ke kewaye damu.”
Tasleem ta juyo, ta faɗa jikinsa tana kuka. A karo na farko, hawaye masu zafi suka gangaro daga idon Amaar shima. Zuciyar sa na kuka da shiru.
Gidan Madam Nablah ya zama filin fama.
Soyayya ta koma yaƙi.
Hasken aure da aka yi kwanaki bai iya kakkaɓe duhun da zuciya ke ɗauke da shi ba.
Nasreen...
Rana ta shigo da sabuwar damuwa. Nasreen ta fito daga ɗaki cikin yanayi na gajiya da rashin kwanciyar hankali. Duk da ta kasance matar aure, ba ta jin hakan. Zuciyarta tana ji kamar wata ce ke kwace mata mijinta a gaban idonta.
A cikin dare ta kasa yin bacci tana jin yanda Abeesh yake furta sunan Catrina a cikin barcin sa, ta kasa jure hakan kwana tayi tana kuka tare da addu'a sai kuma sallar dare da take yawaita yi har sallar Asuba....
A safiyar yau Nasreen tana zaune a falo tana jiran fitowar Abeesh...
A lokacin da Abeesh ya shigo falo yana shirin fita, Nasreen ta tare masa hanya. Idanunta sun yi jawur, zuciyarta na rawa da tsoro da fushi da ƙuduri, cikin fushi da ɗaga murya ta ce
"Ya Abeesh, na gaji! ina so yau a cikin mu biyu ka zaɓi ɗaya, ita ko ni? Ni matar ka ce, na shiga gidanka da fatan soyayya da Amana. Amma tun ranar farko na gane cewa zuciyarka ta ƙi zama da ni.”
Abeesh ya tsaya cak. Fuskar sa cike da damuwa. Ya juyo yana kallonta cikin tafarfasan zuciya. Ya ce
“Nasreen... ki barni nayi zaman fahimta da zuciyata. Ba na son ki ji zafi, amma gaskiyar ita ce Ina son ku duka biyu."
Nasreen ta dafe zuciyarta. Kamar an watsa mata ruwan zafi. Ta yi tsit na ɗan lokaci kafin ta ce da ɓacin rai:
"Wato baza ka iya zaɓa ba? Wato... ka amince da ni saboda aurena ne kawai, amma ƙaunarka na wajen wata ‘yar iska da ba a san asalinta ba”...
Abeesh ya ce da zafin rai:
"Ki kiyayi harshen ki Nasreen! Catrina bata cancanci ki zage ta haka ba."
Nasreen tana kuka ta ce
"To taya zan zauna da kai idan ƙaunar ka tana wajen wata?"
Ta fashe da kuka, ta juya ta nufi ɗakin ta da gudu, tana yarfe hannu cikin kuka da zafin zuciya.
A wannan lokacin, Catrina tana tsaye a bayan labule. Ta ji komai. Idonta na walƙiya da jin daɗin nasarar da ke ƙara bayyana. Amma ba ta nuna komai a fuska, sai shiru da salo.
Tana murza yatsunta cikin natsuwa, ta furta da sassanyar murya:
“Zuciyar maza kamar ruwa ce... sai wanda ya iya tafiyar da jirgi ke kai labari.”....
---
Daren Ranar...
Nasreen ta rufe kanta a ɗaki. Ba cin abinci, ba sha ko fita falo ta kasa Sai hawaye da addu’o'in da suka hana ta narke wa gaba ɗaya...
Abeesh yana ɗaki shi kadai, yana ganin laifin kan sa, sai dai zuciyarsa tana cikin rikici. Catrina kamar wani shaƙin ruwan sihiri ce, yana jin ya rasa ikon fitar da tunaninta daga ransa...
---
Washegari...
Madam Nablah ta lura da fushin da ke yawo a cikin gidan. Sai dai ta ƙi magana. Ita dai burinta a gama auren ne, yanzu hakan ya faru — hakan yasa ta tsiro da tafiya zuwa wata ƙasa daban wanda zata ɗauki tsawon lokaci kafin ta dawo...
Tasleem na ƙoƙarin rarrashin Nasreen a gefe ganin halin da take ciki, itama ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba jin abubuwan da suke wakana a tsakanin ƴar uwarta da mijinta akan wata banzar yarinya...
Asmeen kuwa tana lura da yadda Shaprees ke ƙara saduda da hakuri, abin yana shiga ranta sannu a hankali, ko da tana ƙoƙarin musawa.
---
Abeesh...
A cikin dare, yana zaune a falonsa shi kadai. Idanunsa na kallon bango, amma zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa yana maganar zuci
“Na aurar da zuciyata gida biyu – daya da shari’a, ɗaya da soyayya... Amma yanzu soyayya ta koma rikici, shari’ar ta koma kunci.”
Sai kawai murya ta fito daga bayan sa — Catrina ce ta shigo sanye da doguwar riga mai launin ja, murmushinta ya cika dakin.
Tana furta
“Ina jin sirrin zuciyar ka... Abeesh. Ka bar zuciyar ka ya huta. Ka zaɓi wacce zuciyar ka ke so... ba wacce duniya ke so ba.”...
Ta matso kusa da shi, ta zauna. Yana kallonta, yana jin duniya ta tsaya masa, akoda yaushe ƙara rikita shi take, especially idan yana kallon fuskar ta sai yaga a koda yaushe kyan fuskar ta na daɗa wanzuwa, ba ƙaramin shiga zuciyar sa tayi ba, haka kawai yake jin cewa bazai iya rayuwa ba tare da ita ba.......
*MU HAƊU A KASHI NA GABA.....*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
45 to 46
Washegari...
Nasreen da Abeesh ne suke zaune a dadduma dake harabar gida wurin shakatawa suna cin abinci ba tare da kowa ya yi magana wa ɗan uwansa ba, suna cikin wannan halin sai ga
Catrina ta nufo wurin a slow cikin iya taku, ta sha kwalliya kamar amarya ta biyu. Wani kamshi mai ƙayatarwa na fita daga jikinta, fuskarta cike da annuri da ƙarfin gwiwar mace mai nasara.
Sai da ta zaga idonta a kansu sannan ta zauna kusa da Abeesh – ba tare da tsoro ko kunya ba, tana furta sannun ku fa, nazo taya ku breakfast....
Abeesh bai ce komai ba, Bai janye jikinsa ba, Bai ma kalle su ba.
Nasreen ta girgiza kai Zuciyarta kamar za ta fashe. Ta san abin da ke wakana, amma ta rasa yadda za ta yaƙi soyayyar sihiri,
Catrina ba ta yi wa Abeesh komai ba amma ta ɗauke zuciyar sa gaba ɗaya da salon ta da kuma iya sarrafa zuciya...
“Abeesh...” Nasreen ta ce cikin sanyin murya tana ƙoƙarin dafa hannunsa.
Janye hannunsa ya yi yana kallon gefe domin yasan maganar ta baya wuce akan Catrina...
Ta ce
“Dan Allah... Ka kalle Ni, Ina cikin damuwa zuciyata cike take da ƙuna, kar fa ka manta nifa Amarya ce ko sati bamu yi ba......"
“Nasreen... Ki barni,” Abeesh ya ce, yana miƙewa tsaye tare da faɗin
“Zan tafi hospital na makara....”
Catrina bin sa tayi da ido tare da ƙayataccen murmushi akan fuskar ta....
Itama Nasreen cikin fushi ta miƙe ta bar wurin da gudu domin bata ƙaunar jin wata kalma daga bakin Catrina domin a yanda ta fusata za'a iya samun matsala...
Catrina ba tare da ta damu da komai ba, buɗe kuloli tayi tana ƙoƙarin zuwa abinci zata ci....
--------OTHER SIDE
Asmeen da Shaprees...
Shaprees yana ƙoƙarin ƙara samun shiga a zuciyar Asmeen. Ya koyi yi mata girki, yana kai mata tea, duk wata kulawa yana ƙoƙarin bata, duk wasu abubuwan da ya kamata tana yin su shi yake yi mata domin kada ta wahala....
Amma duk da haka bata gama yarda da shi ba,
zuciyarta ta hana ta gasgata cewa mutumin duhu zai iya sauyawa zuwa haske. Duk da haka a jikinta tana jin sauyin—amma zuciyarta na tsoro.
Yau, ya sameta zaune a tsakiyar gado tana karanta wani ɗan littafin addu'o'i...
Shi kuwa a wannan lokacin ne ya shigo da kulolin Abinci yana faɗin "Amarya na kammala girkin domin nasan kina jin yunwa sosai...
Shaprees ya matso da kulolin abincin ya ajiye su akan glass table na ɗakin, shima ya zauna akan gadon a gefen ta, yana kallon ta cikin kulawa...
Ya ce
“Kin ci wani abu ne?” ya tambaye ta.
Idonta akan littafinta ta ce
“Ban ci ba.”
Ya ce
“To, mu ci tare.”
“Ka barni kawai,” ta ce cikin sanyin murya...
“Asmeen...” ya furta sunan cikin tattaunar murya, ya zamo kalar tausayi sannan ya ce
“Ni ba wanda kika sani bane a baya, Ina son in gyara, in rayu da ke cikin alkhairi.”
Duban fuskarsa tayi cikin tsoro da rudani. Zuciyarta na harbawa a hankali, ta ce
“Kayi hakuri… bani da ikon amincewa da zuciyarka yanzu, ka ƙara bani lokaci....."
Ta cigaba da karatun ta a cikin zuciya...
Shapreen lumshe idanuwansa ya yi tare da furta "Oh my god...."
Ya ce "okay ga nan Abincin idan kin kammala zaki iya zuba wa ki ci, zan koma room ɗina...."
Asmeen ba tare da ta kalle shi ko ta furta wani abu ba, har ya fice,
Yana shiga room ɗin sa kamar zai rausa ihu haka ya faɗa saman gado a wahalce, kansa a kife akan gadon yana hawayen rashin nasara....
Wata murya ce ta ratsa cikin kunnuwan sa mai daɗin sauraro, a zabure ya ɗago yana kallon wani haske da yake kewaye da Sofia cikin doguwar riga fara sol, sai sheƙi take da murmushi kwance akan fuskar ta...
A hankali ta furta "ina mai jin baƙin cikin ganin hawaye a fuskar mijina...."
Da gudu Shapreen ya nufo ta tare da kai hannu zai rungume ta sai kawai ya ji ya rungumi iska domin a zahiri ita ɗin ce take tsaye a matsayin ruhi ba'a cikakkiyar mutum ba...
Ta ce da shi "baza ka iya taɓa Ni ba Shaprees domin ba ni ce a matsayin matar ka ba yanzu, nasan yanzu zuciyar ka tana ƙoƙarin komawa yanda kake mai haske amma dole saika fuskanci ƙalubale a gaban ka, kafin Asmeen ta gama yadda da kai domin sai ka jure, domin ita yarinya ce ƙarama, da farko ka nuna mata ƙiyayya hakan yasa yanzu take tsoron amince da kai...."
Shapreen kamar zai fashe da kuka ya ce "Sofia na gaji! bazan iya jure hakan ba, ina ƙoƙarin bata farin ciki a koda yaushe amma ita gani take kamar cutar da ita zan yi, ta kasa sakin jiki da shi why?...."