x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 193

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
bamu bar su sun zo nan ba..."

Amaar ya ce "meyasa baku sanar mun ba a tin jiya?..."

Shi har ya manta kwana yayi a sume.

Sojan ya ce "sun ce daga Kaduna suke kuma mun san bakada kowa a Kaduna shiyasa muka riƙe su a can cikin quarters...."

Amaar ya ce "su nawa ne?..."

Sojan ya ce "mata biyu namiji ɗaya..."

Amaar abun mamaki ya bashi jin har da mata, yana cikin tunani yaji Sojan ya ce "amma matan ƴan biyu ne domin kamar su ɗaya sak..."

Tasleem tana jin haka tayi saurin ɗagowa tana kallon Sojan,
Sojan yana ganin ta ya zabura tare da nuna ta da yatsa yana faɗin "Ogah inaga fa matan Aljanu ne domin kamar su ɗaya sak da wannan ta zaunen..."

Sai a lokacin Amaar ya kawo a ransa cewa ƴan uwan Tasleem ne, itama Tasleem a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "Nasreen and Asmeen..."
da gudu tayi waje ko tsaya ɗaukar jakar ta bata yi ba,
Shima Amaar bin bayanta yayi da Sojan....


NEXT NEXT NEXT


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 23 to 24




Tasleem tana isa wurin da ƴan uwanta suke a durƙushe bata san lokacin da kuka ya yanko mata ba, itama durƙusawa tayi tare da rungumo Asmeen, daga lokacin Asmeen ta suma akan ƙirjin Tasleem, a ruɗe ta fara jijjiga ta tana ƙiran sunan ta "Asmeen! Aasmeen!! ke Asmeen dan Allah ki tashi babu abinda ya faru da ke..."

Itama Nasreen hankalin ta ba ƙaramin tashi ya yi ba duk wahalar da tasha hakan bai hanata jijjiga Asmeen tana kuka itama.

Tasleem ta ce "Nasreen kin sha wahala sosai dan Allah kuyi haƙuri...."

Nasreen cikin fushi da takaici ta finciko Aasmeen daga kan Tasleem ta rungume ta sosai tana hararar Tasleem tare da faɗin "wannan tashin hankalin da muka shiga duk ke ce sila, hankalin mu ya tashi duk saboda ke, because of you mun kwana a haka yanda kika gan mu kamar wasu ɓarayi, ga can Abeesh yanda sojoji suka masa abin tausayi...."

Tasleem tana hawaye ta ɗaga kai ta kalli Abeesh yanda yake ta tsallen kwaɗo a wahalce gaba ɗaya ya fita hayyacin sa domin mintuna kaɗan zai iya haɗiyar ransa, ɗan dakatawa ya yi yana hutawa Sojan nan ya ɗaga dorina ya zabga masa a baya, a zabure Tasleem ta miƙe da gudu ta nufi wurin sa tana ƙiran sunan sa cikin kuka, tana zuwa tasa hannu ta ɗago Abeesh wanda ya kife a ƙasi, zaunar da shi tayi tare da faɗin "Sannu Ya Abeesh, kayi hakuri dan Allah...."

Sojan daka mata tsawa ya yi yana faɗin "ke wa ya baki umarnin ɗago shi? wace ce ke?..."

Tasleem cikin takaici da cije leɓɓe ta ɗago tana masa wani irin kallo na raini kafin daga bisani ta ɗaga hannu ta zabga masa mari tana huci ta ce "baka da matsayin da zaka san ko ni wacece, idan kuma ka takura kanka akan sanin ko ni wacece to zaka mutu ne..."
Sojan ya ce "whattt ni kika mara?..."

Tasleem ta ɗago hannu zata ƙara masa marin ya yi saurin riƙe mata hannu yana zaro mata rikitattun idanuwansa yana huci kamar tsohon zaki,
Tasleem tana ta yunƙurin ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata amma ta kasa domin ba ƙaramin riƙo ya yi mata ba..

Ba tare da Sojan ya ankara ba ya ji shima an damƙe masa hannun da ya riƙe Tasleem da shi, ɗagowa ya yi yana kallon Amaar ya ce "Oga wannan yarinyar hannu tasa ta mare ni..."

Fuska ba annuri ya ce "ka sake mata hannu..."

Tasleem tana ta yunƙurin zare hannun ta daga riƙon da sojan yayi mata, sannan shima sojan Amaar ya riƙe masa hannu da gasken gaske domin ji kake hannun yana ƙaras ƙaras alamun ƙashin hannun ne yake goce wa, Sojan ya ce "Oga my hand please..."

Cikin tsawa Amaar ya ce "na ce ka sake mata hannu..."

Sojan yana sakin Tasleem wani irin naushi Amaar ya kai masa akan lips ɗinsa har sai da ya dungura...

Tasleem itama cike da takaici ta ɗaga hannu ta zabga wa Amaar mari,
ba tare da ya motsa ba ya lumshe ido kafin ya buɗe har ta ƙara masa marin ta ɗayan ɓangaren.

Sojojin wurin ne suka motsa zasu zo wurin Amaar ya yi saurin ɗaga musu hannu yana girgiza musu kai alamar a'a...

sauƙe idanuwansa ya yi akan kyakkyawar fuskar ta wanda ya hargitse tana huci ta ce "na tsane ka wallahi, duk da ban san ka ba, ban san asalin ka ba amma ji nake kamar na kashe ka, duk kai ka jawa ƴan uwana shiga wannan tashin hankali, meyasa ka shigo rayuwa ta? dan Allah na roƙe ka da sunayen Allah ka fita daga cikin rayuwata tin kafin ka jawo mun matsala...."

Amaar ya ce "idan kuma ban fita ba fa? me zai faru?..."

A gigice Tasleem ta furta "zaka mutu ne, duk wanda ya shigo mana rayuwa mutuwa yake...."

Murmushi ya yi tare da jinjina kai cikin salo ya juyar da eyes ɗin sa kan Nasreen wacce take zaune Asmeen a kwance kan cinyarta itama su ɗin take kallo tana mamakin ta yanda suka haɗu har suka fara wannan cakwakiyar..."

Amaar ya juyar da kansa kan Tasleem yana girgiza kai ya ce "bazan iya fita daga cikin rayuwar ki kai tsaye ba sai dai idan kece kika cire ni da ƙarfin gaske, ta hanyar kisa, na fison ke da hannunki ki rabani da rayuwata ba wai aga gawata lokaci guda ba..."

Tasleem tana hawaye ta ce "inda inada halin kashe ka, to da yanzu ba wannan labarin ake ba..."

Buɗe tafin hannunsa ya yi tare da faɗin "bindiga..." yana alamu a sojan sa ya miƙo masa bindiga, kafin mintina aka ajiye masa bindigar akan hannunsa ba tare da sanin abinda zai aiwatar ba, idonsa akan Tasleem ya ce "ga bindiga ki harbe ni a wurin da zan mutu Lokaci guda..."
wurga mata ya yi ita kuwa ta cabke tare da kunna kunamar bindigar ta saita shi tare da faɗin "kana tunanin bazan iya bane..."

Amaar ya ce "nasan zaki iya shiyasa na baki damar aiwatar wa..."

Sojojin sa ne suka fara "Please Oga don't allow her..."

Ɗaga musu hannu ya yi tare da faɗin "ku dakata mun..."

Nasreen ta gama tsurewa tana tunanin shin Tasleem zata iya harbe shi ko kuma pretending ne,
Shi kuwa Abeesh tinda ya kifar da kansa bai ƙara ɗagowa ba tsabar tsananin wahalar da ya sha....

Amaar idonsa akan Tasleem wacce ta saita shi da bindiga ya ce "ki saita kan goshi na kina harba wa a take zan mutu, ko kuma a saitin zuciyata nan ma ko minti ɗaya bazan ƙara shurawa a duniya ba..."

Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "da kuwa zan fi kowa farin ciki idan ka bar duniya, zan harbe ka a saitin zuciyarka ne saboda anan ka ajiye soyayyata, wannan soyayyar kuwa so nake na dagargaza ta..."

Jinjina kai ya yi sannan ya ce "Go ahead my beautiful girl..."

Tasleem kamar wacce aka bata umarni lokaci guda ta harba bindigar sai ga bullet ya fasa ƙirjin sa...."

Amaar a zabure ya ɗora hannunsa akan wurin da ta harba wato kan ƙirjinsa ta ɓangaren dama...

Nasreen a zabure ta da ka uban ihu tare da furta "Tasleemmmm...."

Haka sojojin suka nufo shi, a ruɗe Amaar ya ɗaga musu yatsa yana karkaɗawa alamar kar su nufo shi,
Jin ƙarar harbi ne yasa Asmeen farfaɗowa a tsorace ta rungumi Nasreen tana faɗin "wayyo sun harbe mu ko? mun shiga uku sun harbe mu..."

Abeesh shima ɗagowa ya yi yana kallon Tasleem cike da mamaki ganin yanda ta harbe shi, duk a tunanin sa pretending take duk da ta farmake shi a gidan su, duk da ba shi aka harba ba amma ya ji zafin harbin har cikin zuciyar sa, yana motsi da lips ɗin sa a hankali ya furta "kin fasa masa ƙirji...."

Amaar tin harbin farko da ya durƙusa da gwiwowinsa bai ɗago ba, hannayensa akan ƙirji gaba ɗaya idanuwansa sun rikice sun yi jawur tsabar azaba, sai da ya ɗau tsawon mintuna kafin yayi ƙarfin halin ɗago wa ya sauƙe idanuwansa waɗanda suka canza launin ja akan fuskar ta, ga bakinsa yanda jini yake ɓulɓulowa, murmushi ya yi sannan ya ce "kin tabbata a saitin zuciyata kika harbe ni?..."

Tasleem a yanda ta riƙe bindigar bata sauƙar ba tana kuka ta ce "eh! to ka mutu mana! me kake jira ne?..."

Amaar yana fitar da murya daƙer ya ce "to ai baki harbe ni a yanda zan mutu da wuri ba, ba'a saitin zuciyata kika harba ba, nan ne saitin zuciya..." ya ƙarasa maganar yana nuna ɓangaren ƙirjinsa na hagun....

Tasleem ta ce "okay nayi kuskure yanzu bari na gyara kuskurena na harbin ka a yanda bai kamata ba, cire hannunka yanzu zan tarwatsa zuciyar takan...."

Amaar yana durƙushe gwiwowinsa a ƙasi ya cire hannayensa daga kan ƙirjinsa, ga yanda jini ya wanke masa gaban rigarsa kamar wanda aka masa wanka da jini,
Ya ce "zuciyar ai daman taki ce not mind, I love you Tasleem...."

A fusace ta ƙara saita bindigar saitin ƙirjinsa tana shirin harba ta ji kukan Nasreen tana faɗin "wai ke baki da imani ne? ke wata iriyar shashasha ne marar son mai sonki sai maƙiyinki..."

Tasleem idonta akan Amaar ta ce "abun burgewa ne kaso maƙiyinka..."

Asmeen wacce hankalin ta ya gama dawo jikinta ta ce "dan Allah Tasleem kar ki sake aikata kuskuren da kika aikata yanzu, na roƙe ki shi ɗin mutumin kirki ne..."

Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "bai dame ni ba sanin ko shi waye..."

Amaar lumshe idanuwansa ya yi tare da faɗin "ki aiwatar da abinda kika yi niyya My...."

Ya furta hakan tare da jiran sauƙar bullet, haka zuciyar kowa take bugawa ita kuma Tasleem hannunta take motsawa tana shirin danne kan bindigar, girgiza kai tayi tana kuka ta wurgar da bindigar tare da juya wa da gudun gaske ta bar wurin, kai tsaye motarta ta shige a ɗari ta bar quarters.....

Amaar kifar da kansa yayi saboda tsananin zogin da yake ji, ba ƙaramin zubda jini ya yi ba, haka ya yi ƙarfin halin tashi daƙer yana takawa, duk yanda ya taka sai jini ya zuba, sojoji ne suka yo kansa zasu kawo masa ɗauki Amaar ya yi saurin ɗaga musu hannu alamar dakatarwa yana girgiza musu kai domin a halin yanzu ba bakin magana, dakatawa suka yi domin su na matuƙar jin maganar sa, Amaar yana tafiya yana tangaɗi wani irin hajijiya ne ya ɗauke shi yana shirin faɗuwa sai ga Nasreen da Asmeen sun nufo shi da gudu suka tare shi, haka suka saka shi a tsakiya wannan ta riƙe gefen sa wannan ma haka, da haka suke tafiya, shima Abeesh tashi ya yi ya nufi yanda suke yana zuwa shima ya riƙo shi, hannun sa ya lanƙaya ta wuyansa sannan ya riƙo bayansa, ita kuma Nasreen ganin Abeesh ya karɓe su yasa ta cire gyalen kanta ta danne masa wurin harbi yanda jini zai rage zuba.

Amaar sam ya ƙi barin sojojin sa su kusance shi sannan ya hana a kaishi asibiti still baya son a ƙira masa ko wani doctor, da haka suka ƙarisa shigewa gidansa, a falo suka tarar da masu aiki ko wacce tana harƙoƙin gaban ta basu san me ke faruwa ba, ganin Amaar a wannan halin ne yasa su tsorata da sauri suka dafe ƙirji tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me ya faru da shi?..."

Nasreen kallon su tayi cike da damuwa ta ce "dan Allah ina ne part ɗin sa zamu shigar da shi ne..."

Ɗaya daga cikin masu aikin ce ta ce "innalillahi ke ba yanzu kika fita ba? ya naga kin koma mutum biyu?..."

Itama Asmeen nufan su tayi tana faɗin "please ba lokacin wannan maganar, ina zamu kai shi?..."

A tsorace suka nuna saman upstairs yanda yake, su na mamakin tambayar da suke mu su kamar basu san bedroom ɗin sa ba, still ga mamakin gani mutum biyu a matsayin ɗaya....

Nasreen kallon Abeesh tayi ta ce "Ya Abeesh mu kai shi da gaggawa please, ya raunana sosai..."

Haura upstairs suka yi masu
End Ads