x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 196

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tsari. Wata ƙatuwar alƙalami na zinariya da jini ya zana akan ƙasa, yana karanta kalmomin da Madam Nablah ta koya masa—amma yana haɗa su da kalmomin Sophia, waɗanda suka fito daga wani tsohon littafin da Madam Nablah bata san yana da shi ba. Wannan tsari ne mai matuƙar haɗari—zai iya dawo da Sophia ko ya tarwatsa shi gaba ɗaya. a hankali ya lumshe idanuwansa sannan ya ce

"Zan dawo da ke. Amma ba yadda Madam Nablah ke so ba—sai yadda nake so."

Shaprees ya buɗe idonsa – idanu masu duhu, amma zuciya tana kiran sunan matarsa da har yanzu yana gani cikin mafarki.

“Sophia…” ya furta a hankali. “Na rantse, zan gano yanda zan dawo da ke – ko da kuwa da ran wasu ne.”

Sannan ya kuma cewa
“Na rantse da jinin da na zubda don tsafin nan – idan har Sophia ba zata dawo ba, sai na ga bayan Madam Nablah.”


Wani irin sautin dariya ya ji daga sama, ya ji muryar Madam Nablah kamar ta wata halitta daban tana faɗin

“Kayi haƙuri, Shaprees. Ita matarka ta mutu, amma ina da ‘yan matan da ba su da tabo – Asmeen zata iya haifar maka da yara masu iko domin tana da zuciyar sarauta...”



Shaprees ya ce da zuciya mai ɗaci:

“ me zai hana ki mallaka mun duk biyun Asmeen da Tasleem – in mallake su?..."



Madam Nablah ta ɗan ƙame, sai kuma ta ce da siririyar murya:

“Idan ka nemi duka biyun ba za ka samu ko ɗaya ba. Amma in ka zama mai biyayya, za ka samu ɗaya… kuma iko zai koma hannunka.”

*NEXT_NEXT_NEXT*

New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

EP 31 to 32



Asmeen tana kwance akan gado tana tunanin abubuwa da dama, Cikin zuciyarta akwai yawaitar tambayoyi game da abubuwan da ke faruwa kwanan nan — sauyawar halin Mahaifiyar su, asarar mahaifi, da kuma wutar da ke yawo a cikin gida ba tare da asali ba.

Sai taji an buɗe ƙofa — Madam Nablah ce ta shigo cikin natsuwa amma da idanu masu bayyana tsaurin zuciya. Tsarinta ya canza fiye da yadda Asmeen ta saba gani — akwai nau’in iska mai sirrika a jikinta, kamar wadda ta shigo da zafi da sanyi lokaci ɗaya.

Madam Nablah ta zauna kusa da Asmeen, tana kallonta da murmushi mai cike da nufi.

Madam Nablah ta ce
"Asmeen, ya kamata ki shirya zuciyarki. Lokaci ya yi da za ki yi aure."



Asmeen ta ɗago ido cikin mamaki, sannan ta ce:

"Aure? Aure kuma yanzu? Amma wa zai aureni? Kuma meyasa yanzu, Mommy?"



Madam Nablah ta ɗan murguɗa leɓe, tana duban wata tagar duhu da ke gefen dakin tare da faɗin

"Zan haɗa ki da Shaprees. Shi matsafi ne — amma ba kamar sauran ba. Na shigar da shi cikin tafiyata, kuma yana da muradin kafa sabuwar gini da mu. Zaki zama ginshikin wannan mafarki."



Zuciyar Asmeen ta buga da sauri — sunan Shaprees ya faɗo kamar ƙarar bindiga cikin kunnenta, cikin wani irin sanyi da tsoro
Ta ce

"Mommy… wannan Shaprees, mungu ne so yake ya cutar da mu."

Madam Nablah ta ɗaga hannunta cikin izza, tana dakatar da ita
Daga bisani ta ce

"Kada ki saurari hayaniyar zuciya. Wannan duniya ba ta da tsarki, Asmeen! Idan muna so mu rayu — mu mamaye — sai mun haɗa haske da wuta. Shaprees zai kawo ƙarfin da muke buƙata. Kuma ke — za ki kawo tsarkin da zai ɗaure zuciyarsa."


Asmeen ta ɗan ja baya daga inda mahaifiyarta ke zaune, idonta cike da shakku da rudani.
Ta ce
"Amma Mommy… zuciyata ba ta amince da shi ba. Ina jin wani abu marar daɗi idan naji sunansa."



Madam Nablah ta matso kusa da ita, ta kama hannunta da ƙarfi da sanyi a lokaci guda.

Madam Nablah
a sirrance ta furta

"Kin san me? Wannan shine dalilin da yasa dole ne ki aure shi. Idan hasken ku ya haɗu, wataƙila zai zama abin da muke buƙata — ko kuwa… zai ƙone."


★★★★★

Bayan kwanaki biyu, a cikin wani filin tsarkakakke da aka gina da duwatsu masu ɗauke da tambarin tsafi, Madam Nablah ta shirya wata walima ta musamman. An kawata wurin da fitilu masu haske kamar taurari, amma a tsakanin wutan, akwai ƙyaftin wuta mai kala ja da ruwan dorawa — alamar tsafin wuta.

Wannan ƙayataccen wurin an shirya shi ne saboda Shaprees da Asmeen, da kuma Abeesh da Nasreen walimar ganawa da juna kafin ayi taro na musamman...


Asmeen ta shiga cikin wurin, sanye da riga mai wedding gown wanda yake jan ƙasi, Idonta cike da tsoro, amma zuciyarta a daure take, domin ta yanke shawarar jurewa komai. Wani sanyi ne ke yawo a jikinta, duk da irin zafin wuta a kusa.

A can gefen ƙarshen filin, Shaprees yana tsaye, sanye da tufafin matsafa, baƙi ƙirin da zinari a gefen wuya. Fuskar sa ta bayyana kwanciyar hankali, amma idanunsa sun bayyana wani nau’in azaba da tsantsar kishi. Ganin Asmeen ya motsa wani abu a cikin zuciyarsa — tunanin Sophia, da kuma wutar fansar da ke ruruwa a jikinsa.

Asmeen ta matso kusa da shi, tana ƙoƙarin karanta fuskarsa. Amma kafin ta iya magana, Shaprees ya fuskance ta da wani murya mai sanyi amma mai ƙarfi:
Ya ce
"Ke ce Asmeen Ƴar matar da ta haifar da ƙaddarar rayuwata"


Asmeen ta kalle shi, tana jin girgiza daga wannan furuci. Amma ta tsaya da tawali’u.

Ta ce:

"Ni ce, kuma ba ni da laifi a cikin abin da ya same ka. Amma na zo ne da niyyar zaman lafiya… ba tsoro ba, ba ƙiyayya ba."



Shaprees ya ɗan murguɗa leɓensa, ya juya gefe kamar yana gujewa idonta. Sai ya ce:

"Zaki auri wuta, Asmeen! Amma ki sani, wutar da nake dauke da ita ba ta da tausayi. Idan kika ƙone, kada ki ce ba a gargaɗe ki ba."

Abeesh da Nasreen kuwa suna zaune a kan wasu tsararrun kujera sun sha kwalliya gwanin burgewa, kana ganin fuskar su kasan akwai farin cikin masoya akan fuskar, kamar babu wani damuwa a cikin zuciyoyin su...

Gefe guda Tasleem ce take zaune akan kujera ita kaɗai sai ɗaga kai take tana zuba ido taga ta ina zata fara ganin Amaar domin baya wurin, gaba ɗaya ta shiga damuwa, a yanzu idan Amaar yayi nisa da ita gani take kamar za'a ƙara cutar da shi ne, bata son zama babu shi, especially idan ta tuno da mungun hatsarin da ya faru da shi sai tayi tunani inama ace fatar jikinsu a haɗe yake yanda duk yanda zai taka tare da ita zai yi, ga yanda take kallon Asmeen cikin tausayawa masu ɗauke da hawaye. Tana jin wani abu na fargaba yana motsawa a cikin zuciyarta — wani ɓoyayyen sirri na mahaifiyarsu yana shirin faruwa wanda ake shirin haɗa wa da Asmeen,
A cikin ranta ta furta.

"Idan dai Shaprees yana da wuta… to, zan zamo ruwa domin kashe wannan makircin..."

A yanzu zuciyar Tasleem tayi sanyi sakamon dakatar da ita da Amaar ya yi akan wasu abubuwan da take so ta aikata akan mahaifiyar su,
Ya zaunar da ita sannan ya mata nasiha akan illar bijirewa iyaye, ya ƙarfafa mata gwiwa akan ta riƙe addu'a sannan tana taya mahaifiyar ta da addu'a cewa Allah ya shirye ta ya dawo da ita kan hanyar turban musulunci,
A lokacin ta zamo kamar ruwa domin a halin yanzu babu maganar da take ji sai na Amaar, a yanzu tunaninta da ƙwaƙwalwar ta da zuciyarta duk sun zamo mallakin Amaar, ta bar hannun Madam Nablah sakamakon ƙarfin Addu'ar da Amaar ya dage mata da shi, baya bacci koda rintsawa ne sai bautar Allah, da yawan addu'o'i akan ahalin gidan nan domin ya fahimci suna fuskantar barazana gaba ɗayansu, balle shi kansa ya rigada yafi ƙarfin Madam Nablah domin cikin zuciyar sa haske ne mai yawan ambaton Allah subhanahu wata'ala, zuciyarsa tafi ƙarfin wani tsafi ya mallake ta, na kusa da shi ma baya tunanin tsafi zaiyi tasiri yanzu a cikinsa....

Madam Nablah ce itama ta shigo cikin tsararren wurin cikin doguwar riga baƙa tana taku cikin ƙasaita, takalmin ta na ƙara ƙaras ƙarass,
duk zuba mata ido suka yi har ta nemi wuri ta zauna a gefen Tasleem..

Asmeen da Shaprees su ma sun nemi wuri sun zauna a wuri na musamman da aka tanadar musu...

Tasleem wacce tunaninta ya zurfafa bata ma san Madam Nablah ta shigo ba, tana tunanin Amaar wanda ake shirin daƙile mata shi a karo na biyu, tana tunanin bazata taɓa Auran kowa ba in ba Amaar ba...

Madam Nablah, wacce ke zaune a kujera na musamman a gefen Tasleem, tana kallon fuskar ta, gaba ɗaya ta gama karantar sirrin zuciyarta ta furta cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce

"Tasleem… bazan taɓa haɗa ki da Amaar ba. sai da zaɓi guda – ya mutu, ko ki manta da shi har abada. Ba zan haƙura da haɗin ƙauna tsakanin zuri’ata da maƙiyina ba."


Tasleem ta lumshe ido, tana jin kamar zuciyarta na fashewa. Amma ta farka da ƙarfin zuciya, ta matsa kusa da Mahaifiyarta ta ce:

"Na san kina ɓoye wani abu, Mommy. Amma na sha wahala sosai don na fahimci wanda nake so, kuma bazan bari tsoron ki ya hana ni bin gaskiya ba. Ko da ace Amaar maƙiyinki ne – me ya sa? Me ya Miki ne da har ya kai haka?"



Madam Nablah ta yi shiru, idonta na sauya launi zuwa duhu, tamkar wuta, Amma kafin ta iya amsawa,
Asmeen ce, ta nufo wurin Tasleem cikin riga ta aure, amma idonta cike da hawaye.

Asmeen ta zo dab da Tasleem sannan ta furta cikin raɗa

"Tasleem… akwai wani abu da ya kamata ki sani. Ban taɓa amincewa da auren Shaprees ba. Na yarda ne domin Mommy ta ce dole, amma ina jin kamar ana shigar da ni cikin wani abu mai hatsari."

Tasleem tana hawaye kafin ta furta wani abu suka ji
wani sassanyar muryar mace, iya su kaɗai ne suke jin sautin Muryar, Sophia ce, ruhinta na yawo a cikin haske.

Tana furta

"Kada ku yarda. Shaprees yana cikin wahala, zuciyarsa ta rikice. Amma wani abu na kirki ya saura a cikin zuciyar sa Kuma Asmeen – ke ce za ki iya kai shi ga warkarwa, ko kuwa ki bar shi ya zama wuta mai cin komai."

Cike da mamaki suke kallon juna ba tare da sun fahimci kome ba, Asmeen cikin tsoro ta ce "Muryar wacece wannan?..."

Girgiza kai Tasleem tayi sannan ta ce "Ruhi ce, ina tunanin tanada alaƙa da Shaprees..."


A wannan lokacin ne Amaar ya shigo filin, duk da an hana shi shiga, cikin kaya na alhurma, ya kalli Madam Nablah sannan ya taka izuwa yanda take a zaune dab da Tasleem.....

Ya ce da ita

"Ki ƙi ni, amma ba za ki hana gaskiya ta bayyana ba. Zai zo lokacin da kowa zai san cewa wannan haɗin aure da kike so – shine makamin da zai juyo ya hallaka ki."

Tasleem na zaune bayan ta lallami Asmeen ta koma wurin Shaprees da zama, tayi farin cikin ganin Amaar a wannan lokacin, Idonta akan Mommyn su tana mata wani irin kallo na ƙiyayya..

Madam Nablah murmushi tayi tare da kawar da kanta gefe ba tare da ta furta komai ba domin a halin yanzu shakkar Amaar take, tasan yanada ƙarfin iko daga haske, sannan yanada tarin addu'o'i wanda shine ya zamo makarin sa idan ta cigaba da kai masa hari itace zata ƙone, hakan yasa ta haƙura ta barsu amma a cikin zuciyar ta tana furta cewa "akwai lokacin da yaƙi zai turnuƙe tsakanin haske da duhu, a wannan lokacin ne zata yi sadaukarwa na musamman ga halattacciyar jini, kuma a lokacin Amaar zai ɗanɗani kuɗar sa...

Dalilin da yasa Madam Nablah ta haɗa Shaprees da Asmeen tsafinta ya sanar mata cewa ƙoyayen haihuwar Shaprees suna hasken ƙarfi wanda amfani dasu zai iya sa ta zama sarauniya mai mulkan bil adam da Aljanun duniya, zai zama sai da umarninta kowa zai aikata abun kansa, ma'ana idan tayi amfani da jinin yaron da Shaprees zai haifa kuma ya zamana jinin yaron ya shafi jinin Asmeen domin sirrin dake jikinta, dalilin da yasa Madam Nablah ta kashe Sophia take kuma ƙoƙarin haɗa Auren sa da Asmeen....

Abeesh kuma akwai shaƙuwar jini tsakaninsa da Madam Nablah wanda bazata iya cutar da shi ba, duk abinda yake mata bazata taɓa cutar da shi ba duba ga yanda ta raine shi, Allah ya ɗora mata ƙaunar sa a cikin zuciyar ta, tin yana yaro kuma tana son yaro namiji, bata shaƙu da ƴaƴanta kamar yanda ta shaƙu da shi ba...

Amaar kuma tin lokacin da wannan ƙibtila'in tsafin da ya same aka sanar mata cewa "Amaar shine makaryin tsafinta sannan shi zai kashe wutar tsafin da ta kunna, tin yana yaro da zaran ta ganshi ko ya zauna kusa da ita sai taji ƙunar azaba a cikin zuciyar ta, sannan idan zuciyoyin mutum biyu suka haɗu to haske zai kawar da duhu, Amaar da Tasleem da zaran sun yi Aure to komai zai bar ta, zata rasa komai, baƙaƙen Aljanun da suke jikinta duk zasu ɓace su barta, ZULQARNAIN wutar dake jikinsa zai narke ya zama ruwa, hakan yasa Madam Nablah take ƙin su......

Bayan kwana 2

Bayan an daidaita lamurra, Amaar ya yanke shawarar cigaba da zama a gidan Madam Nablah don kula da Tasleem. Tasleem kuwa kullum tana kuka, tana rokon gafarar Amaar.
ba wai ƙiyayyar da ta nuna masa ba sai don lokacin da Madam Nablah zata hallaka shi ta kasa ceton sa..

A koda yaushe suna tare ita take masa komai yanzu, ta sauƙar da duk wani girman kanta da jini da kai domin ta ɗauki Amaar a matsayin malama mai bata kariya, ta dogara da Allah sannan ta dogara da Amaar domin ya fita ƙarfin Addu'ar da zai kawar da sharri,
A wannan lokaci Tasleem tana sauƙowa daga upstairs tunaninta yana wani wuri, har yanzu abubuwa basu gama sakin ta ba, a hankali take taka benin bata ankara ba taji ƙafar ta ya zame sai kawai tayi baya zata faɗi, daidai lokacin da Amaar zai wuce ganin ta yasa ya tafi a slow kamar wani zaki ya riko ta tare da mannota kan ƙirjinsa, a tsorace Tasleem ta ɗago nan suka kalli juna,
Murmushi Amaar ya yi tare da faɗin

"Kin taimake ni da kika faɗi a cikin zuciyata, ba tare da kin je ƙasa ba!"

Tasleem ta sakar da wani ƙayataccen murmushin da tinda take bata taɓa yinsa ba mai kyalli, lokaci guda kuma hawaye ya cika idonta. tana magana cikin rawar murya:

"Yaa Amaar... Ka yafe min. Ban san cewa kai ne ba, kuma ban san na cutar da kai ba."

Sake dogon numfashi Amaar ya yi sannan ya ce "Oh my god Beb Tassl har zuwa yaushe zan gaya miki cewa ki cire wannan batun a bakin ki, abinda ya wuce ya wuce meyasa zaki na tunawa, kar ki damu ƙaddarar mu ne tazo da haka, yanzu ba gani kina kallona ba? to Allah bai sa zan mutu ba..."

Amaar ya dafa kafadarta da lallami, ya kuma ce wa

"Koda ban yafe ba, zuciyata ta riga ta yafe. Kuma zuciyar da take gafara, ita ce mafi lafiya."



Abeesh da Nasreen suna cikin sabuwar soyayya mai dauke da barkwanci da nishadi. Su biyu suna da matukar nishaɗi, musamman Nasreen wacce kullum tana kokarin saka Abeesh dariya.
A safiyar yau ne a bayan gida cikin tsararren wuri kamar stadium, a
End Ads