take, madubin ya fara juyawa, yana haska launuka dabam-dabam.
**
“Na ce ku bani haske... Ku bani abin hangowa! Ina son ganin wanda ya juya tsarina, wanda ya tsallake mutuwa! Waye wannan mutumin? Waye wannan da ke ɗauke da ikon da bai kamata ya rayu ba?”
A cewar Madam Nablah.
A hankali, madubin ya fara nuna hoton Amaar a kwance, yana magana a cikin zuciyar sa. Amma fuskar Amaar ta bayyana ne cikin duhu—madubin na ƙoƙarin hana Madam Nablah ganin cikakken fuskar sa.
Madam Nablah ta ƙara daka ƙara da cewa
“Ku buɗa min! Na mallaki ikonku! Na rage rayuka fiye da dubu, ba ku isa ku ɓoye min ba!”
Sai kuma wani murya mai zurfi ya fito daga cikin madubin, murya mai girgiza ƙwaƙwalwa ya furta
“Ba komai zaki gani ba… yana da kariya, wanda ba za ki iya keta ba.”
Madam Nablah ta ja da baya da sauri, hannunta na rawa, idanuwanta na ƙara huda da baƙin iska.
Ta ce
“Kariya? Waye zai iya kare wanda na hallaka?”
Madubin ya koma duhu, ya ɓoye komai. A take, idon Madam Nablah ya fara kadawa da alamar fushi. Ta juyo daga gaban madubin, ta buge wani kwano da ke gefenta.
“Wannan kuwa… bai mutu ba! Wannan mutumin da Tasleem ta harba… akwai wani abu da ban gane ba!”
Ta fara kaiwa da komowa a dakin, tana saƙar zare a cikin zuciyarta.
“Tasleem! Yarinyar nan fa ta fara juya ni. Sannu a hankali mafarkinta na zama gaskiya. Idan ba a hanzarta ba, zata zama babban barazana gare ni!”
Ta tsaya cak. Wani aljanin gefenta ya bayyana daga ƙungurmin inuwa. Ba shi da fuska mai bayyana kamar wata inuwa ce dake numfashi.
“Me kike so mu yi da ita?” – in ji muryar aljanin.
Madam Nablah ta kalli inuwar da ƙyam, sannan ta ce:
“Na shirya. Lokaci yayi da zan sake haɗa wani tsafi—wanda zai mantar da Tasleem komai. Sai dai kafin nan, dole na fara da wanda ya juya makirci na… duk da ban gane waye bane tukuna.”
Ta juyo gaban madubin tsafi, ta ce da ƙarfi:
“Zan tono shi da hannuna! Ko da kuwa daga ƙasan ƙasa yake…”
**
A wannan lokaci, Madam Nablah bata san cewa ƴaƴanta suna kusa da tono sirrinta ba. Amma sai dai wani abu yana yawo a zuciyarta—ana matsa mata daga wani ɓangaren da ba ta fahimta ba. Kuma ita kanta tana fara jin tsoron wani abu: ta fara jin ƙyamar zuciyar Tasleem.
Madam Nablah ta fito daga dakin tsafinta da takalman ta masu tsini suna kara-kara akan tiles din gidan. Fuskar ta cike da damuwa da kulle-kullen mugunta. Duk da bata iya ganin fuskar Amaar ba a cikin madubin tsafi, amma zuciyarta na kara tabbatar mata da cewa akwai wani mai iko da ke kawo cikas ga tsarinta, kuma yana kusa da ƴaƴanta.
Ta iso falon, hasken shuɗi daga hayakin tsafi yana yawo a cikin inuwa. Ta zauna akan kujera cikin izza, sannan ta kalli bango kamar tana ganin ta cikin shi.
“Na tabbatar ɗaya daga cikin su ne. Ko dai ɗaya daga cikin ƴaƴana, ko kuma wani daga cikin waɗanda suke yawo kusa da su. Amma wanda ya dawo rayuwa… shi ne mai haɗari.”
Ta ɗauki wani ƙaramar faranti mai madubi daga saman wata kwandon karfe. Ta zuba wani ruwa kamar jinin jaki a ciki, sannan ta ɗora farantin a saman tafin hannunta.
Tana faɗin
“Dole na yi wani abu kafin su gane komai. Idan har shi mutumin da suka ce an harba bai mutu ba, to Tasleem zata fara tuna da shi. Kuma idan hakan ta faru…”
Ta lumshe idonta, sai ga wani jini ya fara fitowa daga hancinta. Aljani ne ya fara karɓar ikon zuciyarta. Muryarta ta canza, ta koma kamar muryar tsohuwa daga wani zango daban.
“Zamuje a hankali... amma da tabbatacciyar mugunta.”
Ta dafa ƙirjinta, idonta na rawa. Sai wata murya daga cikin kanta ta ce:
“Nablah, lokaci yayi da zaki sake kunna Randa-t-Tasfir. Ki shafa mantau a zuciyar Tasleem. Ki goge komai da zai tuna mata da wannan mutumin!”
Madam Nablah ta ɗauki wasu garwashi da ganye, ta sa su a wani kwanon zinariya. Ta kunna wuta, sannan ta zuba wani ruwa wanda ya fara baƙar da iska gaba ɗaya.
Ta furta
“Tasleem! Kina jin na? Daga yau, duk abinda ke da alaƙa da mutumin nan... zaki fara mantawa da shi. Kamar bai taba rayuwa a zuciyarki ba!”
Ta daka ƙara, idonta ya ɗauke da haske. A wani lokaci na ɗan kankanin lokaci, wani hazo ya tashi daga gindin falon da Tasleem ke ciki.
**
A gefe guda kuwa...
A cikin ɗakin Amaar, yana kwance, sai yayi wani nishi mai nauyi. Idonsa ya buɗe kadan, yana jin wata ƙuna a ƙirjinsa. Kamar an taɓa sa shin. Ya fahimci cewa ana ƙoƙarin juyar da tunanin Tasleem.
“Wannan warin... tsafi ne... ita ce...” – ya furta a hankali.
Ya ɗan yi ƙoƙarin tashi, sai dai jikinsa bai gama karfi ba yana furta
"Dole in kare ta kafin ta manta da ni gaba ɗaya!"
**
Madam Nablah ta sake lumshe ido, tana jin nasara a zuciyarta. Amma abinda bata sani ba shine:
makircinta yana samun cikas daga wani ƙarfin da ba a iya gani da ido—karfin da ke cikin zuciyar Tasleem da Amaar... wanda zai iya karya kowanne irin tsafi.....
Lokacin yamma ya gabato Rana ta fara dusashewa, iska tana kadawa da sanyi mai ɗauke da wani warin tsami. Tasleem tana cikin ɗakinta, zaune a gefen gado, tana kallon bango da zuciya mai nauyi...
Idonta a lumshe, amma hankalinta bai kwanta ba. Kamar wani abu na yawo a zuciyarta yana karairaya mata tunani. Tana ƙoƙarin tuna fuskar mutumin da ta harba—wanda ke biyo mata a mafarki da a zahiri. Amma yanzu… komai na fara dushewa.
Cike da damuwa take faɗin
“Shin... har gaske na taba sanin shi? Me yasa nake jin kamar... ya shuɗe ne a raina?”
Ta dafe kanta.
Da gaggawa, idanuwanta suka buɗe.
“Sunansa ma... sunansa?”
Kamar wata zararriya tana tunanin abubuwa da yawa a cikin zuciyar ta, Tana ƙoƙarin tunawa, amma zuciyarta na hana ta. Fuskar da ta saba gani duk lokacin da ta lumshe ido yanzu kamar hazo take gani
Ta ce
“Wayyo Allah... menene ke faruwa dani?”
Ta miƙe daga inda take, ta nufi madubi tana kallon kanta. Amma da ta kalli fuskar ta sosai… sai kawai taga wata surar mace a cikin madubin tana murmushi. Amma wannan murmushin... bai da armashi, yana da shaiɗanci da ruɗani.
Sai kwatsam, madubin ya fashe da wani irin ƙara, wani hazo ya fito daga ciki, ya rufe fuskar Tasleem. Ta ɗan zabura baya, tana girgiza kai tare da faɗin
“Babu wanda zai iya... juya zuciyata... babu wanda zai manta mun da shi...”
Amma a cikin zuciyarta, muryar wani da ba nata ba take ji ana furta
“Babu Amaar. Bai taba wanzuwa ba. Wannan tunanin karya ne. Wani abu ne kawai da kike sawa a ranki... kuma lokaci ya yi da zaki manta da shi har abada.”
A daidai lokacin, Nasreen da Asmeen suka dawo gida. Suna shiga cikin falo, suka ji sanyi mai ɗauke da warin wani abu kamar ƙonanniyar ganye. Suka kalli juna.
Nasreen ta ce
“Asmeen... kina jin wani abu?"
Asmeen ta ce
“Ina jin kamar tsafi. Dama kinsan gidan nan baya zaman lafiya.”
Suka nufi ɗakin Tasleem, suna kiran sunanta.
“Tasleem! Kina lafiya?”
“Ki buɗe mana ƙofa...!”
Amma Tasleem tana tsaye a gaban madubi, idonta baƙi ƙal-kal, tana kallon kanta kamar wata da bata gane kanta ba. daga nan sai hawaye suka fara gangarowa daga idonta. Ta kama kanta da hannayenta biyu tana faɗin
“Ni wacece ne? Waye nake nema? Me nake tunawa ne...? Shin ina mafarki ne?”
Nasreen daƙer suka buɗe ƙofar suka shige da sauri, suka ruga da gudu tare da rungumar ta.
Nasreen ta ce
“Tasleem! Menene ke faruwa?”
Itama Asmeen tambayar ta tayi tana faɗin
“Me ya sameki haka?”
Tasleem ta kalle su, idonta cike da hawaye ta furta
“Waye wanda na harba? Me yasa nake jin kamar na rasa wani bangare na zuciyata? Me yasa nake jin kamar an sace ni... daga ciki?”
Asmeen ta kalli Nasreen, zuciyarta cike da tsoro.
Nasreen cikin kuka take faɗin
“Tsafi ne... wallahi tsafi ne ke kokarin karya ta. Amma bazan bari ba.”
**
A gefe guda...
Madam Nablah tana zaune a ɗaki mai duhu, tana jin murya cikin kanta na faɗin:
“Zata fara mantawa... zata daina tunawa... lokaci yana tare da mu.”
Amma kuma... wani canji ya fara tasowa daga zuciyar Tasleem. Wannan baƙin hazo da tsafi… yana samun cikas daga wani ɓangare na ruhinta da tsafi ba zai iya shafanta ba, tsatsan ƙauna da soyayyar Amaar da bata da izinin mantawa da ita.
★★★
Yamma ta ƙure. Rana ta narke cikin duhun dare. A cikin ɗakin Amaar, wutar fitila tana kunne da hasken rawaya, yana zaune kan gado, bandage har yanzu na manne a kirjinsa, idanunsa a lumshe, numfashinsa mai nauyi. Zuciyarsa na tafasa da abubuwa da dama, amma wani abu daban ya fara ƙona shi tun daga ciki…
Yayi ƙoƙarin rufe idanu domin samun natsuwa, amma a zuciyarsa yana jin wani irin bugun bugun zuciyar wata – bugun zuciyar Tasleem.
“Tasleem...” ya furta a hankali. “Ina jin kamar tana cikin haɗari...”
Wani irin ƙamshi mai wari da tsami ya doki hancinsa duk da babu komai a ɗakin. Sai zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi.
“Ba daidai bane... zuciyarta na ƙara shigewa cikin duhu. Wannan ba Tasleem ɗina bace... an fara rugujeta daga ciki...”
Ya miƙe a hankali, duk da jikin nasa har yanzu yana rauni. Amma zuciyarsa ta yi nauyi da damuwa. Ya isa gaban madubi yana kallon kansa, ya dafe gefen bango da hannunsa ɗaya, idanunsa sun canza launi, wani haske mai kama da ruwan sama ya fara bayyana a jikin sa.
A hankali ya furta
“Na sha alwashin kare ta... ko da da rai na ne...”
Sai kawai ya fara jin wani murya daga cikin kansa – muryar wani wanda ya ceci rayuwarsa a lokacin da aka jefa shi cikin ruwa shekaru ashirin da suka wuce.
“Lokaci ya kusa, Amaar. Ikonka yana dawowa, amma ƙiyayya da soyayya sun fara yakar juna a zuciyar Tasleem. Idan tsafi ya cinye zuciyarta bazata tuna da kai ba… sai dai ka rasa ta har abada.”
Ya dafe kirjinsa.
“A’a... bazan bari hakan ta faru ba. Ko da zata ƙi ni... zan kareta. Amma ban isa na bari ta mutu da bakar zuciya ba...”
A cewar Amaar.
Sai kawai wani haske mai ɗumi ya fara fita daga hannunsa na hagu, yana yawo a cikin ɗakin – wani ƙaramin iftila’i da ya nuna cewa ikon da aka ɗora masa a lokacin da aka ceci rayuwarsa yana dawowa a hankali.
Ya furta cikin salo:
“Dole in gane hanyar shiga cikin mafarkinta... domin a can za a yi yaƙin farko.”
A wannan lokacin, wayarsa ta ɗauki kira – Nasreen ce ke kiran sa da gaggawa.
“Amaar! Ka shirya, mun dawo gida... Tasleem na cikin wani mummunan yanayi! Mun iso yanzu amma ba zamu iya samun taimako ba… sai kai!”
Cikin rawar jiki da ƙarfin zuciya, ya ce:
“Ki ƙara riƙe ta, ban da kowa da zai iya fitar da ita daga wannan duhun sai ni.”
Ya miƙe da ƙyar, ya ɗaura rigar sa, duk da jiki yana rauni, amma zuciyarsa ta fara sauya tsari – daga rauni zuwa azama yana faɗin
“Tasleem... ba zan bar ki a hannun zuciyar tsafi ba. Komai zai faru, sai kin tuna da ni.”......
A ɗakin ta dake saman bene, Tasleem ta haye gado tana karkarwa, idanunta sun lulluɓe da hawaye, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma abun mamaki – tana jin wani abu a ranta, kamar ana tunkudata cikin wani wuri mai duhu, amma daga ciki akwai murya – muryar da ba ta san daga ina take fitowa ba.
“Ki guje wa hasken zuciyarki, Tasleem… ki rungumi duhu… ki yarda da ƙiyayya, kin fi ƙarfi idan zuciyarki ta cika da tsana...”
Tana riƙe kanta, tana girgiza kai:
“A'a… ba haka nake ba. Ni ba mugunwa bace... Me yasa nake jin kamar zuciyata tana canzawa? Me yasa nake jin kamar bana ƙaunar kowa... har kaina ma?”
Nasreen da Asmeen sun juma da barin ɗakin sakamakon tiririn wutar ɗakin, gaba ɗaya tsoro ne a cikin zuciyoyin su...
Tasleem ita kaɗai ce a ɗakin kuma daman ita kaɗai ake buƙata.
Wata ƙatuwar guguwa ta mamaye ɗakin ta – hasken wuta ya ɗauke, labule ya fara yawo akan iska, zafin daki ya hauhawa. Cikin wannan yanayi, ta fara ganin madubi a bango yana sauya launi – ya koma baƙin zurfi kamar ramin shaidanu.
Sai kuma ta fara ganin hoton kanta a cikin madubin – amma ba Tasleem bace kamar yadda ta san kanta ba. Wata sigar ta ce – idanu jajaye, gashi a warwatse, tana murmushi da baki cike da jini.
“Kece Tasleem na gaske... Kece zuciyar da aka daƙile. Ki zo ki karɓi ikona... Ki manta da Amaar, ki manta da kowa...”
Tasleem ta ja da baya tana kuka, ta durƙusa a ƙasa, tana rokonsu su daina:
“Ku barni! Ku bar zuciyata! Ni ba haka nake ba!”
jikin ta ne ya fara rawa da ƙarfi, kamar wutar lantarki na shiga jikinta sai da ta saki wani irin ƙara mai ban tsoro – wani haske ya fita daga cikinta na dan lokaci, ta sake faɗuwa.
Wannan tsafi na ƙoƙarin cire hasken da ya rage a ranta – ƙaramin haske wanda har yanzu bai mutu ba.
A ƙasan falo kuma su Nasreen da Asmeen ne suna cikin firgici. Sai da suka yi yunƙurin hayewa sama, sai suka tsaya cak – saboda ganin Madam Nablah tana tsaye a tsakiyar falo da idanu kamar ba na mutane ba, tana kallon saman bene, tana karanto wata ruɗaniyar addu’a cikin yaren aljanu.
Nasreen ta matsa kusa da Asmeen cikin muryar tsoro:
“Asmeen... mece ce wannan murya haka? Kuma me ya faru da Mommy...? Kamar ba ita bace...”
Asmeen ta ce:
“Idan har Tasleem tana sama yanzu… to akwai buƙatar mu dakatar da wannan... Amma ba mu da iko...”
A wannan lokacin ne su ka ji ƙarar motar Amaar ya tsaya a ƙofar gida.
Lokaci ya ƙure ko Amaar zai iya tsallake duhun da ke hana kowa hawa sama, ko kuma Tasleem zata faɗa tarkon da Madam Nablah ta kulla tun tuni.
“Tasleem... ki tsaya har zuwa isowata,” Amaar ya furta a zuciyarsa, yana kallon saman gidan da hayaki da hasken duhu ke fitowa…
Amaar ya fito daga motar da sauri. Da kallo guda ya gane gidan na cikin wani yanayi da ba a saba gani ba hayaki mai duhu yana fita daga tagogi, iska tana kadawa kamar hadari na shigowa, kuma wutar rana ta ɓace daga saman gidan duk da gabar rana ce.
"Tasleem..." ya ambaci sunanta da ƙasa cikin murya, idanuwansa sun cika da tsoro da damuwa.
Kamar wani haske daga sama, sai Amaar ya fara jin wata irin ƙara a kunne, kamar ƙira daga wani ruhin tsarkaka – kira wanda ya saba jin sa tun lokacin da aka ceci rayuwarsa a cikin ruwa shekaru da suka wuce.
A wannan lokacin ne wani murya mai zurfi ta dawo masa a rai:
"Lokacinka yayi, Amaar. Ka fuskanci duhun da ya raba ku... Ka shiga da zuciya tsarkaka, domin kai kaɗai ne zai iya warware abinda aka daɗe ana gina wa."
Amaar ya lumshe ido, ya dafa ƙirjinsa inda aka harbe shi. A wurin nan yake jin ƙarfinsa – ruhinsa yana ɗauke da haske wanda ke iya karya tsafin da Madam Nablah ta ƙulla.
Sai da yaja numfashi, ya furta:
“Bismillahir Rahmanir Rahim... Allah ka bani ikon tsallake duhun da zai hana ni ceton zuciyar da ta rasa kanta.”
Da haka ya taka ƙafar sa cikin falo.
Yayin da ƙafarsa ta taka ƙasa – kamar ƙasa ce ta wani duniya. Lokaci ya tsaya, iska ta tsaya, sai wata ƙara ta tashi daga cikin hayaƙi:
“Wannan gida ba naka bane, ruhun wuta zai karyaka, ka janye Amaar!”
Madam Nablah ce ta furta hakan da wata murya da ba kamar ta ɗan adam ba. Idanunta sun yi jajaye, tana tafiya a hankali zuwa ga Amaar, tana ɓalle masa karatu a harshen aljanu.
Amma Amaar bai ja da baya ba. Ya matsa kusa da ita. Kowane taku yana fitar da haske daga ƙafarsa – kamar yana takawa a wani wuri na tsarki.
Ya tsaya gaban Madam Nablah:
“Na dawo ba don na yaƙe ki ba, sai don na ceci abinda kika kusan lalata... Ina neman ceto Tasleem daga duhun da kika jefa ta ciki!”
Kafin Madam Nablah ta yi wani ƙari, Amaar ya furta kalmomin addu’a da aka koya masa lokacin da ya rayu bayan fadowa cikin ruwan nan, kalmomi da ke iya karya tsafi mai duhu:
“Allahu Akbar kabīra, walhamdulillāhi kathīra, wa subhānallāhi bukratan wa aṣīla...”
Haske ya buɗe daga jikinsa, ya haura sama, ya daki tagar da ke zuwa sama inda Tasleem ke kwance cikin suma. Wata ƙara ta tashi daga cikin bangon madubi — madubin tsafin ya tarwatse!
Madam Nablah ta ja da baya tana kururuwa:
“Kayi kuskure Amaar! Kai ne silar lalacewata... Amma ba zaka fitar da ita daga hannuna ba!”
Sai ga Abeesh ya fito daga ɗaki, cikin fushi da ƙarfin zuciya. Ya tsaya gefen Amaar:
“Zan tsaya tare da kai Yaya... Duhu bai isa ya cinye gaskiya ba.”
Nasreen da Asmeen suma sun tsaya a ƙofa suna karanta Ayatul Kursiyy da Suratul Falaq a ƙasa cikin fargaba. Haske yana cigaba da bayyana...
Saman ɗaki kuwa, Tasleem ta fara motsawa. Idanuwanta ya buɗe amma har yanzu tsananin hayaƙi da duhu ya