x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 188

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
rufe ta...


Jirjirin iska ya fara kadawa cikin falon, ƙarar murya da karatun Ayatul Kursiyy daga bakin su Nasreen da Asmeen na karuwa, Abeesh ya tsaya gefen Amaar yana girgiza kai cikin kuka, zuciyarsa cike da jin zafin ƙaddara da yanda duniya ta juya musu, amma a tare da dukkan su guda hudu, haske yana fitowa daga ƙasan ƙafafunsu, yana tunkuɗe duhun da Madam Nablah ta shafa.

Madam Nablah tana ja da baya, tana furta kalmomi cikin harshen da ba a fahimta, jikin ta yana ƙara canjawa – kamar ba ta mutum ba, ta fara ɓarin jini a bakinta da hancinta, hakan ya nuna cewa ƙarfin Amaar yana cin galaba akan tsafinta.

Amaar ya kalli sama, inda ɗakin Tasleem ke sama – ya lumshe idonsa.

A zuciyarsa ya ce:

“Allah ka karya duk abin da ke tsakanin mu da ita. Ka warware igiyar da aka ɗaure rayuwarmu da ita ta ruɗu.”



Sai da ya taka step ɗaya, ya fara hawa matakalar bene...

Amma kafin ya kai ƙofar matakala – ƙarfin shocking ya saukar masa daga sama!

Zuuuummmm!!

Wutar da Madam Nablah ta haɗa shekaru ashirin da suka gabata don hana shi da Tasleem haduwa ta tashi daga cikin ƙasa ta buge shi da ƙarfi! Amaar ya durƙusa ƙasa da ƙyar, ƙirjinsa yana bugawa, numfashinsa yana fita kamar wani wanda aka yi masa lantarki.

“Subhanallah…” ya furta a hankali.



Sai Abeesh ya nufo shi, amma shi ma shocking ɗin yana so ya buge shi, sai dai Amaar ya daga masa hannu:

“Kada ka kuskura ka taɓa ni yanzu… wannan shirme ne da aka haɗa shekaru da suka wuce... Sai ni kaɗai zan iya fasa shi.”



Ya dafa ƙirjinsa. A can ya ke jin wani tsarki na waje da baƙin ciki na ciki – rikicin da yake cikin zuciyarsa yana neman karya masa ƙarfin ruhi.

Idanunsa sun fara kadawa da hawaye, ya tuna yanda suka shaƙu da Tasleem tun suna yara... yanda suka rike hannun juna da dariya a bakin su... yanda take cewa masa:

"Amaar, karka taɓa bari na..."



Sai ya furta da ƙarfi ya ce

“Na rantse da Allah albarkacin wannan rana... ba zan taɓa barin ki ba!”



Da haka sai ya miƙe da ƙarfin zuciya, ya cigaba da hawa matakala, kowane mataki da ya taka – shocking yana bugunsa – amma haske yana ƙara fitowa daga jikinsa. Tsafi yana ƙonewa kamar ganyen busassu.

Kafin ya kai sama, wani sabon salo ya bayyana a cikinsa – kalmar da ya daɗe bai furta ba ya furta a zuciyarsa:

"Ya Allah, idan har ni ba zan iya ceton ta ba... ka tura wanda zai iya. Amma kar ka bar rayuwarta cikin duhu!"



Da haka, Amaar ya isa ƙofar ɗakin Tasleem. Ya jawo handle ɗin ƙofar a hankali… ƙofar ta buɗe da ƙara kamar ana warware sarƙar duhu.

Tasleem na kwance a kasa cikin wani zobe na hayaki, idanunta a lumshe, jikin ta yana rawa, sai wata murya daga cikin bangon dakin ke cewa:

“Kar ka taɓata, Amaar... idan kuka kusanci juna – za ku ƙone tare!!”



Amma Amaar bai tsaya ba. Ya tako a hankali, yana sauke ajiyar zuciya. Ya durƙusa a gabanta.

Yana kallonta cike da tausayi.

“Zan fi son in kone tare da ita, fiye da barin ta cikin duhu.”



Da hannunsa ya mika ya dafa hannunta...

Zuuummmmmmmm!!!

Wani karfi na shocking ya fasa dakin gaba daya!

Haske ya tashi daga hannayensu, duhu ya washe! Idanun Tasleem suka buɗe cikin wani irin girgiza... suka zuba ido cikin na juna…




Shin zata gane Amaar ne?
Shin ruhinta zai tuna da shi kafin tsafi ya sake mamaye ta?
Shin Madam Nablah zata ƙara wani sabon farmaki?

*GAREKU MASU KARATU ASHA KARATU LAFIYA ....*


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 29 to 30



★★★

Tasleem ta zuba idanu cikin na Amaar, idanu masu cike da hawaye da hasken da ke tasowa daga ƙasan ruhinta. Wani sauti mai rauni ta fito daga bakin ta, kamar tana ƙoƙarin fadar wani abu, amma muryarta ya makale. Amma cikin zuciyarta, wata ƙwaƙwalwa ta fara motsawa... wani abu da ba a manta shi da sauƙi ba.

“Amaar...”

Kalmar ta fito daga bakinta cikin tattausar murya,
Amaar ya ji ta kamar an buga gangar farin ciki a kunnen sa.

Idanunta sun cika da hawaye. Wani ɓangare na zuciyarta na kokarin faɗuwa cikin duhu, amma wani ɓangare kuma – hasken da ke fitowa daga hannun Amaar – na tunasar da ita soyayya, amana, da wani alkawari da suka ɗaura tun suna yara.

Madubin bangon ya fara fashewa gaba ɗaya. Wata murya mai ƙarfi ta fito daga cikin duhun:

“A'a! Wannan ba zai faru ba! Zuciyarta ta nawa ce! Na shafe komai da kuke kira ƙauna! Babu wuri gare ka a zuciyarta!”
Muryar Madam Nablah ne.

Madam Nablah ta haura sama cikin siffar da ba mutum ba – idanuwanta jajaye kamar wuta, fuskarta na nuna zafin tsafi da haushin haske. Amma kafin ta karasa kusa da su, wata gagarumar igiyar haske ta haska dakin gaba ɗaya!

Wani murya daga sama – mai laushi kuma mai ƙarfi – ta busa kamar iska, tana cewa:

“Lokaci ya ƙare, Nablah. Tsafi ba zai iya shafe abinda Allah Ya rubuta ba. Zuciyar da aka haɗa da gaskiya ba za ta taɓa zama duhu dindindin ba.”

A wannan lokaci ne Amaar ya daga hannunsa na hagu – inda ikon da aka ɗora masa ya fi ƙarfi. Haske ya bayyana daga can, kamar hasken safi ya bayan yanzu dare ne,
Ya ce da karfi:

“Ki bar mu haka Aunty Nablah! Tsafinki ya ƙare – zuciyar Tasleem ba wurinki bace!”

Madam Nablah tayi ƙara mai tsayi da zafi – jikin ta ya fara tarwatsewa cikin hayaki. Wutar dake fitowa daga cikin jikinta ta dawo masa, Cikin wani kakkarfan ƙara ta bace gaba ɗaya cikin hasken da Amaar ya bayyanar, kamar ba ta taɓa wanzuwa ba.

Zuuuwwwwww!

Duhu ya ɓace. Gidan ya koma kamar yadda yake. Hayaki ya washe, Tsit ya sauka – tsit ɗin da ke bayyana ƙarshen gwagwarmaya....

Amaar yana riƙe da hannun Tasleem. Ita kuma, idanunta sun cika da hawaye, tana kallon sa ba tare da rudani ba. Tana jin numfashinsa, kuma zuciyarta na amsa kira – kira na ƙwaƙwalwa, soyayya, da alkawari.

“Amaar… na tuna. Na tuna komai,
na tuna wallahi, kai ne Mommy na ta jefa cikin ramin ruwa sannan ta canza daga mutum zuwa dabban daji, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni mi musiba ti wa aklif li khairan min ha..."


A lokacin ta fashe da kuka. Ya jawota jikinsa, duk da har yanzu yana ɗan jin karamin wutar shocking har yanzu, amma bai bar riƙonta ba.


"Ki kwantar da hankalin ki, ban mutu ba, na dawo gare ki my Tasleem,
kuma nace miki ba zan taɓa barin ki ba, na dawo kenan....”

Tasleem tana kuka ta ce "Ya Amaar nayi kewar ka sosai, ka dawo gare ni amma nayi kuskure rashin fahimtar ka, kayi hakuri Ya Amaar na aikata kuskure..."

Toshe mata baki ya yi tare da faɗin "ki dakatar da wannan shirmen nakin, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai ƙara faruwa da ke, sai dai mu tsara yanda zamu gudanar da sabuwar rayuwa ...."

Tasleem tana kuka ta rungume shi sosai...


Asmeen, Nasreen, da Abeesh sun hau bene da sauri. Da suka gan su riƙe da juna cikin dakin da aka cika da duhu kafin yanzu, suka tsaya cak da hawaye a idanu, zuciyoyinsu cike da mamaki da farin ciki.

A ƙasa kuwa, wani ƙaramin wuri ya buɗe – kamar ƙofofin aljanu – daga cikin falo. Amma kafin wani abu ya fito, wani sautin ƙaho na haske ya buɗe sama, yana hana duhun sake hawa.

Haske ya cigaba da cika gidan, kamar ana wanke dukan ƙwayoyin cutar da suka jima a can. Tsafaffen gida ya dawo gida. Haske ya dawo. Gaskiya ta yi nasara akan tsafi.


---

Kwana biyu bayan haka...

Tasleem na zaune a gefen ruwan swimming da ke bayan gida, tana kallon ruwa, hannunta na cikin na Amaar. Sunyi shiru na lokaci mai tsawo, kafin ta ce cikin sanyi:

“Duk lokacin da zan fara mantawa da wacece ni... kai kake tuna min.”

Amaar ya ce, yana kallon ta da murmushi:

“Saboda zuciyarmu daya ce. Kuma idan ina da rai – zan kasance a kusa da ke.”

A wannan lokacin wuni suka yi a tare wuri ɗaya.....


★★★★★


Ɓangaren Shaprees

Duk abubuwan da yake faruwa a gidan Madam Nablah ya sani amma sai dai bai ɗauki hakan a matsayin damuwar sa ba, abinda ya kawo shi cikin ahalin su shine ɗaukar fansa, har yanzu akwai wannan ƙudirin a zuciyar sa, kuma ya shirya akan mallakan tsafi shima, yana son ya karɓi ikon tsafi saboda wata manufar sa, kuma ya sa a ransa cewa sai ya dawo da Sophia rayuwa.....

Madam Nablah ta ajiye makamin yaƙin ta akan Amaar a wannan lokacin domin sai ta yi shiri na gaske amma har yanzu ƙiyayyarsa ruruwa yake a cikin zuciyar ta,
ta koma kan Shaprees domin amsa ƙiransa, kallo ɗaya tayi masa ta gama karantar sirrin zuciyarsa na son karɓan tsafin wuta domin dawo da Sophia matar sa,
Madam Nablah maimakon taji wani abu a ranta sai ma ta ƙarfafa masa gwiwa akan karɓa masa tsafi a wurin shugabanta ZULQARNAIN.

Bayan kwana biyu ta shirya kai shi wurin tsafin ta.

Idan ya tuna wannan ranar, yakan ji kamar ya haukace
Daren da Shaprees ya rasa Sophia, zuciyarsa ta mutu kafin jikinta ya mutu. Wani murɗaɗɗen baƙin ciki ya shaƙe zuciyarsa. Bai gane yadda aka kashe matarsa ba, amma wata mata mai idon zinariya ta bayyana a lokacin da zuciyarsa ke tsaka da faɗuwa. Ita ce Madam Nablah.

A yayin da yayi shiru zuciyarsa tana tuna masa da wasu abubuwa da yawa, kwatsam ya ji Madam Nablah ta furta

"Ka rasa? Ina jin wannan azabar," ta ce cikin wata murya mai zuma amma mai daɗin daci. "Amma akwai hanyar da za ka ƙwato darajarka—da ikon fansa."

Shaprees bai ce komai ba. Amma ido ya cika da shakku da hasarar da yake son mayar da fansa.

“Zan kaika wajen wanda ya bani iko. Idan ka dace, zai baka wuta.”


---

A Ƙasar Tsafi

Sun sauka a wani wuri mara rana, inda haske ke fitowa daga harshen wuta da ke yawo a ƙasa kamar kogi. Wani katafaren mutum mai jikin toka da ido kamar gawayi yana zaune akan wani tsafaffen kujera, kujerar hawa-hawa ne da igiyoyin zinariya ke zagaye da shi. Wannan shi ne ZULQARNAIN, shugaban tsafin wuta.

ZULQARNAIN ya duba Shaprees kamar yana leƙen ƙwakwalwarsa. Sai ya yi magana:

“Wuta bata baiwa zuciya mai sanyi iko. Amma ina jin baƙin cikinka yana ƙone maka tunani...."
Madam Nablah ta ce "kai mai niyya ne... Za ka iya ɗaukar fansa da wuta, ko wuta ta ƙone ka gaba ɗaya.”



Madam Nablah ta ɗora hannunta a kafadar Shaprees, kamar tana turashi gaba cikin mawuyacin zaɓi. Shaprees ya matso kusa da gurin wuta.

“Zan ɗauka. Ko da kuwa zata ƙone ni gaba ɗaya.”



ZULQARNAIN ya ɗaga hannunsa sama, wuta ta fita daga ƙasa, ta dunkule cikin siffar kwallo. Ya miƙa wutar ga Shaprees. "Yanzu kai ne matsafi. Ka ɗauki wutar zuciyarka, ka horar da ita. Amma ka sani—duk wanda ya ƙone da wannan wuta, ba zai sake zama ɗan adam ba.”

Shaprees ya karɓi wutar, tana shiga cikin zuciyarsa ta hanyar idonsa. Sai jikin sa ya ƙone da wuta amma bai jin zafi, sai wata irin shauƙin iko da duhu.

Madam Nablah ta murmusa. “Yanzu ka zama nasa. Ka zama na wuta. Amma ka tuna, ni ce nake da mafita a ƙarshen hanya.”


Bayan komawar su Shaprees ya ƙera wani gidan ƙasa dake cikin daji anan yake cigaba da ƙirƙirar sabbin tsafikan sa,

Shaprees yana koyon amfani da wutar – da nufin dawo da Sophia – amma wata zuciya ta fara tashi a cikinsa wacce ke tambayar: “Ina sakamakon wannan iko idan ba zan iya dawo da ke ba, Sophia?”


Wurin da Shaprees ke zaman dare ya dishe da duhu, sai kwatsam wani haske mai taushi da ƙamshi irin na fulawar Firdausi ya cika ɗakin. Shaprees ya buɗe idanuwansa da sauri, zuciyarsa na bugawa, domin har yanzu yana fama da azabar tunanin Sophia. Amma a can — cikin wannan haske — ta bayyana.

Sophia, kamar yadda ya santa, amma cikin ƙarin ƙyalli da kwanciyar hankali. Hawaye yana bin fuskarta mai tsabta, amma idonta yana da ƙarfi fiye da yadda ya taɓa gani.

“Meyasa kayi haka, Shaprees? Kana da zuciya mai kyau amma yanzu ka gusar da ita...” ta ce cikin murya mai taɓa zuciya.
“Ina tare da ayoyin Allah. Kai kuma ka karɓi tsafi. Taya kake tunanin zan kusance ka? Dawo da ni rayuwa ba zai taɓa yiwuwa ba. Na rigada na bar duniya, wacce ta kashe ni. Na bar ta da Allah.”



Shaprees yana kallon ta da hawaye a ido, amma wutar zuciyarsa na ƙone masa. Hannunsa ya ruɗe, yana ƙoƙarin isa gareta.

“Babu amfanin ɗaukar fansa,” Sophia ta ci gaba da kuka. “Ka auri ɗaya daga cikin ƴaƴan Madam Nablah kamar yadda ta umarta. Sunada kyakkyawar zuciya, haske ne ke fita daga jikinsu… amma kada ka cutar da su.”



Shaprees ne ya yi magana cikin ɗaga murya — cikin masifa da ɓacin rai ya ce

“To me yasa kika bar ni, Sophia? Na rasa komai! Na rasa ki! Kuma yanzu kina ce min in bar fansa? Ba zan bar jininki ya zube a banza ba. Wallahi sai na ɗauki fansa. Sai Madam Nablah ta san cewa mutuwar ki ba zai tafi a iska ba!”



Ya runtse idonsa da ƙarfi, yana juyi kamar mahaukaci, ya cigaba da cewa

“Na san ba zan iya tin karar Madam Nablah ba – ikon ta ya fi nawa. Amma zan cutar da ƴaƴanta. Tasleem da Asmeen duk zan mallake su – domin ta ji zafin da na ji!”



Haske ya fara ja baya. Sophia tana kuka ta fara ɓacewa. Amma kafin ta bace, ta faɗi abu na ƙarshe:

“Ka shige cikin duhu, Shaprees. Amma ka sani, ba kowanne haske ne zai daina bin ka har gobe ba. Tasleem da Asmeen — idan ka cutar da su — hasken da ke cikin su zai ƙone zuciyarka fiye da kowacce wuta.”


Shaprees ganin Sophia ta ɓace ne yasa shi goge hawayen fuskar sa, yana sakin numfashi mai nauyi, zuciyarsa ta tsinke gaba ɗaya. Babu abin da ya rage illa fansa. Ya yi shiru, sannan ya ce:

“Wuta ta bani ƙarfi. Amma yanzu lokaci ne da zan fara shuka ta cikin ƙauna – ƙaunar ƙarya. Zan yaudari ɗaya daga cikin su, ko duka. Zasu zo mini da zuciyar su, amma ni kuwa zan tare su da azaba.”



Duhu ya gama shanye shi. Amma hasken Sophia ya bar ƙura mai kyau a cikin zuciyarsa – wacce zata sake bayyana wata rana... amma sai bayan ya gamu da ɗaya daga cikin ƴaƴan Madam Nablah, ɗaya wacce zuciyarta zata tsaya masa har ma ta motsa wutar zuciyarsa cikin sabuwar hanyar da bai zata ba......


Shaprees ya zauna cikin duhun dakin ginin tsafi, fitilar bakaken harshen wuta suna walƙiya a cikin kwayar idonsa. Ya ɗora hannunsa kan kwanon giyan madubi wanda ke nuna fasalin Sophia—matarsa da ta rasu sakamakon tsafin Madam Nablah. Wani baƙin hayaƙi mai wari ya taso daga cikin kwanonin, yana dunkulewa cikin siffar mace mai haske—kamar Sophia, amma kamar ɓoyayyen haske.

Ya furta

"Na karɓi iko saboda ke, Sophia," ya faɗa cikin muryar da ke cike da ƙiyayya da ɓoyayyen ƙauna. "Zan dawo da ke. Ko da hakan zai ƙone duniya baki ɗaya."

Madam Nablah ta shiga cikin ɗakin ta hanyar hayaki, murya tana ɓullowa da ƙarfi amma da wani salo mai kwantar da hankali. "Shaprees... lokaci ya yi. Ɗaya daga cikin ƴaƴana zata zama naka. na sake baka zaɓi a karo na biyu shin Tasleem... ko Asmeen?.."

Shaprees ya yi shiru. Idanunsa suka yi duhu, amma cikin zuciyarsa akwai wani ƙaramin ɗan haske—ba hasken tsafi ba—hasken Sophia, da nufin fansa...

"Zan zaɓi Asmeen," Shaprees ya faɗa, yana kallon Madam Nablah da ido mara ƙyalli. Amma zuciyarsa tana faɗin cewa
"Wanda kika ba ni, shi zan yi amfani da shi wajen rugujewa. Ko Asmeen ce, ko Tasleem. Wata rana sai kin ɗanɗani zafin da kika saka min..."

Madam Nablah ta murmusa. "Ka zama namu gaba ɗaya yanzu, Shaprees."


★Bayan Sati biyu

A Ƙarƙashin Ƙasa

A can wani ƙarƙashin duhu wanda babu wanda ya sani sai Shaprees, yana ƙirƙiran wani sabon
End Ads