x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 180

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ko ya yi gigin tsayawa da su..."

Amaar maida idonsa yayi kan su yana mamakin irin furucin da ake akan su, cikin sassanyar murya ya furta "wai da gaske ne?..."

Asmeen girgiza kai ta fara yi tana kuka, a razane Nasreen ta riƙo hannun Aasmeen tare da faɗin "kin ga zo mu tafi..."
Ba shiri suka bar wurin...

Amaar kallon mutumin ya yi sannan yasau murmushi yana faɗin "shin akwai wata hallakar da zanyi a gaba wanda ya wuce na baya??..."

Mutumin ya ce "Ni dai na gaya maka gaskiya yauwa sai anjuma..." daga nan yayi tafiyar sa...

Amaar tsayawa yayi wuri ɗaya tare da lumshe idanuwansa, ƙwaƙwalwar sa ce ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru da shi kamar a mafarki,
Fuskar Madam Nablah da bazai taɓa manta kamannin ta ba ya fara gani lokacin da ta zama Kurar daji, da idanuwanta da suka canza zuwa wani launi da ban, da lokacin da Madam Nablah ta ɗaga shi sama ta sake shi a cikin ramin ruwan hallaka dai-dai lokacin da Nasreen da Asmeen suka ƙwalla ƙiran sunan Tasleem,
A ruɗe ya buɗe idanuwansa jin wannan sunan da bazai taɓa manta shi a cikin ƙwaƙwalwar sa ba, jin suna ta ƙiran sunan Tasleem yasa ya nufi wurin su da gudun gaske, domin a duk yanda yaji mace mai suna Tasleem sai ya neme ta sannan ya yi ƙoƙarin taɓa koda hannun ta ne domin tabbatar da asalin Tasleem ta hanyar jin shocking,
A yanzu ya samo asalin Tasleem ɗinsa wato ƴar uwar su Nasreen da Asmeen...

A bakin titi ya iske su suna tsaye su biyu Nasreen da Asmeen ko wacce da damuwa akan fuskar ta,
Muryar Amaar suka ji yana faɗin "lafiya kuwa??..."

Nasreen da Asmeen a tsorace suka juya suna kallon sa tare da kawar da idonsu suna kallon mutanen wurin, kowa idonsa akan su ana nuna su alamar maganar su ake.

Amaar ne ya sake furta "me yake faruwa ne?..."

Nasreen ce tayi ƙarfin halin cewa "Ƴar uwar mu ce ta fito cikin damuwa ta shige mota ta tafi, bamu san ina ta tafi da motar ba..."

Asmeen ta ce "naga an ƙira ta a waya kamar wani magana aka sanar mata, daga nan ta tafi da sauri cikin fushi..."

Nasreen ta ce "ke ma dai kinsan koda yaushe a cikin fushi take, yanzu aina zamu same ta?..."

Amaar ya ce "ga can mota ta shin zan iya kai ku yanda take?..."

Nasreen ta ce "a'a bama son wani abu ya faru da kai, mun gode zamu jira ta..."

Amaar ya ce "ku na nufin kuce na gamsu da abinda wancan mutumin ya faɗa akan ku?..."

Asmeen ta ce "ka yadda da shi tabbas abinda ya faɗa maka gaskiya ne, shiyasa muke rayuwarmu mu kaɗai, babu wanda yake shiga shirgin mu..."

Amaar ya ce "kar ku damu akan abinda mutane zasu ce akan ku, Indai kuna da kyakkyawar zuciya babu wanda zai ci galaba akan ku, ni ina tare da ku babu abinda zai cutar da ni..."

Nasreen da Asmeen har zuwa wannan lokacin basu dawo normal ba, ko wacce da hawaye akan fuskar ta...

Amaar ya ce "a matsayina na ɗan uwanku Musulmi inaso ku mun wata alfarma dan Allah..."

Nasreen ta kalle shi cike da mamaki ta ce "wani irin alfarma?..."

Da murmushi akan fuskar sa ya ce "inaso ku bani dama na zama abokin ku na amana, wanda zai rinƙa saka ku cikin farin ciki sannan mai tare muku faɗa a koda yaushe..."

Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi sannan suka mayar da eyes ɗin su kan sa, Nasreen ta ce "har ka tuna mun da wani ɗan uwan mu wanda muka rasa shi tsawon shekarun baya, ya kasance shine mai tare mana faɗa kuma mai kishin mu, mun rasa shi har abada..."

Asmeen tana hawaye ta ce "YA AMAAR..."

Nasreen itama tana hawaye ta jinjina kai...

Amaar yana tsaye shima sauran kaɗan hawaye ya yanko masa yayi saurin kawar da kan sa gefe tare da faɗin "Allah sarki! Ina so ku bani damar maye gurbin sa..."

Asmeen da sauri ta furta "mun baka..."
Nasreen kallon Asmeen tayi tana sakin murmushi, duk basu san lokacin da suka tsinci kan su cikin farin ciki ba,
Shima yana murmushi ya basu damar shiga motar sa zasu bi bayan Tasleem ta hanyar connecting location da phone number ta....

Cikin lokaci ƙanƙani suka isa wurin da motar ta take a tsaye cakk,
Asmeen ta ce "wannan ne motar mu, i think tana ciki..."

A ruɗe Nasreen ta ce "Polo Grand Hotel?..."

Sai a lokacin Asmeen ta lura da yanda suka zo, a zabure ta furta "Hotel kuma, me tazo yi?..."

Amaar idon sa akan motar ya ce "tana cikin motar bata fita ba, ina tunanin tana jiran fitowar wani ko wata..."


Su ma suna cikin mota basu fita ba, sai gani suka yi wani saurayi ya fito daga cikin Hotel ya nufo motar ta, yana zuwa ya fara knocking, saurayin irin masu jiji da kai ɗin nan ne, tantiran ƴan daba domin har da sigari a hannun sa yana zuƙa...

Bayan wasu mintina sai ga Tasleem ta buɗe murfin motar ta sai da ta fara sauƙar da ƙafar ta ɗaya kafin wasu seconni ta fito da ɗayar cikin ƙasaita da izzah ta fito a cikin motar tana taku a hankali sai ƙarar sautin takalmin ta ake ji har ta zagayo yanda saurayin yake a tsaye yana busar taba,
Tsayawa tayi a gaban sa tare da goya hannayen ta akan ƙirji, ga wani tsararren black glass akan dara-daran idanuwan ta suna facing juna...

Cikin izzah ta furta "Sarkin ƴan daban yanki Arewa, gagara hukuma...."

Wani irin mahaukacin dariya ya yi tare da hura mata hayaƙin tabar bakin sa, yana faɗin "ba iya hukuma ba gagara kowa ne..."

Murmushi ta sau ko motsi bata yi ba balle hayaƙin tabar sa ya dame ta, ta ce "ban da kowa domin baka kai ka gagari kowa ba har yanzu da sauran ka..."

Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin "me ke tafe da ke murɗaɗɗiyar yarinya mai murɗaɗɗen tunani, ai da kin mun magana har wurin da kike zan je na same ki, amma yanzu ina cikin jin daɗi na da Babies ɗina akan gado kin zo kin takura mun akan na fito waje, shin meya hanaki shiga cikin Hotel ɗin?..."

Tasleem tana tsaye fuska ba alamar annuri ta ce "kar ka yi kuskure dangantani da shiga cikin Hotel sannan ba wai jin daɗin kaina ne yasa na biyo ka har yanda kake ba, ba muhawara nazo muyi ba..."

Nasreen suna cikin mota ta ce "me Tasleem take a wurin wannan mutumi marar ɗa'a?..."

Asmeen ta ce "kamar tattaunawa suke akan wata magana, amma meye alaƙar dake tsakanin su, a sanin mu Tasleem bata tsayawa da kowa tayi zance saboda bata da lokacin kowa..."

Amaar idonsa akan ta ya kasa furta komai...


Tasleem cikin fushi ta furta "Meyasa kayi mata fyaɗe?..."

Mutumin jin tambayar da tayi masa ne ya sa shi tintsirewa da dariya ya ce "Amma kin raina mun wayo yarinyar nan, yanzu don nayi fyaɗe har sai an tambaye ni Meyasa nayi? ka ji banza! jin daɗin rayuwata mana, wai ma tsaya kina magana ne akan waye? kinsan sunada yawa akwai yara sannan akwai ƴan mata akwai tsofi shin wa ye daga ciki?...."

Haka zuciyar Tasleem yake hauro wa kamar ta murɗe masa wuya amma da haka ta daure cikin ɗaga murya ta furta "Yarinya ƙarama ƴar shekara uku marainiyar Allah wacce ake rainon ta a gidan marayu, fara zuwan ta makaranta kenam ka shiga cikin makarantar kayi mata fyaɗe saboda kaga babu wanda zai ɗauki hukunci akan ka, to wannan yarinyar tana cikin ƙarƙashin kulawa ta, duk ƙananun yaran da suke cikin gidan marayu tamkar jinin jikina nake jin su, da hannuna na yi rubutu na ɗauki yara 15 ƴan shekara 3 zuwa 4 na sanya su a makaranta, a cikin motata na ɗauke su na kai su makaranta na biya musu kuɗin makaranta, yau kwana uku da fara zuwan su, yau kuma aka ƙira ni ake sanar mun ta'addancin da kayi musu, kayi wa ƙananun ɗalibai biyar fyaɗe a lokaci guda kuma kana tunanin baza'a yi maka komai ba saboda kana yaron Minister, tirrrrrrr...."

Tinda Tasleem ta girma bata taɓa yin kuka ba sai yau, ta cikin glass ɗin kan idonta hawaye yake tsiyaya kamar da bakin gora....

Duk waɗannan maganganu da tayi babu wanda bata ɗaga murya kowa ya ji ba,
Su Nasreen dake cikin mota duk suna jin abinda take faɗi, haka hawaye yake tsiyaya a cikin idon Nasreen itama, Asmeen kuwa ba abinda take faɗi sai Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Shima Amaar ya jinjina wa rashin imani irin na wannan mutumin...


Mutumin da ake ƙira da Firoj ɗan gidan Ministan garin ba abinda yake sai dariya, haka yake ɗaga murya shima yana faɗin "wannan ba sabon abu bane a wurin Firoj, ƙananun yara ya irin shekarun ta sun fi dubu waɗanda nayi wa fyaɗe, wasu sun mutu wasu sun warke wasu suna kwance ba lafiya duk na sa ni........"

Kafin Firoj ya rufe baki har Tasleem ta zuciyo ta zabga masa mari akan fuskar sa, kafin ya ankara ta riƙe kafaɗunsa biyu tare da ɗago da ƙafarta tayi amfani da gwiwarta da iya ƙarfin ta ta buge masa tsuriya, ba shiri ya durƙusa ƙasi yana ihu tare da riƙe wurin,
Tasleem ƙafa tasa ta canki ƙirjinsa ya faɗi ta baya yana kallon sama, kafin ya ɗago ta ɗora ƙafar ta da take sanye da takalmi mai bala'in tudu da tsini ta taka tsuriyar tare da miƙe wa tsaye akan sa, haka take ta tattaka tsuriyar da takalminta ta wurin tsinin.

Firoj ba abinda yake sai ihu gaba ɗaya ƙarfin jikin sa ya ƙare sai buga hannayensa yake a ƙasi,
Kafin ka ce mai mutane har sun taru masu video kowa yi yake, ana gulmar ɗan gidan Minister,
Sai da ta gama lugwigwita masa masarrafai duk babu wanda ya dakatar da ita kafin ta sauƙa akan sa, tana murmushi ta nufi bayan both ɗin motarta ta buɗe ta ɗauki wani sanda na ƙarfe ta koma yanda yake kwance yana birgima, haka ta fara doka masa wannan ƙarfe a duk wurin da tasan zai raunana, da ta samu kan gwiwarsa ta fara kwaɗa masa sai da ta karya masa ƙafa ɗaya sannan ta gurɗa ƙafa ɗaya, ta koma kan hannayensa nan ma sai da ta karya masa hannaye biyu...


Nasreen da Asmeen kuka suke suna so su fito su dakatar da Tasleem kar tayi kisan kai amma Amaar ya riƙe su, yaƙi barin su fita, sai roƙon sa suke amma yaƙi bari sai ma key da ya sa a motar gaba ɗaya yanda baza su iya buɗe wa ba,
Har cikin zuciyar Amaar so yake sai yaron ya suma domin a faɗar sa bashi da amfani a cikin al'umma, in ma kashe shi tayi a cewar sa babu abinda za'a mata....

Nasreen a tsawace take faɗin "wai kai bakada imani ne? so kake ta kashe shi itama a rataye ta? shin kasan shi ɗin ɗan gidan waye ne? ɗan gidan Minister ne fa, kuma nasan dole sai an kamata...."

Amaar cikin ɗaga murya ya furta "Tasleem bazata taɓa kamuwa ba koda kashe shi tayi, ko shugaban ƙasa bai isa kamata ba, a yanzu zan buɗe ku ne kuje ku dakatar da ita saboda kar ta shiga bakin duniya cewa tayi kisan kai, bazan so hakan ba...."

Yana kaiwa nan ya buɗe motar sa, da gudu Nasreen da Asmeen suka fice, nufan yanda Tasleem take ta dukan Firoj suka yi domin a halin yanzu ko motsi ya daina yi, baya cikin hayyacin sa amma duk da hakan Tasleem bata daina kwaɗa masa ƙarfen nan ba, duk ta faffasa masa kai....

Nasreen da Asmeen ne suka rirriƙe ta tare da ƙoƙarin jawo ta gefe da ƙyar domin kokuwa suke, Tasleem ba abinda take furtawa illa "ku sake ni na ƙarasa ɗan banza, yau ni zanyi ajalinsa, ku sake ni nace shin kun san abinda ya aikata mun ne?..."

Nasreen itama cikin ɗaga murya ta ce "baza mu sake ki ba Tasleem, bakida hankali ne zaki yi kisan kai..."

A tsawace Tasleem ta furta "banida hankali Indai akan marayun yara ne..." tare da yin wurgi da Nasreen har sai da tayi dungure sau uku sai gata a gaban Amaar wanda fitowar sa kenan a cikin motar sa,
A fusace ta juyar
End Ads