x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 190

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ganin bata taɓa fita takai dare ba..."

Nasreen cike da damuwa ta ce "yanzu ya zamu yi? number ta yana tafiya amma ba'a picking ..."

Asmeen ta ce "duk saurin jin bacci na yau kamar wanda aka ɗauke mun bacci, bana jin sa ko kaɗan saboda rashin ƴar uwar mu, daga zuwa restaurant shikenam ta ɓata babu labarin ta?..."

Nasreen ta ce "Asmeen ba muyi tunanin dubo part ɗin Ya Shaprees ba, ko zaki je ki duba mana ita..."

Asmeen ta ce "kin dai san Tasleem ba zama zata yi a part ɗin sa ba..."

Nasreen ta ce "by in case mana, ko ina ma ai zamu duba tinda nema muke..."

Asmeen ta ce "Allah na gani bazan iya zuwa part ɗin Yaya Shaprees a wannan daren ba, ki rufa mun asiri mutumin da yanda kasan kwarton sama haka yake..."

Nasreen tsaki ta ja tare da faɗin "ke fa kinada matsala, to ni bari naje..."

Har tayi gaba Abeesh ya riƙo ta tare da girgiza mata kai yana faɗin "ita tasan dalilin da yasa bazata je ba, meyasa zan bari ke kije?..."

Nasreen ta ce "Ya Abeesh dole zan je na duba ta acan, hankali na bazai taɓa kwanciya ba, Allah ya bamu uwa bamai kula da ƴaƴanta ba, why baza mu kula da junan mu ba...."

Ta ƙarasa maganar tana kuka, Asmeen ce tazo ta rungume ta tana rarrashin ta, Abeesh ya ce "idan kun ƙira wayar ta tana shiga?..."

Asmeen ce ta bada amsar "eh..."

Ya ce "zamu yi amfani da phone number ta wurin yin tracking domin mu gano a yanda take ..."

Nasreen a ruɗe ta ce "eh! ehh hakan ma zamu yi, da tinda mun yi tunanin haka da bamu sha wahala ba..."

Hakan kuwa suka yi gaba ɗayan su fita suka yi, su na zuwa suka shiga mota tare da nufan bakin gate,
Security ne suka dakatar da su tare da faɗin "ina zaku je a wannan daren?..."

Nasreen ta ce "please gaggawa muke, yanzu zamu dawo..."

Security ya ce "Madam ta bamu umarnin idan dare yayi kada mu bar kowa ya fita daga gidan nan haka kuma na waje bazai shigo ba..."

Abeesh ya ce "okay bari na sallame ku yanzu idan Madam ta dawo sai ta dawo da ku, tinda inada right ɗin koran ku a gidan nan..."

Security kallon sauran ya yi sannan ya ce "ba komai zaku iya wuce wa tinda su matan suna tare da kai, amma bakwa neman escort ne?..."

Abeesh ya ce "No...."
sannan aka buɗe musu get suka fita,
suna bin hanyar da suka yi tracking number Tasleem har suka isa unguwar da take, abun mamaki ya basu ganin su a headquarters, ta ko ina sojoji ne, kafin su shiga ciki sai da wasu sojoji suka dakatar da su,
Abeesh ya kalli su Nasreen sannan ya ce "ku sassauta damuwar ku, bama son su fahimci akwai matsala..."

Bayan Soja ya yi musu knocking a glass car ɗin su, ya ce "daga ina sannan ina ku ka nufa?..."

Ga haske ta ko ina kamar rana Abeesh ya ce "mu baƙi ne zamu je........"

Sojan ya ce "baƙi daga ina?..."

Abeesh ya ce "daga Kaduna...."

Sojan ya ce "zuwa ina?..."

Abeesh ya ce "yallaɓai ga shi kuwa mun iso, akwai gidan ɗan uwan mu a cikin nan unguwar zamu sauƙa a gidan sa ne..."

Sojan ya ce "gidan wa?..."

Nasreen ce ta kalli wayarta ta duba sunan gidan da Tasleem take sannan ta kalli sojan ta ce "gidan Major A.J Banglash...."

Nasreen ta faɗa ne ba tare da tayi tunanin mai irin sunan da ta taɓa ji ba, sai Asmeen ce tayi saurin kallon ta tana mamaki taya tracking ɗin da suka yi zai nuno musu gidan Major A.J wanda suke ƙira da Ɗan uwa..."

Daga baya itama Nasreen sunan dawo mata cikin kwakwalwa ya yi tana tunanin taya zai kasance gidan Major AJ?..."

Sojan jin sunan da suka ambata ne yasa shi mamaki sam bai yadda dasu ba jin daga Kaduna suke, alhalin yasan cewa Major AJ ba ɗan nan ƙasar bane kuma yana daga cikin manyan sojojin cikin quarters...
Alama da hannu yayi wa sauran sojojin duk suka zo wurin, Nasreen da Asmeen zazzaro idanu suka fara yi cikin tsoro da fargaba suka ce "mun shiga uku..."

Sojojin su na zuwa suka ce duk ku fito daga cikin motan nan, haka aka tsare su da tambayoyi, daga masu musu tsawa sai masu zaro musu jajayen idanuwa gaba ɗaya sun shiga cikin firgici, idon Asmeen ne ya sauƙa akan wata maroon jeep car, leƙa number motar tayi taga na gidan su ne, taɓa Nasreen tayi tana nuna mata motar Tasleem, Nasreen zaro ido tayi ga hawaye duk ya wanke mata fuska ta ce "Ya Abeesh motar Tasleem..."

Shima gani ya yi tare da girgiza kai yana faɗin "da mun sani tin farko mun sanar musu gaskiyar abinda yake faruwa, gashi nan ƙarya ta jawo mana damuwa..."

Asmeen ta ce "abu ɗaya ne kawai ya jawo mana wannan rikicin shine sanar musu da muka yi daga Kaduna muke, yanzu kuwa ba damar canza magana domin bazasu taɓa yadda damu ba...."

Nasreen ta ce "ai kuwa dole zamu sanar musu gaskiya..."

Abeesh ya ce "yanzu meye abun yi?..."

Duk wannan tattaunawar da suke yi suna durƙushe ne da gwiwowinsu sun ɗaga hannu sama, ga sojoji a kewaye da su, a haka suka kwana har asuba hannu a sama, duk wacce ta rintsa to a tsawace za'a tayar da ita, Asmeen tasha kuka kamar ranta zai fita ga ta gaji sosai, hannu duk ya yi tsami, ƙafafuwa duk sun tutturje, kan gwigwarta ba ƙaramin ciwo yake mata ba, tana sauƙe hannu soja zai darara mata tsawa haka itama Nasreen gaba ɗaya ƙafafuwan ta kamar wanda aka sa ƙaton dutsi aka danne mata su ko rintsawa bata yi ba gaba ɗaya idanuwansu sunyi jajawur tsabar azaba da kukan da suka sha,
Shi kuwa Abeesh kwana ya yi yana tsallen kwaɗo wani sojan yana binsa a baya da dorina, yana tsayawa za'a zabga masa dorinar, gaba ɗaya ya fita hayyacin sa....

Da Asuba misalin ƙarfe 6 da rabi gari ya washe sosai, sai a lokacin Tasleem ta samu damar farfaɗowa tana kame da goshin ta, ganin ta a kwance akan carpet ne yasa ta miƙe tana dudduba jikinta, taga ko ina yayi jawur kamar ƙonuwar wuta, tana cikin wannan halin ne sai ga Amaar ya fito daga toilet yana goggoge sumar kansa da towel da farar jallabiya a jikinsa wanda ya tsaya masa a iya gwiwa, dake shi ya juma da farfaɗowa har ya yi sallar asuba.

Ganin ta farfaɗo ne yasa ya nufi yanda take tare da faɗin "kina lafiya, fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya naga jikin ki duk ya yi ja, ya kamata na duba lafiyar jikin ki..."

Gaba ɗaya a ruɗe yake wannan maganar idonsa akan ta, domin ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, shima kamar wanda ya tashi daga jinya eyes ɗin sa a shashshanye.

Tasleem tsabar takaici da haushi tama rasa bakin magana, ido kawai ta zuba masa hawaye kuwa ya gagara tsayuwa sai girgiza kai take, tana tunanin wani irin hukunci zata ɗau akan sa, suna cikin wannan halin suka ji yo knocking,
Amaar idonsa akan Tasleem ya bada izinin shigowa, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ne ta shigo tare da faɗin "Sir an kammala breakfast, za'a kawo muku nan ne ko a bar muku a dinning?..."

Amaar hararar ƴar aikin yayi sannan ya ce "kin gaishe da Madam ɗina?..."

Ƴar aiki haɗiyar yawu tayi kanta a ƙasi ta ce "ina kwana Madam ?..."

Tasleem a fusace ta kalle ta tana faɗin "da ban kwana ba zaki ganni a gaban ki a tsaye?..."

Ƴar aiki kai a ƙasi ta ce "Allah ya baki haƙuri..."

Tasleem tsabar masifa har jijiyoyin wuyan ta sun tattashi, fuska tayi jawur ta ce "lokacin da akayi rabon haƙuri ba'a halicce ni ba..."

Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli ƴar aiki ya ce "je ki kawo mana nan ...."

yana furta wa tayi waje domin Allah take ta bar room ɗin nan domin zata iya yiwa Tasleem rashin kunya idan ta musguna mata...

Tasleem gaban Amaar ta je ta tsaya tana nuna shi da yatsa tare da faɗin "kai kuma Insha Allahu ni ce ajalinka, kana ji ba nace ni zan zamo ajalinka, a hannuna zaka mutu, wallahi ji nake kamar na shaƙe wuyan ka a yanzu..."

Amaar ba abinda yake sai murmushi idonsa akanta,
Mai aiki ce ta dawo da paranti kuloli a hannun ta, tsayawa tayi sannan ta ce "Sir aina za'a ajiye?..."

Tasleem ce ta je har gaban ta sannan tasa hannu ta karɓi parantin sannan ta dawo gaban Amaar fuska a ɗaure ta ɗaga parantin sama ta sau a ƙasi, kulolin abincin duk suka tawarwatse, ƴar aiki toshe bakin ta tayi da hannayenta biyu tana zaro ido ta ce "ke kina da hankali kuwa? Abinci mai daraja zaki wulaƙanta?..."

Wani irin juyi Tasleem tayi ta shaƙo wuyan Ƴar aiki tare da manne ta a jikin bango tana faɗin "meye to? saboda ba abinci a gidan ubanki shine zaki rikice kina so ki mun rashin kunya? daman haka ƴaƴan talakawa kuke da zaran kun samu wurin hutawa sai ku nemi ku falle..."

Amaar cikin sassanyar murya ya furta "Tasleem...."

Juyowa tayi tare da hankaɗa ƴar aiki saida ta faɗi ƙasi tayo kan Amaar tana faɗin "ehen ko zaka rama mata ne?..."

Amaar kallon ƴar aikin yayi sannan ya ce "ke bar ɗakin nan..."

Haka ta tashi ta karkaɗe jikinta tabar ɗakin...

Amaar ya maida idonsa kan Tasleem sannan ya ce "me kike son ci? zan shiga kitchen da kaina na girka miki abunda kike so..."

Dogon tsaki taja tare da furta "bani da lokacin ka ..."

Nufan toilet tayi taje ta ɗauro alwala sannan ta tsayar da sallar asuba tare da lafula,
Daga nan ta ɗauki handbag ɗin ta da wayar ta, tana duba wayar taga 100 missed call ƙiran Nasreen ne sai ƙiran Asmeen da na Abeesh zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "innalillahi, ban taɓa kwana a wani wuri ba sai wannan lokacin ta dalilin ka, gashi yanzu na tayar da hankalin ƴan uwana, wallahi nayi danasanin saninka a rayuwata, ka shiga rayuwata da yawa...."

Tana kuka tabar ɗakin, tana sauƙa falo ta tarar da ƴan aiki su huɗu a wuri ɗaya suna gulma,
Tasleem tsarguwa tayi ta kasa yin haƙuri sai da ta same su, tana zuwa ta ce "duk kuyi mun kneel down..."

Kallon juna suka shiga yi kafin suka ce "me muka miki da zaki ce muyi kneel down?..."

Tasleem ta ce "ko baza kuyi ba?..."

Suka ce "gaskiya ba zaman ki muke ba don haka baza muyi ba..."

Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "gaskiya ne..."

Shima Amaar fito wa ya yi ya ce "meya faru?...".

Ƴan aikin ne suka sanar masa abinda yake faruwa...

Kallon Tasleem ya yi Sannan ya ce "meyasa zaki hukunta su? ni nayi miki laifi ni ya kamata ki hukunta ba su ba...."

Tasleem ta ce "okay kai zo ka mun kneel down..."

Duk ƴan aiki zaro ido suka yi tare da faɗin "a'a ki bari mu zamu yi, domin bai cancanci wannan wulaƙanci ba..."

Ta ce "meyasa da farko dana saka ku bakuyi ba? saboda haka yanzu reshe ya juye da mujiya..."

Tasleem kallon Amaar tayi sannan ta ce "kai zo nan, kayi abinda na saka ka...."

Amaar bai ji komai ba haka yaje gaban ta ya yi kneel down.

Ta ce "ka ɗaga hannun ka sama..."
Hakan kuwa yayi kamar yanda ta umarce shi...

Wata daga cikin ƴar aikin ce tayi murya ƙasa-ƙasa ta cewa sauran "Asiri fa tayi masa..."

Wannan furcin ne ya sauƙa akan kunnen Amaar, murmushi ya yi sannan ya ce "ba Asiri bane, tsananin so da ƙauna ne..."

Duk shiru suka yi da sauri suka bar falon, ita kuwa Tasleem zama tayi akan kujerar falon ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana karkaɗa ƙafa, sai faman danna wayar ta take, shi kuma idonsa akan ta ji yake kamar ana ƙara masa ƙaunar ta ne, yana kuma farin ciki ko ba komai ta yaye masa damuwa ɗaya, wato na matsalar ƙwaƙwalwa, yanzu yabar wannan matsalar...

Suna cikin wannan halin sai ga wani soja ya turo ƙafa ya shigo, har ya buɗe baki zai yi magana idonsa ya sauƙa akan Ogansu, da sauri ya ƙarisa shigowa ciki tare da faɗin "Ogah ya haka kuma?..."

Tasleem ko ɗagowa bata yi ba balle ta kalli yanda suke.

Amaar ya ce "No kar ka damu faɗan cikin gida ne, wannan ɗin sarauniyata ce nayi mata laifi shine take hukunta ni..."

Sojan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba sai dai babu yanda ya iya, ya sanar da abinda ya kawo shi yana faɗin "Ogah wasu ne suka zo wurinka tin jiya cikin dare misalin ƙarfe 12 zuwa 1 amma
End Ads