x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 39 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 114001 words
  • 117000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 199

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ɗauke da sanyi da iska mai daɗi...

Miemie ta zama ruwa itama ruwan ya ɓace..

Haske ya wanke sahara.
Faɗa ya tsaya.
Kowa ya kowa yanda ya fito, domin ba a yanda zasu samu Madam Nablah a halin yanzu, ga tana shirin hallaka su da wuta mai tsananin ƙuna...


★★★★★

A can bayan duniyar da mutane ke rayuwa, bayan saharar haske da duhu, akwai wani tattakeƙen lambu, da itatuwa masu baƙin ganye kuma rana bata fito wa a wurin sai wata mai launin ja.

A tsakiyar wannan wurin akwai ƙaramar dafaɗɗiyar alfarwa, wadda take gefen wata tafkin ruwa...

A cikin wannan alfarwa, Nasreen ce ke kwance.

Ita ba matacciya ba.
Ita ba kuma rayayya ba.
Sai dai kamar ana tsare da ruhinta cikin wani yanayi na barci mai zurfi....


💤 NASREEN CIKIN BARCI MAI RAI...

Nasreen wacce take bacci da duk motsin zuciyarta.
Idonta a rufe, amma murya tana fitowa daga cikin zuciyarta tana cewa:

"Abeesh... ina jin ka... amma ba zan iya miƙa hannuna ba... Ina jin sanyi... amma na kasa tashi... Waye ya tsare ni a nan?"


Ruwan tafkin yana zagayawa da ƙamshi mai sanyi da ƙara kamar kuka.
A gefe guda,
Madam Nablah ce ke zaune tana saka rawaya a cikin ruwa, tana ambaton wasu kalmomi cikin harshen da babu mai iya fassara wa sai halittu.

Ita kaɗai tasan a yanda ta ɓoye Tasleem, sannan ta bayyana a yanda ta ajiye Nasreen..

A lokacin da Catrina ta so kashe Nasreen da duhu, Madam Nablah ce ta karɓi ruhin Nasreen ba tare da barin ta mutu ba, ta kaita wannan wuri domin tsare rayuwarta har ta ci galaba akan haske....

Madam Nablah ta ce cikin wani sanyin murya da kuma ƙarfi, tana faɗin

"Ance mata zata mutu, amma ni nace a’a. Nasreen zata yi rayuwa, ba sai da kujerar mijinta ba… Sai da zuciyarta da ƙaddara.
Ta ci jarabawa, amma har yanzu akwai sabo a zuciyarta. Sai na goge komai, sai na shafe komai, sai na miƙe domin magance matsaloli... sannan zata tashi daga bacci, ki cigaba da hutawa ƴata Nasreen......"


💔

A cikin barcinta, hawaye suka gangaro daga gefen idonta.
Zuciyarta tana kiran sunan Abeesh, kuma tana jin laifin da ta yi masa lokacin da ta fara zargin sa da Catrina...

A cikin baccin take maganar zuci

"Idan na tashi daga wannan wuri, zan nuna soyayya kamar yau ce rana ta ƙarshe... Amma idan ban tashi ba, ku faɗa wa ƴan uwana cewa ina ƙaunar su.... Ku faɗa wa Abeesh cewa na yarda da shi har karshen numfashi..."...


★★★★★★ Kai tsaye Tsaunin da ta ajiye Abeesh ta nufa dake wata duniyar da bana mutane ba...

A wani tsauni mai hayaƙi da turɓaya, wanda wuta ke fita daga ƙasa kamar ana hura shi daga zuciyar duniya, Madam Nablah ce tsaye — jikin ta na ƙuna da harshen wuta, idonta kamar ƙarfen da aka ƙera domin hukunci.

A ƙasan wannan tsauni, a cikin wata ƙaramar rami da duhu ya lullube shi, Abeesh ne kwance yana fitar da numfashi mai rauni, jikinsa babu ƙarfi, ba motsi, amma zuciyarsa har yanzu tana bugawa da ƙauna, damuwa, da ruɗani.

Madam Nablah tana tsaye tana jiran zuwan wadda ta ƙira.

🌑 CATRINA CE TA BAYYANA

Cikin wata walkiya da iska mai mugun ƙamshi, Catrina ta bayyana.
Jikinta a gajiye daga faɗan da suka yi da Tasleem, amma idanunta na cike da jaraba na rudani.

Da ta hango Abeesh a ƙasa cikin yanayin rashin lafiya, ƙirjinta ne ya buga,
Sai ta ɗan yi baya, tana fadin:

"Wannan... wannan Abeesh ɗin ne...?"


Madam Nablah ba tare da ta ce komai ba sai da ta juya kanta a hankali, ta ɗauko ƙaramar wuƙa mai kaifi daga bayanta, wacce take walkiya da jini, sannan ta miƙa mata tana cewa:

"Kamar kin fara jin tausayin kauna ko? Kin manta cewa ke sarauniyar duhu ce, Catrina. Ya kamata ki wargaza ƙauna, ba wai ki gina ta ba..."


Catrina ta ɗauki wuƙar da hannunta yana rawar jiki.
Ta kalli fuskar Abeesh, ta runtse ido, hawaye na cika idonta duk da bakinta yana dariya, domin ita a koda yaushe a cikin dariya take ko da tana kuka..


Madam Nablah ta ce:

"Ina buƙatar ki yanke dangantakarki da zuciyarki, domin a wannan darasi, zuciya rauni ce. Ki nuna cewa kin fi zuciyar ki ƙarfi, Kashe shi... kafin ya kashe ki da ƙaunar sa."


Catrina ta ce:

"Na ƙi. Na ƙi! Banza nake kiran kaina sarauniyar duhu idan bazan iya amfani da duhun ba, zan yi amfani da duhu domin tarwatsa kowa amma ba zan iya cutar da Abeesh ba, Kullum idan na gan shi zuciyata tsinke wa take... Ban san yaushe na fara jin sa a cikin raina ba... Hakan yasa ba zan iya kashe shi ba!"


Madam Nablah cikin ɓacin rai ta ce:

"Kin gaza, Catrina! Kin zama rauni, kin koma mace mai ciwon ƙauna... Kin manta ni na gina ki! Ni na kore ki daga mutunci zuwa iko! Kuma yanzu ke kin kasa... akan wani ɗan adam?!"


Catrina ta ce:

"Na ƙi zama yanda kike so. Na ƙi zama wuta Saboda hatsarin ta. Ban son zama kamar ki. Kuma idan zaki kashe shi, ki fara kashe ni tukun...."


Madam Nablah karɓan wuƙar daga hannun Catrina ta yi tare da faɗin:

"To... na fahimta.
Amma ki sani... da zarar kin ɗauki hanyar ƙauna, shikenam kin zama ƙaramin haske... kuma ina ci gaba da ganin haske a jikinki. Wannan zai zama ƙarshen ki, Catrina, idan kin ci gaba..."


Sai ta juya da wuƙar, ta buga ta ƙasa, ta ɓace cikin wuta.

Itama Madam Nablah ba har cikin zuciyar ta take faɗin ta kashe Abeesh ba, akwai abinda take son shirya wa...


Catrina ta zauna a gefen Abeesh tana kuka.
Ta riƙo hannunsa a hankali tana cewa:

"Ka tashi, ka yi magana dani... Ka ce min ka yafe min... ko aƙalla ka ce min baka yafe ba..."

Sunkuyar da kanta a kan ƙirjinsa tayi, hawaye suna sauƙa.
Duhu ya ƙara rufe tsaunin, da alama wani sabon abu yana gab da faruwa...

Catrina na zaune gefen Abeesh, hannunta na dafe da goshinsa, hawaye na gangarowa daga fuskarta mai cike da wulakantacciyar soyayya da nadama. Duk da ta kasance cikin duhu, duk da ta rayu a ƙarƙashin horo da umarnin Madam Nablah, akwai wani abu a ranta da ke bijirewa — wanda ko ita kanta ba ta fahimce shi ba:
Abeesh.

Tana kallon shi, sai ta furta da murya mai sanyi :

“Me yasa baka da taurin zuciya kamar mu? Me yasa soyayyarka ke da sauƙin ƙona ruhin wanda bai san me ƙauna take nufi ba? Abeesh... ka karya mun zuciya da soyayyar ka...”


Iskar tsaunin ta ƙara zafi, kamar tana ƙona hawayen da ke zubowa daga idonta. Duk da haka, ta cigaba da magana, tana shafa fuskarsa da ƙaramar ƙarfinta domin ƙarfin ikon ta ƙara raguwa take a yayinda take zubar da hawaye...

Ta ce:

“Na ga duhu, kuma ni duhu ce, na ji daɗin sukar mutane. Na yi nesa da zuciyata... amma kai ka ja ni na fara dawo da ita. Na fara jin yadda zuciya ke bugawa idan tana cikin ƙauna.”


Ta kalli hannuwanta waɗanda suka saba azabtar da zuciya, yanzu suna rawar sanyi da tsoro. Sai ta ɗaga kanta, ta kalli sararin tsaunin, tana fadin:

“Idan hukuncina mutuwa ne saboda ƙaunar wanda nake zaton maƙiyi na, to na yarda. Amma kar ku ci gaba da cutar da shi... don Allah, kar ku taɓa shi...”


Cikin ɗan lokaci, wani ƙarar numfashi ya fito daga cikin ƙasan tsaunin. Abeesh ya motsa. Hannunsa ya dan motsa kamar wanda aka kwantar da shi tsawon lokaci.

Catrina ta zaro idonta cike da farin ciki, numfashinta ya tsaya cak.
ta ce da murya mai rauni:

“Abeesh... Abeesh? Ka na jina?”


Abeesh bai buɗe idonsa ba, amma ƙirjinsa na tashi da sauƙa. Wannan ne karo na farko da numfashinsa ya sauya tun da aka kwantar da shi.

Catrina ta matso da fuskarta kusa da kunnensa, tana fadin:

“Na sani... ka ji ƙiyayyata. Na sani... Na taɓa Nasreen. Na jefar da mafarkinka, Amma na fara yin nadama... kuma ko zan mutu saboda haka, na amince..... Ka yi shiru, Abeesh! amma zuciyarka ta gaya min komai.”


Kamar dai wani abu na faruwa daga nesa...

Catrina ta juyo da sauri.
Ba a iya ganin wanda ke zuwa ba, amma da alama wani abu ne ke matsowa kusa.

Idanunta ne suka cika da ruɗani, tana girgiza kai tana cewa:

“Kada ku zo ku ɗauke shi. Ku bar ni in gyara kuskurena. Ku bar ni in nuna masa cewa zuciya na iya tuba, koman zurfin duhu.”


Ta sunkuyar da kanta bisa ƙirjin Abeesh, ta cigaba da fadin:

“Idan har zaka tashi, ko da zaka ce bani da amfani a gareka, zan karɓa. Ko da zaka watsa ni da kalmomin ƙiyayya, zan saurara. Amma kayi min alfarma... ka tashi. Dan Allah, ka tashi…”


Da wannan kalmomi, hawaye suka zubo daga idon Abeesh — a hankali, ya buɗe idonsa...

Sai ya ce cikin murya ƙasa-ƙasa

“Ke ce...?”


Catrina ta girgiza kai cikin hawaye, tana murmushi mai raɗaɗi ta ce:

“Ni ce... kuma ban cancanci amsarka ba.”



Madam Nablah tana tsaye a saman wani dutse mai kaifi a cikin tsaunin da aka ɓoye Abeesh. Gashinta yana motsi kamar harshen wuta, idanunta kuwa suna lumshewa a hankali. Amma zuciyarta na girgiza ganin Catrina ta tsugunna jikin Abeesh da hawaye, tana tunanin taya Aljana zata kamu da ƙaunar bil adam na tsanani....

Ta furta da siririyar murya mai cike da iko da izzah:

“Catrina… Catrina… Ba ki zama ni ba, kuma bazaki taɓa zama kamar ni ba....Amma ki sani cewa ke duhu ce, kuma kina kokarin dauƙo haske? Da Soyayya? Lallai… kina kuskure, yarinya.”


Catrina ta ɗago idonta, jini na zuba daga hancinta da idanuwanta Tana kallon mahaifiyar ruhi da girmamawa da tsoro ta ce:

“Na rasa meye gaskiya… amma yanzu na san me nake so. Ba ku bane. Ba cutarwa ba. Na san cewa zuciya zata iya rayuwa da ƙauna.”


Madam Nablah ta tintsire da dariya mai cike da haushi, tana sauƙowa ƙasa daga kan tsauni cikin hayaƙi, ƙasa na ƙonewa da wuta a inda ƙafarta ke taka wa. Lokacin da ta tsaya gaban Catrina, ta ɗaga hannunta, wata wuƙa mai kamar an harhaɗa ta da wuta da jinin halittu ta bayyana.

Ta furta da murya mai ƙarfi:

“Ga zaɓi: ko ki tafi ki ɗauko Abul, mahaifin Abeesh da Amaar ko kuma... ki kashe Abeesh da kanki.”


Zuciyar Catrina ta tsaya. Kamar an fesa ruwan sanyi a jikinta. Sai ta girgiza kai a hankali ta ce:

“Kada ki jarraba ni da hakan. Bazan iya kashe shi ba, wallahi bazan iya ba... koda kuwa duhu zai ƙona ni, koda kuwa kin cire ni daga hallita ne bazan iya kashe shi ba.”


Madam Nablah ta ɗan lumshe ido. A fili ta nuna bacin rai, amma a zuciyarta baza ta taba bari a cutar da Abeesh ba balle ta sa a kashe shi, barazana ne kawai....

Domin Madam Nablah... tana son Abeesh.
Jin sa take kamar ita ta haife shi, duk da yana da ɗabi’a mai kyau, Ƙwazo. Tausayi. Gaskiya. Kuma hakan ya sa ta tsani wannan halin, amma tana ƙaunarsa....

Cikin barazana take faɗin:

“Idan bazaki kashe shi ba, ki tabbatar kin kawo min Abul. Idan ba haka ba... ke da shi zaku hallaka tare.”


Catrina ta juyo, tana kallon Abeesh, tana shafa goshinsa da yatsanta, wanda a halin yanzu baya cikin hankalinsa, haka yake binsu da kallo ba tare da yasan abinda suke faɗi ba..... Zuciyar sa Nasreen kawai take ƙira.

Catrina ta ce:

“Zan kawo miki Abul... Amma idan na dawo, kar ki kuskura ki taɓa shi. Na rantse da wutar da kika raina ni da ita, zan juyar da ita akanki idan kika ƙetare haddi.”


Madam Nablah ta bace da harshen wuta ba tare da ta furta komai ba...

A nan ta bar Abeesh bata ɗauke shi ba, ta bar shi, saboda wani abu a ranta . Ba zata taɓa iya kashe shi ba…



Catrina
Ta kalli hanyar sama, ƙarfin zuciyarta yana ƙaruwa, duk da hawaye na gangarowa ta ce:

“Wannan ba faɗa ce ta duhu kawai ba... Yanzu zuciyata tana ƙoƙarin ƙin kowane mungun aiki. Amma zan kare wanda nake so, koda kuwa rayuwata ce fansa.”


Sai ta ɓace cikin iska… domin taje ɗauko Abul......



*💋HASKEN RUHI💋*


*🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀*


It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person.

*WhatsApp 09065443871*


*🌹 ASMEETAH WRITER 🌹*


*BOOK TWO__________PAID_____₦300*


Page 3 to 4



Bayan fafatawar haske da duhu, Tasleem bata koma gida ba.

Madam Nablah, cikin wayo da zurfin mugunta, ta hango cewa Tasleem ce kaɗai za ta iya rushe komai da ta gina tsawon shekaru na tsafi da jini, Don haka ta ɗauke ta

Ta ɓoye Tasleem a wani wurin da haske baya iya haska wa, cikin kogin tsafi mai rai, wanda ruwansa ba ruwa bane kawai, tsantsar sinadarin ruhi da sirrin duhu ne ke gudana ciki. A ƙasan kogin akwai wani ɗaki da ruwa baya shiga cikinsa amma kogi ne ke kewaye shi.

Tasleem tana zaune cikin wannan ɗakin, Jikinta a sanyaye,
gadon da take kwance akai ba a cikin ruwa yake ba, amma ko'ina a zagaye da ruwan kogi, wanda kifayen tsafi ke zagayawa cikin iko...

Kowane kifi yana da launin ido daban wasu ja, wasu kore, wasu ruwan duhu.
Suna kallon ta kamar suna tsaron sirrin wani babban sihiri.

A wani lokaci, Tasleem takan sauƙe numfashi tana kallo sararin ruwan da ya rufe ɗakin daga sama, tana maganar zuci:

“Mommy... kin tsorata da haske na. Amma kin manta haske baya buƙatar daƙi mai duhu. Idan zuciya ce haske, zai iya gutsura duhu duk inda aka kulle shi.”

🏚️

Amaar ya shiga firgici na rashin Tasleem, ba yanda mai shiga nemanta ba amma ko ƙyallen ta ya rasa, gaba ɗaya bashida natsuwa.

Ya rasa Nasreen, ya rasa Abeesh. Kuma yanzu Tasleem ma ta ɓace.

Duhu kamar ya sake lullube shi. Amma zuciyar sa ta ƙi amincewa da asarar Tasleem.
Yana jin kamar zata dawo, amma yana jin tamkar an tsare ta a wani wuri...

Kullum yana tare da Abul wanda har yanzu ba ya iya magana sosai, amma idanunsa suna nuna damuwa da wata babbar matsala da ke maƙale a kansa,

Amaar yana riƙe da hannun Abul cikin damuwa a daren yau, yana furta a hankali:

“Abul, ba zan bari su cutar da mu ba. Na san akwai sirri, akwai tsafi, akwai zalunci amma akwai gaskiya. Kuma gaskiyar zata fito, koda kuwa ta fito daga cikin kogi.”


Ya lumshe ido, hawaye na zubo wa...



🌊 TSALEEM A KOGIN TSARIN RUHI

Duhu da sanyi da shiru su ne abokan Tasleem a cikin ɗakin ƙasa da ruwa, inda kifayen tsafi ke shawagi a zagaye da ita. Kowane motsi na su yana da ma'ana, kamar wasu wakilan wani sarki ne da ke jarrabar zuciyarta.

Tasleem na zaune akan gadon da ruwa baya taɓa jikinsa daga ɗakin baya ratsa wa, amma ƙamshin ruwa yana lullube ta, tamkar ana so a rage mata ƙarfi cikin salo, Idanunta sun canza launin baƙi da ɗigon haske a tsakiya...

Ta taɓa ƙirjinta, tana jin zuciyarta na bugawa da gaggawa.
Ta ce:

“Wannan ba ƙarshe ba ne…” ta furta cikin sassanyar murya ta kuma cewa

“Haske baya mutuwa...”


★★★★★

Amaar ba ya barin Abul shi kaɗai ba. Tunda ya fara fahimtar cewa Abul na da wata matsala ta ruhaniya, baya iya bacci ba tare da ya gan shi ba.

Catrina kuwa — tana lura da hakan. Kullum tana leƙen inda suke, tana tunanin lokacin da zata shigo ta ɗauki Abul kamar yadda Madam Nablah ta umurta. Amma kullum Amaar yana tsaye kusa da shi, wani lokaci har ya zauna ƙasa yana karanta masa addu’a ko kuma yana furta wa kansa:

“Abul ka riƙe zuciyar ka. Ni da kai za mu bayyana komai. Tasleem za ta dawo. Gaskiya zata fito…”

Bayan duhu ya shiga, babu motsin kowa, Asmeen da Shapreen na part ɗin su, iya Abul da Amaar ne kawai a wannan part ɗin,
Catrina ce ta doso wajen cikin dare — sanye da mayafin duhu, ido kamar wuta. Amma tana iso kusa, sai ta tsaya daga nesa, tana hangowa daga cikin inuwa. Amaar yana zaune ne a gaban Abul yana duba fuskar sa cikin kulawa da alama suna wata magana ne...

Catrina ta dafe bango, ta kalli yatsun hannunta da suka fara rawar jiki. Zuciyarta ta ambaci sunan Abeesh har yanzu tana jin son sa yana ci mata rai.

A zuciyarta ta furta:

“Madam Nablah ba za ta fahimta ba… Ni ba zan iya cutar da Abul ba. Kuma bazan iya ɗauke shi a gaban Amaar ba.”

Ta juya a hankali tana jin kamar idan bata cika umarnin Nablah ba, zata fuskanci fushin da bata taɓa gani ba.

🔥

Madam Nablah tana kallon Catrina daga cikin madubin ta na tsafi tana jin ranta na tafasa, tayi magana cikin masifa tana faɗin:

“Wanda yaƙi aiwatar da umarni... ya zaɓi hallaka kansa da hannunsa.”


Sai ta ɗaga hannu wata ƙaramar ƙwarya ta bayyana a gabanta, tana tafasa jini ta ce:

“Tasleem tana nan a kulle babu yanda zata dakatar Amma duk da haka Catrina ta kasa…”


Ta dakata. Idonta ya canza launi — daga ja zuwa baƙi kirin ta kuma faɗin:

“…zanyi amfani da mafarki na ƙarshe: tsafi mai ɗauke da hawaye. Kuma zan iya yin abinda kowa zai bar duniya.”


★★★★★

Tasleem wacce take cikin ƙalubale kullum tana tsammanin ceto amma babu wanda yazo yanda take hatta Madam Nablah tinda ta ajiye ta bata ƙara sauraronta ba, tayi kukan har ta gaji, ga wurin da take ikon ta baya aiki, amma wurin da take babu abun cutar wa, tsararren ɗaki ne wanda komai da komai akwai shi, duk abinda ake buƙata akwai, daga ɗaki tana hango ruwan da yake zagaye da ɗakin da kifaye masu gadinta na sihiri...

Ruwa ne ke kewaye
End Ads