Nasreen ta tsaya tana kallon komai da hawaye — wannan masauƙi ba wurin firgici bane, ba wurin ƙaura bane — wurin kwanciyar hankali ne da ta dade tana nema.
Miemie ta kalleta da murmushi sannan ta ce:
"Ki huta. Ki wanke zuciyarki da kuka idan kina so. Amma ki sani — ba komai ke ƙarewa ba. Wasu lokuta tafiya ce kawai ta canza hanya."
Nasreen ta kwanta akan gado, Ruwan sama na ci gaba da tafiya a waje, kifaye na wucewa da annashuwa. Idonta na rufe a hankali, zuciyarta na raguwa da nauyi — wannan daren ba zai ƙare da kuka ba....
Ranar ta waye cikin kwanciyar hankali ga Nasreen. A karon farko tun bayan aurenta, ta farka ba tare da kuka ko tsoro ba. Wurin da take kwana kamar mafarki ne — kamar wata duniya da aka adana domin masu yawan zubar da hawaye.
Miemie ta kawo mata abinci mai ƙamshi, sannan ta zauna gefenta tana faɗin:
"Zuciyarki tana bukatar lafiya kafin komai. Amma kin cancanci a ƙaunace ki gaba ɗaya ba rabin zuciya ba. Kuma Abeesh... ba zai fahimci darajar ki ba sai ya rasa ki."
Nasreen ta lumshe ido da hawaye masu ɗumi. Har yanzu, tana ƙaunar mijinta, a koda yaushe tunaninta baya wuce akan Abeesh, bata san a wani hali yake ciki ba, ta bar shi da Catrina amma daga nan bata san komai akan abinda ke faruwa ba...
★★★★
A rana ya ta yau Madam Nablah ta shirya zuwa yankin da ta ajiye Nasreen, a yayin da ta bar Abeesh a tsaunin da ta ajiye shi, sai dai kuskuren da ta yi shine Catrina ta san a yanda Abeesh ya ke, hakan yasa Catrina itama ta yanke shawarar ɗauke Abeesh, hakan kuwa akayi, bayan tafiyar Madam Nablah, Catrina ta sace Abeesh ta tafi da shi can duniyar ta na duhu, wanda ba wani bil adama da ya isa ya shiga sai da izinin ta, har zuwa yanzu Abeesh bai farfaɗo ba....
Madam Nablah zuwa yanda Nasreen take ke da wuya, tana zuwa ta tarar da gadon da take kwance empty, ƙirjinta ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske har sai da Idanunta suka koma kamar na garwashi tsabar fargaba, haka ta fara dube-dube amma ba labarin Nasreen! fita bakin ruwa tayi tana lelleƙa ruwan dake zagaye da ɗakin amma ba motsin ta, lumshe idanuwanta tayi tana hasasho ƙasin ruwa ta ko ina kota faɗa ciki amma babu komai a cikin ruwan sai baƙaƙen halittun ruwa...
Madam Nablah wani tsafi tayi sai ga wani madubi ya bayyana a gabanta, tana son ganin a yanda Nasreen take, amma wani abun mamaki bata iya ganin yanda Nasreen take ba, domin an toshe hanyar yanda baƙin ruhi zai ga sirrin duniyar ruwan Miemie...
A fusace Madam Nablah ta rausa ihu tana faɗin:
"Kuna ina ne baƙaƙen halittun ruwan nan?....duk ku fito ina son ganin ku yanzu...."
Sai ga halittun ruwan sun fara bayyana marasa daɗin gani, tsabar yawan su bazasu ƙirgu ba,
baki a haɗe suke faɗin:
"Ga mu mun bayyana a gabanki ya sarauniyar wuta..."
Madam Nablah tana huci ta ce:
"Me ye amfanin ku a cikin ruwan nan in har zaku bar bil adama ta tsere muku?....shin tana inaaa? ta ya zata bi ta ruwa ta tsallake tarkona?..."
Suka ce:
"A gafarce mu Sarauniyar wuta, wacce ta fi ƙarfin mu ce ta bayyana ta ceceta, amma ba don ita ba bil adama bazata tsere mana ba...."
Madam Nablah ta ce "wace ce ta bayyana a cikin tsauni na, nan tsaunina ne babu wata halittar da take da ikon bayyana ko ina wacece, ko aljana ko mutum, nan ɗin masaraunta na ne...."
Ta ƙara sa tana ɗaga murya cikin ɓacin rai...
Aljanun ruwa suka ce:
"Wacce ta ke da iko akan faɗin ruwan duniya da wajen duniya ce ta bayyana, Sarauniyar mu na ruwa, duk da mun kasance baƙaƙen Aljanun ruwa amma babu da ikon dakatar da ita...."
Madam Nablah ta ce:
"Kuna nufin ku ce Sarauniyar ruwa ce ta ɗauke mun ɗiya? amma wannan ruwan yankin nan nawa ne ba nata ba..."
Aljanun suka ce:
"Kin manta ne amma ke sarauniyar wuta ce, baki da iko akan ruwa..."
A fusace Madam Nablah ta ce:
"Ku ɓace mun tin kafin na ƙone ku...."
Nan halittun ruwa suka fara komawa cikin ruwa, suka bar ta da takaici, itama bata juma ba ta ɓace....
A wani tsaunin daji ta sauƙa domin bata da ikon zuwa duniyar Miemie dole ta haƙura ta jira lokacin da zata bayyanar mata da ɗiya...
Yanda Abeesh yake ta nufa domin yau ta sha alwashin zata sadaukar da ruhi, ko Catrina ta kawo mata Abul tayi sadaukar wa da shi ko kuma ta yi sadaukar wa da Abeesh duk da tana jinsa a ranta amma hakan zata haƙura da shi......abinda ta tarar ne ya ƙara ɗaga mata hankali, ganin babu Abeesh a yanda ta ajiye shi kuma ta dasa masa baccin da bazai farka ba sai da ikon ta, amma da ta tuno da Nasreen itama baccin ta dasa mata kuma ta farka sai abun ya ɗaure mata kai, ganin babu Abeesh yasa ta saddaƙar domin a cikin wannan tsaunin babu yanda zai iya zuwa domin duk mallakin ta ne, tana iya ganin duk wanda ya shigo da wanda zai fita, lumshe idanuwanta tayi tana son ganin yanda Abeesh yake, a cikin kwakwalwarta ta ga Catrina tana ɗauke da shi ta hanyar iska ta ɓace da shi, da sauri ta buɗe idonta tana sakin numfashi, bata san lokacin da ta durƙusa a ƙasi ba tana faɗin;
"Kin ci amanata Catrina! Kin yaudare ni Catrina!! Kin butulce ni Catrina!!! meyasa zaki ɗauke Abeesh alhalin ba jinsin ki bane, kin wuce duniyar ki da shi amma zan jarraba ikona ganin na dawo da shi, Indai ke ce bazan ji fargaban ratsa duniyar ki ba...."
Wasu zafafan hawayen jini ne suke zuba a cikin ƙwayar Idanunta....
Itama lokaci guda ta ɓace sai ga ta a duniyar Catrina, sai kuma akayi rashin sa'a itama Catrina tana ɗauke da ƙarfin ikon da babu wani wanda zai iya shiga duniyar ta komen ƙarfin ikon mutum.
Madam Nablah ba yanda bata yi ba don shiga duniyar Catrina amma ta kasa, tayi tayi ta haɗa da tsafi amma ta kasa da haka itama ta haƙura ta koma yanda ta fito...
Catrina tana cikin tsararren gidan ta a cikin ɗaki tana kwance a gefen Abeesh da yake kan bacci har yanzu, ta san da zuwan Madam Nablah amma bata bayyana ba, murmushi tayi tare da faɗin:
"Devil Mom kina tunanin ke kaɗai kika iya wasan? kina tunanin ke kaɗai kike da ƙarfin iko? to kinyi kuskure domin nan duniyata ne, bazaki iya shigo wa ba, kuma Abeesh nawa ne babu mahalukin da ya isa ya karɓe shi daga hannuna ko waye shi, zan Aure shi, zan mallake shi sannan zai zama jinsin Aljanu shima...."
Wani ƙayataccen murmushi ta sau kan ta akan ƙirjinsa....
Madam Nablah ganin abubuwan da ta tsare su na kuɓuce mata ne yasa ta yi saurin zuwa yanda Tasleem take domin itace babbar matsalar ta shiyasa ta tsareta a wurin da babu wanda ya isa ya je...
Tasleem tana can cikin ɓoyayyen kogi a ƙasar duhun ƴan tsafi, inda babu wani haske ko numfashi ke isa.
Madam Nablah ce ta bayyana mata, ta kalle ta da tsantsar takaici sannan ta ce:
"Ke ce kaɗai za ki iya lalata abin da na ginata tsawon shekaru. Don haka za ki zauna a nan har sai lokacin da numfashin Amaar ya ƙare."
Tasleem na kuka tana ƙiran sunan Amaar da karfin hali, amma muryarta na nutsewa cikin ruwa mai tsafin mantuwa.
★★★
Amaar! a gefe guda, ya rasa nutsuwa. Ya yi ta neman Tasleem amma bai ga wata alamar inda ta shiga ba. Zuciyarsa ta karye. Yana tunanin ashe soyayyar da ya fara sake gina wa zata sake dusashewa?...
Yana tare da mahaifinsa, yana zazzagar hawaye da zuciyarsa mai rauni ya ce:
"Na rasa Tasleem, Abul. Na yi rantsuwa zan kare ta – amma yanzu…"
Abul cikin kyarma domin tsufa ta kama shi sosai ya ce:
"Wataƙila ba ka rasa ta ba, Amaar. Wataƙila akwai hanyar da za ka same ta – sai dai sai ka sake buɗe zuciyar ka ga tsafi da haske."
Amaar cikin rashin fahimta ya ce:
"Ban fahimta ba Abul..."
Abul ya sau numfashi tare da faɗin:
"Zaka fahimta in har kana son ceto abar ƙaunarka..."
A cikin ruwan da babu haske, inda hatta rana ke kasa haskakawa, Tasleem na kwance cikin wani ƙaramin ɗaki na ruwa, ƙafafunta an ɗaure su da sarƙar ruhi – wacce ba a iya yankewa sai da zuciya mai gaskiya. Kuka ya ƙure mata, amma zuciyarta na da ƙarfi fiye da yadda Madam Nablah ta zata.
Tana faɗin:
“ Ya Amaar… Zan dawo gare ka. Idan har zuciyar ka na raye da ƙauna ta... Zan ji numfashinka da yardar Allah....”
Madam Nablah tana zaune a cikin masarautar ta dake yankin ta, lissafi yana shirin jagule mata, tana cikin nazari sai agogon hannunta ya fara ƙara, cike da mamaki Madam Nablah ta kalli agogon hannunta domin ta saita wannan agogon bazai taɓa yin ƙara ba sai wani da dalili....
Zaro ido Madam Nablah ta yi tare da washe baki, bata san lokacin da ta kurma ihun farin ciki ba, har sai da Kura da zakin gefenta suka tsorata, suma haka jikinsu yake ci da wuta tsabar an ƙera su da wuta ne, Madam Nablah miƙe wa tayi tana taka rawa da girgiza wutar jikinta na tashi sama, wasan wuta ta fara yi tana furtar da wuta a bakinta, haka jikinta yake ci da wuta duk na farin ciki,
Ɗaga hannunta tayi sama tana kallon sama tare da faɗin:
"Godiya da jinjina ga shugabana ZULQARNAIN!.....An samu babban rabo a sashen ɗiyata Asmeen da Shapreen, zan zama sarauniyar da babu kamar ta a faɗin duniya, Asmeen ta samu ƙaruwar jariri, a wannan rana ya ta yau...."
Farin ciki marar misaltuwa ne yake wanzuwa a zuciyar Madam Nablah, duk wani ƙunci da damuwa sun wanke a zuciyarta....."
A fili take faɗin:
"Yanzu zan koma duniyar mutane domin ganin abinda yake faruwa a sashen gidana, zan ga lafiyar Asmeen sannan zan bata kariya sosai..."
Tana kaiwa nan ta ɓace a cikin wuta, bata tsaya a ko ina ba sai a duniyar mutane a wani filin da ba mutum ko ɗaya...
A bakin titi ta tsaya ta ƙira number security gidanta, kafin nan da ƴan mintuna sai ga zafafan motoci sun zo ɗaukar ta....
A babban falon gidan Madam Nablah Asmeen da Shapreen da Amaar da Abul ne suke zaune, suna tattaunawa akan ɓatan yaran gidan,
Tasleem da Nasreen da Abeesh...
Duk basu san cewa Madam Nablah tana hanyar dawowa ba, har ta shigo gida babu wani ƙara ko alamar tsayuwar mota, tana fito wa daga cikin mota ta nufi ciki....
A mashigar falo Madam Nablah ta saurari tattaunawar su,
Abul yana buɗa musu hanyar da zasu samu Tasleem, yana nema musu mafita..
“A cikin zurfin ƙasar da ke ƙarƙashin wuta, akwai wani Malamin da zai iya tona asirin ruwan tsafi. Sai dai wajensa cike yake da haɗari, kuma babu wanda ke iya zuwa wurin sai da ni'imar gaskiya.”
Amaar ya kalli mahaifinsa ya ce:
“Idan wannan ne hanya guda don in dawo da Tasleem, to ni zan tafi.”
Shapreen ya ce:
“Ba za ka tafi kai kaɗai ba. Ni da kai zamu je. Na samu ɗaukakan haske daga wurin Asmeen, itama tasan da hakan, zamu tsire da yardar Allah.....”
Madam Nablah dake leɓe a bakin ƙofar falo duk ta saurari shirin su, basarwa tayi tare da shiga falon da murmushi akan fuskar ta, da sallama a bakin ta...
Asmeen dake zaune ganin Madam Nablah yasa ta miƙe da gudu ta je ta rungume ta tana faɗin:
"Oyoyo Mommy! Mommy ina kika je haka tsawon watanni bakya nan, kuma bamu san inda kika je ba..."
Madam Nablah tana shafa fuskar ta tace:
"Yanzu ga shi na dawo ai, bazan ƙara tafiya na barku ba rabin raina..."
Asmeen ta ce:
"Mommy baki san abubuwan da suke faruwa ba, nayi ta neman wayanki bata shiga..."
Asmeen ta fashe da kuka...
Madam Nablah cikin damuwa take faɗin :
"Me yake faruwa ne Daughter?..."
Ta nuna kamar bata san komai ba...
Amma Abul da Amaar da Shapreen duk sun san cewa tasan abinda yake faruwa duk da bata nan...
Asmeen tana kuka tana faɗin:
"Mom! Nasreen tayi hatsari ta mutu, ga Yaya Abeesh shima an rasa shi ko labarinsa babu, itama Tasleem babu sake jin labarinta ba, shin me yake faruwa ne?..."
Madam Nablah ta ce:
"Whatttt? me ya faru da su haka?..."
A lokacin da aka sanar Tasleem ta bace, Madam Nablah ta nuna alhini da mamaki kamar kowanne mutum. Amma a zuciyarta, tana jin daɗin cewa ta hana soyayyar Amaar girma – domin Tasleem na zama barazana ga ikonta.
Sai dai ba ta san cewa a gefe guda, Shaprees ya gano inda ta ɓoye Tasleem. Amma bai sanar da kowa ba, domin yana shirin ya taimaka a sirrance.
Asmeen ta ce:
"Duk bamu sani ba Mommy..."
Madam Nablah jan hannunta tayi suka je su ka zauna, duk babu wanda ya mata magana a cikin su, itama Madam Nablah binsu tayi da ido ba tare da ta furta komai ba...
Asmeen ta kalli Shapreen ta ce:
"Ya Shaprees baka ga mommy ta dawo bane?tsawon watanni bata nan amma yanzu ta dawo baku nuna farin cikin ku ba...."
Shaprees yana hararar Madam Nablah ya ce:
"Ba'a irin waɗannan ake nuna farin cikin dawowar su ba, sai dai ayi baƙin ciki domin Annoba ta dawo..."
Ya kalli Madam Nablah sannan ya ce;
"Kada ki nuna pretending akan baki san abinda yake faruwa a gidan nan ba, domin nafi kowa sanin halinki, da kuma ƙarfin tsafin ki...."
Asmeen a fusace ta ce
"Ya Shaprees ya isa haka, mahaifiyata ce fa kake faɗa mata maganganu son ranka, oh wato ta gama maka amfani da ta Aura maka ni koh?..."
Shaprees ya ce:
"Tin kafin kisan waye ni nasan Mahaifiyarki, kuma tin kafin kizo duniya nasan wacece ita, don haka ko me na ƙirata ta cancanci haka domin ita baƙar Annoba ba, wanda bata ƙyale ƴaƴanta ba ma balle wasu, idan baki sani ba mahaifiyar ki ce ta kashe mun matata mafi soyuwa a cikin zuciyata, sannan ta Aura mun ke akan wasu dalilan ta da ƙara ƙarfin ikon ta, jira take ki samu ciki tayi sadaukarwa kuma lokaci ya yi, tasan cewa yanzu kinada ciki shiyasa ta dawo, kuma Tasleem a hannunta take, haka Nasreen da Abeesh...."
Madam Nablah tana zaune bata ji komai a ranta ba don Asmeen tasan ko ita wacece domin sauran ma sun sani, ita kaɗai ce aka bari a duhu...
Asmeen ta kalli Shaprees dakyau sannan ta ce
"Duk waɗannan maganganun ƙarya ne, kunyi don ku tozarta mun uwa, kuma a yanzu nake so ka bani takardar saki na Shaprees...."
Shaprees ya ce:
"Idan har kika rufe bakin ki akan maganar saki to zan baki kariyar da bazaki taɓa faɗawa cikin tarko ba..."
Madam Nablah kanta a sunkuye ta ce wa Asmeen "Daughter kada ki tsaya ɓata yawun bakin ki, a yanzu inason Shaprees ya rubuta miki takardar saki ko kuma mu bar musu gidan..."
Asmeen ta fuskanci Shaprees sannan ta ce:
"Ka bani takardar saki na Shaprees tin kafin duniya tasan da zaman mu, domin zan maka wulaƙancin da baka yi zato ba, nasan wacece mahaifiyata amma bazan taɓa yadda cewa ƴan uwana a hannunta suke ba, kuma bazan juri ganin kana wulaƙanta mun uwa ba...."
Sai a lokacin Amaar ya buɗe baki ya ce wa Asmeen,
"Yana dakyau ki kulle wannan bakin nakin tin kafin ke ma ki faɗa tarkon da ba tsira, saboda na fahimci kinada ƙaramar ƙwaƙwalwa, su ƴan uwanki da suke da tunani mai kyau ai sun fahimci komai...."
Asmeen ta buɗe baki zata yi magana Amaar ya darara mata tsawa, tare da faɗin
"Ki mun shiru, ki nemi wuri ki zauna..."
Asmeen ta zauna domin tana shakkar Amaar..
Amaar ya kalli Madam Nablah sannan ya ce:
"Idan kin dawo ne don saboda wani iko naki to ki sani komai ya Kusan zuwa ƙarshe..."
Madam Nablah tana zaune ita kaɗai sai dariya take ta yi....gaba ɗaya ta mayar su mahaukata.
Amaar ne ya ɗago da Abul suka wuce cikin ɗaki, shima Shaprees miƙewa ya yi tare da barin falon, Asmeen ce da mommynta kawai suke nan...
★★★★
A daren yau zuciyar Amaar na ci gaba da girgiza. Tasleem ta ɓace kamar ba ta taɓa kasancewa ba. Sun duba ko’ina Sun shiga duhu da haske. Amma ko alamar sawunta babu.
Amaar ya tsaya a bakin ɗakin mahaifinsa, yana duban sa cike da damuwa ya ce:
“Na ji kamar ta ƙira sunana a cikin mafarki jiya… amma lokacin da na farka, shiru kake ji. Kamar zuciyata ce ke ƙaryata ni.”
Abul yadafa kafadarsa ya ce:
“Wasu mafarkai sune gaskiyar da ba za mu iya fassara ba tukuna. Amma kada ka bari bakin ciki ya cinye ruhinka, na fahimci ƙauna ta mamaye zuciyarka har ta kai ga kana ƙoƙarin mance sauran ƴan uwanka, Abeesh da Nasreen, Tasleem yanzu kawai ka sani...."
Amaar ya zauna kusa da Abul sannan ya ce
. "Abul… ko ka san wata alama da zata taimaka mu wajen gano inda aka ɓoye Tasleem?"
Abul ya lumshe ido tare da faɗin:
"duk shirin da mukayi nasan Nablah taji komai don haka baza muyi amfani da wancan ba, Idan har zuciyar wadda take da alhakin hakan ba ta karye ba, to sirrin zai ci gaba da ɓoye kansa. Amma akwai wata… wadda ta san wani abu."
Amaar ya ƙafe shi da ido ya ce:
"Wacece?"
Abul ya juyo ya ce da ƙarfi: "Tasleem!"
Amaar ya firgita. "Ka ce… Tasleem? Amma ai ita ce aka sace!"
Abul ya ce:
"Ina nufin… ita kaɗai ce ta san inda za a fara neman kanta. Sai dai kafin hakan… sai an buɗe wani sirri