x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 174

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Sannan ta kallesu gaba ɗaya daga sama har ƙasa ko wacce dressing ɗin ta ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, kowa da kalar dressing ɗin ta...

Cikin nuna farin cikin ganin ƴan matan ƴaƴanta ta ce "my triplets daughter I missed you..."

Su ma duk murmushi suka sake cikin jin daɗi da haka duk suka wuce ciki, a babban falo Madam Nablah ta tarar da wani matashin saurayi kyakkyawa mai ji da kansa yana zaune yana fuskantar television, yana ganin Madam Nablah ya yi saurin kawar da kansa gefe domin ko kallonta ma baya son yi, haka ya yi kamar bai ganta ba.

Madam Nablah tsaya kallon sa tayi ga triplets a ta bayanta su ma suna tsatstsaye, murmushi tayi sannan ta ɗauki remove ta kashe tv idonta akan matashin ta ce "Abeesh shin baka ga shigowa ta bane?..."

Miƙewa yayi tare da wurga mata wani irin kallo sannan ya ja dogon tsaki yabar falon, kai tsaye upstairs ya haura yanda room ɗinsa yake.

Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta kawar da idanuwanta daga kallon hanyar da yabi itama haura wani upstairs tayi ta nufi room ɗin ta ba tare da ta furta komai ba...

Triplets duk kallon juna suka shiga yi ko wacce da saƙe-saƙen da take a ranta daga bisani su ma suka wuce room ɗin su dake can saman upstairs na ƙarshe hawa na huɗu, babban room ɗin su ne wanda manyan gado uku ne a ciki, ko wacce da gadonta, sai other room wanda ya kasance nan ne wurin kayayyakin sakawar su wardrobe da mirror sai wasu ƙofofi guda biyu bathroom and toilet room...

Nasreen zama tayi a bakin gadonta hankali a tashe kamar zata yi kuka ta zabga tagumi bisa alamu kamar ta tafi dogon tunani, Asmeen ce ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗarta ta ce "Nasreen!.."
shiru bata amsa mata ba still ta sake ƙiran sunan "Nasreen!!..."

Tasleem wacce ta gaba cire kayan jikinta ta zauna daga ita sai short jeans da singlet ko kallon yanda suke bata yi ba ta nemi gadonta ta kwanta tare da lalumar wani littafin English...

Asmeen da ƙarfi ta sake ambatar sunan Nasreen a saitin kunnenta, a firgice Nasreen ta juyo tana furta "Na'am ABEESH...."

Asmeen zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "Abeesh kumaaaa?...."

Tasleem wacce ta fara karanta littafi a ruɗe itama ta juyo tana kallon Nasreen,
Aasmeen wacce take kusa da Nasreen dafa kafaɗarta tayi cike da tausayawa ta ce "Nasreen wai me yake damunki haka? Abeesh fa naji kin furta, mutumin da yake zaman ƙiyayya da mahaifiyar mu, kinaga ko zama baya yi a wurin da take amma kin ɗauki damuwa kin ɗora masa, meye matsalar ki ko dai son sa kike?..."

Nasreen da sauri ta juyo tana kallon Aasmeen haɗe da girgiza mata kai tana faɗin "ko kaɗan wallahi, indai so na soyayya ne bana jinsa a raina amma ina son sa a matsayin ɗan uwantaka domin shi ɗin jinin mu ne, kin san da cewa mahaifinsa da mahaifin mu marigayi uwa ɗaya uba ɗaya suke, bashi da kowa bayan mu idan bamu ja shi a jiki ba ina zai shiga? ƙiyayyarshi da mahaifiyar mu kuma Allah ne kaɗai yabar wa kansa sani, bamu san me ya haɗa su ba haka muka tashi tin yarinta muka gan su a haka, na farko bamu isa mu tuntuɓi Mom akan abinda ya faru ita da Abeesh ba kuma shima Abeesh da zaran an kawo masa maganar Mom barin wurin yake baya tsayawa ya saurare mu, abun yana damu na wallahi...."

Tasleem dogon tsaki ta ja sannan ta ce "meye to abin damuwa bayan haka kika tashi ki ka gansu, idan baki cire wannan damuwar ba wata rana sai dai a samu gawar ki, ni ban yadda dake ba son sa kike..."

Nasreen murmushi tayi sannan ta ce "kin dai san inada wanda nake matuƙar ƙaun..." bata ƙarisa fitar da maganar ba Aasmeen tayi saurin toshe mata baki da hannu tana girgiza mata kai...

Nasreen cikin fushi ta zamar da hannun Aasmeen daga kan bakinta ta miƙe tsaye tana faɗin "wai har yaushe za'a daina hukunta mu haka ne? nifa na gaji so ake mu mutu babu Aure ne? mun kai minzalin fara soyayya amma kullum a cikin daƙushe mana farin ciki ake, babu abinda muka nema muka rasa a duniyan nan sai abu ɗaya wato farin cikin soyayya, har yanzu bamu san daɗin soyayya ba, kullum a cikin ɓoye soyayya muke saboda kar a cutar da wanda muke so haba dan Allah...."
lokaci guda Nasreen ta fashe da matsananci kuka mai azabtar da zuciya...

Aasmeen itama hawayen take ta miƙe tsaye tare da dafa kafaɗarta tana faɗin "Nasreen idan bamu ɓoye soyayyar mu ba shin ya zamuyi? kina ga fa duk wanda muka fara soyayya da shi a cikin kwana ɗaya sai an samu gawarsa a jikin gawarsa kuma sai an samu takarda mai ɗauke da rubutun sunayen mu gaba ɗaya, Tasleem, Nasreen, Aasmeen duk a rubuce kuma hukuma babu abinda zata iya yi akan mu duk da bamu muke yin kisan ba, nasan a ɓangaren ki Nasreen an samu gawar samari kusan 50 waɗanda suka baki saƙon soyayya, haka nima a ɓangarena an samu gawar samari waɗanda suka ce suna sona da yawa, Tasleem ce kawai take yiwa samari kwarjini haɗe da yi musu wulaƙanci amma duk da hakan har da sunanta a rubuce a jikin takardar da aka samu a jikin ko wani gawa indai ya furta mana kalmar soyayya, Nasreen ba wai soyayyar ce matsalar mu ba, babban matsalar mu shine kashe waɗanda zamu yi soyayya dasu, kashe waɗanda basu ji ba basu gani ba duk a saboda mu...."

Nasreen share hawayen fuskar ta tayi tana fuskantar Aasmeen ta ce "anya kuwa bamu da baƙaƙen aljanu?..."

Aasmeen ta ce "i think so but bakya tunanin Ayub student ɗin school ɗin mu da ku ka fara soyayya dashi akan abinda zai faru da shi?..."

Nasreen ta ce "Insha Allahu babu abinda zai faru dashi domin na tsayar da addu'a ta sosai akan sa, kinga sauran duk basa wuce kwana ɗaya ake kashe su shi kuma Ayub yau satin mu guda dashi, shiyasa nake da hope akan sa...."

Aasmeen jinjina kai tayi sannan ta ce "amma naga ƙoƙarin Ayub da har yake da ƙwarin gwiwar zuwa wurin ki alhalin yanzu kam school kowa gudun mu yake, ba wanda yake son tsayawa a kusa damu balle har soyayya, har sun sa mana suna Mayu, nidai a yanzu bazan ƙara karɓan soyayyan kowa ba domin bazanyi sanadin mutuwar Ɗan mutane ba..."

Nasreen sauƙe numfashi tayi sannan ta kalli wurin da Tasleem take sai faman karatun ta take,
Ta ce "Tasleem ke babu abinda zaki ce a wannan al'amarin ne?..."

Tasleem ɗagowa tayi fuska ba annuri ta ce "kin taɓa jin na tsoma baki na a cikin zancen soyayyar ku? ko kun fiso nima a rinƙa rubuta mun alhakin ɗaukan rai? kun san abinda yake faruwa damu amma kun kasa fahimtar komai, ta sanadiyarku ake hallaka bayin Allah amma ku bakuda imanin da zaku dakatar...."

Nasreen ta katseta da cewa "inda munada halin dakatarwa da tin yaushe mun dakatar..."

Aasmeen ta ce "taya zamu dakatar alhalin bamu san lokacin da abun yake faruwa sai dai mu ji labari..."

Cikin fushi Tasleem ta ce "ehen zaku iya dakatarwa ta hanyar daina soyayya da kowa, hakan ne zai ceci waɗanda ake hallakarwa, soyayyar banza da wofi dole sai anyi ta ne? kuma kunsan in kunyi ta ma ba samun soyayyar ku ke ba sai jawa kan ku zargi ko kuma jawa kan mu gaba ɗaya tinda nima ba'a barni ba, Ni da bana kula kowa babu ruwana da kowa amma sai an samu sunana a rubuce a takardar gawar samari ku, ni yanzu akwai mai zarrah da ikon da ya isa ya tuntuɓeni da maganar soyayya ne? duk da ba kowa yake gane kamannin mu ba amma ni na fita daban saboda mata ma basu ishe ni kallo ba bare maza...."

Nasreen ta ce "Uhmmm Tasleem kenam kin manta ne, amma lokacin da muke primary duk cikin mu kece kawai mai shiga shauƙin soyayya, ke da Amaar Junaid bakwa rabuwa kullum kuna tare duk da a lokacin abokai za'a ƙira ku domin baku kai minzalin Aure ba duk da a lokacin shi yana Jss 3, nasan in badan kin rasa shi ba da yanzu kam sai dai a ƙira ku da Julleit and Romeo tsabar soyayya...."

Nasreen da Aasmeen tafa hannayensu suka yi suna kwashewa da dariya, sannan suka juyo da ganinsu kan Tasleem, abinda suka gani ne ya tayar musu da hankali lokaci guda, ganin Tasleem a wani irin hali ta riƙe kanta sosai da hannu biyu tana faman shiɗewa, ƙwaƙwalwarta ne yake wani irin juyawa yana hargitse wa gaba ɗaya ta fita hayyacinta lips ɗinta ne yake kakkarwa a hankali take furta
"Mom! Mom!! Mom!!! Mom!!!!..."
hannunta riƙe da kanta sai juyi take tayi akan gado kafin su Nasreen su yo kanta har ta faɗo daga kan gado tana hargutsa sumar kanta, idanuwa sunyi lufu-lufu ga wani irin zazzafan hawayen da yake zubo mata, a yanzu dai bata cikin hankalin ta, gaba ɗaya hankalin ya gushe, still bata daina furta "Mom! Mom!! Mom!!! Ba....

A ruɗe Nasreen ta kalli Aasmeen sannan ta ce "gudu ki ƙira Mom kice ciwon Tasleem ya tashi, sauri dan Allah..."

Ganin bazata iya mata wani magani ba yasa ta rungume ta sosai a jikinta tana tottofa mata addu'o'i..

Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Aasmeen tare da Mom sun shigo tare da, tsayawa Mom tayi tana ƙare Tasleem da kallo daga bisani ta ce "duk ku fita can falo ku jira ni..."

Hakan kuwa suka yi Nasreen da Aasmeen fita suka yi daga ɗakin,
Cikin ƙarfin tsafi Mom ta ɗago Tasleem da hannunta ba tare da ta taɓa gangar jikinta ba sannan ta ɗora ta akan gado, itama Mom haurawa saman gadon tayi tare da ɗago kan Tasleem ta ɗora akan cinyar ta, sannan ta ɗora hannunta akan goshinta domin tabbatar da abinda ke damunta,
rufe idanuwanta tayi sosai hannunta akan goshin Tasleem, abubuwan da suke yawo a cikin kwakwalwar Tasleem ta fara gani, haka take ganin video abinda yake cikin ƙwaƙwalwar Tasleem ta cikin ƙwayar idanuwanta ga murya Tasleem tin tana ƙarama yanda yake dukan dodon kunnen Mom, muryar da yake fitowa shine
"Mom! Mom!! kar ki kashe shi Aboki na ne, dan Allah, ina son sa Mom Aboki na ne Amaar Junaid, Mommm kar ki jefa shi cikin ruwan nan mutuwa zai yi, zan rabu da shi Mom ki ƙyale shi Moommmm...."

Da sauri Mom ta buɗe idanuwanta waɗanda suka koma kamar na aljana babu ɗigon baƙi a cikin idanun duk sun koma fari soll, haka take sauƙe numfashi ganin wannan al'amarin ya kasa barin cikin kwakwalwar Tasleem, duk da tin daga lokacin faruwar hakan Devil Mom ta tsafe mata tunanin ta yanda zata manta duk abinda idanuwanta suka gani, zata manta abinda ya faru amma da zaran an ambaci sunan Amaar Junaid Shikenam za'a nemi hankalin ta a rasa, abun zai dawo mata ƙwaƙwalwa wanda in ba'ayi saurin gusar mata da tunani a lokacin ba, ƙwaƙwalwar ta na baya zai iya dawo mata gaba ɗaya wanda komai da komai zata tuna shi shiyasa Mom take tsoron wannan ranar hakan yasa duk kallonta akan Tasleem yafi tsayawa saboda kar a kawo mata maganar Amaar ciwon ya dawo,
a duk faɗin duniyar da take idonta yana kan Triplets ɗin ta, ta cikin madubi take kallon duk abinda suke ko a makaranta, sannan duk mutumin da ya tare mata yara da sunan soyayya sai taga bayan sa, ita take yin kisan da duk ake yi akan triplets sannan ta rubuta sunayensu su uku ta ɗora akan gawa,
Devil Mom takan iya ɓacewa ta ƙoma duk yanda ta ga dama, takan iya ratsa jikin gini tayi wucewar ta, takan iya ɓace wa taje ta samu mutum a duk faɗin duniyan da yake,
tana daga zaune zata tura spirit ɗinta yake yayi kisa ya dawo ya shige gangan jikinta, rubuta sunayen ƴaƴanta da take a jikin takarda sannan ta ajiye akan gawa tana yin haka ne saboda kowa yayi nesa da yaranta....

Idonta akan Tasleem wani irin haske ne ya fito daga cikin idanuwanta ya shige kan goshin Tasleem wanda kota farfaɗo bazata taɓa sanin abinda ya faru da ita ba, daga nan Mom ta sake lumshe idanuwanta lokaci guda ta buɗe su sai eyes ɗin ta suka koma normal yanda suke,
tashi tayi tabar ɗakin a yayinda ita kuma Tasleem wani irin nannauyar bacci ya ɗauke ta....

A falo Madam Nablah ta tarar da su Nasreen da Aasmeen suna ta zarya sun gagara samun nutsuwa duk da ba karo na farko da Tasleem take shiga wannan halin ba amma suna matuƙar damuwa da hakan,
Nasreen ganin Mom ɗin su yasa duk suka je wurin ta suna faɗin "Mom ta tashi ne?..."

Cikin zafin rai Mom ta riƙo sumar gashin su duk su biyun rai a ɓace take faɗin "idan na sake jin kun ambaci sunan Amaar Junaid a cikin gidan nan to duk sai na hallaka ku..."

Daga nan ta sake su tare da nufan upstairs zata nufi room ɗin ta, har zata haura ta ɗaga kanta sama ta order site upstairs taga Abeesh ne tsaye ya goya hannayensa biya akan ƙirjinsa shima idonsa akan ta rai a ɓace...

Kawar da kanta tayi ta shige room ɗin ta...

Nasreen da Aasmeen kallon juna suke cike da mamaki kowa da abinda
End Ads