ya yi tare da faɗin "zan miki baya ni da zaran mun nutsu..."
Asmeen ta ce "wani bayani zaka yi bayan mun fahimci komai, amma kayi kuskure da ka fara sanar mata kana sonta, da ma ta hannun mu kazo zamu fi jawo maka hankalin ta amma kaga yanzu zata saka ka a jerin maƙiyan ta...."
Ya ce "ba komai zan sa ta dawo dani masoyinta na musamman kamar yanda take a cikin zuciya ta..."
Asmeen ta ce "ai kuwa idan kayi haka ka cika jarumi na musamman..."
Nasreen ta ce "kar ka damu Ɗan uwa ina tare da kai kuma zan taya ka jawo maka hankalin ta..."
Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli yanda Abeesh yake a zaune ya zuba musu ido yana tunani a ransa cewa "daman saboda masoyiyar sa wannan mutumin ya shigo gidan nan? lallai ya cika jarumi kenam ba mai feshin magani ba ne ?..."
Yana cikin wannan tunanin sai gani yayi Amaar ya nufo wurin da yake yana faɗin "Please Boom boy ka taimaka mun kaima wurin shawo mun kanta, ita ɗin rayuwata ce..."
Abeesh yamutsa fuskar sa yayi tare da faɗin "who is Boom boy?..."
Nasreen hannu tasa ta toshe bakin ta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar ta,
Asmeen kuwa kwashe wa tayi da dariya tana faɗin "Boom boyyyyy...."
Suna cikin rahar su sai ga Tasleem ta sauƙo daga saman upstairs da gudu tana riƙe da ƙaramin bindiga a hannunta, tsayawa tayi ta saita shi tana faɗin "wato ka raina ni koh? har kana da ƙwarin gwiwar shigowa gidan mu ka furta mun soyayya? to yau sai dai a fita da gawar ka domin bazan ƙyale ka ba..."
Tana kaiwa nan ta harba bindigar daman already ta kunna kunamar bindigar da sauri Amaar ya sunkuya ƙasi bullet ta wuce ta saman sa sai akan plasman, plasman ne ya dagargaje haka Asmeen ta shige ƙarƙashin dinning tana zunduma ihu, Nasreen kuwa bata san lokacin da tayi tsalle ta faɗa kan Abeesh ba,
Abeesh shima rungumar ta ya yi sosai yana tunanin ta yanda bullet zai fara shigan sa domin ba ƙaramin tsorita ya yi ba, itama Nasreen tana rungume dashi sai zabga ihu take tana faɗin "dan Allah azo a taimaka mana, Tasleem ki daina kar tsautsayi yasa ki harbe mu wayyo Allah..."
duk toshe kunnuwa suka yi tsabar ƙarar bindiga sai farfasa abubuwan falo ake irin su glass da su flowowi, ta ko ina Tasleem harbi take tana bin Amaar da gudu, duk yanda yayi da gudu haka take binsa tana harbi, har yanzu bata yi nasarar samun sa ba, nufan wurin dinning ya yi Asmeen ta kwarara ihu tana faɗin "dan girman Allah ɗan uwa kar ka yo ta nan ka taimaki rayuwata..."
Abeesh riƙo hannun Nasreen yayi tare da ɗagota suka nufi upstairs da gudu, cikin sa'a suka shige bedroom tare da rufe ƙofa...
Iya Amaar ne da Tasleem suke ta zarya a falo gaba ɗaya sun yi kaca-kaca da falon, sun farfasa komai na falon, hatta kujeru duk sun fuffuje da harbin bullet, daƙer Amaar ya ɗauki pillow kujeru guda biyu ya yo kan Tasleem da gudu kafin ta ankara ya yi tsalle ya faɗa kanta, gaba ɗaya faɗuwa suka yi akan carpet tana ƙasi shi kuwa yana saman ta ya danne hannayenta da filellikan kujerun da ya ɗauko yanda bazasu ji shocking ba, ya sakata a tsakiyar sa ba tare da ya danne ta ba sai iya hannayenta da ƙarfin sa yanda bazata samu ƙarfin ture shi ba,
tana ƙoƙarin tashi amma ta kasa har ƙarfin ta ya ƙare haka tana ji tana gani ta kwanta tana kallon sa fuska a murtuƙe sai sauƙe numfashi take, shima kallon cikin ƙwayar idanuwanta yake tare da sakin murmushi ya furta "saboda tsananin ƙaunata da kike ne yasa zaki kashe ni?..."
A fusace ta furta "na tsane ka wallahi ni ka ɗaga ni..."
Kan sa yake matso dashi saitin fuskar ta zai sumbace ta, ganin abinda yake shirin yi ne yasa ta fara jujjuyar da kanta tana faɗin "bana so, kar ka sumbace ni, bana so, na gaya maka zan tsine maka albarka, ja'iri kawai..."
Numfashin su ne yake haɗe wa yana shirin haɗe musu baki, ta ce "wallahi kana kawo bakin ka zan cije ka..."
Sauran kaɗan ya haɗe musu baki ya yi saurin kawar da lips ɗinsa zuwa kan sumar gashin ta, cikin so da ƙauna ya sumbace ta akan gashin ta a hankali gudun kar su ji shocking...."
A hankali yake hura mata iskar bakin sa ta ko ina, haka yake bin fuskarta da iskar bakin sa, ita kuwa ganin ba yanda ta iya ne yasa ta lumshe idanuwanta, ji tayi yana mata magana a sai tin kunnen ta a hankali cikin sexy voice "calm down! calm down!! calm down!!!...."
Sai da ya fahimci ta samu nutsuwa tukun yayi saurin miƙe wa tare da ɗaukan abubuwan da yazo da su ya fice kafin ta ankara ta tashi....
Asmeen tana ƙarƙashin dinning idonta a kansu baki ya gagara rufuwa tsabar yanayin da suka shiga ne ya sanya ta nishaɗi....
Abeesh tinda suka shiga room ɗin sa suka tsaya a bakin ƙofa Nasreen kuma ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tayi lumuuu, shima kansa ya ɗora akan tsakiyar kanta ya lumshe ido gaba ɗaya basa cikin hayyacin su, Abeesh ƙamshin sumar kan Nasreen ba ƙaramin hargutsa masa ƙwaƙwalwa ya yi ba...
Tasleem har zuwa yanzu bata buɗe eyes ɗin ta ba, bata ma san Amaar ya tafi ba sai dariyar Asmeen ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta, a zabure Tasleem ta tashi daga kwancen da take a ƙasin carpet ta lalumo bindigar ta tana jujjuyawa tare da faɗin "yana ina? yana ina? yau sai nayi maganin sa..."
saita Asmeen tayi da bindigar tana faɗin "ina wannan ja'irin mutumin yake?..."
A tsorace Asmeen ta ce "kin ga dan Allah ki ajiye bindigar nan kar tsautsayi yasa ki harbe ni, shi kam ya daɗe da tafiya..."
Tasleem ta ce "kashhhh! naso na ragargaza masa ƙwaƙwalwa..."
Suna cikin wannan yanayin sai jin sautin motar Mommyn su suka yi ta dawo,
A ruɗe Asmeen ta ce "innalillahi Mommy ta dawo..."
Tasleem haura saman upstairs tayi tana riƙe da bindigar ta,
Da gudu Asmeen ta haura saman upstairs room ɗin Abeesh taje tana bubbuga ƙofar, sai a lokacin Abeesh da Nasreen suka dawo hayyacin su, sai ji suka yi Asmeen tana faɗin "Nasreen mommy ta dawo..."
Nasreen zaro ido tayi tana faɗin "mommy ta dawo?..."
Cikin jin kunya Abeesh ya nufi cikin room ɗinsa ita kuma ta buɗe ƙofa ta fice, a tare suka sauƙa falo ita da Asmeen daidai lokacin da Madam Nablah ta shigo falo tana taku kamar bazata taka ƙasi ba, ganin yanda falon ya koma ne yasa ta tsaya cakk tana bin falon da kallo, cike da mamaki ta ce "whattt! me nake gani haka?..."
Nasreen da Asmeen bakin su a haɗe wurin faɗin "your welcome Mom..."
Madam Nablah ta ce "ba wannan ba taya falo na ya koma haka? wasan dambe ku ka yi ne? ko an mayar mun da falo kasuwa ne ban saniba..."
Duk girgiza kai suka yi alamar a'a,
Ta kuma cewa "shin yaƙi akayi ne? ko farmaki aka kawo muku?..."
Ganin basu da amsar da zasu bata ne yasa suka ce "Mom ɓera ne..."
Asmeen ta ce "ɓera ne ya fito falo saboda jin warin feshin magani da akayi, shine muke ta gudu..."
Madam Nablah ta ce "Amma harbin bindiga nake gani ata ko ina, har a jikin bango, da kujeru ga plasman bullet ya fasa mun shi, flowowin ɗakin duk sun ragargaje, jikin frig alamar bullet, wai shin wani irin asara ku ka tamka mun ne haka? kayayyakin ɗakina masu bala'in tsada kun mun asarar su duk a saboda ɓera..."
Asmeen ta kuma cewa "bindigar mu muka ɗauko zamu harbe ɓeran shine yake ta guduwa ko ina shiga yake, tsautsayi ne a yafe mana..."
Madam Nablah fuska ba annuri tana kallon gefe ta ce da su "ku tafi ku bani wuri..."
Haka suka ja jiki a sanyaye suka koma can room ɗin su...
Madam Nablah ganin ba kowa a falon ne yasa ta lumshe idanuwanta, ta ɗago da hannayen ta sama sai ga wani irin haske mai launin green sai ga falon ya fara juyawa, a hankali a hankali har ya fara juyawa da gudun gaske, itama Madam Nablah haka take juyawa a cikin falon har sai da falon ya koma duhu ƙirin baka iya ganin abinda yake ciki, har ya koma normal, sai da falon ya ɗau tsawon mintina sha biyar daga bisani sai ga haske ya bayyana,
Innalillahi wani irin tsaruwa falon yayi kamar ba'a Nigeria ba, komai da komai an canza kayan furnitures, kujeru na musamman masu bala'in tsada wanda babu mai irin su a doron ƙasa, plasman kuwa daga ƙarshen bango har ƙarshen bango tsabar girman sa, tsaruwar falon bazai misaltu ba...
Tana kammalawa ta haura saman upstairs can room ɗin ta, falon kamar babu abinda ya faru a cikin sa,
Bayan awanni Asmeen ce ta sauƙo falo ganin yanda falon ta koma ne kamar wacce tayi ɓatan kai, haka take ta kallace-kallace ta kasa gane wa shin a gidan su take ne ko kuma ƙasar waje aka fita da ita, tsabar ta gama tsora ta da gudun gaske ta koma room ɗin su, tana zuwa ta jawo hannun Nasreen suka fito falon a tare, itama Nasreen abinda ta gani ne ya tada mata da hankali, a ruɗe ta ce "a yaushe aka sauya komai na gidan? hatta fentin an sauya launin sa.
Tasleem itama fitowa tayi, tsaya wa tayi tana bin falon da kallo daga bisani ta ce "Aljanun nan sun iya gyara kam..."
Nasreen da Asmeen kallon ta suka yi tare da faɗin "Aljanu kuma?..."
Tasleem ta ce "eh in ba su ba wani bil adam ne zai iya wannan aikin a wuni guda?..."
Nasreen gaba ɗaya itama abun ya ɗaure mata kai...
Madam Nablah tana kallon su ta cikin ɗakinta ta mirror, yanke hukuncin kawar musu da tunanin taya akayi aka maida falon na musamman tayi, tana cikin room ɗinta ta ƙirƙiri skeleton robot kamar mutane sannan ta sanya musu Aljanun da zasu zauna a jikin robot suna aiki kamar mutane, duk abinda aka sanya su suyi zasu yi, bayan ta gama ƙirƙiran su ta kuma basu umarnin su koma falo, haka robot suka fara motsi su biyar suka fita daga cikin room ɗin Madam Nablah suka nufi falo,
A jere su biyar suka fara sauƙo wa falo,
Asmeen ce ta fara ganin su a tsorace ta nuna su da yatsa ba tare da tayi magana ba, su ma sauran kallon wurin da take nuna wa suka yi, Nasreen ganin su yasa ta zaro ido waje tana faɗin "ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, meye waɗannan skeleton?..."
Tasleem kuwa tana ganin su kanta yayi wani irin sarawa kamar wanda aka kwaɗa mata guduma,
Madam Nablah ce ta biyo bayan su tare da faɗin "ku kwantar da hankalin ku waɗannan robot ne kamar yanda ku ke gani ana showing ɗin su a TV, duk siyan su nayi daga yau zasu rinƙa rage ayyukan gida, har girki su zasu na yi, gyaran gida su ne, komai da komai sannan duk abinda ku ke buƙata ku sanar musu zasu yi muku..."
Asmeen cike da mamaki ta ce "Mom irin robot ɗin da muke gani a Film yau su ne a gidan mu? ...."
Madam Nablah ta ce "eh su ne, musamman nasa aka kawo mun su daga China..."
Nasreen ta ce "Mom kina nufin kice su suka tsara falon nan? amma kuma naga komai na falon an chanza..."
Madam Nablah ta ce "daman ina ajiye da kayan furnitures, yau kuma nasa aka kawo mun waɗannan robot suka tsara mun falon kamar yanda na umarce su..."
Asmeen ta ce "wow so beautiful, abinda nake gani like dreams yanzu kuma gasu nan a realty...."
Tasleem gaba ɗaya hankalin ta bai kwanta da waɗannan robot ba, ji take ƙirjinta yana bugawa sannan kanta kamar ana buga mata guduma,
Tasleem nufan wurin robot tayi yanda suke a jere ta tsaya a gaban su tana ƙare su da kallo, idonta tasa a cikin ɗaya daga cikin robot tana kallon can cikin idonsa, gani tayi a cikin eyes ɗin sa wuta ne yake ta ci, haka tabi duk sauran da kallo su ma haka suke, lokaci guda taji wani irin hajijiya yana shirin ɗaukar ta...
Madam Nablah idonta akan Tasleem tana tunanin ita ce kawai zata kwabsa mata, tana da saurin gane sihiri shiyasa Madam Nablah bata yinta sosai duk da jininta ce,
Tasleem ce ta fara faɗin "ni gaba ɗaya hankalina bai kwanta da su ba, bana son su gaba ɗaya, dan Allah a fitar da su daga cikin gidan nan, bana son ganin su..."
Madam Nablah ce tazo ta tsaya a gaban Tasleem tare da faɗin "Kinga Tasleem sai dai daga yau kar ki ƙara fito wa falo ki rinƙa zama acan cikin room ɗin ku domin babu yanda zan kai su, kamar yanda na tsara haka zasu cigaba da gudanar da aikin su a cikin gidan nan, sannan zasu rinƙa mun recording duk abinda yake faruwa, don haka ki koma can bedroom ɗinki, abinci da komai duk za'a rinƙa kai miki can...."