x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 197

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tafe da sandarsa, yana fadin:

"Mai dauke da sirrin zuciya, kada ka manta… masoyi na gaskiya ba ya ɓoye sirri mai wuta, ruwan da kuke sha, yana iya zama madara ko guba."

Suna kallon juna cikin mamaki.

Nasreen ta ce

" Ya Abeesh… kana jin akwai wani abu da muke wulakanta gani?"

Abeesh yana kallon tsohon ya ce

"Ka sanar mana gaskiyar abinda kake nufi, nasan maganarka bazai wuce akan Madam Nablah ba..."

Tsohon ya nuna Nasreen sannan ya ce "ina magana ne akan wannan yarinya, ki kula da kan ki domin akwai sirrin tsafi...."

Abeesh ya kalli Nasreen cikin damuwa ya ce

"Zan tona komai daga yanzu. Idan akwai sirri tsakanin ki da tsafin Madam Nablah, wannan daren zai zama farkon haskenmu ko ƙarshenmu."

Tsohon ya ce:

"Akwai wani ƙugi a ƙasan gidan nan, an rufe shi da tambarin zinariya. A can ne aka binne asalin wutar Madam Nablah. Kuma, idan wani daga zuriyar gidan ya shiga ƙugin nan da zuciya mai tsabta, zai ga gaskiya gaba ɗaya...."

Daga nan tsohon ya ɓace ɓatt,
Nasreen cikin tsoro da fargaba ta rungumi Abeesh tana ihu, da sauri ya toshe mata baki zuciyarsa na ɗar-ɗar yana tunanin maganganun Aljanin tsoho da ya fito musu, cikin tashin hankali suka shige gidan, a lokacin misalin ƙarfe 12 na dare....


A falo suka tarar da Madam Nablah zaune akan sofa tana facing plasman alamun kallo take, ba komai ne yasa ta zauna a falo a wannan lokacin ba sai jiran dawowar su Abeesh, kallon su tayi cikin izzah da ƙasaita tana yamutsa fuska kamar bazata yi magana ba ta ce

Meyasa kuke hidimar gaban ku ba tare da bin umarni na ba, you support to tell me idan zaku fita wani wuri and then bana son yawon dare...."

Abeesh gyara tsayuwar sa yayi yana kallon ta tare da goya hannayensa akan ƙirji ya ce "bin umarnin ki dai-dai yake da faɗawa cikin wuta, shiyasa muke tsarkakakkiyar rayuwa cikin haske, bama buƙatar duhu ya shigo rayuwar mu...."

Madam Nablah murmushi tayi sannan ta kawar da kanta daga ganinsa, tana jinjina kai ba tare da ta furta komai ba,
Abeesh yana gamawa ya bar falon kai tsaye upstairs ya haura zai nufi bedroom ɗinsa.

Nasreen tana tsaye kanta na kallon ƙasi duk da halin da mahaifiyarta ke ciki bata daina mata biyayya ba, sannan kuma tana matuƙar jin shakkar ta saɓanin Tasleem,
ta juma a tsaye a gaban Madam Nablah ba tare da kowa ya furta komai ba, sai yanzu Madam Nablah ta samu bakin furta "ki bar gabana, like kije ki kwanta..."

Nasreen godiya tayi tare da barin wurin har zata hau saman beni ta hango Amaar ya shigo falo yana ɗauke da Tasleem wacce tayi bacci, yayi mata ɗaukar luɗa alamun a ɗakinsa tayi bacci, yana sakin murmushi idonsa akan Nasreen wacce ta zuba musu ido tana sakin murmushi itama..

Madam Nablah a firgice ta miƙe tsaye tana kallon su, idanuwanta kamar zasu faɗo tsabar zazzaro su da take cikin fushi gasu manya ne daman, tana huci haka Amaar ya wuce da Tasleem ko kallon yanda take bai yi ba, duk a tare suka haura saman upstairs da Nasreen tana masa dariya....

Itama Madam Nablah a fusace ta bar falon ta nufi bedroom ɗin ta,
Ba jumawa Amaar ya sauƙo bayan yaje ya kwantar da Tasleem, ya nufi room ɗin sa shima.....



A gefe guda kuma, Shaprees ya ƙara fusata. Duhu yana ƙara karfi a jikinsa. Amma cikin zuciyarsa, muryar Sophia tana ƙara bayyana, tana damunsa da tunanin gaskiya. Ya fito daga ɗakinsa da dare, ya nufi gidan ƙasa da ya ƙirƙira domin gudanar da tsafin sa, A can ya zana zane a ƙasa ya kira ruhin da ke ƙunshe da sirrin rayuwa da mutuwa.

Yana zaune ya furta cewa:

“Na yarda da duhu don in dawo da Sophia. Amma yanzu gaskiya tana fara rikita ni. Ina so in san, shin ina kan hanya?”

Wani murya ne ya bayyana, da suffar mutum kamar ruhi da idanuwa jajawur
ya ce:

“Ka rasa hanyar gaskiya tunda ka rungumi wuta saboda soyayya. Amma yanzu, akwai hanya ɗaya – idan Asmeen ta san gaskiya to zaka cimma burin ka, Idan kuma ka ci gaba da ɓoye gaskiya komai zai ƙone.”.........



A gefe guda.

Tasleem tana cikin bacci ta faɗa cikin wani mafarki mai ɗauke da haske, lokaci guda ta ganta a cikin gajimare wanda ba koda kukan tsuntsu ne, iya zallar haske ne sannan tana sanye da fararen kaya har ƙasi da mayafin kai wanda aka rufe mata sumar gashi, sai waiwaye take tayi amma bata tarar da kowa ba, bata wani tsorata ba domin tasan haske ne ke bibiyan ta ba abun cutarwa ba..

Tana tsaye taga wani mutumi fari da farin gemu yana sanye da fararen kaya shima a jikinsa, haka yake kamar ruhi domin ba mutum bane hakan yasa ya fito mata a mafarki domin ya tunatar da ita gaskiya,
Tasleem murmushi ne a kwance saman fuskar ta ganin tana tare da haske,

Cikin muryar nutsuwa dattijon nan ya fara magana kamar haka:

“Kin taɓa sha ruwa daga ruwan da aka gauraya da wutar ruhi. Ke ba mutum ba ce kawai — ke rabin ruhi ce, rabin jini. Kuma zuciyar ki na ɗauke da makullin rugujewar Madam Nablah.”...

Tasleem cikin rashin fahimta ta ce

“To me ake nufi da hakan?”..

Dattijon ya ce

“Dole ne ki fuskanci mahaifiyarki da gaskiya. Kuma idan Amaar yana tare da ke, ku shiga ƙugin zuma kafin Duhu ya maye gurbin Domin kuna da alaƙa da juna fiye da yadda kuke tunani.”

Tasleem tana motsi da lips a hankali ta furta "menene ƙugin zuma?...."

Dattijon ya ce "Hmmm... Ƙugi na zuma wannan ba kalma ce da yara ke taɓa ambatawa ba, sai wanda ya san asalin wani sirri,
Idan baki manta ba a nan ne kika taɓa ganin wani dattijon mutumi a tsare babu haske a yanda yake saboda tsananin tsafi, to nan ne gefen ƙugin zuma, asalin ƙugin zuma kuwa sai kinyi da gaske kafin kin san wurin, idan kika shiga nan ne gaskiya zata bayyana kanta, nan ne komai zai ruguje na tsafi, rayuwa zata dawo sabuwa..."

Tasleem a ruɗe take faɗin "a yaushe wannan al'amarin zai fara aiki?..."

Dattijon yayi murmushi sannan ya ce "dalilin da yasa zamu wakilce ki akan tsarin tafiyar mu, zalunci ya yi yawa, muna son haske ya kawo ƙarshen duhu, daga yanzu ke ce sarauniyar Haske, mun riga da mun naɗaki akan wannan mulkin, na kuma isar da saƙo a gareki...."

Tasleem ta ce "taya za'a ban sarauniyar Haske alhalin ban san komai game da haske da duhu ba?...."

Dattijon ya ce "a sannu a hankali zaki gane komai da idon sarauta, akwai wasu baiwa da muka zuba miki bayan bayyanar gaskiyar mafarkin ki, matakin da muke so ki kai a wannan zango shine ki bayyana gaskiya, domin haske tana tafiya ne da gaskiya, idan ba haske to ba gaskiya haka kuma idan ba gaskiya to kuwa ba haske, ki bayyana wa su Amaar yanda mahaifinsu yake, kuje ku cece shi daga halin da yake ciki na tsawon shekara ashirin, kada ki wuce awa 24 baki taimakawa tsohon nan ba.... Sarauniyar Haske....Ku hadu da wanda aka ɓoye – ku ƙaraɗe duhun da haske – kafin lokaci ya kure.”....


Tasleem tana hawaye tare da faɗin "Insha Allahu zan taimake shi, a yau ...."

Dattijon haske ya ɓace ba tare da ya sake cewa komai ba, daga nan Tasleem ta dawo baccin ta, a ruɗe ta tashi zaune tana jero addu'o'i...."

Itama Nasreen tashi tayi jin yanda Tasleem take ta addu'a cikin fitar hayyaci, tambayar ta take tayi tana faɗin "lafiya kuwa Tasleem? wani irin mafarki kika yi haka ..."

Sai a yanzu Nasreen ta lura da sumar gashinta da ya koma fari tass kamar furfura, babu alamun ɗigon baƙi, a tsorace ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Tasleem ya sumar gashin ki ta koma fari?.."

Tasleem bata damu ba kawai hannu tasa ta shafa kanta, sai a lokacin gashin ya fara komawa baƙi kamar yanda yake...

Tasleem cike da mamaki take maimaita wa Nasreen abinda ya faru a cikin mafarkin ta, ta sanar cewa "an bata mulkin sarauniyar Haske...."

Ta cigaba da cewa "Nasreen....taya zan fara gudanar da wannan al'amarin?...."

Nasreen ta matso kusa da ita tare da rungumar ta ta ce "ki bi gaskiya sai ki cigaba da kasancewa a cikin haske shine abinda wannan mafarkin yake ƙunshe dashi da kuma sarautar ki, duk wata gaskiyar da kike ɓoyewa ya zamana kin bayyana ta, kada ki ɓoye sirri sannan kar kiji tsoron duhu wannan shi ake nufi da sarauniyar Haske...."

Wannan bayanan Nasreen ya ƙarfafa mata gwiwa sosai, ta jinjina kai sannan ta furta "dole gaskiya zata yi nasara akan ƙarya dole haske ta wargaza duhu, yanzu ne daidai lokacin da zan buɗe wata gaskiyar da na daɗe ina ɓoyewa...."

Nasreen ta miƙe tana faɗin "meye wannan gaskiyar?..."

Tasleem ta miƙe tsaye tare da faɗin "UNCLE JUN mahaifin su Amaar da Abeesh...."

Nasreen itama miƙewa tayi tsaye tana faɗin "haƙiƙa wannan al'amarin babba ne, kuma ya rataya a wuyan sarauniyar Haske ta ceceshi daga cikin duhun da yake domin zuciyarsa haske gare ta...."

Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "naji an fara ƙiran asuba muyi sallah kafin naje na samu Ya Amaar da wannan batun...."

A cikin safiyar yau mai cike da shiru, wanda iska ke kadawa a hankali, Tasleem ta sauko daga saman bene Idonta cike da hawaye, zuciyarta kuma kamar ta fashe da sirrin da ta dade da boyewa. Tana shirin shiga ɗakin Amaar.

Bayan Tasleem ta je ɗakin Amaar bata same shi ba ya tafi masallaci shi da Abeesh, zaman jiran sa take har ya dawo, ganin ta a zaune cikin damuwa yasa ya ƙara sa wurinta da sauri yana faɗin "lafiya kuwa Baby Tasl?..."

Tasleem miƙe wa tayi ita tana hawaye ta ce:

"Ya Amaar..… idan na faɗa maka gaskiya, zaka cigaba da sona?”

Amaar ya tsaya yana kallonta daga bisani ya ce
“Soyayya ba ta dogara da sirri ba. Amma gaskiya tana ƙara ƙarfinta.”


Tasleem ta furta cikin kuka
“Ni ba cikakkiyar mutum bace. A yanzu na zama sarauniyar Haske wacce aka bata ragamar rushe tsafin Madam Nablah wacce take ƙoƙarin ruguza gaskiya akan ƙarya, Na zama haske ne domin na sanar da duk wata gaskiyar da ake ɓoyewa....”

Amaar ya rungume ta da ƙarfi.
Yana faɗin
“Tasleem… duk da haka, ke ce kike jaddada min farin ciki, ina mai farin ciki domin kin zo da haske, ba duhu ba.”...


Tasleem tana hawaye ta ce "akwai wata gaskiyar da nake ɓoye muku amma a yau kuma a yanzu zan sanar maka koda wuta zata ƙone ni...

Amaar ya jinjina kai sannan ya ce "wuta bazata taɓa cin sarauniyar Haske ba...."

Tasleem ta ce "idan na lumshe idanuwana ƙwaƙwalwata takan kawo mun abubuwan da ke ɓoye, a cikin idanuwa nake iya ganin komai tamkar video nake gani koda mutum yana cikin ƙasin ƙasin ƙasa ne, na samu wannan baiwar ne sakamakon ɗaurani da akayi a matsayin sarauniyar Haske...."

Ta kalli Amaar sannan ta kuma cewa "aikin da zan fara yi da wannan baiwar tawa shine zan gano sirrin dake zuciyar Shaprees ne, shin yana son Auran ƴar uwata da zuciya ɗaya ne ko kuwa shima akwai shirin da yake shiryawa yanzu nayi ƙoƙarin dakatar da shi....

Tasleem ta lumshe idanuwanta lips ɗin ta ne ya fara motsi a hankali tana faɗin "bayyana mun sirrin zuciyar Shaprees...."

Amaar kuwa zuba wa kyakkyawar fuskar ta yayi da kallo, ji ya yi ta fara faɗin

“Wannan… wannan shine Shaprees… da Sophia a zane a cikin zuciyar sa, Amma me yasa yake zaune da Madam Nablah yana dariya, bayan ta aikata masa mummunan laifi, ta ruguza masa farin ciki ta hanyar kashe masa matarsa Sophia.?”....

Da sauri Tasleem ta buɗe idanuwanta tana zazzaro su, tare da faɗin "kenan ɗaukar fansa ya kawo shi gidan nan? har yana shirin Auran ƴar uwata da niyyar cutar wa ?..."
Ta kalli Amaar wanda shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba...

Da sauri Tasleem ta ɗauko biro da takarda ta fara rubutu kamar haka:

"Shaprees zaiyi amfani da ke ne, yana son janyo ki cikin shirin da zai iya sa ya dawo da matarsa wacce ta daɗe da mutuwa, ko da kuwa hakan shi zai halaka....

Ta gama rubutun tana furta wa a fili, sannan ta furta "Chuchu...."
Sai ga wani tsuntsu ya bayyana ata window ɗakin Amaar yanda yaji ƙiran kenan, tsuntsu fari tass shine ɗan amanan Tasleem, tana matuƙar ji da wannan tsuntsun nata in zata yi aike da ya shafi letter shi take aikawa, da sauri ta nufe shi tana faɗin "wannan saƙon ka kai mun zuwa ga Asmeen yanzu...."

Ta lanƙaya masa a wuya lokaci guda ya fura zuwa aiken..

Amaar kallon ta kawai yake cikin tausayawa, sannan yayi matuƙar farin ciki da wannan muƙamin da aka bata domin su zata amfana, zata kare su daga faɗawa cikin hallaka....

Tasleem ta tsaya a gaban Amaar cikin tausayawa ta ce "akwai wata gaskiyar da nake son sanar maka kuma ya shafe ka sosai, amma kafin nan sai na duba halin da yake ciki da kuma hanya mafi sauƙi yanda zamu gano shi...."

Amaar a ɗan ruɗe ya ce "shi wa?...."

Tasleem ta ce:

"Ya Amaar, don Allah ka saurare ni. Zan faɗa maka wani abu mai girma… wani abu da zai iya canza rayuwarmu gaba ɗaya."

Amaar yana tsaye idonsa akan fuskarta, ya ga wani irin tsoro da damuwa akan fuskarta a hankali yace:

"Na saurare ki, Tasleem. Kar ki ɓoye komai."

Tasleem lumshe idanuwanta ta yi tare da furta:

"Naga wani tsoho a cikin wani duhun ɗaki dake can cikin ƙasa yana ɗaure da igiyoyi na tsafi, yana neman taimakon haske, wannan gaskiyar idan na bayyana shi Madam Nablah zata iya cutar da shi ko ma ta kashe shi gaba ɗaya..."

Amaar cikin rashin fahimta yake faɗin "waye shi ɗin? meyasa yake cikin tarkon Mahaifiyarki?...."

Ta kuma maimaitawa tana hawaye a yayin da idanuwanta suke buɗe furta:

“Na ga wani tsoho... Yana cikin ɗakin ƙasa a kulle, Na ga idonsa suna kallo kamar yana magana da ido. Amma idan na faɗa, Madam Nablah zata iya hallaka shi!”

Cikin damuwa da fusata Amaar ya danna hannayensa cikin sumar gashinsa kamar zai yi hauka yana faɗin "oh my god! what is wrong with you Tasleem ki sanar mun who is him?...."




Tasleem murya na rawa ta furta:

" Wannan tsohon shine Mahaifinku,
Tabbas na san inda mahaifinku yake a ɓoye... yana raye."....

Amaar a ruɗe yake kallon Tasleem ya ce

"Wane mahaifi?"

Tasleem ta ce

"Mahaifin ka da Abeesh
End Ads