x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 45 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 132001 words
  • 134606 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 204

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kar ya dokan jinsi, ta shigo duniyar mu bada izinin mu ba...."


Catrina ta sunkuya tana kallonta da murmushi ta ce:

"Kina so ki ceci Abeesh? to wannan zoben shi zai dakatar da Auren nan ta hanyar salwanta, kuma ga shi a hannu ba, tashi ki karɓa idan har kina da ikon dakatar wa...."

Nasreen ta kasa amsawa saboda tsananin azabar da take sha, Amma cikin zuciyarta, ta fara jin cewa ta kusan mutuwa, Ta yi juyayi sosai.

Haka take jin wani abu tsoka-tsoka yana faɗowa daga marar ta...

Zubar cikin da ta fara yana ƙaruwa, ɗaya daga cikin manyan Aljanun da ke tsaye ya furta da karfi:

"Doka zata fara aiki akan wannan halitta, ku ɗauke ta kuje ku kwantar da ita akan tabarmar ƙaya na wuta, daga nan har ta ƙara sa mutuwa...su kuma ma'aurata su zauna akan shiri domin yanzu za'a ɗaura Auren..."

Abeesh ya fuskanci Catrina yana faɗin:

"Zan so ki har abada, Catrina."

Catrina ta ce:

"Zan ba ka iko, Abeesh. Amma za ka sadaukar da komai."

Abeesh ya ce:

"Na riga na rasa komai."

Abeesh ya ɗauki zoben, ya saka a hannunta. Aljanun suka danna ƙara a sama na farin ciki kafin a ɗaura auren gaba ɗaya…domin sai itama ta saka masa zoben kafin Auren ya ƙullu....

Catrina ɗago da nata zoben tayi tana sakin ƙayataccen murmushi zata saka masa a yatsa shima...

Duk wannan abun ya faru akan idon Nasreen da take kwance kafin a ɗago da ita, domin Catrina ta sanar cewa a barta tana so a ɗaura Auren akan idonta...

Wani irin ƙarfin zuciya ne ya wanzu a jikin Nasreen, a ruɗe ta miƙe ta yo kan su tana jan ƙafa ga yanda jini ya ɓata mata duk ilahirin jikinta, kafin su ankara da ita Nasreen ta fizge zoben hannun Catrina da take ƙoƙarin sanyawa Abeesh....

tana karɓan zoben ta jefa a bakinta ta haɗiye zoben tana kuka...

Catrina kamar wata mahaukaciya haka ta zabga uban ihu ganin Nasreen ta haɗiye mata zoben da ta sha wahala kafin ta samo shi...

Nasreen tana tsaye lokaci guda ta fara hawayen jini, jini na fita ta bakinta tana murmushi ta ce:

"Meye amfanin zuwa na in har bazan iya dakatar da Auren ba? ko yanzu na mutu nasan naci galaba akan ki, na tarwatsa Auren da ƙarfin zuciyata bada ƙarfin iko ba, na karanci littafin ku nasan mahimmancin zoben Auren ku, sau ɗaya kuke mallakar zoben Aure idan ku ka rasa shi shikenam babu Aure har abada.... Catrina! Idan kina son Aure to ki cire zoben hannun Abeesh kiyi amfani da shi wurin Auren wani amma ba Abeesh ba...."

Catrina ce ta taho da gudu tare da ɗaga Nasreen sama ta doka ta a ƙasi, ta haura saman cikinta ta fara tsalle tana faɗin:

"Kin cuce ni Nasreen! har yaushe zaki barni na huta ne? to kamar yanda kika dakatar da Auren sai naga yanda zaki rabani da Abeesh, kuma bazai taɓa komawa jinsin mutane ba...."

Haka Catrina take surutai tana tattaka cikin Nasreen...

Nasreen gaba ɗaya ta fita hayyacinta, jini ne yake fita ta ko ina a jikinta, baki da hanci da hawayen jini da jini ta farji gaba ɗaya ya mamaye ta, jini ne yake kwaranya a ƙasin ƙafafun ta still idonta akan Abeesh wanda ya rasa wani irin hukunci zaiyi mata na lalata masa Aure da tayi....

Catrina tsabar baƙin ciki fashewa tayi da kuka ta sauƙa akan Nasreen, da gudu ta bar wurin tana ihu, Abeesh ne ya zo yanda Nasreen take tare da durƙusawa a gabanta yasa hannu ya damƙo sumar gashin ta ya ɗago ta, yana mata wani irin kallo da idanuwansa masu launin shuɗi...

Nasreen tsabar taurin zuciya haka tasa hannu ta cakumo gaban rigar Abeesh hannu na kakkarwa, ta rungume shi sannan ta kafa goshinta akan nasa tana gogawa, duk ta ɓata masa kaya da jini, sai cakumarsa take lips ɗin ta na ɓari kamar wacce tayi wanka da ruwan ƙanƙara...

Abeesh lumshe idanuwansa ya yi kamar wanda aka hana shi ture ta, Nasreen kwantar da kanta tayi akan ƙirjinsa daga nan numfashin ta ya tsaya, ta tayi doguwar suma....

Abeesh jin bata motsi yasa ya hankaɗata ta yi baya ta faɗi, ya miƙe tsaye tare da barin wurin ya nufi yanda masoyiyarsa take wato Catrina.....

Manyan Aljanu ne suka bada umarnin aje a jefa Nasreen cikin ɗakin duhu na tsaro, yanda ake ajiye Aljanu masu laifi.....


__________________★★★

Ɓangaren Amaar da Abul...

Amaar ya shirya tafiya don neman yanda Tasleem take...

Abul yana tsaye a gaban littafin hasken ruhi, wanda ya buɗe da karfin addu’a, sannan wani madubi mai sihiri ya bayyana a tsakiyar ɗaki.
Wani haske mai kyalli yana fito wa daga cikin madubin, yana buga cikin zuciyar Amaar da ke tsaye a gefe, yana shirin fita da niyyar neman Tasleem...

Abul ya ce:

“Ka je da karfin zuciyarka, ka dawo da ita... Allah ya bada nasara.”

Amaar ya amsa da Amiin Sai kawai ya shiga cikin hasken kamar wanda aka janye shi ciki, yana shiga madubin ya ɓace. Littafin ya rufe da ƙarfi kamar bai taɓa buɗuwa ba.
Abul ya tsaya da kuka a idanunsa yana masa addu'a da fatan nasara...

---

Amaar A Dajin Tsafi

Amaar ya buɗe idanunsa a wani wurin da ya kasa fahimta. Tsohon daji ne mai haɗari ga Itatuwa jajaye kamar jini. Ganyayen da ke kwance a ƙasa suna ƙamshi irin na sihiri, ga wani ƙawataccen ruwa a zagaye da duhu da walkiya yana yawo a gefe.

Amaar da ƙarfi ya furta:

“Tasleem!!!”
“Tasleeeeeem!!!”


Amaar ya ci gaba da ihu da karfin zuciya. Muryarsa na rabuwa gida biyu, kamar tana fita daga sama da ƙasa lokaci guda.

Amma babu amsa...


A cikin ruwan tsafi, Tasleem tana kwance. Idanunta a rufe, tana shan azabar ruhi da rikicin zuciya, kamar mafarki take jin muryar Amaar tana ƙira.

A ruɗe Tasleem ta ɗago tana faɗin:

“Ya Amaar... Ya Amaar, ina nan! Ka zo gare ni, don Allah ka zo!”

Ta fara kuka. Hawaye na gangarowa daga fuskarta yana gauraye da ruwan da ke kewaye da ita.

Amma Amaar…baya jin sautin muryar ta..

Ya ce:

“Inda kike, ki bani alamar ki... na zo nemanki ne...!”

Ganin ba wata alama ne yasa ya durƙusa tare da dafe hannayensa a ƙasa. Zuciyarsa na bugawa da rashin ƙarfi.
A gefe, wani haske a cikin ruwan ya fara kyalli, kamar yana amsa zuciyar Amaar....

Miƙewa ya yi yana cigaba da dube-dube domin Abul ya sanar masa cewa a wannan yanki take...

Amaar yana ta yawo cikin dajin sihiri, zuciyarsa na masa zafi da fargaba. cikin sa'a sai idonsa ya sauƙa akan wani sashen ruwa da ke haskakawa da launin zinariya da kumfa masu walƙiya.
Haske mai kama da fuskar Tasleem ya bayyana a cikin ruwan.

Amaar cikin farin ciki ya furta:

“Tasleem! Na ganki… Na sameki! Ina zuwa!”

Cikin gudu da ƙauna, Amaar ya nufo wurin ruwan. Amma kafin ya kai…
ZAP!

Wata irin ƙara mai sanyi ta buga masa kirji.
Mashi mai baƙin sihiri ne ya caka masa cikin ƙirjin zuciyarsa.

“ARRRGHHHHHH!!!”

Wani irin ihu ya yi tare da faɗu wa ƙasi yana riƙe da kirji...

Daga cikin duhun dajin, wata annura mai duhu ta bayyana.
Cikin iska ta bayyana Madam Nablah ce sanye da baƙaken kaya, tana tafiya a hankali.
Idanunta na ci da wuta ja kamar goran wuta.

Madam Nablah cikin ƙarfin sihiri ta ce:

“Me kake tunani? Za ka iya kubutar da ƴata daga hannuna? Kai yaro mai ruhi, wani irin shirme kake haka ..?”

Amaar yana yunkurin miƙewa, amma jikinsa na girgiza cikin ruɗani ya ce:

“Ba zan bari ki cutar da Tasleem ba… ko da kuwa zan mutu.”

Madam Nablah ta yi tsaki, ta ɗaga hannunta, hasken sihiri ya shiga zagaye shi...


Tasleem, wacce ke kwance cikin ruwan tsafi, ta ji ihun Amaar yana karaɗe wurin.
Sai ta taso da karfi cikin tashin hankali, idonta cike da hawaye take faɗin:

“Ya Amaar! Ya Amaar!! Ki bar shi! Don Allah Mommy! Kar ki cutar da shi!”

Amma ruwan yana hana muryarta fita...duk ɗaga muryar da take a iya yanda take muryar take tsayawa..

Ta fara cukuikuya ruwan tana ƙoƙarin fita, amma ruwan yana tura ta baya kamar tsohon azzalumi...



Amaar yana ƙoƙarin tashi daga ƙasa, yana jan numfashi, amma mashin tsafi da ke kirjinsa yana sosa rayuwarsa
Madam Nablah ta taka kusa da shi, ta dafa kansa da hannunta mai wuta, sai ta furta:

“Zan fitar da hasken ruhi daga gareka, ka zo da ƙafa zuwa ga halaka.”

Tana faɗar haka, wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga jikin Amaar.

Madam Nablah ta tsaya a gaban Amaar hannayenta a buɗe, tana busar ƙarshe na sihiri daga cikin bakinta.

Wani haske ne ya bar kirjin Amaar, ya shige cikin tafin hannunta.

Nan take...
Amaar ya faɗi ƙasa – babu motsi, jijiyoyi sun daina gudu, idanuwansa sun rufe, jikin sa ya rame kamar an tsotsa jini...

Madam Nablah cikin annashuwa ta ce:

“Hasken ruhi ya fita daga gare ka, yaron banza....ke kuma sai ki yi kuka da mutuwarsa, kar ki daina har abada.”

Ta saki wata ƙara mai cin kunne kafin ta ɓace cikin duhun daji kamar ba a taɓa ganinta ba...

Amaar ya bar duniya gangan jikinsa yanzu taɓo ne bushasshe, mashin tsafi yana kwance a zuciyarsa, rayuwa ta gushe daga jikinsa.
---

A Cikin Ruwan Tsafi:

Tasleem tana can cikin ruwan tsafi, jikinta yana ɓari amma sannu a hankali ta fara jin wani yankakken sarkar tsafi da ke rataye a wuyan ta yana motsi..

Idanunta sun ci karo da wani kaɗan daga cikin hasken Amaar wanda bai shiga hannun Madam Nablah ba yana shawagi cikin iska sama da ruwan.

Tasleem cikin kuka ta furta:

“Ya Amaar... ka tafi? Ka bar ni?”

Nan take hankalinta ya rikiɗe.
Sai ta tsayar da kuka, ta fara karanta addu’o’i da wani salon karatun ruhi da Abul ya koya mata kwanakin baya.

Tana faɗin:

“Haske ya fi duhu. Ruhin da ya tsira zai iya dawowa. Idan zuciyata ta ƙira shi... zai ji ni!”

Sai ruwan tsafi ya fara birkicewa, yana ƙara yin harzuƙa
Wani ƙaramin zobe da ke ƙasan ruwan ya bayyana... zoben da Amaar ya taɓa bata a ranar da suka kasance don gudanar da ƙaunar su...

Ta kamo zoben da hannunta ya na rawa, ta ɗaga sama, tana ɗaga hannunta cikin addu’a da kuka da ƙarfi:

Tasleem cikin karfin murya da hawaye take faɗin:

“Ya Ubangiji, kada ka bar shi haka! Idan akwai rabon rayuwarmu, ka dawo da shi… har ya ji sunana.”

A daidai lokacin, haske mai launin azurfa ya fito daga cikin zoben, ya nufi cikin sararin sama.
---

Jikin Amaar na kwance a ƙasa — kamar gawa.

Sai wani haske mai launin azurfa ya sauƙo da sauri daga sama…
Ya lulluɓe gaban kirjin Amaar, inda mashin tsafi ke nan...

An fara jin dankarewar numfashi, wani ƙaramin amfani ya motsa a gefen leɓensa...

Tasleem ta tsallake ruwan tsafi da ikon Ubangiji da ƙarfin hasken da ke cikinta. Ta tarwatsa ruwan da hannayenta, jikinta yana rawa, zuciyarta cike da firgici da fargaba.

Bayan ta fito, ta gan shi a hankali ta furta... "Amaar...."

Jikinsa na kwance kamar gawa, babu numfashi, fuskarsa cike da dumin mutuwa.

Tasleem cikin murya mai sosa rai ta ce:

“Ya Amaar... don Allah ka tashi... ka tashi ka kalle ni!”

Ta rungume shi tana kuka sosai, ta ɗora hannunta akan mashin da ke tsakiyar ƙirjinsa, tana kuka
Tana ƙoƙarin tura hasken ta cikin zuciyarsa, amma hasken nata na koma baya, kamar ana ƙin karɓa.

Cikin kuka ta ce:

“Ka tashi, don Allah... kai ne fa, kai ne ka ce zaka ƙare min rayuwa da tsaro… ka ce zaka tsaya min!”

Amma jikin Amaar bai motsa ba. Komai yayi shiru.

Nan da nan wani haske ya bayyana a sararin dajin, yana sauƙowa da nutsuwa da annuri.
Wani ruhin tsarki ya bayyana daga cikin hasken, yana ɗauke da wata jita mai launin azurfa, kafaɗunsa na walkiya, idonsa cike da kwanciyar hankali da lafazi mai daɗi ya ce:

“Kuka ba zai yi tasiri a nan ba, 'yar haske. Amma wannan—”

Ya miƙa jitar sauti gare ta ya cigaba da cewa

“—ki raira kiɗan ruhinsa. Wannan sauti zai ƙira shi daga duhun da ya shiga. Amma dole ne ki daure. Zai ɗauki lokaci, kuma bazai yi sauƙi ba a cikin ƙankanin lokaci....”

Tasleem ta karɓi jitar, tana kallon ta da hawayen fatan alheri.
Sai ruhin ya ɓace, hasken ya lafa. Dajin ya koma shiru.

Ta zauna kusa da Amaar, ta haɗa hannayenta a kan jitar, ta lumshe ido tana nufin zuciyarsa da soyayya.
Sai ta fara kaɗa jitar da yatsun ta cikin sautin da ba’a taɓa ji ba — kukan tsantsar soyayya da ɓacin zuciyar rashin masoyi.

Sautin ya shiga iska, yana shawagi, yana girgiza ciyayi, yana bugawa a cikin duhun dajin...

Duk lokacin da ta buga jitar, cikin Amaar na ɗan motsi, amma bai tashi ba.

Tasleem cikin murya mai rauni ta ce:

“Ina raye ne saboda kai, Ya Amaar… bana so ka tafi… ka dawo gare ni.....”

Ta ci gaba da bugawa... duhu ne ya fara mamaye wurin...
kuma Tasleem bata fasa ba.



*GA MASU SON CIGABAN BOOK A TUNTUƁENI A WANNAN NUMBER 09065443871...*

*MASU SON TURO KUƊIN LITTAFIN SU GA ACCOUNT NUMBER 9065443871 ASMA'U MUHAMMAD AUWAL. OPAY BANK....*

*GA MASU SON TURA KATIN WAYA GA NUMBER 09065443871 MTN OR 07087352025 ZAIN....*

FATAN NASARA 🙏🙏🙏🙏

Kyautar page ya ƙare sai a daure a biya kudin cigaba ... Nagode sosai 🙏




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads