x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 187

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
“Tasleem, ki guje su. Kar ki bari su yi nasara. Karki manta da haske ko da duhu ya rufe komai.”



Amaar ne.

Yana kan gadonsa a bedroom amma ruhin sa yana nan kusa da Tasleem kamar yana ƙoƙarin kiran zuciyarta, yana ja da tsafin da ke kulle a rayuwarta.

Kallon da Tasleem ta yi da kyau a cikin wannan haske, sai ta fara hango fuskar Amaar cikin haske, da idanunsa na tausayi da yawan magana.

“Kai... Kai ne…?!”



Sai wani irin shocking ya sake bugarta daga ƙirji zuwa ƙafafu. Tayi ihu da ƙarfi, ta faɗi rubda-ciki a ƙasa.

Tunaninta ya tafi da gani. Hankalinta ya tashi. Idanuwanta sun ɗauke. Amma zuciyarta ta ƙwace daga ƙulle. Tana cikin suma, tana hawaye, tana cewa

“Na harbi wanda nake so... wanda zuciyata ke ƙira, wanda hasken ruhina ne…”



Kuma a cikin wannan halin — sannu a hankali ta fara gane cewa wancan yaron da ta taɓa ƙauna tin yarinta — Amaar ɗinta ne!



ƁANGAREN AMAAR...

Amaar ya buɗe idanuwansa cikin nutsuwa, murmushin ciwo a saman fuskarsa da hawaye masu ɗumi a cikin kwarmin idanuwansa. Abeesh na gefensa ya tsare shi da ido, shi da Nasreen da Asmeen gaba ɗaya zuciyarsu ta yi rauni da girman gaskiyar da suka ji. Sun gane wannan mutumin shine Amaar ɗin su, yaron da aka ce ya ɓace shekaru ashirin da suka shuɗe.

Amaar ya dafe ƙirjinsa da hannunsa ɗaya, ya sauke ajiyar zuciya, sannan da raunanniyar muryar ya ce:

“Na gode da kulawar da kuka bani. Ban taɓa tunanin zan sake ganinku a rayuwa ba... Na rasa komai a duniya – amma Allah ya dawo mun da rayuwata ta gaskiya.”


lumshe ido yayi tare da zubda hawaye ya kuma cewa

“Madam Nablah… ita ce ta jefa ni cikin ruwan duhu na tsafi. Tana son ta hallaka ni gaba ɗaya, amma Allah bai yarda ba. Na rayu…”



Asmeen ta ce

“Wa ya cece ka Ya Amaar? Wa ya zamo garkuwa a cikin wannan duhun?”



Amaar ya ɗan jiyo kansa gefe, kamar yana jin zafin tuna wani abu mai nauyi sosai a ƙwaƙwalwarsa. Idanunsa suka ƙanƙance, sai ya ce

“Zan faɗa muku wata rana… Ba yanzu ba. Amma ku sani har yanzu ba a gama wannan faɗar ba.”



Daga nan sai ya kama hannun Abeesh da ƙarfi yana faɗin

“Kada ku faɗa wa Tasleem. Kada ku ce mata ni ne Amaar. Kada ku bari Madam Nablah ta gane ni. Har sai lokacin da na shirya… akwai wani abu da nake buƙatar na tabbatar da shi.”



Nasreen cike da damuwa ta ce

“Har zuwa yaushe zamu daina ɓoye sirrin nan? Idan aka gano cewa kai ne Amaar fa? Ko kuma Tasleem ta tuna da kai da kanta?”



Amaar ya kalli Nasreen da ido masu tsananin natsuwa da kwanciyar hankali ya ce

“Zuciya tana da hanyar da ba a iya shan kwaya a ɓoye ta ba. Zuciyar Tasleem zata gane ni, amma lokacin da ya dace.”



Daga nan suka yi masa sallama. Nasreen da Asmeen suka kalli Abeesh da idon tausayi, yana so ya zauna da Yayan shi tsawon shekaru basu ga juna ba,
daƙer suka samu ya yadda zasu tafi tare yana kuka, suna kuka..

Suna cikin mota suna tafiya cikin yamma, Asmeen ta ce:

>“Shiyasa Mommy bata taɓa barin mu shiga bedroom ɗinta ba… Ashe akwai wani shirin da take a ɓoye”



Nasreen ta jinjina kai cikin alhini ta ce

“Shiyasa Mommy da Tasleem ba sa shiri,
Tasleem ta taɓa faɗa mun cewa tana mafarki Mommy tana shan jini, amma ban taɓa yarda da ita ba.”



Ta share hawayenta sannan ta ƙara da cewa:

“Tasleem na da baiwa… Zuciyarta na gane gaskiya kafin baki ya furta.”......



ƁANGAREN AMAAR...

Shi kuma Amaar ya zauna shi kaɗai, jikin sa a manne da bandeji babu kaya a jikinsa, idanunsa sun zurfafa cikin tunani. Kallon gilashin taga yake yi, yana hango rana tana faɗuwa ga duhu yana shigowa.

“Tasleem…” ya furta da ƙaramin murya.



Sai ya rufe idanunsa, zuciyarsa ta ɗauko masa shekarun yarinta, lokacin da Tasleem ke masa dariya, suna gudu a ciyawa, tana ce masa

“Kai ne Hasken Ruhi na…”



Sai ga hawayensa sun gangaro Zuciyarsa ta gama raunana Kuma ba wani bandeji da zai warkar da raunin da ke cikin zuciyar sa.....


ƁANGAREN MADAM NABLAH…

A cikin duhun dakin tsafi, hasken wuta mai shuɗi yana walkiya daga wani ƙaramin madubi mai jini a cikin gilashi, wanda aka ɗaure da ruƙon zinariya mai zane-zanen gargajiya. Wurin tsafin ya cika da hayaƙin turare da gurnani na shiru – kamar ana karanta wata duniyar da ba a iya gani da idon duniya.

Madam Nablah na zaune akan tabarma ta zinariya, tana sanye da tufafin bakake masu yalwa, hannayenta a buɗe, dukkan tafin hannunta cike da wuta mai yawo kamar ruwan zafi.

Cikin murya mai sanyi na mugunta, take furta yaren tsafi

“Zaaaa'qil... H'azmaar... Ayyukan da Maruuk!”
Bana hangen zuciyar maƙiyina, Bana gani abinda ke ɓoye.”



Madubin tsafin ne ya fara girgiza. Sai hayaƙi ya shiga zagaye a cikinsa – hayaƙi mai launin jini. A hankali siffar wani fuska ta bayyana… fuskar Amaar.

Madam Nablah ta ɗan motsa daga inda take zaune, ido a zarr kamar ba ta yarda da abinda take gani ba.

“Na tura ka cikin ruwan hallaka! Me yasa kake raye?!”
Waye ya cece ka?! Waye yake baka kariya daga tsafina?!”



Ta miƙe da sauri, ta taka gaba ta danna hannunta a tsakiyar madubin. Sai wani irin zafin wuta ya fesa mata – madubin ya ƙi bada cikakken bayani Ya ɓoye wani bangare.

“Wannan tsafi ba cikakke bane… akwai wani karfi da ya hana ni ganewa...”
A cewar Madam Nablah.


Nan take siffar wasu fuska biyu suka bayyana a gefe:
Nasreen da Asmeen.

A ruɗe ta ce
“Ƴaƴana!” Ta furta da ƙarfi. “Kuna tare da shi? Kuna kusa da mutumin da zai rushe mun mulki?!”



Idanunta suka cika da wuta, kamar yadda ƙarfin jikin aljanu ke ƙara ratsa kanta. Tana jin wani mugun zafi yana tashi daga ƙasan cikinta. tana tangaɗi da haka ta zauna a wurin amma bata faɗi ba, sai dai ta farka da sabuwar murya, murya mai haɗe da na wani tsatso daga duniyar tsafi
tana faɗin

“Ba za ku yi nasara ba, Wannan ƙyauren nawa ne. Ruhi ba zai iya haskakawa a cikin duhu ba…”



Madubin ne ya bushe da hayaƙi ya ɓace. Sai wata ƙaramar ƙwarya ta karye a gefe, Hannu biyu suka ɓullo daga ƙasa hannuwan aljanu suna miƙa mata wani baƙin zobe da wasu sabbin kayan tsafi.

Madam Nablah ta ɗauki zoben ta cusa ɗaya a yatsanta, ta ce

“Tasleem zata dawo gare ni… koda da jinin Amaar zan ɗaure zuciyarta!”



Ta sa dariyar mungunta mai amo, ta ɗaga hannunta sama – wutar tsafi ta sake fitowa, tana zagaye dakin da wani sabo, mafi ƙazantar shiri...


ƁANGAREN TASLEEM…

Tana kwance a cikin bedroom ɗinta, tana numfashi da ƙyar. Gumi na keto mata, jikinta yana rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata fito daga kirjinta. Har yanzu bata manta da abin da ya faru ba, robot ɗin da suka rikide, murya mai ban tsoro, rawar duhu, da faɗuwarta daga saman beni amma abin mamaki ta farka lafiya.

Sai dai akwai wani abu dabam da take ji a jikinta yanzu… wani nauyi a zuciya, kamar an cire mata wani ɓangare na rayuwa amma ta kasa sanin me ke faruwa.

Ta zauna akan gado, ta riƙe kanta da hannaye biyu, tana kuka a hankali.

“Wayyo Allahna… me nayi? Me yasa nake jin kamar akwai wani sirri da ya ɓuya cikin rayuwata? Kuma waye wannan mutumin da na harba? Waye shi a rayuwata?”



Ta tuna fuskarshi, fuskar Amaar, fuskar da ke da wani sanyi da zafi a lokaci guda. Sai zuciyarta ta tsinke da ciwo. Idanunta suka cika da hawaye.

“Na kashe mutum? Na kashe shi? Amma me yasa tun daga ranar dana gan shi nake jin wani abu dabam? Me yasa idan ya kalli idona nake jin tamkar ya san sirrina fiye da yadda ni kaina na sani?”



Tana cikin wannan tunanin ne sai taga kyakkyawan locket (abun wuya) a gefen gadonta. Bata san daga ina ya fito ba. Tana ɗagowa, ta buɗe… hoton wata yarinya ce a ciki da yaro gud, Ita ce – Tasleem ce da wani yaro wanda ya haɗe da ita.

Sai wani irin shocking ya daki zuciyarta. Sai zuciyarta ta fara bugawa da karfi ta ce

“Wannan hoton… me yake nufi?! Wannan yaron…”
Ina tunanin na san fuskar nan... amma ta ina? Me yasa yake min kama da…”



Nan take ta fara jin jiri. Sai ta fadi a saman gadon, tana huci, tana fitar da gumi. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kamar ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin faɗa mata wani abu, amma akwai wani abu da ke hana shi fitowa fili.

A cikin baccin da ya ɗauke ta, ta fara mafarki. A mafarkin, ta tsinci kanta tana gudu a cikin jeji – tana gudu daga wani abu, amma daga can gaba sai taga Amaar tsaye, yana mata murmushi. A bayansa kuma akwai wata mace mai bakaken kaya, idonta jajaye kamar wuta…

“Karki kuskura ki tuna!”
“Kar ki gane waye shi… idan kika gane, rayuwarki zata ɓace!” – Muryar Madam Nablah ce.



Ta kurma ƙara a mafarkin – sannan ta farka da ihu!

Ta miƙe da sauri daga gado, huci na fita daga bakinta, hawaye na gangarowa. Ta dafe ƙirji.

“Zan tafi! Zan tafi inda na bar shi. Ko da kuwa ya mutu ne – sai na tabbatar da hakan da kaina.”



Da sauri ta saka hijabi, ta fice daga gidan zuciyarta cike da rudani da alhini, amma wani ɓangare na zuciyarta na kokarin farka da gaskiyar da aka daɗe ana ɓoye mata…



NEXT NEXT NEXT

SAI DAI KUYI HAƘURI YAU BANYI EDITING BA, KODA ZAKU SAMU TYPING ERROR KU SHARAR KAWAI😃😃....


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*


https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 27 to 28



Tasleem na tafe da sauri kamar wadda gobara ke binta. Fuskarta cike da ruɗani da tarin tambayoyi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kusan ta yi kamar mai hauka, saboda abinda take ji, abinda take tunani—da kuma abinda take fargaba ta aikata.

A daidai shiga falon gidan nasu kenan, sai taga su Nasreen da Asmeen na shigowa cikin gaggawa daga ƙofar baya.

Da ta hango su, ta nufe su da sauri, jikinta na rawa.

“Ina yake? Ina wannan mutumin? Daman yana raye? Na ji kamar yana kiran sunana… don Allah ku gaya mun gaskiya! Ku gaya mun shi ɗin waye!”



Asmeen ta tsaya cak, tana kallon Tasleem kamar zata yi kuka, amma sai ta haɗiye kukan ta ce

“Ke Tasleem, me kika aikata?! Shin kina da hankali kuwa?!”



“Wato har ke Asmeen?” Tasleem ta furta tana kallon su da kuka,

“Ni fa ban gane ba, kawai na ji wani abu dabam tun da na gan shi! Amma ban san me yasa na harbe shi ba… wallahi bazan iya rayuwa da wannan laifin ba!”



Nasreen ta matso kusa da ita, ta kama hannunta cikin tausayawa domin sun gano yanzu duk abinda Tasleem ta aikata da taimakon tsafin da ya gusar mata da zuciya ne cikin basar wa ta ce

“Laifi ki ka aikata! Kema kin sani. Kuma ki sani wannan mutumin ba kamar kowa bane! Amma ki daina tambaya… idan lokaci yayi, za ki gane shi.”



Tasleem ta girgiza kai da ƙarfi, zuciyarta kamar zata tarwatse.

“Toh gaya mun! Ku gaya mun kawai ko ya mutu ne?!”



Asmeen ta juyo da sauri tare da faɗin

“Ba zai mutu ba insha Allah, amma ki shirya fuskantar abinda kika aikata..."



Tasleem ta sunkuyar da kai tana hawaye, tana jin nauyin abinda ta aikata ba don ta sani ba, sai don wani abu na ciki da ke hura mata wuta.

Nasreen ce ta kalli Asmeen tare da girgiza mata kai alamar tayi shiru da wannan batun.

**

A nan ne ƙarar buɗewar ƙofa ta katse su. Fuskar Madam Nablah ce ta bayyana, tana shigowa falon kamar guguwa Idanuwanta jajaye, fuskarta ba Annuri, kamar wadda ta dawo daga duniyar aljanu.

Nasreen da Asmeen suka tsaya cak, jikinsu ya ɗan yi sanyi. Tasleem ta juyo da sauri, da mamaki a fuskarta ta ce

“Mommy? Ina kika je jiya? Kuma me yasa fuskarki haka?”



Madam Nablah ta wuce su kamar ba ta ji ba, idonta na ɗauke da wata ƙwayar duhu, kamar ba ta cikin hayyacinta, ta tsaya dab da fitilar falon, sai ta juyo a hankali, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya.

“Me kuke aiwatar wa a cikin gidan na? Me kuke ɓoye mun?”



Nasreen ta tsaya da ƙarfi, tana fidda numfashi ta ce

“Ba zaki gane ba Mommy… sai ranar da Allah ya nuna miki gaskiya.”



Madam Nablah ta ƙura mata ido, ba tare da tace komai ba. Idanunta sun nuna alamar karin haɗari da bacin rai.

**

Abeesh da yake jin hayaniya a ƙasa tun daga ɗaki, ya leƙo, amma ganin ya hango Madam Nablah ne yasa ya juya da sauri ya koma, Bai taɓa jin zuciyarsa ta ƙone kamar yau ba. duk kyautatawar da aka yi mata amma hakan bai hana ta hallaka mahaifinsa da ɗan uwansa ba.


Tasleem ce ta katse su da kuka tana faɗin "amm inason ganin sa, ba'a son raina na harbe shi ba, Allah yasa bai mutu ba...."

Madam Nablah wacce take shirin barin wurin jin kalaman Tasleem ne yasa ta dakata, a slow ta juyo tana tambayar su "wa kika harba?..."

Da sauri Nasreen da Asmeen suka ce "babu komai"

Madam Nablah hannu tasa ta juyar da Tasleem tana son ganin abinda ya faru ta cikin ƙwayar idanuwan ta, cikin fushi da tashin hankali Tasleem ta hankaɗe mahaifiyar su tana faɗin

"kar ki taɓa ni domin ke Annoba ce, ki fita daga cikin rayuwar ta na tsane ki, ina ji a jikina cewa kin raba ni da abubuwa mafi muhimmanci a cikin zuciyata, ke kika kashe mana mahaifin mu sannan kika ɓoye Abul Abeesh a cikin ɗakin duhu, bai kamata na cigaba da ɓoye waɗannan sirrika a cikin zuciyata ba, ki sani sai na kawo ƙarshen ki...."

Nasreen da Asmeen sumar tsaye suka yi jin mutuwar mahaifinsu da kuma Abul Abeesh yana raye,

Madam Nablah zaro idanu tayi waje tana mamakin jin waɗannan kalamai daga bakin Tasleem....

Tasleem ta cigaba da cewa "sannan akwai abinda kika raba ni dashi wanda yana da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta, tabbas na gan shi a cikin mafarki na kuma na ganki kema da wasu rikitattun idanuwa, meye sunan sa? meye sunan sa? sunan sa A.. A.. Am, yana zuwa mun a matsayi spirit, shi ɗin haske ne wanda na tabbata da wannan hasken zai tarwatsa baƙin tsafin ki..."

Madam Nablah kanta ba ƙaramin ɗaukan zafi ya yi ba, cikin fushi ta lumshe idanuwanta lokaci guda ta buɗe su da wani irin jajayen idanuwa, idanuwanta sai farfatsin wuta yake, a tsawa ce ta yi wa su Nasreen magana da cewa "ku fita ku bani wuri yanzun nan"... cikin wata ƙatuwar murya, yanzu ta fito a asalin ta na matsafiya...

Nasreen da Asmeen haka jikin su yake ɓari cikin tsoro da fargaba suka yi waje da gudun gaske...

Itama kuma Tasleem riƙo hannunta tayi tana jan ta har ta kaita can room ɗin su ta wurga ta saman gado...

Madam Nablah tsabar tashin hankalin da ta shiga ta ma rasa abinda zata yi haka tabar ɗakin a fusace tare da rufe ƙofar...



Amaar yana kwance akan gadon sa ba abinda yake tunawa illa Tasleem, ya runtse idanu, yana furta a zuciyarsa

“Tasleem… ki yafe mun. Lokaci yana zuwa. Lokaci da komai zai bayyana. Amma yanzu... Sirrinmu yana da daraja.”


Madam Nablah na zaune a ɗakin tsafinta wanda ke cikin ɗayan ɓangaren gidan da ba kowa ke iya shiga ba. ɗakin duhu ƙirin amma dakin na ɗauke da hasken fitilar tsafi—wato wuta mai shuɗar haske da ke fitowa daga ƙasan wani tafki mai duhun ruwa.

Ta durƙusa gaban madubin tsafi wanda yake rataye cikin iska, ba tare da ya taɓa wani bango ba. Duhu ne ya mamaye zagayen madubin, sai hayaƙin da ke fitowa daga hanci da bakinsa yana motsi kamar numfashi.

Madam Nablah ta daura hannunta biyu a saman madubin, ta lumshe ido, sannan ta fara karanto wani irin yare da ba a saba jin shi ba tana furta

“Naqaatu-t-Tilum... Sarwaqeen Al Jabaroot... Izran Tumma... Qadhaab!”



Sai wani ƙarin hayaki mai ƙanshi irin na jikin bil’adama ya turnuƙe madubin. A
End Ads