ba sai yanda take da ikon kashe mata wutar da ta rura, tana tunanin a yanda ta samu wannan ƙarfin, kawar da tunanin ta tayi tare da faɗin "Tasleem ni ce Annoba?..."
Abeesh ne ya tsaya a gabanta cikin fusata ya ce "abinda yafi Annoba ma kin fi, ke shugaban shaiɗanu ne wanda baza ki mutu cikin haske ba, ke da shiga Aljanna sai dai ki ga masu shiga amma ke yanda kike sarauniyar wuta haka zaki tabbata a cikin wutar jahannama da yafi wutar da kike da shi zafi da raɗaɗi..........."
Kafin ya ƙarasa maganar ya ji sauƙar mari akan fuskar sa, ɗagowar da zai yi yaji an ƙara zabga masa marin ta ɗayan ɓangaren, cike da mamaki yake bin Nasreen da kallo wacce jin maganganun da yake jifan mahaifiyarta da su ne yasa ta taso, tana kuka tana faɗin "Ya Abeesh na gode sosai, sakayyar da zaka mun kenam? Mahaifiyata wacce ta yi silar kawo ni duniya har muka san juna yau ita ce kake yiwa fatan tabbata a jahannama? nake ga ko wani irin hali take ciki bai kamata waɗannan munanan kalaman sun fito daga bakin ka ba, fatan shiriya da addu'a ya kamata mu dage mata ko Allah zai dawo mana da ita dai dai, to bari ka ji har yau har gobe uwa uwata ce kuma nafi sonta fiye da wani na, kuma Alhamdulillah ita ta raine ka, a hannunta ka tashi har ka mallaki hankalin kan ka....."
Abeesh jinjina kai ya yi tare da faɗin "good! wato bata cancanci haka ba koh? duk da irin tozarcin da tayi mana ta kawar mana da farin ciki, ta ruguza mana farin cikin ahali, ki kalla wannan shine mahaifin mu ki dube shi dakyau tsawon shekaru Ashirin tana riƙe da shi a wurin da babu haske, a ɗaure da wasu irin caka hakan ma fuskar sa a rufe da baƙin hula, ba abinci mai kyau ba ruwa mai kyau a haka ya cigaba da rayuwa har zuwa wannan lokacin amma ki saura da sanar mun wai a hannunta na taso na girma, Allah ya wadaran irin wannan rainon domin ni ban gode ba, gwara ta barni akan titi ina gararan ba har na girma, wannan Ɗan uwana ne jinin jikina ki dubi irin zaluncin da tayi masa tin bai mallaki hankalin kan sa ba, tayi ƙoƙarin raba shi da duniya, Nasreen kin ban mamaki da har zaki shigar wa mahaifiyar ki faɗa...."
Nasreen tana kuka ta ce "ba wai ina goyon bayan ta bane, fatan azabar da kake mata ne sun yi yawa..."
Ya yi saurin katse ta da cewa "Azaba ita ta zaɓarwa kanta, dole nayi mata fatan tabbata a cikin ta...."
Nasreen ta ce "Yaa Abeesh ba ita bace...."
A fusace ya ce "ba ita bace to ke ce? ko ma wacece tasan abinda take ba daidai bane, please Nasreen leave me alone kin fiye son kan ki da yawa...."
Tana kuka zata yi magana ya darara mata tsawa tare da faɗin "nace ki ƙyale ni kowa ya yi rayuwar sa..."
Nasreen tana kuka tare da girgiza kai ta bar falon da gudu kai tsaye upstairs ta haura can ɗakin su....
Amaar kuwa har yanzu bai gama dawowa dai dai ba, ga hajijiyan da yake shirin ɗaukar sa...
Sauran kaɗan ya faɗi Abeesh ya yi saurin riƙo shi tare da faɗin "please bro kar ka rufe eyes ɗin ka...."
Tasleem itama wacce idanuwanta suka disashe tsabar kuka kallon jikin Amaar ta yi wanda wuta ta gama cin rigar jikinsa sai iya fatar sa ake gani duk ya yi jawur, zaro ido tayi waje ganin yanda wutar tsafi ta ratsa jikinsa haka wutar yake yawo a cikin jikinsa, a hankali ta ɗago da hannunta ta ɗora hannun akan ƙirjinsa, kaf sai da ta gama janye wutar jikin sa kafin ta sauƙar da hannunta tana yarfewa, domin wutar ba ƙaramin ƙarfi gareta ba, sai a lokacin Amaar ya dawo hayyacinsa ganin yanzu an cire masa raɗaɗin da yake ji a jikinsa, jikinsa ya dawo normal kamar wuta bata taɓa ba, Abeesh ne ya zaunar da shi duk suka zauna......
Madam Nablah tana tsaye ta kafa idanunta akan wanda take hari wato Abul, Abul shima ita yake kallo ganin irin kallon da take masa ne yasan akwai abinda take son aikatawa yanzu, kafin ya gama iddasa tunaninsa har ta mulmulo wuta daga hannunta zata jefa wa Abul a fusace Tasleem ta darara mata tsawa tare da furta "Mommy...." ta kunna haske ta hanyar amfani da hannunta ta saita Madam Nablah da wannan hasken, a gigice Madam Nablah ta rufe fuskarta da hannu tana faɗin "Tasleem meye haka, kinada hankali kuwa? zaki kashe mun idanu, wayyo Allah bana son haske, bana son haske zaki tarwatsa ni....."
Madam Nablah sai da ta durƙusa ƙasi gaba ɗaya haske ya zagaye ta, haka take fitar da farfatsin wuta....
Tasleem kuwa gaba ɗaya ta canza zuwa asalin sarauniya, idanuwanta sun koma fari soll ba ɗigon baƙi sannan sumar gashin ta shima ya koma fari soll ga yanda haske kamar walƙiya yana fita daga cikin tafin hannunta zuwa kan Madam Nablah, haske da wuta ne suka haɗu, cikin ƙarfin wuta ZULQARNAIN ne ya buɗe idanunsa ganin haske yana shirin cin galaba akan wuta, cikin ƙarfin ikonsa yake magana da zuciyar Madam Nablah yana faɗin "idan kika bari haske ta ci nasara akan ki zaki rasa komai, ki miƙe da ƙarfin ikon ki, Nablah ki buɗe idanunki haske ne a gaban ki...."
Madam Nablah duk taji wannan maganar da ZULQARNAIN ya yi mata, a fusace ta miƙe tsaye cikin ihu da fusata lokaci guda ta tarwatsa wannan hasken dake cutar da ita ta hanyar kunna wata azababbiyar wuta marar jin rarrashi da taimakon ZULQARNAIN.....
Haske da wuta ne suka zama ƙanƙara tare da tarwatse wa suka zama kamar duwatsu, Tasleem ce tayi baya zata faɗi Amaar ya yi saurin riƙo ta, ita kuwa Madam Nablah yanda ta tsaya cikin jarumta ko motsi bata yi ba, ga yanda sumar gashin ta ya tarwatse duk suka rufe mata fuska...
Duwatsun haske ne suke ta sheƙi da walwali a falon ga kuma na wuta shima yana fitar da nashi ƙyallin, cikin ƙatuwar murya Madam Nablah ta ce "kina so ne kici nasara a kaina? to kin yi ƙarya Devil Mom bata faɗuwa ƙasi...."
Tasleem ta ce "Mom duk ke kika jawo, ke kika fusata ni...."
Madam Nablah ta ce "taya kika samu wannan ƙarfin ikon? wannan ikon daga wurin wa kika samo? ta sanadiyar wa kika samu matsayin sarauta? saurauniyar haske kina shirin yaƙa ta,
Shikenam! Shikenam!! Shikenam!!! ku cigaba da zama a cikin fadata akwai ranar ƙin dillanci...."
Tana kaiwa nan ta nufi upstairs da gudu, ɗakinta ta shige tare da rufe wa, tana shiga ta fara sakin numfashi daƙyar tana rungumar jikinta, wani irin raɗaɗi take ji a cikin jikinta, zazzaɓi ne yake shirin rufan ta, bata san lokacin da ta fara hawaye ba, kwanciya tayi akan gadonta tayi rubda ciki tare da kifar da kanta, tana takaicin yanda Tasleem ta zama Sarauniyar haske....
Tana cikin wannan halin ne taga ɗakin ta ya turnuƙe da duhu, tsantsar duhu ne babu haske ko ziri ɗaya, da sauri ta tashi zaune tana kallace-kallace ko hannunta bata iya gani, rufe idanuwanta tayi sosai sannan ta buɗe su sai suka juye zuwa garwashi, farfatsin wuta ne yake fito wa daga cikin eyes ɗin ta, anan ne take iya ganin komai, wutar idonta ya kawar da duhun, abinda ta gani shine baƙar kuliya, wani irin kuka kuliyar tayi sai hasken ɗakin ya dawo normal amma idanun Madam Nablah basu dawo yanda suke ba, kallon kuliyar take da idon sanayya, kuliyar ce ta tako har yanda Madam Nablah take a zaune a bakin gadonta, a lokacin ne kuliyar ta dawo mutum, wata zureriyar budurwa ce ta bayyana mai tarwatsattsen gashi irin mai ƙullin nan, tana sanye da baƙaƙen kaya fuska ɗauke da murmushi a yayinda idanuwanta suke nan baƙi ƙirin ba ɗigo haske ko ɗaya, kamar yanda idon kuliya yake haka nata yake, a hankali idanuwanta suka washe zuwa normal, ta dawo kamar asalin mutum itama zama tayi a gefen Madam Nablah.....
Madam Nablah kallo ɗaya tayi mata ta sau murmushi tare da faɗin "Catrina Baby Sarauniyar Duhu mai kawar da haske...."
Catrina cikin izzah ta ce "nasan kina buƙatar taimako hakan yasa nazo gareki...."
Madam Nablah ta ce "Nagode miki sosai Sarauniyar Duhu...."
Catrina ta ce "a duk yanda haske yake to tabbas ni duhu ina wurin, an bayyanar da sarauniyar Haske a gidan nan hakan yasa nima na bayyana...."
Madam Nablah ta ce "lokaci yana gab da kawo kansa, Sarauniyar haske da kuma Sarauniyar Duhu a yayinda ni kuma Sarauniyar Wuta nake tsakiyar ku...."
Murmushin ƙeta Catrina tayi sannan ta ce "idan kuma Sarauniyar ruwa ta bayyana fa?...."
Madam Nablah a zabure ta kalli Catrina, haka suke kallon juna, idon Madam Nablah ne ya koma wuta yana fitar da farfatsi, a yayin da itama idon Catrina ya koma duhu ƙirin.....
*NEXT NEXT NEXT*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
39 to 40
Catrina cikin muryar sarauta ta sake furta.
“Devil Mom... ke ce Sarauniyar Wuta. Ni kuma Catrina ce Sarauniyar Duhu. Na jiyo ƙarar rikitacciyar zuciyarki ne yasa nazo domin taimaka miki...."
Madam Nablah sauƙe numfashi tayi tare da faɗin
“Ki ce min da gaske ne Tasleem ta zama Sarauniyar Haske?”
Catrina ta matso kusa da ita sannan ta furta
“Haske da Ruwa sun haɗa hannu. Miemie zata Bayyana, Ita ce Sarauniyar Ruwa, Kuma za su sake jan hankalin ƴar ki — don ta jagoranci hasken da zai iya halaka mu.”
Madam Nablah ta miƙe tsaye da murya mai cike da wutar ƙiyayya ta ce
“To me zai hana mu murƙushe su gaba ɗaya? Ni zan ƙona su, ke kuma ki ɗauke su cikin duhu — ki hana su gani!”
Catrina ta ce
“Bazan iya daidaita ruwan Miemie ba, domin ƙarfin ikon ta ya ninka nawa Amma zan taimaka miki da sabbin aljanu. Wannan karon ba zaki ƙara faɗuwa ba Nablah...."
Madam Nablah ta murmusa da mugun nufi. Idonta ya ɗauke hasken wuta sannan ta ce
“Zamu fara da zuciyar Shaprees, Kafin su karɓi zuciyar Ruhi ta karɓi zuciyar sa, domin yana so ya bijirewa wuta da duhu...."
Catrina ya ce
“Idan Shaprees ya ci gaba da dawowa daga duhu, zan iya ɗauke masa zuciyar sa, gwara ya rasa rayuwar tasan gaba ɗaya...."
Madam Nablah ta ce "ki saurara zamu bi komai a hankali ɗaya bayan ɗaya sai mun dai-dai ta rayuwar su, yanzu abu na ƙarshe da nake so na gudanar shine ɗaura Auren Shaprees da Asmeen da kuma Abeesh da Nasreen, a yau nake so a fara shirya komai gobe kuma Aure, Abul Abeesh zan bashi dama ya cigaba da rayuwa cikin ƴanci na wasu kwanaki...."
Katrina ta ce "Dakyau..."
Sannan Madam Nablah ta cigaba da cewa "zaki cigaba da zama a wannan gidan a matsayin baƙuwa, kada ki bayyanar da kan ki tin yanzu sai komai ya fara girmama tukun..."
Katrina ta kuma cewa "Dakyau..."
Madam Nablah ta kuma cewa "gobe ranar shagalin biki zamu ɗauke Tasleem, zata kasance a wani ɓoyayyen wuri da yake da sirri, wanda gano yanda take abu ne mai hatsari...."
Katrina ta ce "Dakyau amma a wani wuri kike tunanin za'a ɓoyeta wanda haske zai gagara shiga?..."
Madam Nablah ta ce "tafkin tsafi na, cikin ƙasin ruwa na wani yanki na dana mallaka domin ba iya Miemie ce kawai mai gudanar da ruwa ba, akwai nawa ɓangaren ruwa amma bana haske ba...."
Katrina ta ce "Dakyau! na jinjina miki...."
Madam Nablah ta ce "yanzu zaki bayyana a cikin gidan a matsayin baƙuwa amma ki canza waɗannan baƙaƙen kayan nakin zuwa normal kaya kamar na mutane, sannan ki gyara fuskar ki kiyi kwalliya ki bayyana kamar tauraruwa...."
Murmushi Katrina tayi sannan ta ce "haba Sarauniyar Wuta shin kin manta wacece Katrina? nifa kyau na ta musamman ce, ƙirƙirarren kyau wanda ba ruwanta da kwalliya kullum a cikin kyau take...."
Madam Nablah ta ce "hakane! yanzu kin zama ta gida, ki bayyana musu tamkar ɗawisuwa...."
Dariya Katrina tayi lokaci guda ta canza kayan jikinta zuwa wasu matsatsun kaya na fitar hankali, surar jikin ta ya bayyana kamar gimbiyar kyawawa, shigar jeans tayi da wata ƙaramar riga wanda ya bayyanar mata da cibiya, gashin nan ya gyaru har wani sheƙi yaƙe, tayi kyau sosai gata farar fata ce...
Juyi tayi cikin salo sannan ya buɗe ƙofa ta fice, sauƙar ta falo bata tarar da kowa ba, haka take bin falon da kallo, ta ko ina haske ne, jinjina kai tayi sannan ta furta "Haske! mai ƙayatar da komai amma a cikin zuciya ta ina mai baƙin cikin ganin kowa a cikin haske...."
Tana cikin maganar zuci idonta ya sauƙa akan Abeesh wanda yake sauƙo wa falo cikin sauri yana sanye da farar jallabiya, bai lura da Katrina ba sai da ya shigo falon, kallon ta yake cikin rashin sani haka ya nufi bakin ƙofa idonsa akan ta ita ɗin ma shi take kallo tana sakin ƙayataccen murmushi, bai tsaya sauraronta ba haka ya fice domin sauri yake zai tafi masallaci, Amaar kuma ya tafi can headquarters sai cikin dare yake dawowa....
Katrina neman wuri tayi ta zauna tana yamutsa fuska,
Nasreen ce ta fito daga kitchen tana ɗauke da kulolin abinci zata kai can room ɗin Abul.....
Ganin murɗa-murɗan gashin mace ta baya yasa ta shiga tsakiyar falon tana son ganin fuskar yarinyar, itama Katrina kallo ɗaya tayi mata sannan ta ce "sannun ki triplets daughter...."
Nasreen kallon sama da ƙasa take mata daga bisani ta ce "sannu fa amma sai dai ban waye ki ba, daga ina?..."
Katrina ta ce "ba buƙatar tambayata daga ina nake domin babu yanda za'ayi nazo gidan da ban sani ba..."
Nasreen ta ce "Ayya baƙuwa muka yi kenan? to sannun ki..."
Daga nan ta bar falon kai tsaye ɗakin upstairs ta haura yanda zai kaita room ɗin Abul, tana shiga ta tarar da Tasleem zaune a kusa da Abul tana bashi madara a baki cikin kulawa...
Tasleem ɗagowa tayi tana kallon Nasreen da kuloli a hannunta ta ce "haba Nasreen kin cika sanyin jiki, Abul yana jin yunwa kin gagara gama abincin da wuri, ƙarshe madara take bashi...."
Nasreen ajiye kulolin tayi tare da faɗin "Afuwa nake nema Saurauniyar haske..."
Abul yana jin su sai murmushi yake ta sakar musu cikin so da ƙaunar su idan ya tuno da Mahaifinsu kuwa sai ya ji tausayinsu...
Tasleem hararar Nasreen tayi sannan ta ce "bana so ki daina, ai ba'a koda yaushe nake sarauniyar ba...."
Nasreen ta ce "haba sarauniyar mu, ya haka ne kam..."
Tasleem tana turo baki ta maida idonta kan Abul sannan ta ce "Uncle ka ganta ko? na ce bana so ta daina...."
Abul kallon Nasreen ya yi sannan ya ce "ƴata ki daina