Catrina na zaune a gaban madubi tana kallon ruwan hoda mai motsi da ke nuna tasirin hatsarin. Ta saki wani shu’umin murmushi tana faɗin:
“Wannan itace rana ta farko. Na raba Nasreen da Abeesh, yanzu sai na mallake shi har da zuciyar sa gaba ɗaya…”
Amaar ne ya shigo gidan cikin fushi, idanuwansa sun ƙumbura da hawaye,
Bayan shigar sa tsayawa ya yi a tsakiyar falo yana kallon su Tasleem da Asmeen waɗanda suke zaune suna kuka, zuciyarsu cike da firgici da damuwa.
Tasleem ganin Amaar yasa ta miƙe da sauri ta nufe shi tana faɗin
“Ya Amaar, me ya faru?! Ka ganta?! Nasreen tana lafiya?!”
Asmeen ma ta miƙe ta zo da sauri, ta ce:
“Dan Allah ka faɗa mana gaskiya, kar ka ɓoye komai…”
Amaar bai ce uffan ba. Sai da ya shafe sumar kansa, ya ɗan ja numfashi sannan ya girgiza kai cikin raunanniayar murya ya ce
“Motar ta ce ta fāɗa rami… motar ta ƙone…”
Asmeen da Tasleem suka dafe ƙirji a tare suka kurma ihu suna faɗin
> “Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un!!”
Asmeen durƙusawa ƙasa tayi ta kama kai tana kururuwar kuka, Tasleem kuwa ta dafe bango tana jijjiga kai cikin tsananin firgici da hajijiyan da yake shirin kayar da ita tana faɗin
“Kana so kace ta mutu?!”
Tasleem ta tambaya da rawar murya.
Amaar ya ce:
“Ba mu ga gangar jikin ta ba... amma... motar ta ƙone sosai. Abeesh shima ya suma a wurin. An garzaya da shi asibiti.”
Cikin kankanin lokaci Abul ya fito daga ɗaki, yana jin hayaniya. Ya tsaya a bakin falo yana kallon kowa cikin tsananin mamaki da damuwa ya ce:
“Meye wannan ihun? Me ya faru da Nasreen?”
Amaar ya je ya durƙusa gaban mahaifinsu:
“Abul… wata babbar mota ce ta bugi motar Nasreen, ta kife tare da ƙone wa. Ba mu ga jikinta ba. Amma…”
Abul ya ɗaga hannunsa sama yana faɗin:
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Nasreen…?”
Zuciyar Abul ne ta shiga bugu da ƙarfi. Ya jingina da bango yana huci. Kowa ya ruɗe. Ana kuka.
Sai kwatsam Catrina ta fito daga ɗakinta da lumsassun idanu, a fuska kamar bata san me ake ciki ba. Ta tsaya a ƙofar falo tana kallon su gaba ɗaya ta ce:
“Lafiya? Me ake kuka akai?”
Tasleem ta juyo cikin fushi mai cike da hawayen bakin ciki ta ce:
“Lafiya?! Ke! Kin yi nasara! Kin raba mu da Nasreen ko?! Ashe burinki kenan, to burin nakin ya cika?!”
Catrina ta ɗan zaro ido, ta soma wani murmushin ƙarfin hali ta ce:
“Ni kuma? Me nayi?”
Asmeen ta nufo ta cikin tsananin fushi, ta nuna mata yatsa tana faɗin:
“Karki ɗauke mu mahaukata kamar ki. Mun san ke kika jawo wannan! Wani abu ke faruwa kuma ke kika haddasa shi, inda baki shiga tsakanin masoya ba da duk hakan bata faru ba, ta silar ki ƴar uwata ta kai kanta ga hallaka....!”
Catrina ta kalle su duka, sai ta juyo ta dubi Abul da Amaar, ta ce:
“Wannan wautar ya isa haka. Kuna kuka ne akan wata wacce ta yanke shawarar barin mijinta ba tare da jin shawara ba?”
Amaar ya ɗan matso kusa da ita, cikin murya mai sanyi da kuma ƙarfi yana cewa:
“Catrina… ya isa haka. Kin daɗe kina wasa da zuciyoyin mutane. Kinyi abubuwan da suka gaza fassara. Idan har akwai adalci a doron ƙasa, to Allah zai tona miki asiri.”
Catrina shiru tayi idonta ya fara sauya launi na ɗan lokaci – launin shuɗi mai duhu – amma sai ta yi saurin lumshe da idon...
Sai kwatsam Abul ya dafa bango, yana faɗin:
“Zan faɗa muku gaskiya… Wacece Catrina… kuma me take shiryawa...”
Kowa ya juyo ya zuba masa ido.
Tasleem ta ce:
“Abul ka ce gaskiya... Ka san wani abu game da ita?”
Abul yayi shiru na dan lokaci, yana kallon Catrina, lokaci guda ya dafe ƙirjinsa... sai kawai ya faɗi ƙasa sumamme.....!
Labarai na yamma da dare suka cika kafafen yaɗa labarai:
"Muna cikin jimamin rasa wata matashiya mai suna Nasreen wadda mota ta buge ta a kusa da hanyar Sabon Gari. Motarta ta kama da wuta, an samu kuntayen kayanta da wasu takardu masu nuna sunanta. amma sai dai mun rasa gawar ta, muna tunanin ta ƙone ƙurmus cikin gobarar..."
Idon duniya na kan hatsarin. Amma ba kowa ya san gaskiyar abin da ya faru ...
Amaar na ƙoƙarin ɗaga mahaifinsu Abul bayan ya faɗi a kasa. Shi kaɗai ke da nutsuwa amma zuciyarsa cike take da firgici. Tasleem da Asmeen suna kuka sosai har sai da suka ji muryar labarai na dukan dodon kunnen su..
Idon Asmeen ya sauka a kan television, ta soma kallon motar da suka nuna ta ƙone amma ba gaba ɗaya ba Sai kayan cikin mota da aka nuna, rigar Nasreen da wani ɗan hijabin ta...
Asmeen ta furta:
"Innalillahi!!! Wayyooo ALLAAAAH!!!"
Tayi wani irin ihu mai taɓa zuciyar wanda ke raye, ta faɗi ƙasa sumammiya—numfashinta ya narke, jikinta yayi sanyi.
Amaar ya ruɗe gaba ɗaya.
Ga kuma Tasleem ta fara riƙe kanta tana fadin:
“Ina jin haske… Amma cikin duhu… zuciyata zata fashe…”
Sumar kanta ne ya fara canza launi. Daga baƙi zuwa fari mai kyalli kamar zaren azurfa. Idanunta suka koma fari sol kamar ba su da jijiya.
Tana surutu da wata murya mai sanyi ta cigaba da faɗin:
"A gaban zuciyar rana ta tashi. Haske ya motsa. Na yarda da hasken gaskiya. Amma duhu yana kusa… Catrina ce duhun!"
Amaar da ya lura da lamarin Tasleem ya tsorata. ɗagata ya yi cikin sauri, ya nufi ɗakinta ya kwantar da ita, ya kulle kofa da key.
Catrina wacce tin yaɗuwar Abul ta koma cikin ɗakin ta, tana zauna a gefen madubi tana kallon kanta. Sai tayi murmushi mai cike da mugunta.
“Nasreen… yanzu dai kin ɓace. Wannan dukan tsarabar ta haske ta fara raguwa. Amaar, Asmeen… Tasleem… sai dai kuyi ta kuka, amma ba zaku iya hana ni mallakar komai ba.”
Sai ta ɗauko wata ƙaramar ƙwarya mai tagulla daga ƙasan gadonta. Ta buɗe. A ciki akwai ƙasan zuciyar maciji da gashin mutum—duk sune al’adun mugunta da take amfani da su.
“Zan shige zuciyar ka gaba ɗaya. Zaka zama nawa. Sai dai fa… Nasreen ba zata dawo ba. Kuma idan ta dawo...”
Sai tayi murmushi:
“...zan karɓe ranta da hannuna.”.....
Amaar bayan ya kai Abul da Asmeen asibiti sai da ya dubo Abeesh shima ba'a hayyacin sa yake ba, ya juma a asibitin kafin ya tuna da Tasleem a kulle a ɗakin,
A gurguje ya fito daga cikin hospital ya shige motar sa, lokacin misalin ƙarfe 8 da rabi ne..
Bayan komawar sa gida.
Ya shigo gidan da takun sa mai nutsuwa, ya nufi ɗakin da ya ajiye ta cikin tsanani. A hankali ya buɗe ƙofar
Tasleem tana zaune gefen gado, sumar kanta har yanzu na ɗauke da wani launin fari mai kyalli. Amma idanunta cike da hawaye. Runtse su tayi kamar tana kokarin toshe wasu wahayi masu raɗaɗi daga cikin zuciyarta.
Amaar yana ganin haka – ya ƙaraso ba tare da faɗin komai ba, ya zauna kusa da ita, ya rungume ta cikin So da ƙauna...
Tasleem ta fashe da kuka a kirjinsa, tana faɗi cikin rawar murya:
"Na gano duk wata gaskiya Yah Amaar… Na tafka babban kuskure. Ni ce Sarauniyar Haske – amma na kasa ceton Abeesh daga hannun duhu... na kasa ceton Nasreen daga hallakar mugunta... Littafin Hasken Ruhi na ya buɗe kansa a daren nan... Gaskiya ta bayyana!"
Amaar ya yi shiru, yana shafa bayanta, zuciyarsa na bugawa da dukan sirri da tsoron abin da zai ji daga gareta.
Tasleem ta cigaba da cewa:
“Na ga cikin wahayi… Catrina ba mutum bace, Ita ce Sarauniyar Duhu. Wacce aka haifa daga duhun dare, aka renata da ƙiyayya, aka koya mata hanya guda na hallaka haske…
Ita ce Kuliya wacce Littafin Ruhi ya ambata tana ɓoye a cikin mutane, tana cikin gidan nan tana shan ƙaunar da ba nata bace…”
Sai ta dafe kirji tana faɗi da murya mai tsuma zuciya:
“Na kasa hango komai game da Nasreen, Kuma Catrina... ita ce ta shirya komai akan ɓatan Nasreen....!”
Amaar ya ɗago fuskarta, yana kallonta da idanu masu cike da tausayin gaskiyarta.
Ya ce:
“Ki saurara Tasleem… Babu wani kuskure da haske ya tafka idan yana cikin gaskiya. Abinda ke faruwa yanzu shine lokacin da ya dace mu gano gaskiya ba bamu yi tunanin haka ba, zamu tinkare ta ba wai muji tsoron ta ba,
Littafin Hasken Ruhi ya buɗu? To yanzu lokaci ya yi da zamu buɗe shafi na gaskiya.”
Tasleem ta kalle shi da hawaye a idonta tana murmushi mai ɗauke da rauni ta ce:
“Zan tashi, Yah Amaar… Zan kareku. Amma sai mun fuskanci gaskiya – Catrina dole ne ta ɓuya domin ta ci nasara. Amma yanzu… ni ce haske da ba ya ɓuya.”
ƁANGAREN MADAM NABLAH ....
A daidai lokacin da duniya ke kuka da mutuwar Nasreen, wasu suna kwance a asibiti suna yaƙi da rai, wasu suna juyayin kuskuren su, Madam Nablah tana zaune a cikin wani daƙin duhu wanda ba'a duniya take ba, tana can duniyar Aljanu,
Wuri ne dake da tsakanin haske da inuwa, inda ruhinta ke da cikakken iko.
Madubinta mai sarrafa gaskiyar abubuwa yana a gabanta – tana kallo, tana jin komai, tana ƙare wa komai kallo kamar sarauniyar da ba ta iya barin masarautarta amma ta san duk abinda ke wakana.
Madam Nablah tana zaune cikin wata kujera mai baƙar fata da ƙyalli, tana kallon madubin yayin da hoton hatsarin Nasreen ya bayyana. Lokacin kafin mutanen duniya su Ankara Madam Nablah ta miƙa hannunta cikin madubi ta zaro ruhinta daga jikinta – ruhin da ke cike da iko da saurin walƙiya.
A cikin sa’a ɗaya, ta bayyana a cikin hatsarin, ta tsayar da lokaci – ta tsamo Nasreen cikin wuta, ta ɗauke ta da hanunta mai cike da sirrin sihiri, ta ɗauke ta cikin hayakin da ba ya barin alama, ta ɓace da ita daga idon duniya.
Nasreen yanzu tana kwance a cikin wani ɗaki mai tsarki da sirri. Furen duwatsu ne a jikin bango, kyandirori masu ƙyalli suna haskaka ko ina, iska mai daɗi tana kadawa daga sama. Bata farfaɗo ba – har yanzu cikin sumarta take – amma hankali da lafiya na jikinta na dawowa sannu a hankali.
Madam Nablah tana zaune a ƙasan gadon tana shafa gashinta, tana zuba mata ruwa mai ƙyalli daga kwaryar zinariya. Duk da azancin halinta da muguntar zuciyarta ƙaunar ƴarta tana da nauyi da ƙarfi.
Ta furta:
"Na san zaki yi zargin wani abu akaina idan kika farka... Amma bazan bari ki mutu ba, Nasreen... Ni na haife ki, kuma ke ɗiyata ce. Duniya zata ɗauka kin mutu. Amma ni – ba zan rasa ki ba."
Madam Nablah ta ajiye ƙwaryar ruwa, ta ɗauko ƙaramar ƙwalba mai ruwan zinariya ta zuba akan leɓen Nasreen. Ta lumshe idonta tana karanta wani sirrin zikirin duhu da haske.
"Wannan ba ceto bane kawai... Wannan shine tabbatarwa cewa har yanzu ni ce uwa... Kuma har yanzu ke ce haske na... duk da ni duhu ce."
Idonta a lumshe take furta hakan...
Kowa ya saddaƙar Nasreen ta mutu duk duniya har da su Tasleem da Amaar domin akwai yanda Hasken Tasleem bazai iya hasko mata wani wuri ba, misalin wurin da Madam Nablah ta ajiye Nasreen, ba'a duniya ba, a duniyar Aljanu take...
Madam Nablah tana kula da ita a ɓoye cikin so da ƙauna,
Bata fatan ƴarta ta zama duhu kamar ita, kuma zata cigaba da riƙe Nasreen ba tare da kowa ya sani ba...
Madam Nablah ce ta bayyana a ɗakin Catrina ba tare da mutanen gidan sun san ta dawo ba,
Catrina ta miƙe daga kujera da sauri, idonta cike da firgici ta ce:
"Devil Mom?!"
ta furta a firgice.
"Ya kika dawo ta hanyar nan?! Wannan ɓangare ne na sirri..."
Madam Nablah, cikin sautin murya mai ƙarfi da iko, ta taka zuwa gareta ba tare da kallo sakin fuska ba ta ce:
"Ba dawowa nayi ba, Catrina,"
ta furta da ƙarfi.
"Na zo domin KE! Kuma bazan yarda ki ci amana ba."...
Catrina ta matsa baya kafin ta iya ƙara ko kalma, Madam Nablah ta miƙar da hannunta guda ta shaƙo wuyanta, ta ɗagata da hannunta daya kamar ƙaramar ƴar tsana.
Catrina tana juyi, tana fizgewa, tana ƙoƙarin kiran wata ƙarfi, amma babu wani sihiri da yake aiki a gaban uwargida Madam Nablah.
Madam Nablah ta ce:
"Kin manta jinin da ke jikinta shine jini na! Kin manta ita ɗiyata ce, Nasreen ce Haskena!
Me yasa kike ƙoƙarin halaka ta?!"
Murya na girgiza ɗakin tsabar ƙarfin muryar tsafi...
Catrina tana harba ƙafarta, hawaye na zubowa na tsoro da fargaba. Domin tasan Madam Nablah tana cikin fushi... kuma idan fushin ta ya kai iyaka, babu wanda ke iya tsira mutum ko Aljan....
Madam Nablah ta cigaba da faɗin:
"Na san komai. Na san wahalar da kike bawa zuciyar Abeesh, kika ƙazantar da rayuwarsa, kika saka zuciyar Nasreen cikin ruɗani.
Amma ki sani... Na zuba miki ido ne, duk wanda ya taɓa Nasreen zai fuskance ni ba a matsayin uwa ba a matsayin sarauniyar wuta...!"
Madam Nablah ta jefar da Catrina da ƙarfi—ta bugu da jikin bango sannan ta gangaro ƙasa tana tari. Jikinta yana karkarwa.
"Wannan shine gargaɗi na,"
Madam Nablah ta ce yayin da fuskarta ta ɗauki duhun walƙiya.
"Ki kula sosai Catrina. Wannan gidan ba naki bane. kina ƙarƙashina ne amma kada ki jarabce n da barin ƴata ta mutu, domin idan ta mutu zaki fuskanci fushi na,
Idan kika ƙara yunkurin taɓa ko ɗaya daga jinin jikina ba zan ƙara gargadi ba—sai hallaka."
A take, Madam Nablah ta ɓace cikin duhu, kamar ba ta zo ba....
Catrina tana tsaye a gaban madubi cikin fushi take faɗin
" Ina so Nasreen ta bar duniya amma kin je kin ceceta, to kuwa yanzu wasan zai fara, bazan taɓa yin sanyi ba, Abeesh nawa ne ni kaɗai, zan iya kashe kowa akan sa, soyayyar sa tayi zurfi...
Madam Nablah sanin halin Catrina batada hakuri yasa tabi iska taje har asibiti ba tare da kowa ya sani ba, taje ta ɗauki Abeesh ta ɓace dashi, ta ajiye shi a cikin wani baƙin daji, shi kuwa Abeesh baya cikin hayyacin sa, har yanzu bai farfaɗo ba...
Bayan kwana ɗaya an sanar cewa Abeesh baya asibiti, an je an dudduba shi baya nan, ko ina an duba baya nan..
Washegari
Kowa yana asibiti iya Catrina ce kawai a gida....
Catrina na zaune da ƙafafunta a sakale, tana latsar farcen hannunta, fuskarta na ɗauke da wata irin nishaɗi da bakin ciki wanda sai mai duhu zai iya fahimta. Jin motsi a ƙofar falo bai firgitata ba, sai murmushinta ne ya zurfafa, domin tasan wacece ke shigowa.
Tasleem ce ta shigo kamar wuta. Idonta cike da haske, fuskarta ɗauke da tsananin ɓacin rai da ɗokin jin amsar da take buƙata. Bata tsaya kallo ko magana ba, ta je kai tsaye ta ɗagota daga inda take zaune tare da zabga mata mari har sau biyu waɗanda suka sa numfashin Catrina tsayawa na ɗan lokaci.
A fizge ta ce:
"Ke kinada hankali kuwa? Mena miki kika shigo da wannan fushin kamar wacce aka tsige mata sarauta?"
Catrina ta faɗa tana kallon Tasleem da idanuwanta masu ƙyalli da duhu.
Tasleem ta ce
"Bayan laifukan da kika yi shine zaki tambaya me kika yi? Kar ki mayar ni yarinya mana, duk shirin ki na sani, tin farkon zuwanki gidan nan, idonki kawai na kalla na gane cewa ke ba mutum bace..."
Catrina tayi dariya ta ce:
"aww kin gane Ni tin da shine kike wahalar da Shari'a? Eh ni sarauniyar duhu ce wacce zata tarwatsa Miki mafarki..."
Tasleem ta ce
"Kin gama tarwatsa ni ai tunda kika kashe mana ƴar uwar mu Nasreen akan mijinta na halak, sannan Abul yana so ya faɗi gaskiya akan ki, shine kika buge masa zuciya da mashin idonki, sannan yanzu kin ɗauke Abeesh daga asibiti, shin ina kika kaishi?..."
Catrina tayi dariya ta ce
"Gaskiya amma hasken ki baya baki gaskiya Indai zakiyi tunanin ni na ɗauke Abeesh, meyasa zan ɗauke shi?..."
Tasleem ta ce
"Saboda ƙudurin ki mana, ki fito mun da Abeesh yanzun nan kafin na tarwatsaki..."
Catrina ta ce
"Bani na ɗauke Abeesh ba, ban san ina yaje ba"
Tasleem ta ce
"ƙarya kike kinsan yanda yake munafukar banza..."
Catrina ta juyar da kanta tana dariya, murmushi mai duhu yana bayyana a fuskarta. Idonta ya fara canzawa zuwa baƙi ƙirin ba ɗigon fari. Tana furta kalma mai cike da ƙiyayya:
"Hasken ki bai baki gaskiya ba, Sarauniyar Haske. Na ce miki ba ni na ɗauke shi ba... Ko kuwa kina shirin ganin fushina Ni Catrina Sarauniyar Duhu ne?"
Tasleem ta runtse idonta, jikinta ya haskaka gaba ɗaya. Sai ga idonta ma ya koma fari mai kyalli, kafafunta na ɗagawa da ƙarfi kamar bata taɓa taka ƙasa ba. Hasken dake jikinta ya fara zagaya falon—yana ƙona komai da bai dace ba tana faɗin:
"Ƙarya kike Catrina, zuciyata ta gane ki tun tuni! Kin ɗauke shi. Ko da ba ke ba ce, kin san inda yake. Kuma yanzu ba batun faɗa bane—zaki fuskanci fushin da baki taɓa tsammani ba!"
Catrina tayi tsalle gefe tana mai dariyar hauka. Tana faɗin:
"Na gaya miki amma kin ƙi yadda to bawai tsoron ki nake ba, kuma ma babu wani laifin da na aikata a gidan nan, kuma in da kin gane ko ni wacece da farko nasan da zaki ɗauki hukunci duk da nasan babu abinda zaki yi mun...
Tasleem ta matso gaba, numfashinta yana fita da karfi. Har yanzu hannunta na rawa Idonta ya kaɗa da wani irin zurfin haske da ba'a saba gani ba ta ce
"Laifinki ya zarce sa'a Catrina. Ke kika haifar mana da bala’i. Ke kika hallaka rayuwar ‘yar uwar mu. Akan miji da ba