da ƙwayar idanuwanta kan Asmeen wacce ta gama tsorata da irin fusatar da Tasleem tayi har tayi wurgi da Nasreen, ba shiri kuwa ta yi baya da gudu...
Amaar hannu yasa ya ɗago da Nasreen har goshin ta ya fashe sai jinin dake zuba,
Tasleem kallace-kallace take tana neman abun da zata ƙara sa Firoj domin ƙarfen hannun ta duk ya lanƙwashe, idonuwanta ne suka sauƙa akan AMAAR, ta ɗau tsawon seconni tana kallon wurin da Amaar yake, sai dai abun mamaki ba Amaar ɗin take kallo ba, bindigar dake sokare a aljihun wandon sa take kallo, tana tunanin yanda zata je ta ciro shi,
Kafin a ankara har ta tafi da gudu ta ciro bindigar, kafin Amaar ya ankara har ta kunna kunamar bindigar ta sai ta Firoj,
Nasreen da Asmeen ihu suka fara yi suna bata haƙuri akan ta dakata,
Amaar wani irin sufa ya yi tare da riƙo hannun ta ya ɗaga sama dai-dai lokacin ta danna kunamar bindigar sai ga bullet ya fita yayi sama, ga shocking ɗin da yabi jikin su wani irin ihu Tasleem tayi sai da suka ɗagu sama suka doku a ƙasi, bindigar hannun ta ya cillu gefe guda...
Tasleem cikin ƙarfin hali ta ɗago da kanta tana ƙoƙarin juya bayanta tana son ganin wanda ya riƙe ta har wannan shocking ya same ta, kafin ta juya kuwa Amaar yayi saurin tashi jiki na ɓari ya ɓuya a bayan mota,
Dafe goshin sa yayi domin ba ƙaramin juyawa ƙwaƙwalwar sa ke yi ba,
Asmeen da gudu ta nufi yanda yake tana faɗin "Ya Amaar kana lafiya, zan iya taimaka maka?..."
Itama Tasleem tunanin ta ne ya fara gushe wa, ƙwaƙwalwar ta na juyawa, wani irin sauti ta fara ji ana faɗin "Tasleem ki taimake ni, kar momynki ta kashe ni, Tasleem dan Allah, Tasleem ki taimake ni...."
a cikin kwakwalwar take jin waɗannan sautin, itama dafe kanta tayi tana birgima..
Nasreen ganin ciwon Tasleem yana shirin tashi yasa ta tafi wurin da take kwance da gudu tana ƙiran sunanta,
Dai-dai lokacin da motar Minister ta iso da wasu motoci na sojoji da polisawa sai jiniya ne yake ta tashi.
Ta ɓangare guda itama Madam Nablah ta zo da motocin security ta.........
NEXT.......
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 13 to 14
Minister yana sauƙa da gudun gaske ya nufi yanda yaron sa yake a kwance shame-shame, kafin ka ce mai sai ga Ambulance an zo ɗaukan sa, Madam Nablah wacce fitowar ta kenan daga cikin mota idanuwanta suka sauƙa akan Tasleem wacce take ta birgima tana riƙe da kanta sai sambatu take wanda ba'a jin abinda take faɗi, Madam Nablah ganin ƙwaƙwalwar Tasleem ne yake shirin motsawa ne yasa gaba ɗaya hankalin ta tashi, yanzu ba'a gida suke ba balle tayi mata abinda ta saba idan ciwon ya motsa, a yanzu nuna tsafin ta zai bada matsala, babu wanda yasan ita matsafiya ce still ga yaran ta a wurin, tana cikin tunanin yanda zata yi ba zato ba tsammani taji dirarren murya ya sauƙa akan dodon kunnen ta, Minister ne yake zazzaro idanu cikin fushi yake faɗin "Nablah kun wuce gona da ƙiri, shin ɗiyar ki tasan wa ta taɓa kuwa? to ki sanar mata cewa ta taɓo masifa da bala'i akan ta sai tayi nadamar tozarta Firoj da tayi...."
Madam Nablah idonta akan Minister tana sakin murmushi cikin izzah ta ce "Hmmm! Minister kenan tabbas nasan yaron wa Tasleem ta taɓa amma ina so ka sani cewa ita ma Tasleem ƴa ce ga babban mutum wanda duniya ta san shi, idan ka manta zan tuna maka, iya ɗin ɗiya ce ga Governor wannan ƙayataccen garin da muke ciki, sannan mahaifiyar ta Madam Nablah wato ni ba ƙaramar mata ba ce da za'a taɓa mun ƴaƴa nayi shuru na ƙyale...."
Minister ya ce "maganar banza! kina maganar ƴar governor shi da ya juma da barin muƙamin? shekara nawa da shafe shafinsa, a bayan sa govenoni nawa aka yi? to bari kiji wallahi tallahi sai na ɗau hukunci akan wannan al'amarin, zan sa a ɗaure ɗiyar ki a gidan yari har sai yarona ya samu isasshen lafiya..."
Madam Nablah ta ce "Idan kuma ya mutu fa?..."
A fusace Minister ya ce "itama dole zata mutum, sai ta girbi abinda ta shuka..."
Madam Nablah ta ce "okay fatan nasara..."
Daga nan Minister da mutanen sa suka tafi kai tsaye hospital suka nufa yanda aka kai Firoj...
Madam Nablah kallon Nasreen ta yi sannan ta ce "ku kai mun ita cikin mota..."
Nasreen da Asmeen ne suka yi ƙoƙarin ɗago ta suka nufi cikin mota da Tasleem,
Shi kuwa Amaar tinda idanuwansa suka sauƙa akan Madam Nablah ya nemi wuri ya ɓuya amma idonsa yana kanta, ya gagara manta wannan kamannin tin shekarun baya...
Madam Nablah shiga motar ta tayi ga Tasleem a back seat a kwance, da gudu Madam Nablah ta ja mota ta bar wurin sai security ta da suka bi ta a baya, Nasreen da Asmeen su ma motar su suka shiga zasu bi bayan su, cike da damuwa suka ja motar suka bar wurin, Amaar dake tsaye gaba ɗaya fuskar sa ta jagalgale ba alamun annuri a fuskar sa, tsananin damuwa ne a kwance a fuskar sa, yana kukan zucin abubuwa da yawa na farko ya rasa mahaifinsa wanda bai san meya faru da shi ba, a cewar mutane da yayi tambaya sun sanar masa cewa mahaifinsa ya daɗe da rasuwa, amma ba'a san mai ya kashe shi ba,
Sannan ga damuwar rashin Ɗan uwansa Abeesh duk da ya ji labarin yana gidan Madam Nablah amma shi ko kaɗan baya ƙaunar zuwa gidan, saboda baya son kowa ya gane shi a yanzu sai ya gama binciken sa akan Madam Nablah...
Shima motar sa ya shige tare da nufan yanda ya miƙa, abinda ya ra ya a ransa shine zai je can tsohon gidan su, wato gidan mahaifinsa wanda tin lokacin da aka rasa shi gidan yake kulle babu mai shigar sa...
Madam Nablah su na isa gida tasa security ɗaya ya ɗauki Tasleem tare da bashi Umarnin ya kaita can part ɗin ta, itama ta bi bayan su,
Nasreen da Asmeen bayan sun iso a falo suka zauna kowa da damuwa akan fuskar ta, su na cikin wannan halin su ka fara jin ringing ɗin telephone dake ajiye akan table ɗin falo, hakan na nufin ana ƙiran mutanen gidan ne, kowa zai iya ɗaukan ƙira ko a cikin ƴan aikin gidan ma, Nasreen idonta akan Telephone amma ta kasa motsawa tsabar jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba,
Asmeen ce tayi ƙarfin ɗaukan wayar tare da karawa a kunne, tana faɗin "hello wa kake nema a cikin mutanen gidan?..."
Ta cikin wayar ta ji an furta "Asmeen, Asmeen nake nema..."
Cike da mamaki Asmeen ta ce "waye kai ɗin?..."
Shima ya ce "ke ɗin wacece?..."
Asmeen ta ce "naji ka ƙira sunana shin meke tafe da kai?..."
Daga cikin wayar ta ji an furta "kin tafi kin barni da yunwa, uban wa zai yi feeding ɗina?..."
Gaban Asmeen ce ya yi matuƙar bugawa da ƙarfin gaske jin Shaprees ne,
A ruɗe ta ce "kayi hakuri gani nan zuwa, Allah ya huci zuciyar ka..."
Tana kaiwa nan ta ajiye wayar cikin damuwa ta miƙe tana goge hawaye ta fice daga falon, kai tsaye part ɗin Shaprees ta nufa...
Ita kuwa Nasreen kanta ta kwantar akan sopar kujera, da haka har bacci ɓarawo ya ɗauke ta a wurin,
Bayan wasu mintina sai ga Abeesh ya dawo daga wurin aiki, har zai wuce idonsa ya sauƙa akan Nasreen dake ta shan bacci, murmushi ya sau domin ya gane cewa Nasreen ce, zuwa yayi gabanta ya durƙusa yana ƙare ta da kallo daga bisani ya ajiye jakar hannun sa akan kujera sannan yasa hannu ya ɗauke ta, kai tsaye upstairs ya haura ya nufi part ɗin su da ita, yana zuwa ya kwantar da ita akan gado sannan ya tofa mata addu'o'i ya fice a ɗakin yana sakin murmushi shi kaɗai....
Tasleem ce kwance akan gadon Madam Nablah an gama tsafe ta, an juyar mata da tunanin da yake shirin dawo mata, daga nan bacci ya ɗauke ta...
Amaar gidan da ya shiga ainahin gidan su kenan, gidan ya yi kaca-kaca kamar gidan bola tsawon shekaru Ashirin babu mutum ɗan Adam da ya ƙara zama a cikin gidan, yana shiga falo ya tarar da ƙaton photon su tin suna yara shi da Abeesh da Mahaifinsu a tsakiyar su yana rungume da su, photon duk yayi ƙura sai da yasa hannu ya share ƙurar tukun photon ya ɗan haske, ga photon mahaifiyar su, komai na falon yana nan ba'a taɓa komai ba sai dattin da suka yi, ga kujeru da plasman da frig da su dinning table, yana kallace-kallace har ya wuce can bedroom ɗinsa lokacin da yake yaro, wasu abubuwan sa na wasa ne gasu nan da kayayyakin sa, ɗauko jakarsa yayi ya buɗe wasu photunan sa ne a lokacin baya, har da photonsa da Tasleem su biyu da kuma wanda sukayi shi da triplets gaba ɗaya su ukun, da photon sa da Abeesh, ɗaukan photunan yayi zai tafi da su, bayan ya gaba da room ɗin sa ne ya koma falo daga nan ya wuce ɗakin Mahaifinsu, yana shiga hawaye suka fara yanko masa domin ba ƙaramin kewar mahaifinsa yake ba, nan ma ya ɗauki abubuwa masu mahimmanci daga baya ya fice, ya bar gidan gaba ɗaya....
Bayan kwana biyu
Da misalin ƙarfe goma na dare Madam Nablah tana zaune a kujerar falo tana kurɓar coffee idonta akan plasman tana kallon labarai,
Nasreen ce ta sauƙo falo daga upstairs da sallama a bakin ta, ganin Madam Nablah bata amsa sallamar ba yasa ta ƙara maimaita wa still bata amsa mata ba, Nasreen ƙara maimaita sallamar zata Madam Nablah ta katse ta da cewa "Oh my god! wannan wani irin naci ne haka, idan kika yi sallama sau ɗaya ai sai ki haƙura tinda ni ba kurmiya bace..."
Nasreen ta ce "sorry Mom na ɗauka baki ji bane..."
Zama tayi itama idonta akan Madam Nablah ta kuma cewa "Mom yau kwana biyu ban ga Tasleem ta fito daga ɗakin ki ba, shin bata farfaɗo bane har yanzu?..."
Madam Nablah ta ce "Nima jiran farfaɗowarta nake, har yanzu bata farfaɗo ba..."
Nasreen ta ce "subhanallahi amma bata ɗauka irin wannan long time bata farfaɗo ba ai..."
Madam Nablah ta ce "Nima ban san dalili ba..."
Nasreen ta ce "but meyasa Tasleem take shiga wannan halin, nasan akwai silar faruwar haka..."
Madam Nablah ta ce "Nasreen ki je ki kwanta dare yayi, bana son irin wadannan tambayoyi...."
Nasreen ba yanda ta iya haka ta tashi ta bar falon...
Tasleem tana kwance idanuwanta a buɗe tana kallon saman ceiling, ta daɗe da farfaɗowa amma sai dai bata nuna wa uwar cewa ta dawo hayyacinta ba, saboda wasu abubuwa da taga uwar tana yi cikin dare, sannan takan yi wasu tsafinta akan Tasleem ba tare da tasan ta farfaɗo ba, abun ya yi matuƙar ɗaure wa Tasleem kai, tana tunanin duk waɗannan abubuwan na meye su, sannan tana tunanin kar mafarkin ta ya zamo gaskiya, tana so ta tabbatar da gaskiyar mafarkin ta ne yasa bata nuna ta farfaɗo ba saboda tasan mommy bazata bar ta a ɗakin ta ba,
Tana cikin wannan tunanin ta fara jin motsin mutum da sauri ta rufe idanuwanta, ta ɗage motsin ta kamar gawa, Madam Nablah tana shigowa ta nufi yanda Tasleem take a kwance, zama tayi a bakin gado idonta akan ta shafa sumar kanta tayi sannan ta ɗora hannunta akan saitin wuyanta tana son tabbatar da ko ta farfaɗo, Tasleem ɗage numfashin ta tayi har na tsawon seconni daga baya Madam Nablah ta ɗage hannunta akan wuyan ta, dalilin da yasa ta ajiye Tasleem a room ɗinta tana gudun kar a cikin sumar ta bayyanar da duk wani sirrin da yake ranta, domin taji tana wasu sambatu,
Madam Nablah tsaya wa tayi a tsakiyar room ɗin ta tayi wani irin juyi a hankali ta sauya kayan jikin ta suka koma launin baƙaƙe na zuwa Devil would domin akwai meeting ɗin da zasu gudanar,
gashin kanta ya warwatse zuwa gadon bayan ta, miƙar da tafin hannunta tayi sai ga hular tsafi na sarauta ya bayyano akan tafin hannunta, ta ɗora akan ta