x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 182

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sai sheƙi yaƙe dake da zinare aka yi shi.....

Waɗannan abubuwa duk akan idon Tasleem suka faru, ba ƙaramin tsorita tayi ba amma bata nuna hakan ba ko motsi bata yi ba, akan idonta Madam Nablah ta je ta tsaya a gaban ƙaton photon mahaifinsu tare da furta wasu kalmomi sai ga photon ya rabe gida biyu tasa hannu ta buɗe ɓoyayyen ƙofar ta shige, tana shiga ƙofar ta rufu sannan photon ya haɗe...

Tasleem a zabure ta miƙe tare da nufan wurin da sauri, itama tsayawa tayi ta gwada furta kalmar da Madam Nablah ta furta sai ga photon ya ƙara rabewa biyu sannan ƙofar ta buɗu itama ta shige ciki...

wani irin duhu ne a ciki bata iya ganin gabanta sai hasken hular kan Madam Nablah da yake ta haska mata hanyar wuce wa, har ta ɗan nisa, itama Tasleem da sauri take bin wannan haske take bin bayan ta har sai da suka yi tafiya mai nisan gasken Tasleem taga Madam Nablah ta tsaya cakk, cikin tsoro da fargaba ta durƙusa ƙasi tare da laɓewa kar ta juyo ta kalle ta, Tasleem gani tayi Madam Nablah ta tsuguna itama tare da sa hannu ta buɗe wani murfi dake ƙasi kamar ramin rijiya, tana buɗe wa ta miƙe tare da shige wa ciki tana taka matakalar benin da zai kaita ƙasin gida.

Tana shige wa sai ga Tasleem ta taso itama ta nufi wurin tana zuwa itama ta shige ramin, haka take taka wa a hankali domin idan baka yi a hankali ba zaka iya gangarawa ciki, ganin a tsaye zata iya faɗuwa ne yasa ta zauna akan matakalan take ja da mazaunanta a hankali da haka ta isa ciki, bata ƙarasa shige wa ba taga Madam Nablah a tsaye a gaban wani mutumi yana ɗaɗɗaure da kaca akan kujera, fuska a rufe da baƙar hula, dake Madam Nablah tana shiga ta kunna hasken wurin hakan yasa Tasleem take iya ganin komai, Madam Nablah ce tasa hannu ta buɗe masa fuska,
Ta ce "sannun ka da hutawa Abul Abeesh..."

Tasleem zaro ido tayi waje jin an furta Abul Abeesh, idonta akan mutumin sai dai bazata iya gane shi ba domin tin suna yara ƙanana aka ɗauke shi, yanzu kuwa fuskar sa duk ya cika da gashin gemu, ga furfurar azaba da ya cika masa kan sa, a hankali Tasleem ta maimaita "Abul Abeesh" a cikin ranta.

Abul Abeesh murya na kakkarwa ya ce "ina roƙon Allah da kada ya ɗauki rayuwata har sai na ga ƙarshen zalunci ki Nablah, ko kaɗa bakida imani, yanzu da me kika zo mun..."

Madam Nablah ta ce "duk abinda zanyi sai na zo na sanar maka, kuma babu wanda ya isa ya dakatar da ni akan haka, yanzu nazo ne na sanar maka cewa zanyi sadaukarwa..."

Murmushi Abul Abeesh ya yi sannan ya ce "a shekarun baya kin sadaukar da jinin abu mafi muhimmanci a rayuwar ki wato jinin mijinki uban ƴaƴan ki..."

Ƙirjin Tasleem ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, a razane ta ɗauke numfashin ta jin abinda kunnuwanta suka jiyo mata, haka ta ƙara jajirce wurin control kan ta, ta cigaba da saurorin mutumin da ake ƙira da Abul Abeesh...

"A shekarun baya babban yarona yayan Abeesh nasan ke kika salwartar masa da rayuwa ta hanyar sadaukar wa...."

Madam Nablah ta ce "kar ka sako wannan yaron a lissafi na domin jinin sa bai mun amfanin komai ba..."

Abul Abeesh ya ce "Ma sha Allah! Jinin sa bazai taɓa miki amfanin komai ba kuwa har abada..."

Madam Nablah ta ce "hakan na nufin yana raye?..."

Abul Abeesh ya ce "hakan na nufin jininsa ya fi ƙarfin ki kamar yanda jinin Abeesh ya fi ƙarfin ki..."

Madam Nablah cikin izzah ta tintsire da wata iriyar dariya.

Abul Abeesh ya ce "yanzu shin wa ye zaki sadaukar a cikin ahalin ki?..."

Ta ce "abu mafi muhimmanci a gare ni..."

Abul Abeesh ya ce "ɗaya daga cikin ƴan ukun ki..."

Ta ce "tabbas wacce ta gagare ni, ita zan sadaukar, biyun kuma zan Aurar da su..."

Abul Abeesh ya ce "kina nufin kice Tasleema?..."

Ta ce "tabbas..."

Murmushi ya yi sannan ya ce "kiji tsoron Allah Nablah, ƴar cikin ki ma bazaki bar ta ba? to ina miki albishir da cewa Tasleema gagarau ce, tanada baiwar da babu yanda zakiyi da ita, jininta guba ce a gare ki..."

Madam Nablah ta ce "banida lokacin sauraronka, inada meeting da zan gudanar a Devil's World, idan na kammala zan dawo ta nan..."

Hular da ɗauka tare da rufe masa fuska, sannan ta kashe hasken wurin ba tare da ta haura ba ta ɓace ɓatt...

Tasleema har ta saddaƙar da cewa Mommynta ta kama ta domin a halin yanzu bata da ƙarfin jikin da zata haura zama ta fita daga cikin wannan kogon, ganin duhu ya biyo baya kuma babu motsin kowa yasa ta ƙara sa sauƙowa, jiki ba ƙwari ta lalumi yanda hasken yake ta kunna, idonta akan Abul Abeesh dake rufe da hula,
a hankali ta taka wurin da yake a zaune tasa hannu ta buɗe masa fuska,
A hankali ya ɗago da kansa idonsa ya sauƙar kan Tasleema wacce take tsaye itama idonta akan sa, a hankali ta durƙusa a gabansa hawaye ne yake ta gangaro mata cikin kakkarwar murya ta furta "waye kai?..."

Abul Abeesh cikin mamaki ya furta "tsawon shekara da shekaru babu wanda ya taɓa shigo wa nan sai iya mai mallakin wurin, yau an wayi gari wata ta shigo ba tare da sanin shugabar wurin ba, shin bakya tsoron abinda zai faru dake idan aka gano ki?...."

Tasleem tana kuka ta ce "kana nufin kace kai ne mahaifin Abeesh? daman kana raye baka mutu ba?..."

Abul Abeesh ya ce "na mutu a idon mutane amma a zahiri ina nan tsawon shekara ashirin..."

Tasleem ta ce "mahaifiya ta ba ƙaramar munguwar azzaluma ba ce, naji na tsane ta sosai, idan ina ganin wasu abubuwa a cikin mafarki na ban ɗauka da gaske ba sai yanzu dana tabbatar, banaso na zauna a wurinta saboda na kan ji tana ƙarnin jini, nakan ji zuciyata tana bugawa da zaran na zauna kusa da mungu..."

Abul Abeesh ya ce "hakan yasa take so ta sadaukar da ke, amma ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru dake..."

Tasleem ta ce "Allah ne ya kawo ƙarshen kuɓutar ka shiyasa ya kawo ni har yanda kake..."

Abul Abeesh ya ce "a'a ki bar ni a yanda kika ganni, tinda har Allah ya nuna miki a yanda nake kuma kinsan ina raye wannan ma abun a gode masa ne..."

Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "zan sanar cewa kana raye, Abeesh zai yi farin ciki sosai..."

Abul Abeesh ya ce "kar kiyi kuskuren tafka wannan babban kuskure, idan kika yi haka zakiyi sanadiyar mutuwar ki ne da kuma na ɗana Abeesh, alfarmar da zakiyi mun sannan ki ci moruwar ƙwaƙwalwar ki shine ki nuna baki san komai game da mahaifiyar ki ba, kar ki nuna mata cewa kinsan komai akan ta, kinsan ita matsafiya ce, kar kiyi garajen sanar wa wani cewa ina raye, ki zauna a yanda kike, kar ki nuna wa mahaifiyar ki sauyi domin tanada matuƙar wayo, lokaci guda zata iya gano ki...."

Tasleem ta ce "shikenam nima banason wasan ya fara daga yanzu..."

Abul Abeesh ya ce "ki tafi Tasleem, mahaifiyar ki zata iya ankara yanzu..."

Tasleem a ruɗe take faɗin "shikenam! shikenam!! zan tafi..."

Juyawa tayi ta fara haurawa sama da gudu, tana fita daga ramin ta miƙi yanda da ta zo da gudu duk da duhu ne wurin amma tasan ina ta dosa, tana zuwa bakin ƙofa ta samu a ƙarƙame, ta yi ƙoƙarin buɗewa amma ta kasa, tayi tayi amma ƙofa ko motsi, haka take ta bubbuga ƙofa ko ƙara baya yi ga duhu, tana wannan yanayin har lokaci ya ja, domin yanzu ƙarfe 2 zata yi, Tasleem tana zaune a bakin ƙofa har ta gaji da bugawa, can wani tunani ne ya faɗo mata, lokaci guda ta tuno ta kalmar da mommynta ta furta kafin ƙofar ta buɗu, a zabure ta tashi tare da rufe idanuwanta ta furta wannan kalmar sai ga ƙofa ta buɗe, da gudu ta fice, tana fita ƙofar ta rufe kanta, sauƙe numfashi ta ke sosai na gajiyar da ta sha, sai da ta nutsu tukun hankalinta ya daidaita sannan ta nufi wani wardrobe wanda Madam Nablah take yawan zuwa wurin domin gudanar da wasu tsafin ta, hannu tasa zata buɗe taga a rufe, haka take jan murfin wardrobe amma ta kasa buɗe wa, ƙananun drowowi ta fara buɗe wa tana neman key ɗin wardrobe wanda ya fita daban a cikin sauran wardrobe ɗin ɗakin, wannan kana ganin kasan abubuwa masu mahimmancin gaske ne a ciki domin na darma ne wanda key ɗin sa daban yake, ta gwaggwada key ɗin da ta samu da dama amma yaƙi buɗuwa, jefar da sauran key ɗin tayi ta kama hannayen wardrobe da ƙarfin gaske ta fara ja domin a jikin bango yake a manne bazai iya faɗowa ba, tana cikin ja hannunta ta caku da ƙarfen jikin wardrobe nan danan sai ga jini, a zabure ta sau hannun wardrobe tana yarfe hannun domin ba ƙaramin zogi yake mata ba, jinin da ya zuba daga hannunta ne ya ratsa jikin wardrobe wanda sirrin buɗe ta sai da jini, bazai taɓa buɗuwa ba sai an yanke hannu da jini a jikin wardrobe ɗin, hakan ma sai da jinin mai wardrobe ɗin kuma jinin Madam Nablah yazo daidai dana Tasleem hakan yasa wardrobe ɗin ya karɓi jinin, lokaci guda ya fara ƙoƙarin buɗuwa da kansa....


Madam Nablah tana can Devil's World tare da mutanen ta a ciki har da Shaprees suna gudanar da meeting, lokaci guda Madam Nablah taji kanta ya sara mata, idanuwanta suka juye zuwa ja, babu komai a cikin idanun illa zallar jini, da sauri ta buɗe tafin hannunta tare da ɗago da hannun sai ga video ya bayyana akan tafin hannunta gani tayi an buɗe mata secret wardrobe ɗin ta, a zabure ta buɗe manya-manyan idanuwanta waje waɗanda suke cike da jini, idanuwan sun koma zallar jan jini babu ɗigon baƙi ko fari amma bata ga wanda ya buɗe ba, iya cikin wardrobe aka nuno mata wanda ba ita ta buɗe ba....

Kallon mutanen ta tayi sannan ta ce "mun tashi wannan taron domin akwai matsala a yanda nake....



Tasleem ganin abubuwan da suke cikin wardrobe ɗin ne ya ƙara firgitar da ita, abubuwan tsafi ne har da ƴar tsana kusan guda uku, da namijin ɗan tsana an caka masa wuƙa, sai wannan kuma an ɗaure masa kai da igiya, abubuwa na ban tsoro gasu nan kaca kaca, sai wasu kwalabai da suke ɗauke da ruhinan mutane a ciki, Tasleem gani tayi wasu ƙananun halitta sai motsi suke tayi a cikin kwalba kuma kamar mutane amma ƙananu ne sosai domin a cikin kwalba suke,
Tasleem ba ƙaramin razana tayi ba ganin abubuwan nan, bata ankara ba taji kukan kuliya ata bayanta, a ruɗe ta juyo baya ganin kuliyar baƙa ƙirin sai jajayen idanuwa ga ta ƙatuwa sai jowa kanta take, a zabure Tasleem tabi ta gefenta da gudun gaske tana ihu, kuliyar nan haka take sufa tana yowa kanta, duk yanda Tasleem tayi sai kuliyar ta bita, haka suka yi kaca-kaca da ɗakin har tayi nasarar buɗe ɗaki ta fice, nan ma haka kuliyar ta bita, Tasleem ta nufi kitchen itama kuliyar ta bi bayan ta, a ruɗe Tasleem ta ɗauki muciya ta buga wa kuliyar a goshin ta, haka ta fara kwaɗa mata, da taga muciyar bazai mata ba ta lalumo wuƙa ta saita kuliyar ta wurga mata daidai lokacin da kuliyar ta ɓace ɓatt, Tasleem cikin tsoro da firgici haka take sakin numfashi daƙer, da gudu ta fice daga kitchen ta nufi part ɗin su da gudu, tana zuwa ta buɗe ɗaki ta shige tare da rufe wa tasa key tana sakin numfashi na azaba ga yanda gumi ya wanke mata duk ilahirin jikinta, tsayawa tayi tana bin ƴan uwanta da kallo sai shan baccin su suke kowa da gadon sa, toilet ta shige ta watsa ruwa a jikinta sannan ta ɗauro alwala tazo ta tsayar da Sallar lafula, daga wannan lokacin har sallar asuba bata rumtsa ba......



Next Next Next


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 15 to 16



Bayan an ƙira sallar asuba Nasreen ce ta fara buɗe idonta, ganin haske dadau-dadau ne yasa ta buɗe idon gaba ɗaya tare da tashi zaune tana jero addu'o'i, kallon yanda Asmeen take a kwance tayi taga sai sharar baccin ta take, mamaki ne ya mamaye fuskar ta ganin an kunna hasken ɗaki kuma kafin su kwanta sun kashe, za mo wa tayi daga kan gadon zata sauƙa idon ta ya sauƙa akan Tasleem dake zaune akan sallaya, a zabure ta furta "Tasleem..."

Tasleem tana zaune ta haɗe kai da gwiwa sai sharar kuka take tayi, a tsorace Nasreen ta rarrafa kan sallayar tare da rungumar ta tana faɗin "lafiya kuwa Tasleem, meya same ki kike kuka haka? yaushe kika shigo ɗakin?..."

Tasleem gaba ɗaya jikin ta ba ƙwari haka ta kwantar da kanta akan Nasreen tana kuka ba bakin magana...
Gaba ɗaya hankalin Nasreen ba ƙaramin tashi ya yi ba, suna cikin wannan halin itama Asmeen ta farka, duk taruwa suka yi akan Tasleem su na share mata hawaye tare da rarrashin ta,

Asmeen ta ce "ina tunanin ita da Mommy ne kinsan basa shiri..."

End Ads