yake rayawa a cikin ransa, sun kasa fahimtar komai,
Aasmeen ce ta furta "shin me yake faruwa ne?..."
Nasreen ta ce "Nima ban sani ba, amma al'amarin Mom ya fara bani tsoro duk da bamu san komai akanta ba..."
Fuska ɗauke da damuwa idonta ya sauƙa akan Abeesh wanda ya maida kallonsa kansu yana tsaye a saman upstairs ɗin ɗakinsa, bayan sun haɗa ido girgiza mata kai kawai ya yi sannan ya koma room ɗin sa.
Nasreen idonta itama a sai tin yanda room ɗin sa yake ta furta "ina zuwa..." itama ta haura upstairs zata nufi room ɗin Abeesh...
Ita kuma Aasmeen ɗakinsu itama ta haura zata je ta dubo jikin Tasleem....
NEXT NEXT NEXT
UPDATE ZAI RINƘA ZUWA MUKU DA MISALIN ƘARFE 8 NA DARE ....
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 5 to 6
Nasreen ce zaune a kusa da Abeesh a bakin gado cikin tausayawa take kallonsa hannunta akan nashi dake dafe kan cinyarsa, haka take kallonsa yayin da kansa ke kallon ƙasi fuska ba annuri, hannunta ta kai kan haɓar sa tare da ɗago da kansa ta juyo da shi, shima haka ya sauƙar da idanuwansa kan kyakkyawar fuskar ta ba tare da ya furta komai ba, Nasreen cikin sassanyar murya ta ce "Ya Abeesh nasan kana cikin matsala amma ka kasa sanar mun, dan Allah ka sanar mun abin da yake damun ka..."
Kawar da kansa ya yi tare da sauƙe nannauyar numfashi ya ce "Nasreen! kin damu akan sanin matsala ta hakan kuma bashi da wani amfani..."
Nasreen ta ce "ko da addu'a zan taya ka ai..."
Ya ce "ki taya ni da addu'a kawai amma kar ki nemi ki san tashin hankalin da ke tattare da ni, just ki bar ni a yanda kika ganni..."
Nasreen ta ce "Ya Abeesh...."
Ya yi saurin taren bakin ta da cewa "Please Nasreen, na roƙe ki..."
Girgiza kai kawai tayi ta ce "Shikenam ba komai..."
Daga nan ta fi ce daga ɗakin tare da rufe masa, shi kuwa bayan fitar ta wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo masa yana cizan leɓɓen sa....
Nasreen bayan ta koma ɗakin su tarar da Aasmeen tayi zaune a gefen Tasleem wacce ta wuce da bacci.
"Bacci tayi ne?..."
A cewar Nasreen!
Aasmeen amsa mata tayi tana shafan sumar kan Tasleem wacce take bacci.
Gaba ɗaya sleeping dress ne a jikin su bayan sun gama hira ko wacce kwanciya tayi akan gadon ta bayan sun kashe hasken ɗakin.
Misalin ƙarfe 2 na dare Madam Nablah ce take tsaye a jikin wani ƙaton photon mijinta uban triplets ɗin ta, wanda tsayin photon ya wuce tsayin ta sosai, tana sanye da wata baƙar doguwar riga wanda har ƙasi yake ja ta baya, sai da ta gama shafa photon, kan ta a sama tana kallon fuskar mijinta wanda ya juma da mutuwa daga bisani ta rufe idanuwanta ruf, lips ɗin ta na motsi kamar mai karanta abu a cikin ranta nan da nan photon ya rabe gida biyu sai ga wani ƙofa ya bayyano, ƙofar sirrin da ba wanda yasan da wurin, murmushi tayi sannan ta buɗe ƙofar ta shige ciki, ɗakin da ta shiga duhu ne ƙirin baka iya ganin komai hakan ma sai da tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta durƙusa ƙasi tasa hannu ta buɗe wani murfi kamar murfin rijiya nan ta shige cikin ramin tana taka matakala a hankali har ta sauƙa ƙasi, wannan wurin gidan ƙasa kenam domin wurin sai ka ce kogo, hannu tasa ta kunna hasken kogon sai a lokacin haske ya bayyana, Madam Nablah cikin iko da ƙasaita ta jawo wani kujerar gefenta ta zauna a gaban wani dattijon bawan Allah wanda ta ɗaɗɗaure shi da igiyar kaca akan kujera ga ta rufe masa fuska da baƙar hula, ƙafa ɗaya ta ɗora akan ɗaya tana wani irin shu'umin murmushi, lokaci guda tasa hannu ta fizge hular fuskar tare da watsa masa ruwa akan fuska, a ruɗe bawan Allah yake fitar da numfashi kansa ya kasa tsayuwa wuri ɗaya tsabar azabar yau da kullum tsawon shekaru 25 yana cikin wannan kogon a haka, ga fuska cike da farin gemu da duk jikinsa daga shi sai gajeren wando a jikinsa.
Madam Nablah cike da izzah ta furta "Abu Abeesh..."
Dattijo murya na kakkarwa yake faɗin "Nablah na roƙe ki da wannan azabar da kike mun tsawon shekaru ki kashe ni haka na huta, duk da nasan wannan matsalar da kika shiga ba yin kan ki bane, a koda yaushe ina sanar miki cewa ƙwaƙwalwarki baya tattare da ke, akwai wanda yake juyar miki da tunani a koda yaushe, amma nasan duk abinda zan ce miki bazaki saurare ni ba saboda ke ɗin ba asalin Nablah mu bace, ke baƙar Aljana ce kike jikin Nablah mu har ku ka yi amfani da ruhinta ta kashe mijinta wanda take tsananin masifar so da ƙauna, Insha Allahu asalin Nablah zata dawo da ƙarfin addu'o'in da muke mata a koda yaushe...."
Madam Nablah cikin tsawa ta furta "dakata haka Abu Abeesh wa ya sanar maka cewa ni ba Nablah ba ce? tabbas kamar yanda kake fa ɗa kullum cewa an sauya ƙwaƙwalwar Nablah haƙiƙa hakane, amma inaso na sanar maka cewa yanzu wannan ƙwaƙwalwar shaiɗanu ta zama na Nablah, wancan ƙwaƙwalwar kumaaaa...."
Nan ta tintsire da wani irin shu'umemmen dariya har idanuwanta suna farfatsin wuta.
Abu Abeesh girgiza kai ya yi yana faɗin "Insha Allahu bazaki gama da duniya lafiya ba shaiɗaniyar baƙar Aljana, ki sani zaki mutu ne kuma mutuwar wuta..."
A fizge ta miƙe tsaye tana faɗin "babu yanda za'a yi nayi mutuwar wuta Babban Malami domin ni kaina wutar ce mai ƙona duk wanda naso..."
Ta ƙarasa maganar tana wurga masa wutar tsafi daga cikin tafin hannunta, kamar kullum dai tsafin ta baya aiki akan Abu Abeesh, duk tsafin da zata mishi baya kama shi.
Murmushi ya yi sannan ya ce Nablah kenam kar fa ki manta ni ne mai kama Aljanu na ɗaure su sannan babu tsafin aljanin da zai yi mun aiki a jiki, hakan yasa na gagare ki baki da wani zaɓi sai ɗaure ni da kika yi anan kogon..."
Cikin izzah ta ce "in da ka gagare ni shin meya hana ka gudu tsawon shekaru a cikin tarko na, Babban Malami babu abinda zaka iya mun sai dai ka ƙare rayuwar ka a cikin ƙunci da damuwa..."
Abu Abeesh murmushi ya yi tare da faɗin "ban damu da halin da nake ciki ba ni dai roƙo na a gare ki shine kada ki cutar mun da yaro na Abeesh..."
Ta ce "Yaron ka Abeesh yana nan cikin ƙoshin lafiya, sai dai kuma yasa a ransa cewa baka raye a duniya na gama da shafin ka..."
Daga nan tayi wani tsafi madubi ya bayyana sai ga Abeesh akan sallaya yana ta jero addu'o'i.
Murmushi Abu Abeesh ya yi sannan ya ce "ina alfahari da kai yaro na Abeesh, ka cigaba da ibadar ka wata rana zaka ci nasarar rayuwa, zaka ci nasara akan maƙiyan ka..."
Ya ƙarisa maganar idonsa akan Madam Nablah, itama katsar da video tayi ta juya zata tafi taji ya furta
"Ɗan uwana Ƙanina kuma Mijinki yana kwance a cikin kabarin sa yana Allah wadar da Shaiɗanun da suke jikin ki..."
Murmushi Madam Nablah ta yi sannan ta ce "babu Shaiɗanun dake jikina domin ni shaiɗaniyar kaina ne, sai dai ƙwaƙwalwar baya ba irin ta yanzu bane..."
Ɗaukar hular tayi ta rufe masa fuska sannan ta haura sama ta rufe kogon tayi tafiyar ta....
Washegari da safe kowa ya hallaru a dinning za'a yi breakfast Madam Nablah da iyalan ta daga baya sai ga Abeesh shima ya fito ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun wurin, Madam Nablah ita da kanta ta zuzzuba musu a plate kamar yanda ta sa ba kullum idan tana nan, bayan ta kammala itama zama tayi idonta akan Abeesh ta ce "miyasa bazaka gaishe ni ba?..."
Abeesh kan sa a gefe ko kallon yanda take bai yi ba, ganin ta ishe shi da ƙorafi yasa shi tura plate ɗin baya ya miƙe zai bar wurin Nasreen dake gefensa tayi saurin riƙo hannunsa idonta akan sa sai faman girgiza masa kai take tare da zaunar da shi, zama ya yi idonsa akan Madam Nablah ya ce "idan kika ƙara mun magana bazan ci girkin ki ba, kowa ya zauna a matsayinsa..."
Madam Nablah idonta akan plate ɗin abincin ta sai faman caccakan plate take da spoon fuska ɗauke da murmushi, bata ƙara furta komai ba har suka kammala.
Tasleem da Nasreen da Aasmeen sun gama shirin su zasu wuce school har sun nufi bakin ƙofa suka ji Madam Nablah ta furta "Waye Ayub?..."
Gaba ɗayan su daskare wa suka yi a wurin jin tambayar da Momminsu tayi, kallon juna suka shiga yi Nasreen da Aasmeen tinda suka kalli juna babu wacce ta ƙibta ido, ita kuwa Tasleem kanta a ƙasi domin tasan wannan tambayar a iya su biyu ake yi bai shafe ta ba.
Madam Nablah ƙiran sunan Nasreen tayi ta ƙara maimaita wa tana faɗin "Waye Ayub?..."
Nasreen cikin tsoro da fargaba ta ce "am am Mom wani ɗan school ɗin mu ne..."
"Meye alaƙar dake tsakanin ku?.."
A cewar Madam Nablah.
Nasreen ta ce "Mom friend ɗina ne, shi yake mun assignment idan na kasa..."
Jinjina kai kawai tayi sannan ta ce "ku je, sai kun dawo..."
gaba ɗaya fice wa suka yi kai tsaye wurin parking suka nufa sai da suka zaɓi wata tsararriyar mota ƙirar jeep suka fita, Tasleem ita ce mai yin driving...
Shima Abeesh fito wa ya yi cikin shirin sa zai wuce wurin aiki can hospital, haka yazo ya wuce ta gaban Madam Nablah zai fita, murmushi ta sau tana ƙare shi da kallo daga bisani ta ce "sai ka dawo my Son..."
Ko kula ta bai yi ba ya yi ficewar sa....
*SCHOOL*
Tana zaune a cikin class ita kaɗai bayan gama lecture tana rubuta assignment, bata ankara ba taji an furta
"Amincin Allah ya tabbata a gareki ya sarauniyar kyawawa..."
Daga nan shima ya zauna akan kujerar gefenta tare da ɗora hannunsa akan nata wanda take rubutu da shi,
Zuciyar ta ne kawai yake haurowa ta ma rasa wani irin hukunci zata aiwatar, fuskar nan ba annuri ko kaɗan, ga dara-daran idanuwa waɗanda suka kaɗa suka yi ja kamar wata iska haka ta juyo a slow ta sauƙar da zararrun idanuwan ta akan fuskar Ayub tare da zabga masa wasu irin rikitattun mari akan fuskar sa har sau biyu, babu shiri haka ya miƙe a tsorace yana riƙe da fuska yanda ta mare shi, yana sauƙar da numfashi cikin tsoro yake girgiza kai tinin gumi har ya wanke masa fuska yana faɗin "No no no wannan ba Nasreen ba ce Tasleem ce, tabbas wannan Tasleem ce, a hargitse ya kalli yanda abokansa suke a gefe guda su uku ya ce "ku ka ce Nasreen ce a zaune anan?..."
Ɗaya daga ciki ya ce "to ina zamu gane alhalin duk kamannin su ɗaya kuma yau kaya iri ɗaya suka sanya..."
Ayub ya ce "ta ya zaku haɗa fuskar Nasreen da wannan mai fuska kamar jahannama..." juyowar da zai yi ya ga sun haɗa ido, ganin irin kallon da take jifansa da shi ne yasa shi faɗin "Kun ga mu tafi, muje mu lalumo Nasreen..."
Su na fita suka fara sakin dogon numfashi ɗaya daga ciki ya ce "anya wannan bata da Aljanu?..."
Ayub ya ce "Tasleem ai bata shiri da kowa, ko ƙawaye bata da su saboda inaga bazata rasa abokan Aljanu ba..."
Su na cikin tattaunawa sai ga wani ya zo wuce wa ya ce "Ayub ya kake tsaye anan ga can Nasreen tana zaman jiran ka..."
Ya ce "Aina?..."
Acan kan lilo tana karatu.
Daga nan suka nufi wurin, su na zuwa suka tarar da ita tana ta lilo da littafi a hannun ta, tsayawa ya yi ta bayan ta yana taya ta lilawa, da sauri ta juyo tana son ganin wa ye a bayan ta ganin Ayub ne ya sa ta sakin dariya tana faɗin "Ayub kai ne?..."