aikin kansa yayi har ya shigo class, security sun ɗauka turo shi aka yi, shima waje akayi da shi....
Tasleem zama tayi akan wani dakali tayi tagumi sai hawayen dake zubo mata, gani tayi an miƙo mata white handkerchief, ɗago wa tayi tana kallon wanda ya miƙo mata handkerchief ganin wanda yayi mata sanadiyar exam ɗin ta ne yasa ta miƙe tsaye a zabure tsabar tashin hankalin da ta shiga gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa mai zata masa haka ta ɗago da yatsar ta tana nuna shi tare da faɗin "waye kai? daga ina kake? wa ya turo ka wuri na? kazo ka ruguza mun gobe na, shin kana da matsala dani ne? bazan yafe maka ba, ka fita a harƙata...."
Amaar gaba ɗaya bai ji daɗin halin da Tasleem ta shiga ba, ji yake zuciyarsa tana masa raɗaɗi, ganin zubar hawayen ta tamkar ana sauya masa tunani ne, jin sautin kukan ta tamkar ana hura masa wuta ne a cikin zuciyar sa,
A hankali ya furta "Please...."
A tsawace ta daka masa tsawa tana faɗin "ka riƙe Please ɗin ka, babu abinda zaka ce mun, kaima kana ɗaya daga cikin maƙiya na kenan?..."
Girgiza kai tayi tare da barin wurin da gudu,
Shima bin bayan ta yayi, tana gudu yana binta har ta fice a cikin makarantar ba tare da ta ɗauki mota ba, tana tafiya har ta hau kan titi, bata sani ba har ta je tsakiyar titi sauran kaɗan mota ya buge ta Amaar ya yi saurin riƙo hannun ta ya jawo ta, jin shocking yasa Tasleem rausa ihu ta fizgi hannunta daga nashi tayi saman ƙwalta a ruɗe zata faɗi Amaar ya rungumo ta duk da shocking da yake ratsa shi amma bai bar ta ba saboda tseratar da rayuwar ta, basu san lokacin da suka gangara ƙasin ƙwalta ba yana rungume da ita haka jikin su yake kakkarwa kamar ana jona musu electric, a ruɗe suka rabe da juna kowa ya kama gefen sa, ihun Tasleem ne ya jawo hankalin kowa zuwa kan su, kafin kace mai mutane har an taru, Tasleem kamar mahaukaciya ta miƙe tana sossosa jikinta ji take kamar ana hura mata wuta a jikin ta, ba shiri ta jefar da takalmin ta da gyalen da ta yafa sai gashin kanta da ya baje akan gadon bayan ta haka ta cigaba da gudu akan titi tana ihu, gaba ɗaya babu hankali a tattare da ita, haka kanta yake juyawa ko gabanta bata iya gani...
Amaar tinda ya kwanta bai motsa ba yana jin yanda jikinsa yake ta zogin wuta kamar wanda ake hura masa wutar, yana cikin wannan halin sai ga wani mota ya parker a bakin titi, wani soja ne ya nufo yanda yake da gudu...
Tasleem tana cikin gudu sai ga motar su Nasreen ta tsaya a gaban ta, da sauri su ma suka yo kanta su ka riƙo ta tare da jan ta cikin mota, nan da nan suka nufi gida....
Bayan sun koma gida Nasreen da Asmeen ne suke riƙe da Tasleem sun saka ta a tsakiya, a falo suka tarar da Madam Nablah da Shaprees,
Madam Nablah tana ganin su a wannan halin ta miƙe tsaye a zabure tana faɗin "what's wrong with her?..."
Nasreen ta ce "Mom mu dai abinda muka sani shine an kore ta a exam hall sakamakon samun ta da cheating exam amma mun san sharri aka mata, daga nan bamu san komai ba sai ƙiran mu da akayi a waya aka sanar mana cewa tana kan titi tana ihu..."
Tasleem yanda kasan mahaukaciya gashin kanta duk ya tawarwatse sai kuka take tayi tana dudduba jikinta tare da faɗin "ji nake wuta yana cin jikina, wuta ne yake ta cin jikina..."
Madam Nablah idonta akan Tasleem ita kaɗai tasan mai take kallo, abun mamaki ya bata ganin sihirin wuta a tattare da Tasleem, kuma wutar na tsafin ta, dogon tunani ta shiga yanda akayi tayi wa Tasleem asirin wuta, lokaci guda ta furta "AMAAR..." a cikin ranta domin ta tuna lokacin da tayi musu asirin raba gangar jikin su ta hanyar amfani da shocking na wuta, cikin fargaba take furta "ya akayi yanzu kuma sihirin wutar ya dawo gare ta? wanda sai sun haɗa jiki kafin wutar yayi amfani kuma yanzu bata tunanin Amaar yana raye balle su haɗa....
Madam Nablah dawo hayyacinta tayi daga dogon tunani idonta akan Tasleem ta sanar wa Nasreen cewa "ku wuce da ita can ɗakin ku...."
Haka suka wuce tare da haura upstairs.....
Tasleem zama tayi a akan gadonta tana faɗin "zogi nake ji, wuta ne fa yake ta cin jikina, waye shi ɗin? daga ina yake?..."
Nasreen addu'o'i take ta tofa mata ko zogin zai ragu mata, suna cikin wannan halin sai ga Madam Nablah ta shigo tana riƙe da wani glass cup, zama tayi a kusa da Tasleem tare da miƙa mata cup ɗin ta ce "kar ɓi ki sha, zaki daina jin ƙunar wutan..."
Tasleem karɓa tayi takai bakin ta zata sha, ta tuno da kalar tsafin da Mommyn ta take yi, tana tsoron kar ta mata tsafi a cikin ruwan, a ruɗe ta ɗago kanta ba tare da tasha ruwan ba, ta miƙa wa Madam Nablah cup ɗin ta tashi da gudu ta shige toilet, tana shiga ta kunna shower a kanta, haka ruwa yake ta zuba, ta ɗau tsawon minti 15 a cikin ruwan, fuskar Amaar ne yake ta mata gizo, ta kasa daina tambayar zuciyar ta waye shi ɗin? daga ina yake?...."
*NEXT NEXT NEXT.....*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 17 to 18
Tasleem sai da ta watsa ruwa a jikin ta kafin taji sanyi a ranta...
Bayan sati guda da kammala Exam itama Tasleem Mommyn su taje har makarantar tayi magana an dawo da Tasleem ta ƙarasa exam ɗin ta cikin sauƙi...
Yau ranar hutu ne duk sun hallaru a falo hatta Abeesh shima a zaune yake a falo yana danna computer sa, Nasreen da Asmeen kuma suna zaune su na kallon plasman, Tasleem kuma tana kan dinning table da cup ɗin Lipton a gaban ta sai pressing phone ɗin ta take, su na cikin wannan yanayin sai suka ji an fara knocking, Asmeen ta bada umarnin shigo wa, turo ƙofa akayi security ya sanar cewa "mai feshin maganin sauro da ƙwari ne ya zo..."
Nasreen ta kalli Asmeen ta ce "wa ya turo mai feshi kuma?..."
Asmeen kafaɗa ta ɗaga alamar bata saniba itama, suka kalli Tasleem tare da faɗin "Oganniya ke kika turo shi?..."
Tasleem sai da ta kurɓi ruwan tea kafin ta basu amsa da cewa "Oganniya tana can room ɗin ta, sai ku je ku tambaye ta..."
Security ya ce "Indai babu wanda ya turo shi bari na je na kore shi..."
Nasreen ta ce "Ya Abeesh ko kai ka turo shi?..."
Abeesh yana zauna ya ce "kin dai san bana shiga shirgin gidan nan..."
Nasreen kallon Security tayi sannan ta ce "ka ce ya shigo wata ƙil Mommy ce ta ƙira shi..."
Security ya ce "Ok..." sannan ya fice...
Bayan wasu mintina sai ga wani matashin mutum ya shigo falon da sallama a bakin sa, duk amsa masa suka yi tare da kallon yanda yake yana sanye da facemark a fuskar sa, kayan jikin sa irin na ƴar feshi yana ɗauke da abun feshi akan kafaɗar sa,
Sai ga Madam Nablah itama ta sauƙo daga saman room ɗin ta tana riƙe da key ɗin mota tana son fita unguwa, ganin mutum a tsaye yasa ta tsayawa tana ƙare shi da kallo ta ce "from where?..."
Nasreen da Asmeen sun yi mamakin tambayar da mommy tayi masa domin a tunanin su ita ta ƙira shi,
Mutumin kuwa yana tsaye zuciyarsa ce take ta faman bugawa domin Madam Nablah ba ƙaramin tsoro ta sanyawa zuciyar sa ba tin yana yaro ƙarami, ƙarfin tsafin da take amfani dashi ya so yafi ƙarfin ƙwaƙwalwar sa, murya ciki-ciki ya ce "am nima turo ni akayi akan nazo nayiwa gidan nan feshin ƙwari..."
Madam Nablah ta ce "iya aikin da kake yi kenam?..."
Girgiza kai ya yi sannan ya ce "eh a'a ehhh ina gyaran nepa da sauran abubuwa..."
Ta ce "okay dalilin da yasa na tambaye ka kenam, daman inaso naji ko kana gyaran wutar nepa inaso zaka gyara mun wutan ɗakunan gidan nan..."
Mutumin da yayi covering fuskar sa da face mark ya ce "okay ba damuwa..."
Madam Nablah ta kalli yanda Nasreen take zaune ta ce "a ɗakunan gidan nan ina ne wutar ta ɓaci?..."
Nasreen ta ce "Mom nepar ɗakin wardrobe ɗin mu ya lalace, sannan na ɗakin Yaya Abeesh nan ma ya lalace sai kitchen, ina tunanin iya su ne...."
Madam Nablah kallon mutumin tayi sannan ta ce "yau kayi na feshin gobe kuma sai ka dawo kayi gyaran nepa...."
Jinjina kai yayi tare da faɗin "okay Maadam..."
Sannan ta miƙi hanyar fita tana faɗin "ku kai shi yanda zai yi aikin feshin, duk wani lungu ya feffeshe wurin..."
daga nan tayi ficewar ta.
Asmeen ce ta miƙe tana faɗin "muje na nuna maka..."
Idonsa kuwa akan Abeesh yanda yake ta daddanna computer, Asmeen tsaya wa tayi a gaban sa tana faɗin "lafiya kuwa? Malam mai feshi ina ta maka magana..."
Amaar hannu yasa tare da janye face mark ɗinsa, Asmeen cike da mamaki ta buɗe baki ta ce "Ɗan uwaaaa..."
Nasreen jin haka yasa ta ɗago itama ganinsa yasa tayi saurin miƙe wa tana faɗin "laaa kai ne a gidan mu Ɗan uwaa, meya haɗa ka da feshi kuma?..."
Da sauri Amaar yayi mata alamar tayi shiru saboda Abeesh yana wurin...
Nasreen murmushi tayi tare da faɗin "kar ka damu Ɗan uwa, Ya Abeesh bashi da matsalar komai, kuma baya shiga abinda bai shafe shi ba..."
Asmeen tayi saurin cewa "Ɗan uwa wannan shine Yayan mu kuma shine wanda Nasreen zata Aura, ba ruwan sa, shi ɗin salihi ne..."
Amaar ya kasa daina sakin ƙayataccen murmushi, idonsa akan Abeesh,
Abeesh yana jinsu amma ya kasa ɗagowa, sai gani ya yi an miƙo masa hannu, Abeesh kallon hannun ya yi tare da kai idonsa kan fuskar Amaar sai murmushi yake ta sau masa, shima murmushin yayi tare da miƙa masa hannu suka gaisa.
Juyawar da zai yi ya hango Tasleem tana zaune akan kujerar dinning ko kallon yanda suke bata yi ba, nufan yanda take yayi yana zuwa ya ce "hello akwai sauro a yanda kike ne?..."
Shiru Tasleem bata bashi amsa ba, tana magana a cikin ranta "lallai wannan ba ƙaramin rainani ya yi ba, haka kawai ina zaune zai wani mun yi bahagon tambaya..."
Ba tare da ta bashi amsa ba ta miƙe tana mai jan dogon tsaki zata bar wurin, miƙewar da tayi kwatsam idanuwanta suka sauƙa akan fuskar Amaar, wani irin kallo take masa sama da ƙasa daga bisani tasau murmushi itama tana faɗin "kafin ka kora mun sauron wurin, ka fara wanke dattin jikin ka...." ta ƙarasa maganar tana mai ɗaukan cup ɗin ruwan tea ta ɗaga sama tana tsiyaya masa a tsakiyar kansa, haka ruwan tea yake zubo masa ta fuska har cikin rigar sa, ba abinda ya ji a ransa sai ma ƙara tu sa ta da yayi a cikin zuciyar sa, haka yake ta sakin murmushi a hankali ya furta "ke ɗin ta musamman ce, duk abinda kika yi dai dai ne, kuma fushin ki na ƙara miki kyau sosai da sosai...."
Nasreen a cikin ranta take faɗin "tabbas akwai alamar tambaya a tsakanin su..."
Asmeen ta ce "Ɗan uwaa daman ƙaunar ƴar uwar mu kake shiyasa a supermarket kake tambayar ta?..."
Tasleem fuska a murɗe ta wurga wa Asmeen harara, cikin fushi ta bar wurin, har zata haura saman upstairs taji Amaar ya furta "I love you Tasleem, ina matuƙar ƙaunar ki..."
Tasleem tsaya wa tayi tana sauraron sa zuciyar ta ce take ta hargutsuwa, ji tayi bazata iya haƙura ba haka ta juya da gudu ta nufi yanda yake zata shaƙo shi, shi kuwa ganinta yasa ya ware hannayensa biyu tare da faɗin "come and hug me..."
Sai da ta zo dab da shi ta ja burki domin ta tuna shi da zaran ta taɓa shi wuta ne yake cin jikin ta, tsaya kallon sa tayi daga bisani ta furta "waye kai?..."
Yana murmushi ya ce "I'm your lover..."
A tsawace ta ce "shirmen banza, idan baka sanar ko kai waye ba sai na shaƙe ka..."
ta kai hannun ta kusan wuyansa kamar zata shaƙe shi ta fasa, girgiza kai tayi tare da juyawa ta nufi upstairs, haurawa tayi ta shige room ɗin su...
Amaar kamar zai yi kuka haka yake bin ta da kallo, tsananin tausayinta yake sakamakon abinda ya faru dasu tin basu mallaki hankalin kansu ba.
Nasreen ce tayi magana ta ce "Ɗan uwa me yake faruwa ne?..."