da akwatin. Ya kura wa fuskar mai kwance a ciki ido, kodayake an daɗe da rasa numfashi, amma kwanciyar fuskar da sakon ruhi da Miemie ke aika masa suna tada jinin jinƙai da mamaki.
“Ya kamata a kawo ƙarshen wannan duhu,” Miemie ta ce, tana matsowa kusa da akwatin. Ta ɗauko wata ƙaramar ƙaho wacce ke haskawa da ruwan zinariya, ta zuba ruwa a jikin akwatin.
Sai kuma wani abu ya fara girgiza…
Kwatsam, sai jikin gawar ya fara fitar da haske – haske mai launin shuɗi mai ƙyalli – da kamar wani abu yana ƙoƙarin farka daga dogon barci!
Gaba ɗaya suka miƙe tsaye da firgici, Asmeen ta tsaya jikin Shaprees...
Miemie ta juya tana fadin:
“Ruhi yana da ƙarfi idan aka kashe shi da zalunci. A yau, wannan ruhi zai ɗan farka — domin ya bada shaidar gaskiyar da kika ɓoye.”
Madam Nablah ta ja baya tana girgiza kai tare da faɗin:
“A’a, ba zai iya farfaɗowa ba! Na kulle shi da jinin kansa! Na ƙulle shi da alkawari da tsafi!”
“To," inji Miemie, "da haske muke warware duhu.”
A wannan lokacin aka fara jin muryar mutumin da ke cikin akwatin, yana fadin...
“…Nablah... me kika yi min…? Ƴaƴana… Ina ku ke, ina son ganin ƴaƴana…”
Asmeen ce ta fashe da kuka, haka Amaar Idanun sa biyu na cike da ƙwalla — suna kallon jikin mahaifinsu wanda tsawon shekaru suka rayu ba tare da saninsa ba...
Kuma Tasleem — ita ce kawai ta san da wannan sirri… amma yanzu tana ɓoye a wani ɓangaren duniya da babu wanda zai iya ganinta.
A nan labari ya ƙara ɗaukar sabon salo.
Madam Nablah ta fara girgiza tamkar mai hauka. “Ku tafi! Ku barni! Baku fahimta ba, banyi hakan don son raina ba!!”
Miemie ta kalle ta da murmushi mai taushi amma mai nauyin hukunci ta ce:
“Kina da sauran damar tuba... Amma gaskiya ba zata ƙyale karya ta cigaba da mulki ba.”
Falon ya yi tsit, kowa na kallon akwatin da Miemie ta bayyana. Cikin ɗakin akwai Amaar, Asmeen, Shaprees, a cikin wannan falo akwai wata zuciya wadda ke shirin fashewa da tsoro wato Madam Nablah...
Suna cikin wannan halin
Sai ga takun ƙafafu da numfashi mai nauyi yana karatowa daga saman beni. Kafin kowa ya gane me ke faruwa, sai ga tsohon mahaifin su Amaar, ya shigo cikin rawar jiki da hawaye a idanuwansa. Ya durƙusa a gaban akwatin, yana kallon fuskarsa cikin halin da ba'a taɓa ganin sa ba.
Yana faɗin:
"Ahmed..." ya furta da kyar, yana maimaita sunan.
"Kai ne? Kai ne ƙanina da na rasa shekaru ashirin da suka shuɗe? Nablah... me kika yi masa?!"
Kallon kowa ya koma gareta. Miemie ta ɗan matsa gefe, tana kallonsu cikin nutsuwa kamar wata sarki mai hukunci.
Madam Nablah kuwa ta kasa motsawa. Sai idanuwanta suka haɗu da na tsohon mijinta cikin akwatin—mutumin da ta kashe saboda ya gaza amincewa da shaidanci da muguntar ta. Tsohon mijin da ta ɗaure da sihiri, sannan ta ɓoye gawar tasa a ƙarƙashin wani lungu na gidan da babu wanda ke iya ganowa.
Asmeen ta shige jikin Shaprees tana hawaye.. Amaar kuwa ya ɗan matso kusa da mahaifinsa, yana kallon gawar mutumin – ƙanin mahaifinsa da aka kashe a asirce.
"Wannan gawar... shi ne mahaifin su Tasleem, Nasreen da Asmeen?" Amaar ya furta da mamaki.
Miemie ta jinjina kai tare da faɗin
"Na kwance sihirin da aka ɗaura a jikinsa. Ya cancanci a girmama shi, ba a ɓoye shi cikin duhu ba. Amma akwai wata ƙarin asiri da ba a saniba..."
Shaprees ya ɗago kansa da sauri, zuciyarsa na harbawa. Madam Nablah na nan zaune, ba ta motsi kamar wanda ruwa ya cinye, amma idanunta sun cika da wani irin ƙiyayya da tsoro na ɓoye gaskiya.
"Wace irin halitta ce ke, har za ki aikata haka ga mijinta?"
Abul yace, yana girgiza kai, yana mai tuna irin soyayyar da Ahmed ya nuna wa matarsa – amma a ƙarshe, ta ƙare da kisa....
Amaar ya matso kusa da Miemie ya ce:
"Kina da ikon gaya mana gaskiyar komai yanzu, ko akwai wani abin da har yanzu ana ɓoyewa?"
Miemie ta kalli Amaar, sai kuma ta juyo zuwa ga Madam Nablah. Sai ta ce da ita:
"Na bar wannan dama a hannunki. Kifadi gaskiya da bakinki, ko kuma ni da hasken ruwa na mu karasa tone komai..."
A cikin falon da aka cika da zazzafan numfashi, hasken Miemie na kara kyalli a tsakiyar dakin, sai aka ji tamkar duk iska ta tsaya. Idanun kowa sun zube kan Madam Nablah, wadda yanzu zuciyarta ke dukan ƙirjinta kamar za ta fasa. Kamar ba ita ba — uwar da ta jima da ɓoye gaskiya, da ɓoye jikin mijinta na tsawon shekaru, yanzu tana cikin fargaba tamkar wani ƙwararren ɗan laifi da aka cafke a wurin laifi.
Amaar yana kallonta, yana ɗauke da tambayoyi a idanuwansa....
"Ki faɗi gaskiya yanzu!" inji Abul murya na ɓarke da ɗaci. "Me kike da shi a wannan lokacin? Me ya faru da ɗan uwana?"
Madam Nablah ta ƙi kallon kowa. Sai dai ta ja tsaki ga taurin kai, ta ɗaure fuska ta ce:
"Kuna so ku ji gaskiya? To ku saurara..."
Sai ta tashi tsaye. Ta ɗan gyara mayafinta kamar wata sarauniya da ba ta yarda ta sunkuyar da kai ba, duk da an kama ta da laifi.
"Ahmed ya yi kuskure. Na so ya bani ikon mulkin ruhin aljanu da sirrin nasaba... amma ya ƙi. Ya ce ba za a haɗa duhu da haske ba. Na gargaɗe shi, ya ƙi sauraro. Kuma saboda ƙin yarda da ikon da na samu, na kawo ƙarshen sa. Na kuma ɓoye gawarsa a ƙasan gidan nan domin kada wani ya san cewa ni ce na kashe shi."
Zuciyar kowa ta ɗauki bugawa. Asmeen ta rufe fuska da tafin hannu. Shaprees ya ɗan jinjina kai, yana jin tsantsar muguntar da ke cikin zuciyar matar da har yanzu ba ta da kunyar bayyanar gaskiya.
"Kin kashe mijinki?" Miemie ta furta cikin daƙilewar murya. "Kin hana 'ya'yanki su san yanda uba ke nan? Kin ɓoye rai da gaskiya saboda kuɗi da iko?"
Madam Nablah ta saki murmushin ƙiyayya. "Ni Sarauniya ce. Kuma Sarauniya ba ta roƙon gafara. Ban taɓa nadama ba. Duk wani da ya tsaya a gabana, to ya sha keɓaɓɓen hukunci."
Kamar wuta ta faɗa cikin zuciyar Abul mahaifin su Amaar. Ya juya da sauri ya kalli Miemie yana faɗin:
"Kada ki bar wannan ta tafi ba tare da an hukunta ta ba!"
Amma Miemie ta ɗan dafe ƙirji, sannan ta kalli Amaar da Asmeen da Shapreen ta ce:
"Hukuncin wannan ba daga gare ni zai fara ba. Sai zuciyar 'ya'yanta da danginta sun gane hakikanin darajar abin da suka rasa."
Nan take wata guguwa ta shigo cikin falon – amma ba iska bace – ruhi ne mai sanyi, mai tsarki, mai haske, wanda ya dudduba kowa ya shiga jikinsu kamar wani abun lura. Nan take kowa ya fara ganin hoto a zuciyarsa – na kisan Ahmed, na ƙiyayya da fushin Madam Nablah, da irin sihirin da ta taɓa yi.
Sai Amaar ya ɗauki numfashi mai zurfi. Ya ce da Miemie:
"Duk wannan... amma Tasleem ba ta cikinmu. Shin akwai alaƙa tsakanin abin da Madam Nablah ta ɓoye da ɓacewar Tasleem?"
Miemie ta jinjina kai a hankali.
"Wani ƙarin sirri yana jiranku... Kuma har sai kun nemi da gaske, za ku gano."...
Cikin ikon Allah duk abinda ke faruwa Nasreen tana cikin tafkin ruwan MIEMIE tana kallon duk abinda ke faruwa a gidan su, domin Miemie ta bar mata wani madubi yanda zata na ganin video abinda ke faruwa, itama tana nan sai rausa kuka take tana Allah wadai da halin mahaifiyar su, har Idanunta sunyi jawurr....
Itama Tasleem Miemie ta san dabarar da tayi ta bayyanar mata da video abinda ke faruwa ba tare da sanin Madam Nablah ba, Tasleem tana zaune a ɗaure tana ganin abubuwan da ke faruwa, ga mahaifinsu da basu taɓa gani ba yau ya bayyana a matsayin gawa, tasha kuka itama kamar ranta zai fita....
Daga cikin numfashin duhu da tsantsar ruɗani, dakin falon gidan Madam Nablah ya shiga shiru mai nauyi. Miemie ta ɗan yi tsuru-tsuru da idanuwanta masu hasken ruwa, sannan ta juya ta kalli Amaar wanda zuciyarsa ke ƙuna da rasa ƴan uwansa da kuma mamakin makircin Madam Nablah.
“Wannan gawar,” Miemie ta nuna akwatin da Ahmed ke kwance ciki, ta ce:
“ba kawai jikin mataccen mutum bane. Wannan wuri da aka binne shi ya zama makabarta ce ta ƙiyayya da sihiri, soyayya da jinƙai.”
Madam Nablah ta yi dariya mai sauti, tana takawa a hankali kamar wata zakanya mai jin ƙarfinta.
“Gawarsa tana nan, so what? Kwana nawa zai canza rayuwar ku? Ko dai na kashe, ko dai na ɓoye – amma na rayu, kuma ina da iko!”
Sai wani abu ya girgiza cikin falon. Tagogi suka fara motsawa. Fitilun ruwan hoda suka ɗan ɗauke, sannan aka ji murya – kamar ta sama, mai sanyi da mai nauyi:
Ruhin Mahaifin su Tasleem ne ke magana yana faɗin:
"Ba wanda ya mallaki zuciyar duniya. Ko kin kashe gaskiya, za ta dawo da rai. Kuma ko kin ɗaure sirri, dare zai zo da rana."
Gaba ɗaya suka zuba ido suna kallon sama. Idanun Asmeen sun cika da hawaye. Shaprees ya rufe baki da tafin hannunsa, tamkar yana tunanin wani abu mai girma da ke dawowa masa a hankali.
“Ya Allah…” mahaifin su Amaar ya furta. “Na bar ɗan uwana cikin mugun gidan mace da ba ta san mecece ‘yanci ba.”
Miemie ta ɗan juya kamar wata sarauniya, ta miƙa tafinta zuwa ga Amaar, sannan ta ce da shi da murya mai laushi:
“Idan kana son ku samu Tasleem, to sai kun zurfafa cikin ruwan da ke ɓoye mafita. Amma ku sani — ba ƙarfin jiki zai fito da ita ba, sai ƙarfin zuciya.”
Amaar ya runtse ido. Wani zafi na tsananin ƙauna ya zuba masa a zuciya. Bai san yanda yake ji ba — kamar ruwa, kamar wuta, kamar iska. Amma ya san abu ɗaya: Tasleem tana kiransa, duk inda take.
A gefe kuwa, Madam Nablah ta wuce zuwa ɗakinta, tana kuka… amma ba kukan nadama ba — kukan fushin da ta tsinci kanta a ciki. Ta na tafiya a hankali, tana jin Miemie ta zo mata da barazana. Kuma wannan ba zata yarda da shi ba. Ta rantse a zuciyarta tana faɗin:
“Bari su ci gaba da neman Tasleem. Wuta ce za su tsinta a ƙarshe.”
A wannan ranar ne aka sitirta Mahaifinsu Tasleem, Abul da Amaar da Shaprees ne suka yi jana'izar sa a cikin gidan ba tare da sun gayyato kowa ba, cikin dare suka je su ka binne shi....
Bayan sun dawo, Abul yana fama da zazzabin damuwa...
Amaar wanda ke zaune a gefen mahaifinsa, yana lulluɓe shi da bargo.
Kamar dare ne ya zo masa da nauyin tunani. Amma daga can cikin kunnensa, sai ya ji wata murya mai laushi tana cewa:
Miemie ta bayyana cikin hasken ruwa a kusa da tagar ɗakin..
“Amaar, lokaci yana tafiya. Duk da an bayyana gawar da Madam Nablah ta ɓoye, akwai babban sirri da ke can cikin ruwan da ta kulle Tasleem.”
Amaar ya ce:
“Ina Tasleem take? Ina matata? Me ya sa zuciyata ba ta huta ba har yanzu?”
Miemie ta ce:
“Kuna bukatar ku shiga tafkin madalla da hasken rana — tafkin da babu wani sihiri da zai iya kare ku sai zuciyar ku. Amma sai kowa ya haɗa hannu — kai, Shaprees, Sirrin wannan tafki yana cikin zanen bango da ke ɗakin Madam Nablah.”
Amaar ya zabura. Wannan zance ya birkita masa tunani, amma ya bashi ƙwarin gwiwa. Ya san lokaci bai da yawa kuma yasan ba zai bari Madam Nablah ta ci nasara ba.
---
A wannan daren, Madam Nablah ta shiga wani ɗaki mai duhu a ƙarƙashin beni, ɗakin tsafinta mafi ɓoyuwa. Ta ɗauko wani kwanon ruwa mai haske, ta zuba wani ruwan tsafi a ciki. Ta ga fuskar Tasleem a ciki — tana kwance a cikin wata dunƙulalliyar madatsar ruwa, tana numfashi idonta a rufe.
Madam Nablah cikin dariyar mugunta ta ce:
“Ke Tasleem, ni na haife ki, ni kuma zan hukunta ki. Idan na rasa iko akan sauran ‘ya’yana — ke ba zaki gudu ba.”
Washegari da safe .....
Amaar, da idonsa jajaye, ya fito daga ɗakin mahaifinsa. Kamar jarumin da ya taso daga makogwaron haske, zuciyarsa ta ƙazance da niyyar ceton Tasleem — ko da zai shiga ruwan kisa.
Ya tunkari Asmeen a falon gaban gida, inda take zaune da kuka a gefen Shaprees. Su biyun sun rasa kwanciyar hankali tun bayan bayyanar gawar mahaifinsu.
Amaar cikin murya mai ƙarfi ya ce:
“Ya ishe mu zama shiru. Yanzu lokaci ne da zamu gane waɗanda muke da su, da waɗanda suke da mu.”
Asmeen ta kalle shi, hawaye na zuba a idonta.
Ta ce:
“Ya ya zamu fuskanci uwa wacce ta canza mana rayuwa daga tushe?…”
Shaprees cikin taushin murya ya ce:
“Kuma ya ya zamu shiga tafkin da babu mai dawowa daga ciki — tafkin ruwan tsafi wanda ke ɓoye rayuka da yawa?”
Sai aka ji murya daga can gefe — murya mai kama da iska mai kamshi, da sautin ƙaho na ruwa. Miemie ta bayyana a bakin ƙofa, hannunta na riƙe da wani guntu takarda mai ɗauke da zanen da take cewa:
“Wannan shine zanen bango na ɗakin Madam Nablah. Da wannan zane za ku iya buɗe kofa zuwa tafkin da take ɓoye da Tasleem. Amma ku sani…”
Ta tsaya, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, kafin ta ɗora:
“…ba kowa zai iya tsallake wannan tafki ba. Sai wanda zuciyarsa ta tsarkaka, kuma ba shi da wata niyya sai ceton gaskiya.”
Amaar ya karɓi zanen, ya ɗaga kai yana kallon Miemie da wani kwarjini.
Ya ce:
“Zan shiga. Ko da ruwa ne zai cinye ni, bazan bar Tasleem cikin wannan mummunan kulle ba.”
Shaprees cikin zurfin tunani ya ce:
“Zan raka ka.”
Ya kalli Asmeen. “Zan dawo gare ki, da alkawarin cewa wannan karon — ni ne wanda zan kareki, da yaron dake cikin ki ...."
Asmeen ta ce:
“Idan za ku shiga wannan tafkin, ku sani cewa soyayya ce zata tseratar da ku. Ba ƙarfin tsafi ba.”
A cikin dare mai duhu da iska mai ƙamshi, suka fara shirin shiga ɗakin Madam Nablah a ɓoye, domin neman ƙofar ɓoyayyen tafki. Amma Madam Nablah… ta riga ta fara jin motsin shirin su — kuma ta shirya musu wata ƙulli da bazata bar rai ya dawo da sauƙi ba ..…
*💋HASKEN RUHI💋*
*🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀*
It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person.
*WhatsApp 09065443871*
*🌹 ASMEETAH WRITER 🌹*
*BOOK TWO__________PAID_____₦300*
Page 9 to 10
Madam Nablah duk tasan shirin su Amaar akan zuwa neman Tasleem hakan yasa ta toshe duk wata kafa na fita daga gidan, hanyar da zai sadasu da ɗakinta balle su samu hanya ta toshe nan ma, ko ta ina ta kafa ta tsare, da haka har suka haƙura, yanzu hanyar fita daga gidan ma ta gagare su, ba mai shigowa sannan babu mai fita.....
★★★★★
A cikin ɗakin ruwa mai kariya daga Miemie, Nasreen ta kammala shafa ruwa a fuskarta, tana sanye da wani riga na sanyi da Miemie ta tanada mata.
Miemie ta zo ta zauna kusa da ita, tare da wani kwandon ƙamshi da ‘ya’yan itatuwa masu ruwa-ruwa.
Miemie ta ce:
“Zuciyarki ta fara tsarkakewa. Amma yanzu... zuciyar ki na murɗawa.”
Nasreen ta lumshe ido tare da faɗin:
“Ina jin Abeesh a raina. Sai dai... ba ni kaɗai ke raye a zuciyarsa ba. Kuma... wannan ciwo ne da bazan iya jurewa ba.”
Miemie ta ce:
“Zuciyar mace ita ce mafi ƙarfi. Duk wanda ya fasa ta, zai gamu da sakamakon da baya tsammani. Amma na gane... kina da ƙarfin da zai iya ƙara haske a gidan ku.”
Nasreen ta ce:
“Amma Miemie... bazan iya komawa wurin wulakanci ba. Ko auren da Allah ya halatta, idan bai zo da mutunci ba — bashi da daraja.”
Miemie ta kama hannunta ta ce:
“Kin girma, Nasreen. Kin gane duhu da haske. Amma kafin ki yanke hukunci na ƙarshe, zan nuna miki abu guda da zai ƙarfafa miki shawara.”
Ta sa hannunta zuwa cikin ruwa. Ruwan ya fara zagayawa yana kewaya Nasreen, ta nuna mata wani gani mai kama da haske. A cikin ruwan, ta hango:
Tasleem tana kuka, tana kwance a cikin wani zurfin kogi a ɗaɗdaure da igiyar sihiri mai wuta...
Nasreen da sauri ta kalli Miemie tana faɗin, "a ina take? kamar itama a cikin ruwa take, kenan a hannun wa take?...."
Miemie ta ce "tana cikin tafkin ruwan tsafin mahaifiyarku...."
Nasreen ta ce:
"Dan Allah ki taimaka mana ki dawo mun da Tasleem..."
Miemie ta ce:
"Bana shiga duniyar zalunci, na ƙi jinin zalunci saboda haka na haramta wa kaina shiga duniyar baƙaƙen Aljanu..."
Masreen tana kuka taga an nuno mata Abul da Amaar suna zaune zaman ƙunci da damuwa, da Qur'ani a gaban su suna karantawa....
Sannan aka nuno mata Asmeen tana kwance a gado tana riƙe da cikin ta, a ya yinda Shaprees yake gefenta yana ƙoƙarin bata ruwan addu'a sakamakon ciwon cikin dake damunta....
Nasreen ta kalli Miemie sannan ta ce:
"Meya samu ƴar uwata Asmeen?..."
Miemie ta ce:
"Juna biyu gare ta na wata biyu, kamar yanda kike ɗauke da cikin wata biyar kema...."
A ruɗe Nasreen ta miƙe tare da faɗin
"Meeee?..."
Miemie ta ce:
"Tabbas kina da ciki har na wata biyar, amma babu wanda yasan kinada shi, hatta kema sakamakon bacci mai tsawo da kika yi a hannun Mahaifiyarki, sannan itama Mahaifiyarki bata sani ba sakamakon hasken da ya ɓoye cikin, duhu baya taɓa ganin sirrin haske...."
Cike da mamaki Nasreen take kallon Miemie da kuma cikinta tana shafa wa, a hankali ta furta, "menene alaƙata da sirrin haske?..."
Miemie ta ce "Hasken Tasleem ke bibiyar ki domin ta sanya hannunta akan lamarin ki...."
Hawaye ne yake gangaro wa daga kurmin idon Nasreen, hannunta a dafe da cikin ta...
Idonta ne ya sauƙa akan Abeesh dake kwance yana kan bacci, a yayinda Catrina take kwance akan ƙirjinsa...