x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 192

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sai ki mun bayani kice a social media zaki tura ni sai na miki style na video kala-kala yanda zanyi trending, oyaaa muje zuwa...."

A lokacin Amaar ya fara ɗirkar rawa yana girgizawa tare da juyawa yana murguɗa ɗuwawun sa, sannan ya juyo yana tura tsuriyarsa gaba da baya tare da yo wa kanta yana faɗin "yi mun video dakyau ƴan mata yanda zanyi trending sosai na samu followers...."

Tasleem video take amma hankalinta da idanuwanta duk suna kan sa, haka take bin sa da kallo daga ƙasin ƙafarsa har zuwa saman sa, gaba ɗaya jikin sa duk gargasa sun kwanta luf ga tsayi jikinsa fari tass, haka take bin saman faffaɗan ƙirjinsa da kallo, gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, ga waya a hannunta har ta manta mai take da wayan.

Amaar ganin yanda eyes ɗin ta suke a kansa ko ƙibtawa babu duk sun lullumshe kamar mai jin bacci, daga ganin ta yasan bata cikin hayyacin ta, murmushi ya sau tare da girgiza kai ya ciro towel ya ɗaura a kunkumin sa, a gabanta ya tsaya Tare da murza yatsun sa a saitin idanuwanta yana faɗin "yadai ƴan mata kin gama yin video ne?..."

A ruɗe ta dawo hayyacin ta tana dafe goshin ta tare da faɗin "kai baka da kunya samm, haka tarbiyyar ka yake?..."

Amaar ya ce "Uhmm to ki poster mana Kinga sai a tantance a tsakanina da ke waye marar kunya..."


Karɓan wayarta ya yi yana duba video ya ce "yawwa ga shi nayi saving video, aina zaki fara yin posting TikTok ko Facebook ko Instagram?...."

Da sauri Tasleem ta karɓi wayar daga hannunsa tana faɗin "bani wayata kar kayi posting don na fahimci baka da kunya ko kaɗan..."

Tana karɓa tayi saurin goge wa, tare da sakin dogon numfashi tana lumshe ido kamar mai jin bacci...

Amaar murmushi yasau tare da nufan wurin mirror yana ɗaure da towel....


Next Next Next


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 21 to 22


Amaar a tsaye yake a jikin mirror yana shafa cream sai satar kallon Tasleem yake a ta cikin mirror, ita kuwa baki ya gagara rufuwa sai masifa take ta zabgawa ganin ya ƙyale ta bai ce mata komai ba yasa ta ƙara fusata tana faɗin "wai ma mahaukaciya ka mayar dani ne? ina maka magana ko gyaran murya ka kasa yi..."

Sai yanzu Amaar yayi magana tare da faɗin "so kike nayi gyaran muryan ne?..."

Ta ce "Oho dai ban damu ba indai har kana ji na to ka fita daga cikin rayuwata tin kafin nasa ƴan iskan gari su koya maka hankali bar ganin kai soja ne..."

Amaar shi dai murmushi kawai yake yana tunanin lokacin da take ƙaramar ta, yana girgiza kai tare da furta
"Tasleem ɗina bata da masifa sai surutu amma yanzu masifar ma ta koya...."

Cikin rashin fahimta ta ce "me? wato rainin nakan har ya kai haka? har wani Tasleem ɗin ka? wato baka ji abubuwan da na faɗa maka ba ko?..."

Idon ta ne ya sauƙa akan ƙaramin bindigar sa dake ajiye akan gadon sa, cije lips ɗinta tayi tare da nufar wurin da sauri taje ta ɗauko, bai ankara da ita ba sai ji yayi tana faɗin "kai lusarin Soja idan baka ji tsoro na ba ai dole zaka ji tsoron mutuwa ko?..."

Amaar ta cikin madubi ya kalle ta yaga ta saita shi da bindiga, juyowa ya yi yana kallon ta daga bisani ya girgiza kai ya ce "kin manta baki kunna kunamar bindigar ba..."

A fusace ta kunna tare da saita kan goshin sa,
Amaar ya ce "shin zaki iya harbana?..."

Ta ce "to sai me idan na harbeka? ina ruwana da rayuwar ka..."

Ya ce "kina ganin idan kin harbe ni zaki fita daga gidan lafiya kalau?..."

Tasleem tana yamutsa fuska ta ce "to na gwada yin harbin ne?..."

Ya ce "eh gwada mana..." ya furta hakan tare da yo wa kanta daga shi sai ɗaurin towel.

Ta ce "kar ka matso kusa dani na gaya maka, stay away from me, zan harba fa..."

Ganin yazo dab da ita ne yasa ta rufe idanuwanta sosai tare da harba bindigar cikin rashin sa'a babu bullet ko ɗaya a ciki, da sauri ta buɗe ido tana kallon bindigar cikin takaici tayi wurgi da shi.

Amaar kuwa murmushi ya yi tare da faɗin "ashe zaki iya kashe ni?..."

Tana ja da baya ta ce "mai zai hana, me zan yi da rayuwar takan..."

Yana matsa wa kusa da ita, ita kuwa tana ja da baya, bata san lokacin da taje bakin gado ba sai ji tayi ta faɗa saman gado, kafin ta ɗago shima ya rufu kanta ba tare da ya danne ta ba, kamar dai yanda ya mata da ya je gidan su,
Tasleem hannu tasa zata ture shi ya yi saurin furta "shocking, kin manta ne? kina taɓa ni zaki ji wuta, amma idan kina son hakan ya faru bari na danne ki..."

Tasleem a fusace ta fara faɗin "Are you mad? are you stupid? are you crazy? danne ni fa kace zaka yi shin kai ɗin daman ɗan iska ne? ...."

Ya ce "aww daman ke baki sani ba, to bari na nuna miki kalar nawa iskancin..."

Ƙara rufuwa ya yi a kanta yana shirin sumbatar ta tayi saurin katse shi da cewa "dakata! wai meye hakane kasan kai ba mutum bane amma kake son ka cutar da rayuwata, jikin ka wuta baka san da zaran ka taɓa ni tamkar na faɗa cikin wuta bane....."

Murmushi ya yi sannan ya ce "bakya son na taɓa ki ne?..."

Tasleem kamar zata yi kuka ta ce "eh bana so, dan Allah ka ɗaga ni bana son jikinka ya gogi tawa akwai matsala, ni nasan kalar raɗaɗin da nake ji a jikina..."

Tana ƙara shige wa cikin katifar hatta hannun ta bata so tayi motsi da shi saboda kar ta taɓa shi,
Amaar ya ce "okay idan bakya son na haɗa jiki da ke sai kin furta cewa kina sona..."

Tasleem ganin ba yanda ta iya ne yasa ta buɗe ƙaramin bakinta tare da fashe wa da kuka tana faɗin "ina sonkaaaaa...."

Ya ce "wani irin abu ne haka? kin furta kalmar so ba armashi, ki dakatar da kukan ki furta mun kalmar love cikin zazzaƙar muryar ki da baki taɓa furta wa kowa ba...."

Shiru tayi tana kallon sa wani irin takaici take shaƙa babu yanda ta iya haka ta furta "i love you..."

Amaar juyar da kunnen sa yayi sai tin ƙaramin bakin ta yana faɗin "ban ji ba sake furta wa..."

Fuska a ɗaure ta ce "i love you..."

Ya ce "tirrr da wannan murɗaɗɗiyar fuskar taki zaki furta mun wannan kalmar? ki sau fuskar sannan ki yi murmushi sai ki furta mun...."

Tasleem fuska a ɗaure ta ce "bazan yi ba..."

Amaar idonsa ya wurga kan hannunta da ke gefe guda yanda ta miƙar da su, a hankali ya ɗago da yatsar sa ɗaya ya ɗora akan hannun ta, ai kuwa haka jikinsu ya yi shocking sauran kaɗan ya fa ɗa kanta ya yi ƙarfin halin da fa gadon,
Lokaci guda Tasleem ta fara hawaye tana faɗin "shin me ya kawo wannan al'amarin cikin rayuwata, kai ɗin waye ne? Mutum ko Aljan?..."

Amaar yana sakin murmushi daƙer, ƙwaƙwalwarsa ce take ta juyawa, ga bala'in ciwon da yake masa, haka duk san da ya taɓa jikinta ko kaɗan ne sai wannan ƙwaƙwalwar tasa ta motsa, domin ya fita jikkata, a hankali yake furta "Tasleem! Tasleem ki ki kice wa Mommyn ki...."

Yana so ya kawar da wannan tunanin amma ƙwaƙwalwarsa ta ƙi barin sa, abubuwan da suka faru dashi ne yake ta dawo masa sabo kamar yanzu ake aikata abun, idan yana magana akan lamarin baya sanin mai yake faɗa, a yanzu lips ɗinsa ne suke ta kakkarwa yana so ya furta abu amma yana tunanin meye zai zo bakinsa, yana fargaban furta abu a wannan yanayin da yake ciki domin baya son ya tayar da ciwon ƙwaƙwalwar Tasleem....

Tasleem haka take bin fuskar sa da kallo tare da faɗin "kar fa ka danne ni, meye haka kake yi? wai kai ɗin waye ne? ni ka ɗaga ni..."

Ita ɗin ma zogi take ji a jikinta na shocking da ya taɓa ta, daƙer Amaar ya yi control kan sa idanuwansa sun yi jawur shima kallon ta yake lokaci guda walwala da fara'a duk suka ɗauke daga kan fuskar sa, a hankali ya furta "ki furta kina sona, ina so na zama mutum na farko da kika fara furta kalmar soyayya a gare shi...."

Tasleem ta ce "idan na furta maka hakan shi zai sa ka bar ni?..."

Jinjina kai ya yi alamar "eh..."

Murmushi ta sau har sai da ƙayataccen dimple ɗin ta ya lotsa sannan ta furta "i love you..."

Wani irin bugu zuciyarsa tayi lokaci guda yaji kamar an wanke masa duk wata damuwa, bai san lokacin da shima ya sau murmushi ba tare da furta "i love you too baby...."

Tasleem ɗaga gira ɗaya tayi tare da faɗin "to ɗaga ni hankalinka ya kwanta yanzu ko? kasa na furta kalmar da tinda nake a rayuwata ban taɓa furta ta ba hasali ma na tsani kalmar, hankalinka ya kwanta, ɗaga ni to..."

Amaar tunani ya yi cewa yanzu ne yake da damar da zai cire motsawar ƙwaƙwalwar sa ta hanyar haɗa ido da ita na tsawon mintina biyar, idan har ya yi haka ƙwaƙwalwarsa zata huta, zata daina shiga hargutsin da take shiga...

Girgiza kai ya yi sannan ya ce "baki gama ba ...."

Tasleem kamar ta fashe da kuka ta ce "me zan maka again? yarjejeniyar da muka yi kenam cewa idan na furta maka kalmar so zaka ɗaga ni..."

Ya ce "the second one shine za ki tsaya ne mu kalli juna na tsawon minti biyar..."

Tasleem cikin rashin fahimta ta ce "wani irin sihiri kake so kayi da ni?..."

Ya ce "kin ga kayan tsafi ne a cikin ɗakin nan?..."

Ta ce "to meye dalilin yin haka?..."

Ya ce "idan har kina so ki tafi to sai kinyi abinda na sa ki..."

Tasleem ba yanda ta iya haka ta zuba idanuwanta a cikin nasa wanda shima haka yake kallon cikin eyes ɗin ta, kallon juna suke ba tare da sun ƙibta ba, har minti biyar ta cika, tana cika eyes ɗin Amaar suka rufe kan su sakamakon canjin yanayin da ya samu a cikin kwakwalwar sa, gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacin sa haka ya tafi luu ya kwanta akan Tasleem, ga ba riga a jikin sa daga shi sai towel, shocking ɗin da suke ji ya wuce misali Tasleem ihu take tana so ta ɗaga shi daga kanta amma ta kasa, ga tsananin shocking dake gudana a jikin ta, shi kuwa a wannan lokacin baya jin shocking sakamakon suman da ya yi baya cikin hayyacin sa,
Ihu take tana neman ɗauki amma duk wannan ihun babu mai jiyo ta domin Indai ka shigo ɗakin duk motsin da zaka yi babu mai jin ka saboda ta ko ina glass ne a rufe, irin glass ɗin da duk ihun da zaka yi baza'a ji ka ba...

Sai da suka ɗau tsawon minti goma bata samu nasarar ture shi ba daƙer ta tattaro ƙarfin ta duk da shocking ya gama cin duk ƙarfin jikinta ta wantsilar da shi gefen ta, a minti sha biyar minti biyu ne babu da yanzu sun warke da jin wannan shocking amma lamari ya koma baya, in da ace minti 15 ta cika Shikenam zasu daina jin shocking ɗin gaba ɗaya, amma kash minti biyu ya rage, Tasleem a ruɗe ta sauƙa daga kan gadon tana tangaɗi kamar wacce tasha maye, ita ma kafin ta ƙara sa bakin ƙofar ɗakin har ta faɗi sumammiya a ƙasin carpet shi kuma yana kan gado....

Misalin ƙarfe 12 na dare Nasreen da Asmeen ce suke zaune a falo ko wacce tayi tagumi su na jiran dawowar Tasleem, duk ba bu wacce ta rintsa a cikin su ga mommynsu ta ƙarƙame room ɗin ta sun buga mata yafi sau a ƙirga amma taƙi buɗewa, ita kuwa tana can wurin meeting ɗin su da suka saba, shigowar Abeesh ne yasa duk suka miƙe tsaye su na faɗin "ka same ta?..."

Abeesh girgiza kai ya yi tare da faɗin "duk wurin da ya kamata ace naje dubo ta saida naje amma ko inuwar ta ban gani ba, abun zai ban mamaki
End Ads