x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 28 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 81001 words
  • 84000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 208

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Abul...."

Abul shima kukan yake yana goge musu hawaye da tafin hannayensa da suke ta kakkarwa tsabar ɗaurin da yasha....

Abeesh shima fashewa yayi da kuka yana faɗin "Abul na, haƙiƙa an zalunce ka, kuma bazamu taɓa barin wannan tozarcin ta sha a banza ba, domin ka haifi ƴan halak...."

Abul yana rawar murya ya ce "ku bar komai ga Allah! yana sane da komai kuma zaiyi ikonsa akai, ku kwantar da hankalin ku...."

Amaar cikin ɓacin rai ya ce "Abul kayi hakuri amma dole zamu ɗau fansar abinda tayi maka, Kuma yanzu lokaci ya yi da za mu dawo da adalci
ta so ta hallakar dani Allah bai bata dama ba, na samu tsiratarwa daga wurin Sarauniyar ruwa...."

Abul ya kalle shi da murmushi kwance akan fuskarsa ya ce "ka samu tsiratarwa daga wurin Sarauniyar ruwa? Aljanar da babu mai kirkin ta da kuma adalcin ta da yawan fara'a da murmushi, na santa sosai domin ta kasance a cikin littafin hasken ruhi, labarinta na da yawa a cikin littafin saboda mutumtaka da kuma darajar ta, asalin sunanta Aryana ake ƙiranta da suna Miemie, sarauniyar kyawawan Aljanun mata da bil'adama duk babu wanda ya kaita kyau da kyan sura, tana taku kamar ɗawisuwa, naji daɗi sosai daka faɗa hannunta sai kuma gashi ka rayu ata sanadiyar Sarauniya Miemie...."


Amaar cikin tausayawa yake kallon mahaifinsa cikin ƙwarin gwiwa ya ce "hakane Abul, takan yawan kawo mun ziyara a cikin mafarki na, a hannunta na fara girma a cikin wani kogon haske, amma sai dai a matsayin mutum take fito mun, kullum a yarintar ta take bata tsufa....."

Abul ya jinjina kai sannan ya kalli Abeesh cikin murmushi ya ce "yaro na kuma Autana fatan kana lafiya..."

Abessh sake rungumar Abul ya yi yana kuka...

A yayin da Tasleem take gefe guda gaba ɗaya jikinta a mace yake ta kasa motsawa tsabar tsananin kunya da damuwar da ta tsinci kanta a ciki....


★★★★★

Madam Nablah a fusace ta shigo falon tana huci sakamakon maganganun Shaprees na rashin ɗa'a kuma yana so ya bijire mata, ga wasu alamomin da take ji kamar wani abu yana shirin faruwa a ɓangaren Abul Abeesh...

Nasreen wacce fitowar ta kenan daga kitchen ta tarar da Madam Nablah tana haura saman benin part ɗinta,. bata san lokacin da ta furta "Mommy! Mommy!! Mommy!!!...."

Madam Nablah a slow ta juyo tana kallon ƙasin falo yanda Nasreen take ƙoƙarin hauro yanda take da gudu, sai da ta iso compound ɗin part ɗin ta sannan ta tsaya a gaban ta tana faɗin "daman so nake na shigo room ɗinki zanyi miki gyara..."

Madam Nablah cike da mamaki take binta da kallo cikin rashin fahimta ta ce "shin daman kina shiga room ɗina ne?..."

Girgiza kai Nasreen tayi tana faɗin "but Mom laifi ne don na shiga room ɗinki?..."

A fusace Madam Nablah ta ce "amma tinda kike kin taɓa shiga? and tell me wani munafurci kuke shiryawa? ina Tasleem? Ina Amaar da Abeesh?..."

Nasreen lumshe ido tayi cikin tsoro da fargaba ta ce "Mom sun fita ne..."

"Zuwa inaaa?..." Madam Nablah tayi tambayar idonta a cikin na Nasreen wacce take ta faman haɗa zufa....

Nasreen ta ce "i don't no..."

Madam Nablah ta ce "bana buƙatar gyaran nakin, ki tafi ki bani wuri kafin nayi wurgi dake ta taga ...."

Har Nasreen ta juya taji Madam Nablah ta darara mata tsawa kamar daga sama tana faɗin "Keeee! who open my room?...."

A tsorace Nasreen take kallon ta, ta ce "Mom please ki ƙyale ni haka ban sani ba wallahi..."

Kafin tayi wata yunƙuri har Madam Nablah ta shaƙo wuyanta tana zazzaro ido ta ce "gaya mun ina Tasleem? and waye yazo har bakin ƙofar ɗakina ya buɗe da jinina? ...."

Nasreen sai zazzaro ido take tsabar shaƙar da ta sha, har ta fara jujjuyar da ido, numfashi yana shirin ɗaukewa sai a lokacin Madam Nablah ta sakar mata wuya tana huci, a fusace ta tura ƙofar da ƙafarta daman ba'a gama rufe ƙofar ba.....

Tana shiga kai tsaye hanyar da zai kaita ɓangaren Abul Abeesh ta nufa da gudun gaske....

Nasreen a ruɗe ta miƙe tare da sauƙa ƙasin falo da gudu tana tangal-tangal, akan kujerar falo ta faɗa tana sakin numfashi daƙyar....


★★★★★★ Tasleem kanta a ƙasi tana wasa da yatsunta taji an ƙira sunanta cikin rawar murya, Abul ne yake kallon ta da hawaye kwance akan fuskarsa yana faɗin "Ƴata zo mana, ya kika zauna a gefe, ke ma zo naji ɗumin jikin jikina..."

Tasleem fashewa tayi da kuka kamar daman jira take a taɓota ta yi kukan, zuwa tayi ta rungumi Abul tana kuka, shi kuwa sai faman rarrashin ta yake tare da bata hakuri akan ƙaddarar da suka tsinci kansu a ciki....

Tasleem tana rungume da Abul bata san lokacin da ta ɗago a zabure ba, a yayinda idanuwanta suka koma fari soll ba ɗigon baƙi ko ɗaya, sumar gashin ta ma ya koma fari soll like furfura...

Amaar da Abeesh daman sun san tanada wannan ikon, alamun akwai abinda yake shirin faruwa, Abul yana kallon ta cike da mamaki ya ce "me yake faruwa dake ne ƴata...."

Amaar yana fuskantar ta ya ce "Tasleem me ya faru, ki sanar mana yanzu ...."

Cikin rawar murya ta ce "gata nan zuwa, yanzu haka ta nufo yanda muke, ta kusan isko mu..."

Amaar da Abeesh kallon juna suka yi suna ƙoƙarin samawa kansu mafita suna tunanin ta yanda zasu fita da Abul...

Madam Nablah tana zuwa wurin ta tarar an buɗe ƙofar wuta, girgiza kai tayi sannan ta shige still ta samu ƙofar ƙasa yanda Abul Abeesh yake a buɗe, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske tana tunanin waye mai ƙarfin ikon da ya buɗe ƙofar wuta har ya shigo yanda Abul Abeesh ya ke, alhalin babu wanda yasan a yanda yake....

A lokacin Madam Nablah ta rufe ido tare da sauya rigar jikinta zuwa baƙar doguwar riga na baƙin tsafi, fararen idanuwanta suka ɗauke zuwa baƙaƙe, sai idon ya zamo wulik ba haske ko ɗaya, sumar gashin ta duk suka tashi sama kamar wanda iska ke hura mata, cikin murmushin mugunta ta fara taka matakalar benin da zai kai ka ƙasin kogon....

Tasleem hannu ta miƙa wa Amaar shima ya riƙe nata sannan ta miƙa wa Abeesh ɗayan hannun shima ya riƙe, Amaar da Abeesh suka miƙawa Abul duk suka riƙe hannun juna suka haɗa cycle daga bisani Tasleem ta rufe ido tare da motsa lips ɗin ta ba tare da an san abinda take faɗi ba, lokaci guda sai ga haske ya bayyana kafin Madam Nablah ta ƙaraso duk suka ɓace sai ƙurar wurin, Dai-dai lokacin da Madam Nablah ta faɗo wurin, abinda ta tarar ne ya firgita mata ƙwaƙwalwa, ba ƙaramin razana tayi ba ganin babu Abul Abeesh, tsawon shekaru Ashirin tana tsare da shi amma lokaci guda ya kuɓuce mata, tsabar tashin hankali bata san lokacin da ta faɗi ƙasi ba, haka numfashin ta yake fita daƙyar, tana zaune a ƙasin ciyawar wurin.....

Lokaci guda ta kurma uban ihu tana buga hannayenta a ƙasi, wurin ne ya tirniƙe da hayaƙi tsabar ɓacin ran da Madam Nablah ta shiga, ihu take bana wasa ba....


Su kuwa su Tasleem da Amaar da Abeesh ba a yanda suka sauƙa sai a ɗakin Amaar dake cikin gidan, a kan katafaren gadon Amaar suka kwantar da Abul, duk zama sukayi suna farin cikin dawo da cikon farin cikin su da suka rasa, yanzu komai ya dawo hannun su......


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 37 to 38


Madam Nablah ganin ihun takaicin bazai kaita ko ina ba yasa ta zabura a fusace, ganin tafiya zai zame mata aiki yasa ta ɓace lokaci guda bata tsaya a ko ina ba sai a wantalelen falon gidan ta, Nasreen tana zaune akan kujera ganin Madam Nablah ta bayyana kamar wacce aka cillota akan iska a durƙushe akan carpet, idanuwanta jajawur kamar garwashi, cikin fushi ta ɗago tana kallon Nasreen wacce itama a zabure ta miƙe tsaye tare da furta "Mom..."

Madam Nablah miƙe wa tayi tare da faɗin "at this moment not Mom, just call me Devil Mom...."

Kafin Nasreen ta ankare har Madam Nablah ta shaƙo wuyan ta tare da ɗaga ta sama da hannu ɗaya cikin ƙwayar idanunta haka suke ci da wuta, jikinta yana fitar da farfatsin wuta, sumar gashin ta haka suke bin iska su na tashi sama....

Nasreen da ta gama tsure wa bata san lokacin da ta kwara uwar ihu ba sai da gidan ya ɗau sautin, kafin muryar ta disashe sakamakon shaƙar da ta sha, Madam Nablah a fusace ta ce "ina malamin kimiyya?...."

Nasreen abinda ya ƙara firgitar da ita shine jin yanda muryar mahaifiyarta ta koma kamar baƙin Aljanin duhu, ga ƙatuwar murya mai rikitarwa, haka take tambayar ta "ina malam Junaidu? Ina Tasleem? Ina Amaar? Ina Abeesh? Ina suka kai malam Junaid?...."

Magana aka yi ta baya ana faɗin "gamu nan..."

Madam Nablah waiwaya wa tayi da launin eyes ɗin ta na wuta tana kallon yanda aka yi magana,
Tasleem ce ta sauƙo daga upstairs room ɗin Amaar ta shigo falo, bayan ta kuwa Amaar ne sai kuma Abeesh yana riƙe da Abul suna tafe a hankali sakamakon ciwon ƙafar da Abul yake fama da shi, suna shigo wa falo Abeesh ya zaunar da Abul su kuwa suka kasance a tsatstsaye, idon Madam Nablah akan Abul sai huci take tayi, Tasleem ce ta matso kusa da ita tana faɗin "Mom ki sakar mun wuyan ƴar uwata kar ki kashe ta akan laifin da bata aikata ba, in laifi ne ni na aikata ba ita ba, don haka ki sauƙar da ita dan Allah...."

A fusace Madam Nablah ta darara mata tsawa tare da faɗin "kar ki sake haɗa ni da Allah, kuma ni ba Mom ɗin ku bace ni ɗin devil Mom ce...."

Tasleem ta jinjina kai cikin lallami take binta akan ta ƙyale Nasreen, sannan ta ce "mai ta miki da zaki huce takaicin ki akan ta?..."

Madam Nablah ta ce "Meyasa ta munafurce ni? meyasa ta ɓoye mun abinda yake faruwa?..."

Sai a wannan lokacin Amaar ya yi magana yana faɗin "ina mu kike nema? to gamu mun bayyana a gaban ki shin mai zaki mana?..."

Madam Nablah idonta a cikin nashi ta ce "meye dalilin da yasa ku ka shiga gonata?...."

Amaar ya ce "ki tambayi kan ki, ke meyasa kika shiga gonar mu? kin dai san mahaifin mu shine babban gonar mu kuma shi kika taka, kina nufin zamu bar ki ne?...."

Nasreen har ta fita hayyacinta tana shirin daina motsi, idanuwanta sun ƙaƙƙafe, gaba ɗaya hankalin Abeesh ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin a halin da Masoyiyar sa take, da sauri ya kalli Tasleem yana faɗin "Please Tasleem kiyi wani abu kar ta kashe mun ita..."

Girgiza kai Tasleem tayi tare da faɗin "duk abinda zan yi yanzu zai iya cutar da jikinta, kuma dole mahaifiyata ce ko a wani hali take...."

Tasleem ce ta ƙara maida idonta kan Madam Nablah sannan ta ce "Mom! Nasreen fa kike shirin kashe wa ba Tasleem wacce kike ƙi ba, ke fa kika haife ta kuma ita ɗin makullin zuciyar ki ce shin kin manta, daga Asmeen sai Nasreen masu kyautata miki, ni kuma Tasleem ni ce mai bijire miki ni ya kamata ki kashe...."

Tasleem tana kuka tana roƙon ta, har sai da ta durƙusa ƙasi tana mata magiya...

Madam Nablah ganin yanda Tasleem take kuka a durƙushe a gaban ta ne yasa ta jefar da makamin yaƙin ta, a hankali ta sauƙar da Nasreen ta ajiye ta akan kujera...

Da gudu Tasleem ta nufo wurin Nasreen tana ambatar sunan ta tare da rungumar ta....

Ita kuwa Madam Nablah nufan wurin da Abul yake a zaune tayi cikin fushi, kafin ta ƙara sa Amaar ya yi saurin shiga gaban ta yana faɗin "kada ki kuskura, domin kuskure na farko kin yi shi, na biyu kuwa bazan taɓa barin hakan ya faru ba ni Armaan Junaid, kulawar sa ta koma hannu na...."

Madam Nablah girgiza kai tayi tare da sakin murmushin mugunta ta ce "mai zaka iya yi? kaima baka fi ƙarfin nayi da ga-da ga dakai ba, na murƙushe ka hankali a kwance..."

Murmushi shima ya yi tare da faɗin "wancan Amaar ɗin ba shine yanzu a gaban ki ba, wannan Amaar ɗin babu tsoro ko fargaba a zuciyar sa, dai dai nake da na farmake ki...."

A fusace ta ce "mai kake taƙama da shi?...."

A takaice Amaar ya furta "ALLAH...."

A take ta wurga masa wani ɗan ƙulƙulen wuta a jikinsa nan rigar jikinsa ta fara ci da wuta, a zabure Amaar ya ankara haka yake karkaɗe wutar amma wutar sai ƙara ci take, ga yanda fatar jikinsa yake ƙonewa yana jin raɗaɗin ƙunar wutar...

Tintsirewa da dariya Madam Nablah tayi sannan ta ce "nuna mun ikon da kake da shi har kanada ƙwarin gwiwar tinkara ta..."

Abeesh gaba ɗaya hankalin sa tashi ya yi ganin yanda wuta yake ci a jikin ɗan uwansa gaba ɗaya ta gama cin rigar jikinsa, haka yake taya shi kar kaɗe wutar shima haka hannunsa tayi jawur tsabar ƙuna...

Tasleem a ruɗe tayo kansa ganin yana azabtuwa da wuta tana zuwa ta rungume shi a take wutar ta mutu, sauƙe numfashi Amaar ya yi har idanuwansa sun yi ja, jikin sa ya yi burɗi-burɗi da tabon wuta....

Tasleem cikin takaici ta juyo tana kallon Madam Nablah murya na kakkarwa take faɗin "Mom ki dakatar haka, wani irin abu ne haka, meyasa bazaki taɓa canzawa ba, ke wata iriyar annoba ce?..."

Madam Nablah cike da mamaki take binta da kallo, ba mamakin maganganun da take faɗa mata
End Ads