x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 191

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
to tinda bata so..."

Nasreen ta ce "shikenam Uncle na daina..."

Anan suka yi wasa da dariyar su har Abul cikin kulawa Tasleem ta gama feeding ɗin sa....


Abeesh ne ya dawo a yanda ya bar Katrina anan ya dawo ya same ta, har zai wuce tayi saurin miƙe wa tare da tsayawa a gaban sa tana sakar masa raguwar murmushi...

Cikin sassanyar murya ta furta "Sunana Queen Katrina, ni baƙuwace a wannan gidan, zan cigaba da zama daku har lokacin da zan tafi domin hutu nazo, ƴa nake a wurin ƙawar Madam Nablah...."

Jinjina kai Abeesh ya yi sannan ya ce "ƴa ga ƙawar Madam Nablah kenan hakan na nufin ɗaya kuke gaba ɗaya?..."

Katrina ta ce "eh ta hanyar zumunci ba, ina karatu a ƙasar england kafin lokacin da hutu na zai ƙare, fatan kayi farin cikin haɗuwa da ni?..."

Abeesh ya ce "ke ƴar wata masarauta ce? naji kamar a sunan ki kin sakala Queen....."

Katrina lumshe idanuwanta tayi bata son ya fahimci komai game da ita, hakan yasa ta buɗe idon a hankali take kallon sa cikin shauƙin soyayya ta ce "inkiya ne kawai amma ni ba ƴar masaraunta ba ce...."

Abeesh shima murmushi ya yi tare da faɗin "kenam saboda tsananin kyan da kike da shi ne yasa ake ƙiran ki da Queen?..."

Katrina ta ce "kusan haka amma ni nasan banida kyau ai, tsokana ne kawai..."

Abeesh kamar wanda aka zabure shi ya yi saurin toshe mata baki tare da girgiza mata kai yana faɗin "kin yi kuskuren furta hakan Queen, domin ko a duniyar Aljanu sai anyi dace samun mace mai kyan ki, da farko kin ban tsoro na ɗauka Aljana ce ta fito mun a siffar mutum domin kyan ki ya wuce misali..."

Katrina a hankali take lumshe ido tare da buɗe su a hankali cikin shauƙin soyayya da iya makirci, still hannun Abeesh akan kyakkyawan lips ɗin ta, sai a yanzu ya ankare ya sauƙe hannunsa tare da faɗin "sorry ban san lokacin da na toshe miki bakin ba..."

Katrina matso dab da jikin sa tayi tana shafan kyakkyawan sajen fuskantar sa wanda ya kwanta luf, ga ƙamshin turaren da yake tashi a jikinta na fitar hayyaci a hankali ta furta "ba komai, ai kai ɗin na musamman ne baka laifi, koda kayi laifin sai dai a sumbace ka badai a hukunta ka ba domin kai ɗin tauraro ne, kallo ɗaya nayi maka naji ka burge ni, tsorona kar ka wulaƙanta ni...."

Abeesh ya ce "koda matan aljannah suna bina da gudu ke ba abar wulakantawa bane...."

Katrina ta ce "Nagode sosai da wannan matsayin, ina sonka sosai fatan zaka amshe ni hannu bibbiyu..." ta miƙa masa hannu da niyyar musabaha....

Abeesh shima miƙa mata hannu ya yi tare da jinjina kai...."

Dai-dai lokacin da Nasreen ta fito daga ɗakin Abul, ganin Abeesh da Catrina hannu a haɗe yasa ta tsaya cakk, wani irin bugun zuciya taji, a lokacin Katrina ta riƙo fuskar Abeesh tana faɗin "kai ɗin na musamman ne...."

Nasreen wani irin zazzafan hawaye ne ya gangaro mata na kishi..

Falon ne ya ɗauki shiru. Sai karar numfashin zuciyoyin da ke dukan duniya uku: na kishi, na haushi, da na nauyin zuciya.

Sai a lokacin Katrina da Abeesh suka san da zuwan Nasreen...

Catrina ta gyara tsayuwarta da natsuwa kamar sarauniya. Tsayin ta da siffar ta na burgewa, Fatar jikinta fari ne sol irin ta mayu, idanuwanta zinariya mai kama da na halittar duhu, amma tana fakewa da murmushin da ke kwaikwayon na jinƙai.

Ta sauƙe hannunta daga kan fuskar Abeesh, sannan ta juyar da kai tana kallon Nasreen da ke tsaye cike da hawaye da tsananin kishi.

Catrina cikin sassanyar murya ta ce
“Ban son na ruguza miki komai… ban san ko ke ce matar da zai Aura ba, Ni baƙuwa ce kawai.”

Nasreen ta matso kusa da ita, jiki na rawa da zuciya cike da ƙuna cikin zafi ta ce

“Baƙuwa ce ke kike shashshafa mijin wani? Ke kin san me kike yi kuwa?...."

Abeesh haka yake jin zuciyarsa tana ruruwar baƙin cikin abinda Nasreen tayi masa, tsaya kallon ta ma baya son yi cikin fusata ya ja dogon tsaki tare da ƙoƙarin barin wurin, Nasreen tayi saurin riƙo hannun sa tare da faɗin "Ya Abeesh ka saurare ni dan Allah...."

A fusace ya juyo da niyyar marin ta sai kawai ya fasa, cikin zafin rai yake faɗin
"na tsani duk wacce take ƙarƙashin Madam Nablah da kuma goya mata baya akan abinda take aikatawa, kije bana sonki yanzu, ba marin da kika mun ne yasa na tsane ki ba sai don nuna kin fi damuwa da mahaifiyar ki akan mahaifina duk da cutarwar da akayi masa, kin bani mamaki matuƙa, idan kuma kika cigaba da shiga shirgina sai na raunana miki zuciya, ki sa a ranki haka..."

Daga nan ya bar wurin kai tsaye room ɗin Abul ya nufa.....

Catrina ta kalle ta daga sama har ƙasa. Wani irin dariyar ƙeta da raini ta sakar, sannan ta juya gefe kaɗan, ta matsa gaban kujera ta zauna tana ta kallon yatsun kafarta kamar wata budurwar zinariya

Ta ce

“Yana fushi dake… ko baki lura ba? Na shiga ransa a cikin mintuna kaɗan, ke da kike da shekaru da shi baki iya riƙe zuciyarsa ba…”

Wannan magana tamkar sara ne a kunnen Nasreen, Zuciyarta ta buga da ƙarfi, Hannunta har ya ɗago kamar zata daki Catrina, amma sai ta tsaya, Kuka ya hana ta magana, numfashinta ne yake hawa da sauƙa...

Nasreen maganar zuci take

“Me na yi wa Abeesh har ya tsane ni haka? Har ya zama haka?”

Ta juya da sauri, hawaye na sauƙa daga idonta, sannan ta nufi ɗakin su, Da ƙyar ta taka ƙafarta har ta kai ɗakin, ta rufo ƙofa da ƙarfi, ta zube a ƙasa tana kuka kamar karamar yarinya.


---

A falon kuwa Catrina ce ta miƙe tsaye cikin natsuwa. Wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta, na gamsuwa da cigaba da rikita soyayya tsakanin Abeesh da Nasreen. Tana jin daɗin ganin kishin ya fara cin zuciya.

Catrina a cikin zuciyarta ta furta

"Idan ransu ya karye, zuciyoyinsu za su samu girgiza. Idan zuciya ta rikice, ina da damar shigar da duhu..."

Ta tafi da natsuwa zuwa wani ɗaki na baƙi inda Madam Nablah ta tanadar mata wuri, amma kafin ta shige, ta sai da ta kalli saman upstairs mataki na ƙarshe yanda zata ɗauka....

Tana tafe tana maganar zuci

“Zan iya ɗaukar zuciyarsa gaba ɗaya… idan Nasreen ba ta farka ba.”.....

Da haka ta shige ɗakin masauƙin ta.


★★★★★


Daren ya sauka da natsuwa, amma zuciyoyin gida sun cika da hayaniya. A ɗakin baƙi, Catrina ta zauna a bakin gadonta, tana shan ruwan sanyi a cikin kofin gilashi mai tsada. Hasken fitilar dakin na haskaka gashinta mai sheƙi kamar zinariya mai siffar duhu.

A cikin zuciyarta kuwa, akwai fassarar dabaru. Akwai shiri.

Catrina ta furta a hankali

"Zuciyar Abeesh… mai ƙarfi ce, amma tana da rauni idan yana fushi, Nasreen ta manta cewa soyayya ba kyauta ba ce idan ba a kula da ita..."

Ta miƙe. Tana tafiya kamar sarauniya, Ta zura rigar bacci mai launin azurfa, wacce ke kwance a jikinta kamar ruwa. Sai dai ba domin son burge Abeesh kawai ba, har da saƙo: tana son ya manta da Nasreen gaba ɗaya.


---

A gefe guda kuwa...

Nasreen tana kwance a kan gado, idanuwanta cike da hawaye. Tana tunanin kalaman da Abeesh ya faɗa mata. Kamar wuƙa suka ratsata.

Nasreen a cikin ranta take faɗin

"Shin ya manta da yadda muka fara? Da yadda na tsaya masa? Me yasa yanzu yake ƙoƙarin canza mun?"

Tana tashi, ta nufi kofar ɗaki da niyyar komawa wurinsa. Amma ƙafafunta suka tsaya cak. Wani murya daga cikin zuciyarta ta ce “Ki barshi! Idan har zai iya juya miki baya da wacce bai ma sani ba, to ya dace ki ƙyalle shi!”

Sai kuma wata murya mai taushi ta ce “Ki fahimce shi, ki yi haƙuri, ki nemi yafiyarsa…”

Tana tsaye a tsakiyar waɗannan muryoyi, zuciyarta na sarƙe da alhini, idonta na kaɗa wa da hawaye.


---

A ɗakin Abeesh kuwa, yana zaune a bakin gado, tunani fal cikin kansa. Ko da yake yana jin jiki da zuciyarsa sun gaji da Nasreen saboda wata ɓacin rai da ta haifar masa, amma a ƙasan zuciyarsa akwai soyayya mai zurfi da baya iya musawa.

Amma yaƙin da ke zuciyarsa ya ruɗe, musamman da wannan sabuwar halitta mai kyau da ƙamshi kamar sararin samaniya ta fara ƙoƙarin shigar masa rai – Catrina.

Yana da tsattsauran ra'ayi a kan soyayya, ya yarda da gaskiya, biyayya, da sauƙin hyiali. Amma yanzu ya fara ji kamar Nasreen ta canza. Catrina kuma tana nuna masa salo dabam.

Abeesh a zuciyar sa ya furta

“Ta bani kulawa, ta nuna mun soyayyar gaskiya bazan iya juran ganin Nasreen a cikin hawaye da zargi ba... Ba haka nake so ba…”


Misalin ƙarfe 2 na dare....

WURIN ABEESH…
Dare ya tsinke da shiru. Kamar kowane dare, an jima da kashe fitila, sai hasken farin wata daga tagar ɗakin da ke daddarewa a bango, Amma ba barci a idon Abeesh. Sai juye-juye yake yi a gado, yana tunani.

Tunani ne cike da rikici da soyayya, fushi, ruɗani, da sabon abu mai kama da jaraba.

Ji ya yi an buɗe ƙofar ɗakin sa a hankali, juyowa ya yi yana kallon bakin ƙofar.

Catrina ce ta zo masa a hankali, tana daɗa rage tazarar dake tsakaninsu, tana sanye da rigar baccin ta...

Abeesh ya tashi zaune tare da faɗin
“Ke kuma? Me kike nema a nan cikin dare?”

Catrina ta dafe ƙofa tana dariya ƙasa-ƙasa sannan ta ce

“Na kasa yin bacci, Sai naji kamar zan fi samun kwanciyar hankali idan na ganka... King Abeesh....”

Ya runtse ido. Wannan sunan da ya ji a bakin ta tamkar sabon wata ne ya ratsa cikin zuciyar sa da wani salo mai ɗauke da wani sirri, mayar da idonsa ya yi kanta tare da kama bakinsa,
Ya ce

“Wannan ba daidai bane. Ki koma ɗakinki.”

Catrina ta matso kusa da shi sannan ta ce
“Ban zo da mungun niyya ba. Kawai ina so ka san cewa ba kai kaɗai bane a cikin jin zafi…”

Abeesh bai ce komai ba. Sai dai yanda take kallonsa, kamar ta fahimci komai cikin zuciyarsa. Cikin daddadan murya da dabara, ta matsa kusa da shi sosai. Hannunta ya sauka a kan hannunsa, Tana son jin irin karfi ko rauni dake cikin rayuwarsa.

Zuciyarsa na yawo. Bai tura hannunta ba. Amma kuma bai kama ba.

Abeesh ya ce

“Kin san inada rauni Catrina... Kuma ni... ni ba mutumin da ke saurin yarda da sababbin mutane ba ne...”

Catrina ta saka murmushi sannan ta ce

“A lokacin da waɗanda ka yarda da su suka raunata ka, wani lokacin, sabon mutum na iya zama mafita…”

Yayi shiru. Zuciyarsa tana tafasa da ruɗani. Cikin zuciyarsa, yana jin kalamanta suna ratsa shi. Sai dai a lokaci guda yana jin kamar wani ɓangare daga cikinta yana ɓoye wani abu.

Shiru ya shiga tsakaninsu.

Catrina ta miƙe tsaye cikin salo, ta zuba masa idanu.
Sannan ta ce

“Zan tafi… Amma zan dawo. Kuma in Allah ya yarda, wannan zuciyar taka zata dawo da murmushinta.”

Ta juya. Sai kuma ta tsaya a ƙofa, ta ce:

“Nasreen ta rasa hanya. Amma ni zan iya nuna maka sabon titi... Titi na gaskiya... ko kuwa na mafarki.”

Tana kaiwa nan ta fice a ɗakin, tana fita
ta ɓace cikin duhu.


---

A GEFE GUDA – NASREEN…

Nasreen tana zaune a gefen gado, hannunta ɗauke da littafin addu’a. Amma ba karatu take ba – kallo ɗaya kawai take wa shafin,
Zuciyarta na cike da ƙuna.

Wani abu yana ƙona ta fiye da zafin kalmomin Abeesh: yanda ya kalle ta kamar bai taɓa sonta ba, da kuma yanda bai damu da halin da take ciki ba...

Sai dai Nasreen ba mace bace da zata zuba ido ta bari soyayyarta ta rushe. Ta miƙe, ta saka mayafi, sannan ta furta da ƙarfi:

“Zan kare soyayyata. Ko da zan rasa komai. Ko da zan tafka kuka. Amma ba zan bari wata yarinya ta kwace min miji ba.”.....

NEXTTTTTT........


New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

41 to 42



A DAKIN ABEESH…

Tsakar dare ne. Shiru ya mamaye gidan. Daga wani ƙaramin fitilar bango ana iya hango Abeesh zaune a gefen gado, da labulen window a buɗe yana kallon duhun dare yana tunani.

Tunaninsa cike yake da abubuwa biyu: Catrina, wacce ke da wani jan hankalin da ba zai iya fassara ba… da kuma Nasreen macen da ya fara soyayya da ita da zuciyarsa gaba ɗaya — amma ta raunata shi.

Ya dafe kansa. “Me yasa komai ke rikicewa haka?” Yayi tambaya cikin zuciyarsa.

Ƙaran ƙofa ya ji

Ya juyo da sauri.

A hankali ƙofar ta buɗu, Nasreen ce, cikin doguwar riga mai launin ruwan hoda da hijabi a kafada. Idonta cike da hawaye, fuskar ta sharaf da damuwa. Ta tsaya a ƙofar ba tare da ta shigo ba

Abeesh cikin mamaki da ɓacin rai ya ce

“Ke kuma... me kike nema a nan?”

Nasreen cikin murya mai rauni ta ce

“Ina son magana da kai, Abeesh... ka bani minti daya... na roƙeka.”

Ya ɗan kalle ta, yaja numfashi mai nauyi, ya ɗan matsa gefe a gefen gado, bai ce komai ba yayi mata alamar ta shigo.

Nasreen ta shigo a hankali kamar wacce take takawa akan ƙaya. Zuciyarta na bugawa, idonta na kallon sa har ƙasa.

Sannan ta ce

“Na san baka shirya ji daga gare ni ba... kuma gaskiya ne, na yi maka babban laifi. Amma zan mutu cikin nadama idan baka yafe mun ba...”

Abeesh ya ɗago kai ya kalle ta sannan ya ce

“Wani laifi kika aikata har ya sa kika zo da dare neman gafara?”

Nasreen ta durƙusa ƙasi, idanunta cike da ƙwalla ta ce
“Na mare ka, kuma na goyi bayan mahaifiyata, wacce ta raɗa maka azaba har ka rasa komai da ka sani... kuma da zuciya ɗaya nake cewa na tafka kuskure...”

hawaye ne suka zubo daga idonta.

ta ci gaba da cewa
“Nayi kuskure na zaɓar tsoron mahaifiya akan gaskiyar da zuciyata ke gani. Kuma zuciyata ta san kai ne hasken da nake nema. Amma tsoronta da karfinta ya sa na tsorata… nayi maka rashin adalci...”

Abeesh ya kalle ta. fuskar sa a washe Amma zuciyarsa bata sake ba. Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komai ba. Daga bisani yace:

“Kin san mene ne ya fi komai zafi a rayuwa?”

Nasreen ta girgiza kai
Sannan ta ce
“Mene ne?”

Ya ce

“Kin fi jin zafin mari da kalma, amma ni, na sha wahala cikin duhun da mahaifiyar ki ta jefa ni a ciki, na rasa tunani, na rasa imani... kuma da kika mare ni, ba wai fuskata kika mara ba — rayuwata kika ƙara jefa cikin ƙunci.”

Nasreen ta fashe da kuka.
Ta ce
“Idan zan iya komai don in gyara kuskuren nan, zan yi. Zan tsaya a gabanka kullum in zubar da hawaye na har sai zuciyarka ta huce. Zan yi komai don in dawo da kai… Abeesh... kar ka bar ni.”

Shiru ya yi ba tare da ya furta komai ba, Ya tuna kukan da yayi a lokacin da ya rasa komai. Ya tuna yanda zuciyarsa ke son Nasreen... amma yanda ya tsani abinda tayi masa ya wuce misali...

Ya juyo gareta, cikin murya mai sanyi da kuma karfi yace:

“Zan iya gafartawa… amma bana iya mantawa da azaba cikin sauri. Ki bar ni na zauna da zuciyata. Idan da gaske kina sona, ki bani lokaci… ki bani sarari...”

Nasreen ta gyaɗa kai da hawaye, ta miƙe a hankali, ta fita da zuciyarta cike da fargaba da fatan nasara...

★★★★★★

*WASHE GARI*

Ana shirye-shiryen bikin Abeesh da Nasreen, da kuma Shaprees da Asmeen.

Gidan Madam Nablah ya cika da shirye-shiryen biki — kallo ɗaya zaka yi ka fahimci ana shirin wani babban abu. Falo da tsakar gida sun sha ado da launuka masu ban burgewa. an rataya fitilu da fure a jikin bangon gini, ƙamshi na turaren wuta da bakhoor yana yawo har cikin sararin gidan....


Abeesh
Kwance yake a cikin ɗakinsa, yana kallon saman ceiling ... zuciyarsa taƙi nutsuwa. Catrina dai ta riga ta fara nasara wajen ɗaga masa hankali — duk da bai
End Ads