da ɗora tafin hannunta a saitin zuciyar sa tana faɗin "ka cigaba da haƙuri da juriya, na san yanzu ka fara sonta sosai, ina so ka cire fushi a ranka...."
Jinjina kai Shapreen ya yi tare da faɗin "ina sonta sosai, lokaci guda naji ta mamaye zuciyata, Nagode miki da kika taimaka mun wurin kawar da duhu daga cikin rayuwata, kika musanya da hasken alkhairi....."
Sofia wasu zafafan hawaye taji sun fara gangaro mata akan kumatu.....
Shapreen hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba a ruɗe ya ce "me me meya faru Sofia...."
Tana kuma ta ce "ka riga da kasan cewa Sofiyyar ka tana da kishi, har yanzu ban canza ba koda ina matsayin ruhi, zan tafi domin yanzu zuciyar ka ba tawa bace...."
Shapreen a ruɗe yake faɗin "ah ah Sofia kin riga da kin san cewa ke ce duniya ta, kuma har yau ina alfahari da ke, babu macen da zan so sama da ke a rayuwa, sai dai na kwatanta amma ko rabin ki bazata kai ba...."
Girgiza kai Sofia ta yi sannan ta ce "ban hana ka so ta ba amma kada ka manta da ni...."
Tana kaiwa nan ta ɓace, sai ƙamshin haske da ta bari a wurin....
Shapreen zama ya yi a bakin gado tare da cusa yatsun sa a cikin sumar kan sa......
---
Catrina tana zaune a bakin gadon ta sha kwalliya tana sanye da rigar bacci marar nauyi, tana jiran shigowar Abeesh domin ta tura masa message akan tana son ganin sa a ɗakin ta, bata jin daɗin jikin ta..
Abeesh kuwa jin haka bai jira komai ba ya zura jallabiyar sa ya yi waje da sauri, a falo ya tarar da Nasreen zaune tana jan carbi idonta akan plasman tana kallon tapsirin wa'azi..
Yana tsaye ata bayanta domin bata san ya fito ba, tsaya tunanin yanda zai yi ya wuce ɗakin Catrina ya yi domin dole sai ya bi ta gaban ta idan yana son zuwa ɗakin...
Ɗaga kansa ya yi yana kallon agogo, yanzu ƙarshe 12 saura na dare, fuska kawai ya yi ya shige falon, zama ya yi a kan kujerar gefen ta tare da faɗin "baki yi bacci ba?..."
Kallon sa tayi tare da jinjina kai ba tare da ta furta komai ba,
ya kuma cewa "meya hanaki yin bacci a wannan lokacin?..."
Bata ce komai ba idonta akan plasman...
Cikin fushi ya miƙe tsaye yana faɗin "wato kin mayar ni ƙaramin yaro ko? ina miki magana kina wani shan ƙamshi, ni ya dace nayi fushi da ke ba wai ke ba...."
Nasreen ko kallon yanda yake bata yi ba still idonta akan plasman, ciro wasu allurai ya yi a cikin aljihun jallabiyar sa da maganinnuwa yana faɗin "kin ga wancan yarinyar bata da lafiya, tana cikin mawuyancin hali zanje nayi mata allura sannan na bata maganin da ya kamata ta sha...."
Daga nan ya wuce kai tsaye upstairs da zai kai ka can ɗakunan baƙi ya haura da sauri-sauri...
Nasreen har ya gama haurawa bata ɗauke idonta akan sa ba, tana mamakin yanda Abeesh ya zama haka lokaci guda, kuma ma saboda ya raina mata wayo wai wancan yarinyar bata da lafiya....
Haka take ta maganar zuci, ta cigaba da zama zata jira fitowar sa....
Kallon agogo tayi taga ƙarshe 12 yanzu na dare.....
Abeesh ya zuwa ya fara buga ƙofar.
Catrina ta buɗe da murmushi kwance saman fuskar ta...
Catrina ta masa maraba da murmushi mai ɗaukar hankali, tana sanye da riga mai launin ja mai haske, wacce ke bayyana surar jikinta, tana ɗauke da ƙamshi mai ɗaukar hankali.
Abeesh bai ce komai ba, ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita. Kallon ta kawai yake yana jin wani sanyi da dumin sha’awa yana ratsa jikinsa. Catrina ta riƙo hannunsa cikin nata, ta ce da shi da murya mai sanyi
“Ban san yadda zan bayyana maka yadda nake jin ka ba, Abeesh. Amma zuciyarka tawa ce gaba ɗaya...”
Ya kalli idonta, ba tare da ya iya furta komai ba. Sai dai ya ji zuciyarsa na amsawa da karfi. Wannan dare ba dare ba ne na wucewa kawai—zai zama makasudin sauyin soyayya..
haka yake kallon fuskar ta kamar wanda ya samu madubi, daga bisani ya ce
"ke bakya gajiya da murmushi ne? ban taɓa ganin ki cikin fushi ba..."
Catrina zama tayi a bakin gado tare da faɗin "an halicci murmushi nane saboda kai, meyasa zaka ga fushi na kuma...."
“Abeesh...”
ta furta da wata murya mai narkar da zuciya ta ce "cutar kewar ka ne ya kamani, zan iya samun mungun matsala idan na cigaba da zama a haka ba tare da kai ba...."
Sakin numfashi ya yi tare da faɗin
“Zan zauna tare da ke na ɗan wani lokaci, ki kasance da zuciyata, in har shine muradin ki...."
Jan hannunsa tayi ya faɗa saman kanta tana faɗin
“Ba kawai zuciyar ka ba… har ma da dukkan ruhin ka nake so.…”
Kallon cikin idonta ya yi... sai kawai ya sauƙa daga kanta ya zauna a bakin gado yana girgiza kai tare da faɗin "bana son wani abu ya shiga tsakanin mu, har yanzu zuciyata bai gama yanda cewa zan iya aikata wani ɓarna na saɓon Allah ba, in har kina so na da gaske to ki guji jefa ni a cikin wani halin da zai sa na kusanci macen da ba muharrama ta ba, ina nufin zina...."
Catrina jinjina kai ta yi ta ce "nayi maka alƙawarin babu abinda zai shiga tsakanin mu sai alkhairi, amma dan Allah ina so a wannan daren ka zauna dani, ko zan iya bacci...."
Abeesh ya ce "yanzun ya kike jin jikin nakin? na taho da allurai..."
Catrina zato ido tayi ta ce "ni kuma meya haɗani da allura bayan nace cutar kewar ka ke damuna, kaine magani na, ka kwana dani sai na fi samun nutsuwa...."
Abeesh kwanciya ya yi a bakin gado, itama kwanciya tayi a gefen sa tare da rungumo shi tana kallon kyakkyawan fuskar sa....
Nasreen kuwa har misalin ƙarfe 3 ta kai na dare tana jiran fitowar Abeesh daga ɗakin Catrina amma shiru har bacci ya ɗauke ta akan kujerar falo...
Daren ya gangara cikin nutsuwa da ɓoyayyun ruɗani. Abeesh ya kwana a ɗakin Catrina zuciyarsa cike da rikice-rikice, amma jikinsa yana masa jagora cikin natsuwa kamar yana bin saƙon da zuciyar sa ke masa.
-------Ƙiran Asubar Farko akan kunnen Abeesh, buɗe idonsa ya yi yana bin ɗakin da kallo, a hankali ya maida idonsa kan Catrina wacce take kwance akan ƙirjinsa bata samu farkawa ba...
A hankali Abeesh ya ture ta gefe sannan ya tashi jiki a sanyaye ya fice a ɗakin, yana sauƙa falo ya tarar da Nasreen a wurin da ya barta tana kwance akan kujera idonta a lumshe kamar mai yin bacci, sai dai ba baccin take ba, da sauri Abeesh ya wuce gudun kar ta buɗe ido ta gan shi, yana wuce wa Nasreen ta buɗe ido tana jinjina wannan lamarin, tasan Abeesh ne ya wuce domin tin sauƙowar sa ta gan shi, ganin sa ne yasa ta lumshe idonta....
A yau bata tanka masa ba, kuma bata nuna masa cewa tasan a ɗakin Catrina ya kwana ba, haka ta zuba masa ido,
Ganin haka yasa a kwana na biyu Catrina ta ƙara neman sa, a wannan lokacin ƙiran sa tayi tana kuka, ganin haka yasa ya fita nan ma da daddare ne misalin ƙarfe 10...
Fitarsa ke da wuya ya fara leƙe-leƙe gudun kar ya tarar da kowa a falo, duk wannan lelleƙawar da yake Nasreen tana tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon sa, hannun ta riƙe da kofin tea zata sha domin yanzu bata iya cin komai, da haka ya wuce ɗakin Catrina, a yau ma acan zai kwana....
A wannan ranar Nasreen kwana tayi bata yi bacci ba, tana kwance a ɗakin ta tana kuka kamar ranta zai fita. Idonta ya kumbura, zuciyarta cike da raɗaɗin kishi da bakin ciki. ita kaɗai sai juyi take a gado gaba ɗaya kwanciyar hankali ya ƙaurace mata....
Da safiyar gari, kafin kowa ya farka, Nasreen ta tafi ɗakin Tasleem.
Tasleem tana kan sallaya yanda ta idar da sallar asuba, ganin Nasreen a cikin wani hali ne yasa tayi saurin miƙe wa tsaye tare da faɗin
"lafiya kuwa Nasreen? me yake faru wa?...."
Nasreen sai da ta rungumi ‘yar uwarta Tasleem kafin ta fashe da kuka, tana sharar hawaye cikin muryar kuka take faɗin
“Tasleem... na gaji! Kamar a cikin mafarki nake, yana kwana da wata a yayin da ni nake matsayin matarsa! Kuma ya kasa fitar da ita daga zuciyar sa... kina ganin zan iya ci gaba da wannan zaman?”
Tasleem ta saki numfashi da ƙarfi, baƙin ciki da tausayin Nasreen ne suka shige zuciyarta.
Ta dafa kafadarta tana faɗin
“ Na fahimce ki, Nasreen kiyi haƙuri... amma ki barni da ita. Wallahi sai ta gane cewa gidan nan ba na raini bane. Wata iriyar ‘yar bariki ce haka? ko ita ɗin mutum ce ko ba mutum ba ce—wallahi sai na tunkare ta!”...
Tasleem ta share mata hawaye tana faɗin "ki yi haƙuri ki sa salama a cikin zuciyar ki, ki daina bayyanar da damuwar ki a wanda yake son ganin bayan ki, yanzu ki je ki huta zan neme ki...."
Nasreen jinjina kai kawai tayi tare da ficewa daga ɗakin....
---.
Shaprees yana ɗakin su yana kallon Asmeen wacce ta fara narkewa a hankali. A wannan ranar, ta zauna kusa da shi a cikin dakin su na ma'aurata, tana tausayin yadda yake kokarin kyautata mata ba tare da nuna tsana ko kishi ba.
A hankali ta furta
“Shaprees... baka san yadda nake jin ba a raina, na jima ina tunanin kai wani ne dabam, amma yanzu ina ganin... ka cancanci ka samu farin ciki.”
Shaprees ya kama hannunta, yana kallon ta cikin kulawa ya ce:
“Ina so ki yarda dani, Asmeen. Na cire duhu daga zuciyata domin Allah. Soyayya da alheri nake nema yanzu. Kiyi ƙoƙarin bani dama dan Allah...”
Asmeen wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata tare da rungumar sa tana kuka...
Shima rungumar ta ya yi yana rarrashin ta cikin so da ƙauna..
Haka kawai yake jin tausayinta, especially jin ƙudurin mahaifiyar ta akan su....
★★★★★★★
A yau...
Tasleem ta tunkari Catrina da fuska ɗauke da zafin zuciya da tsantsar fushi...
Tarar da ita tayi a zaune a falo tana kallon wani Film na horror..
Tasleem tsaya mata tayi a kai cikin tsantsar matsifa take faɗin
“Ke! Na gaji dake, Kina wasa da zuciyar ‘yar uwata, da mutuncin mijinta. Ko kin manta wannan gida na mutunci ne? Kin raina mana hankali?”....
Catrina ta ɗaga kai tana kallon Tasleem cikin kwanciyar hankali, murmushinta bai gushe ba. Ta ce da ita:
“Wannan gidan ne na mutunci ko kuma mutanen cikin ta?
Hmmmm! Idan zuciyar mutum ta mallaki wani abu, ba laifi bane. Shin idan mijin ‘yar uwarki yana nuna mun soyayya... hakan laifi ne?”
Wani irin cakuma Tasleem tayi wa sumar gashin ta tare da ɗago ta tsaye, Catrina daƙer ta fizgi gashin ta tana faɗin "Ashhhh!! kina hauka ne?..."
Tasleem tana zaro ido waje ta ce
"Yau zan nuna miki yanda ake asalin hauka, Indai zaki cigaba da bibiyan mijin ƴan uwata to sai na gurɓata miki rayuwa, shaiɗaniyar banza, karuwar gida, idan mazajen mutane kike so ki fita can bariki suna jiran wanda bai zo duniya ba ma, amma ba'a cikin gidan nan ba, domin kaf babu la'anannu, da mutuncin mu da darajar mu haka kuma da kimar mu mun kuma san kunya..."
Tintsirewa da dariya Catrina tayi tare da faɗin "da farko dai ki fara zuwa ki tuntuɓi mijin ƴar uwar takin, ki bashi zaɓi shin yana so nane ko kuwa, idan ya baki amsar eh yana sona to kuwa sai dai kuyi haƙuri domin ba bu yanda zaku yi da ni, na zamo muku ciwon ido a cikin gidan nan...."
A fusace Tasleem ta shaƙo wuyan ta tana faɗin "aww haka ma kike cewa? ai kuwa zaki bar gidan nan tinda ba gidan uban ki bane...."
Itama Catrina riƙo ta tayi nan suka fara kaurewa da faɗa...
Tasleem da Catrina sun shiga faɗa mai zafi. Gidan ya ɗauki ƙarar fashewar glashe yanda suke ta faffasawa duk a cikin faɗan, kayan ado da fitilu na falo duk suka faffaɗo ƙasa suna tarwatsewa kamar hayaki, kowa yana ji da ƙarfin sa domin akwai sirrin ƙarfi a jikin su wanda yake ɗauke da Haske da Duhu....
Catrina ta fisgi labulen taga, ta wurga wa Tasleem ta faɗi ƙasi ita da labulen, itama haka ta zuciyo ta miƙe tare da janyo kofunan glass dake jejjere akan dinning ta wurga wa Catrina sai akan goshin ta, nan da nan goshin ya fashe, a ruɗe Catrina ta sau wata ƙara....
Tasleem nuna ta take da yatsa tana faɗin:
"Kin raina mana hankali Catrina! Ke ba mutuniyar kirki bace. Kawai kin zo da niyyar ruguza soyayya ne! Kin fi karfin mu ke?!"
Catrina ɗago wa tayi tare da ɗaga gira, tana goge jinin da ke zubo mata akan goshi, fuska ɗauke da murmushin da ke ɗora wuta a zuciyar Tasleem. Ta ce da ita:
"Na fi karfin zuciyoyin ku gaba ɗaya, Ke ki ke taya ƴar uwarki faɗa akan mijinta, ni kuma na riga da na mallake shi. Na shiga ransa yanda bazai iya manta ni a rayuwar sa ba...."
Tasleem ta furta
“Ukkk!” sannan ta nufi Catrina da niyyar fin karfin ta, suka kama juna da faɗa mai zafi, tana jan gashinta, tana hura hanci cikin fushi tana faɗin
"Sai kin fice daga gidan nan da kanki!"
Catrina kuma ta riƙe rigar Tasleem tana janta itama, har suka faɗi saman kujerar falo nan kujerar ta dungura da su, faɗa suke na gaske, Catrina ganin Tasleem tana shirin fin ƙarfinta yasa ta kafa haƙwaranta akan breast ɗin Tasleem ta garzaya mata ciwo, ba shiri Tasleem ta sau wata iriyar ƙara mai rikitarwa, sai da falon ya ɗau sautin....
Falon ya koma kamar wurin faɗan aljanu.
Amaar da Abeesh jin ƙarar ihu yasa suka shigo falon a guje.
Amaar ya damƙe Tasleem yana kokarin jan ta gefe, yana rarrashi ta...
Tasleem tana kuka tana faɗin "wallahi mayya ce yau saina yi maganin ta, ka barni na zubar mata da haƙora....."
Amaar cikin tashin hankali yake faɗin
“Tasleem! Dan Allah ki bari! Wannan ba hanya bace. Ki duba kanki fa!”
Abeesh kuwa ya ja Catrina yana faɗin:
“Catrina! Enough! Ki dakata! Wannan ba shine nake so ba.”
Tasleem ƙwace wa tayi daga hannun Amaar ta sake nufo Catrina. Gaba ɗaya gidan ya cika da hayaniya da tashin hankali...
Daƙer Amaar ya sake riƙo ta tare da rungumar ta sosai....
A cikin wannan rikici, sai ga Nasreen ta fito daga kitchen hannunta rike da wuƙa mai kaifi. Idonta jajir, zuciyarta na tafasa kamar ruwan zãfi. Ta nufi Catrina kai tsaye da nufin caka mata tana faɗin:
“Kina son kashe mun aure ko? Zaki kashe rayuwata ko? Wallahi sai na nuna miki ni matarsa ce ba ke ba!”
Abeesh da ya hangota da wuƙar ya yi saurin tarar ta da ƙarfi ya damƙe hannunta yana faɗin:
“NASREEN! Ki sauƙe wannan wuƙar! Wannan faɗa ba mafita bace. Kar ki zama mai laifi akan soyayyar da ke rikitar da kowa.”
Nasreen fashe wa tayi da kuka tana ƙoƙarin ƙwace wa tana nuna Catrina da wuƙar, tana faɗin
"Wallahi yau babu abinda zai hana na kashe ta, sai na rabata da rayuwar ta...."
Amaar ya nufi wurin da Abeesh yake riƙe da Nasreen yana faɗin
"Kin ga Nasreen ki kwantar da hankalin ki, ke ce mai hankalin cikin ku ki saurara...."
Kafin Amaar ya rufe baki Tasleem ta tafi da gudu ta damƙi wuyan Catrina tare da girban sawayen ta sai yaraf a ƙasi, Tasleem danne wuyan ta tayi sosai a ƙasin carpet tana faɗin:
"Nasreen zo ki huda cikin ta da wuƙar nan, umarni nake baki yanzu...."