sannan ta nufi yanda Catrina take tsaye a gefen su tana sauraron tattaunawar da suke....
Nasreen tana iskota ta shaƙo wuyan ta da ƙarfi, tana faɗin:
"Zan bar miki shi! Ki cinye shi nama ɗanye idan kina so! Shashasha! Ƙaruwar banza!"...
Catrina kuwa bata ce uffan ba, sai shu’umin murmushi da take yi, kamar tana jin daɗin ruɗanin da ta jefa su a ciki.
Nasreen ta juyo da ƙarfi tana jan akwatin ta tayi hanyar waje tare da faɗin:
"Duk wanda ya biyo bayana, wallahi ban yafe masa ba!"....
Ta fice da hanzari. Kowa ya tsaya kamar babu rai a jikin su...
Catrina maganar zuci take tana faɗin:
"Na fara cin nasara. Amma ba zai tsaya a nan ba... Nasreen, ba barin gidan zaki yi kawai ba — zaki bar duniyar gaba ɗaya ne ...."
Cikin takaici Tasleem ta juyo tana kallon Abeesh, wanda ya zauna a kujera cikin tagumi ya rasa mai yake masa ciwo a jiki,
Cikin ɗaga murya ta ce:
"Shikenan. Hankalinka ya kwanta ko? Matarka ta bar maka gida saboda wata ƙazamar banzar Catrina. Wallahi ka bani kunya!"...
Abeesh a firgice ya miƙe da fushi yana daka mata yatsa cikin nuna yatsa yake faɗin:
"Dakata Tasleem! Kar ki kuskura ki zage ta a gabana!"...
Tasleem ta ɗan zaro ido, hawaye na gangarowa ta ce:
"Saboda na faɗi gaskiya? Kenam tafi Nasreen a wurin ka? tabbas abun nakan ya fara wuce gona da iri, dole akwai wani abu a ƙasa ba baka kawai aka barka ba, amma zan binciko koma menene...!"
A fusace Abeesh ya nufi ɗakinsa a ruɗe, ba tare da ya furta komai ba...
Catrina ma ta shige nata ɗakin ba tare da wata magana ba...
Tasleem ta zauna a kan kujera, tana kuka mai zafi, tana tunanin wani irin hali ƴar uwarta zata shiga..
_____________🚗💥
Nasreen tana tuƙi cikin gudu, zuciyarta cike da takaici da ciwon zuciya tana faɗin:
"Me yasa Abeesh ya zama haka? Me yasa ya canza lokaci guda kamar ba Abeesh ɗina ba? Me yasa zan zauna da mijin da bai girmama ni ba?"...
Tana cikin maganar zuci
Kwatsam — wani duhu ya bayyana a gaban motarta, glass ɗin gaba ya rufe da baƙin hayaki. Nasreen ta firgita tana ƙoƙarin danna birki, domin ba wani ganin hanya take ba, ga shi ba dare bane balle ace dare ne ya yi, misalin ƙarfe 8 na safe ne yanzun....
Cikin baƙin wannan duhu, Catrina ta bayyana a siffar iska, tana murmurshi cikin mugunta tare da faɗin:
"Kin fice da kafafunki… amma ba zaki koma da su ba, Nasreen."...
A ruɗe Nasreen ta dakatar da tuƙin ba tare da ta ga a yanda take ba, ta tsaya ne a tsakiyar road dai-dai shan kwana, kafin ta ankara
Sai kwatsam — wata babbar mota (trailer) ta fito da gaggawa daga ɓangaren hagun, ta buge motar Nasreen. Motar ta dungura ƙasa cikin rami....
Haka motar take ta dungure tana hawa sama da ƙasa har ta je ta bugi wata ƙatuwar mota, kafin ƙingawar ido motar ta tashi da wuta sai da tayi sama kafin motar ta kife a ƙasi, tayoyin motar suna kallon sama a ya yin da motar take ta ci da wuta.....
Daga nesa wasu suka ji ƙarar fashewar mota......
Misalin ƙarfe biyar na yamma, hasken rana yana ɗan dushewa, cikin gidan da ke cike da sirrin duhu da ruɗani, Tasleem na zaune a falo, ta dafe ƙirjinta kamar wacce zuciyarta zata fashe. Tana birgima akan carpet, tana nishi kamar wacce ke shirin mutuwa...
Tana magana a cikin ranta kamar zata haɗi yi zuciyar ta cikin azaba take furta:
"Wayyo zuciya ta zata fashe... wani abu ya faru... nasan wani abu ya faru da jinina... wayyo Allah naaa... Nasreen ta bar gida, amma yanzu kamar ba barin gidan kawai tayi ba, NAJI... NAJI KAMAR RANTA BAYA JIKINTA....!!"
Tana cikin wannan halin sai ga Amaar ya shigo, ya dawo daga wurin aiki ne, yana sanye da uniform ɗin Sojoji, har yana shirin wuce wa idonsa ya sauƙa akan Tasleem wacce take ta birgima a ƙasin carpet....
Da gudu ya ƙara sa wurin da take yana faɗin:
"Tasleem?! TASLEEM!!!"
Ya durƙusa ya ɗago ta, yana riƙe da kanta da hannunsa biyu, yana kallo cikin idanunta masu cike da hawaye da tsoro Ya ce:
"Lafiya kuwa?! Me ya faru?! Ki faɗa mun mana! Tasleem ki faɗa min me ke damunki!"
Tasleem tana kuka cikin ƙarfin murya, tana riƙe da ƙirjinta kamar wacce zuciyarta ke konewa da wuta Ta ce:
"Zuciyata... Yah Amaar zuciyata tana ƙuna... kamar da gaske... zuciyata na konewa... wani abu ya faru da Nasreen, wallahi wani abu YA FARU!!!"...
Sai ga Abul ya fito daga ɗakinsa da sauri jin kukan Tasleem domin da ƙarfi take, shima cikin alhini Abeesh ya fito daga ɗakin da, sai ga Catrina da ke tsaye kamar wacce ke kallon fim.
Amaar ya miƙe ya kalli kowa, sannan ya ce da Abul:
"ABUL, wani abu ya faru. Tasleem ba zata faɗi haka ba idan har ba da gaske bane, Ku ƙira Nasreen a waya! Ku ƙira ta yanzu!!"...
Abul ya ɗauki wayarsa da sauri, yana kiran lambar Nasreen, amma wayar bata shiga. Abeesh shima ya gwada—amma wayar a kashe.
Tasleem ce ta ɗaga kai tana faɗin:
"Wallahi Catrina ke da laifi! Ita tasa ta bar gidan, kuma yanzu na ji a jikina ba lafiya take ba...!"
Catrina ta yi murmushi kaɗan, ba tare da ta ce uffan ba. Abul ya harzuka, yana kallon Catrina da wani irin kallo na fahimtar gaskiya. Ya san akwai ɓoye-ɓoye....
🫀 ASMEEN......
A can cikin ɗakin alfarma, Asmeen na zaune gaban mirror tana shirya kanta cikin kyakkyawan kaya na masarrafa, tana samu farin ciki SOSAI a wurin Shaprees....
Shaprees, mai zurfin ido da juyin tunani, yana zaune a bakin gado yana kallon ta. Yana murmushi da faɗin:
"Wallahi Asmeen, yau ke kika fi kowacce mace kyau. Kin fi gimbiyar aljanu kyawu. Ni ke da sa'a da aka bani ke a matsayin mata."
Asmeen ta dan murmusa cikin yaƙe domin ba jin daɗin jikinta take ba, haka kawai take jin wani abu a cikin zuciyar ta na ƙoƙarin taso wa....
kafin zuciyarta ta buga da ƙarfi!
Ta dafe ƙirjinta da sauri, ta jingina da mirror tana kurma ƙara tare da faɗin:
"WAYYO ALLAH!!! ZUCIYATA!!!"
Shaprees ya yo kanta a ruɗe, yana faɗin:
"Asmeen? Lafiya kuwa?! me ke faruwa?"
Asmeen cikin rawar murya take faɗin:
"Shaprees, zuciyata kamar zata buga. Wani abu ya faru da jinina. Wani abu ya faru da wanda ban san meye ba...... ban san meye ba amma ina jin mutuwa... ina jin bala’i!"...
Sai kuma ta fashe da kuka, tana ƙwalla da gaske. Ta durƙusa a ƙasa tana faɗin:
"Dan Allah ka kaini wurin Tasleem! Ka kaini wurin Nasreen! Ina jin mutuwa! Ina jin zan rasa wani abu mafi soyuwa a cikin zuciyata...!"
Shaprees ya riƙo ta shima yana jin wani abu a zuciyarsa, babu abinda ya gani da idonsa amma zuciyarsa ta motsa da fargaba.
Zuciyarsa ta faɗa masa cewa:
"Wani abu ya tashi daga cikin duhu. Wani abu ya motsa da yuwuwar halaka..."
Shapreen kallon Asmeen ya yi tare da faɗin:
"Subhanallahi ki kwantar da hankalin ki babu abinda ya faru,...."
Haka yake ta faman rarrashin ta...
Amma furrrr Asmeen ta kasa kwantar da hankalin ta domin yanda zuciyarta yake bugawa in bata ga ɗaya daga cikin ƴan uwanta ba za'a iya samun matsala...
Shapreen ne ya ɗago ta tare da faɗin:
"Kin ga tashi mu tafi part ɗin su yanzu, zaki ga babu abinda ya faru da su..."
Dasauri Asmeen ta miƙe ta yi gaba da gudu zata fice.....
★★★★★★
Falon gidan ya kasance cikin shiru sai numfashin da ke fita da ƙarfi ta ɓangaren Tasleem da hawayenta dake bin saman kuncin ta. Kanta na kwance akan cinyar Amaar, wanda ke goge mata gumi da hawaye, shima ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba.
Tasleem har yanzu tana dafe da ƙirjinta, numfashinta na fita da ƙyar, tana furta cikin raunin murya:
“Zuciyata… wayyo Allah, zuciyata tana ƙuna… Wani abu ya faru da jinina, na rantse da Allah…”
Abul da Abeesh suna zaune a kujerun falon suna kallon ta cikin ruɗani da damuwa. Kowa na kallon ɗan uwansa, amma babu wanda ke da amsa, domin har yanzu babu wanda ya san takamaiman abinda ya faru da Nasreen. Sai dai kowa na jin akwai wani abu marar daɗi yana shirin bayyana.
A daidai lokacin — suka ji
🚪 ƘARAR BUƊAR ƘOFA...
Asmeen ce ta shigo cikin falo da gudu, zufa na keto mata a fuska, idonta cike da hawaye, zuciyarta har yanzu na bugawa kamar wata ƙarar ƙaho. Kafin kowa ya ce wani abu, idanunta sun sauƙa kan Tasleem — kwance, kamar wacce za ta gama da duniya.
A ruɗe ta furta:
"TASLEEM!!"
Da sauri Asmeen ta faɗi ƙasa, ta rungume Tasleem tana kuka kamar ƙaramar yarinya, tana faɗin:
"Na gode Allah, na gode Allah babu abinda ya same ki!! Zuciyata bugawa take kamar zata tsage! Tasleem…ina Nasreen?! Ina 'yar uwar mu?!"
Tasleem ta janyo Asmeen cikin ƙarfi, suka rungume juna suna kuka kamar 'yan uwan da bala’i ya raba, amma zuciyarsu ta haɗu.
Amaar ya ƙura musu ido, yana girgiza kai cikin tausayawa da ruɗani. Abul ya sauƙe ajiyar zuciya cikin damuwa,
Abeesh ya lumshe idanu yana jin wani nauyi a kirjinsa da bai iya bayyana wa ba.....
Sai ga Shaprees shima ya shigo falon da sallama a bakin sa yana kallon halin da ake ciki. Ya durƙusa yana kallon Tasleem da Asmeen, ya ce a hankali:
“Me ya faru? Ku gaya min... wani ya mutu ne? Wani abu ne ya faru da wani a cikin gidan nan..?”
Tasleem girgiza kai tayi tana faɗin:
“Wallahi bamu san me ya faru ba. Amma zuciyarmu na sanar da mu cewa wani abu mai muni ne ya faru. Muna jin hakan a jikimmu kamar jininmu muka rasa...…”
Shapreen ya ce
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allah Ubangiji ya rufa asiri, Insha Allahu babu abinda ya faru...."
★★★★★★
🕯️
A can cikin ɗakin ta Catrina na tsaye a gaban madubi tana murmushi. Ta cire doguwar rigarta ga ajiye a gefe ta zauna daga ita sai breziyya da gajeran wando tana kallon kantacikin muguwar shauƙi. Idonta ya canza launi, yana dishewa da duhu kamar wanda ya taɓa wutar ruhi
A sassanyar murya ta furta:
“Sai dai ba ku san wani abu ba... a koda yaushe Ni ce mai nasara... da zarar labari ya iso gare ku cewa motar Nasreen ta kama da wuta...”
Ta lumshe idanu ta ɗauki kwalbar turare ta zuba a hannunta sannan ta shafa a wuyanta tana faɗin:
“Abeesh ya zama nawa, da rai ko da mutuwa... Kuma babu wani daga cikinku da zai iya hanani.”....
🫀
Asmeen ta ɗago kanta daga kan kafadar Tasleem, tana kallon su Amaar da Shaprees, murya na rawa ta ce:
“Shaprees, ba wai bana sonka ba, amma gaskiyar magana shine bazan iya koma wa yankin ka ba in har Nasreen bata dawo gare mu ba, Ku tashi, mu fita neman ta! Bazan iya zama haka ba tare da sanin yanda take ba.....!”
Tasleem ta dafa kafaɗarta, tana hawaye ta ce:
“Nima na yarda... mu tashi mu fita nema. Idan Nasreen tana raye zamu same ta Idan kuma... idan kuma ba ta raye! toh na rantse da Allah... zan bi ta duk yanda ta je.....”
Su kaɗai suke ta surutan su cikin tashin hankali...
Suna cikin wannan halin sai wayar Amaar ya fara ringing....
An ƙiran wayan Amaar ne dake Soja ne ake sanar masa cewa anyi hatsarin mota, mota ta kama da wuta.
A ruɗe Amaar ya miƙe tsaye yana faɗin
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."
Duk miƙewa suka yi suna tambayar sa meya faru..
Tasleem da Asmeen kuwa rungumar juna suka yi suna kuka jin Amaar ya yi wannan addu'ar,
Amaar ya ce
"Anyi hatsarin mota zan je na dubo yanzu domin ba'a sanar mun motar waye ba..."
Abeesh da Shapreen miƙe wa suka yi zasu tafi tare,. Tasleem ta ce:
zata bisu, Amaar ya ce mata
ta zauna a gida suma zasu je ne su tabbatar,.
Itama Asmeen cewa tayi Nima zanje, Shapreen ya ce
"Insha Allahu ba Nasreen bace..."
Abeesh cikin tashin hankali da damuwa ya darara musu tsawa yana faɗin:
"Wai meyasa kuke ja mata bala'i ne? Babu abinda ya faru da ita, matata tana nan da ranta, sharrin zuciya ne ke damun ku.... kuma zan nemo ta a duk inda ta shiga na rantse, kada ku sake ja mata mutuwa....."
Tasleem kuka take sosai tana faɗin
"Wallahi saina je, hankali na bazai taɓa kwanciya ba in Banga wanda yayi hatsarin ba...."
Daƙer Abul ya rarrashe su suka zauna a gida, hankalin su a tashe.....
Amaar, Shapreen da Abeesh sun fito da sauri daga gidan, motar Amaar duk suka shiga gaba ɗaya...
Shuru ya mamaye falon bayan sun bar gidan. Sai kukan Asmeen da Tasleem ne kawai ke karaɗe falon, suna rungume da juna, zuciyarsu na tafasa da fargaba...
Abul yana zaune a kujerar gefen falo, hannu a bisa habarsa yana tunanin abinda yake faruwa. Ko shi kansa bai da tabbacin halin da Nasreen take ciki.
Tasleem ta ɗaga kai tana kallon shi da hawaye, ta ce cikin karayar zuciyar:
"Abul... zuciyata na wani irin bugawa kamar an yayyafa mata wuta... meyasa nake jin kamar mun rasa Nasreen?"
Abul ya ce cikin wata irin murya da ta cika da damuwa:
"Ki zamo mai tawakkali Tasleem... dukkan abinda zai faru yana cikin rubutun Ubangiji. Amma in Allah ya yarda, ba Nasreen bace."
Asmeen cikin kuka da ruɗani ta ce:
"Allah ya sa...."
A can gefe kuwa, Catrina ce ta leƙo daga ɗakin ta cikin sirri, ta dube su da idanu masu cike da mugunta da ƙeta. Sai murmushi ta ke ta saki, tana furta cikin zuciyarta:
“Nasreen, kin bar kofar zuciyar Abeesh a buɗe... yanzu zan cika burina, ko da kuwa da wutar lahira ce..…”
Sai ta koma ɗakin nata, tana tunanin yadda zata tabbatar da cewa wannan tashin hankali zai ƙara ruɗa su gaba ɗaya — domin ta ƙudiri aniyar mallakar zuciyar Abeesh da cikakken ikon gidan.
Tasleem da Asmeen addu'a kawai suke suna fatan Allah yasa ba Nasreen ɗin su za'a tarar ba...
Ba su dena kuka ba. Suna jiran kiran waya ko dawowar su Amaar da labarin meye gaskiya akan wanda yayi hatsari.
Sai Asmeen ta riƙe hannun Tasleem tana faɗin:
“Ko me za a faɗa mana... zamu fuskanta tare. Nasreen ƴar uwar mu ce wanda muke da alaka ta jini, da rai, da ruhi.....”
Tasleem ta share hawayenta sannan ta ce cikin ɗaga murya:
"Idan da gaske ne wannan hatsarin... Wallahi sai na bin ciko ta yanda akayi wannan hatsarin ya wakana, in har Allah ne ya aiko bisa tsautsayi, to tabbas wacce tayi sanadiyar barin ta gidan wallahi saita gane kuran ta....."
*NEXT NEXT NEXT.....*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
49 to 50
TASHIN HANKALI A WURIN HATSARI
Wurin hatsarin ya cika da tarin jama’a da ‘yan sanda. Ana kulle hanya. Ana nuna babbar motar trailer ɗin da ta durkusar da wata mota rami, sai hayaki da ƙauri ke tashi. Amaar ganin motar yasa ya buga birki da ƙarfi yana faɗin:
“Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, na san wannan motar! Motar Nasreen ce!”
Kafin kowa ya yi wani yunkuri, Abeesh ya fice daga cikin motar da gudu, yana ƙwala kira:
“Nasreeeeeen!! Dan Allah karki ce kin mutu! Nasreen!!”
Idanunsa suka sauƙa akan ragowar motar da ta kife a jikin bishiya gaba ɗaya ta ƙone, sai wasu guntayen rigar Nasreen da aka hango kusa da ƙofar motar, sun ƙone rabin su.
Cikin dukan zuciya, Abeesh ya yanki jiki ya faɗi a ƙasa sumamme!
“Abeesh!!”
Amaar ne ya faɗa da karfi tare da ruga da gudu kansa.
Ya ɗago kan dan uwansa yana girgiza shi cikin hawaye, “Abeesh ka tashi! Ka tashi! Allah ya kiyaye Nasreen tana raye...!”
Shapreen yana tsaye cikin firgici yana ambaton addu'o’i. Cikin damuwa ya matso kusa, yana girgiza kai, ya ce:
“Wannan ba hatsari bane kawai… akwai aljani cikin wannan lamarin.”
Ƴan sanda da ma’aikatan agajin gaggawa sun zo da gaggawa suka fara aikin ceto. Aka dauke Abeesh cikin mota domin ya suma sosai, yayin da wasu suka ce:
“Ba mu ga jikin mutumin ciki ba… akwai yiwuwar ta ƙone kurmus.”
Amaar hawa motarsa ya yi cikin ruɗani domin komawa gida, domin shima zai iya faɗuwa idan ya cigaba da tsayuwa a wurin, shi kuwa Shaprees tare suka kai Abeesh hospital,
Amaar a cikin zuciyarsa yana cewa:
“Yanzu taya zan sanar wa Tasleem da Asmeen?Wannan al’amarin ya fi ƙarfin mutum...”
---
A BANGAREN GIDA
Tasleem ta ji wani irin raɗa a zuciyarta, kwatsam ta miƙe daga ƙasa, ta fashe da kuka mai ƙarfi tare da faɗin
“Wayyo Allah! Wani abu ya faru da Nasreen! Na rantse da Allah na ji a jiki na! Wani abu ya faru!”
Asmeen ta riƙo hannunta tana girgiza kai cikin hawaye ta ce