x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 38 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 111001 words
  • 114000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 212

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
naki bane. Na fahimceki tun da farko, amma ban taɓa cewa komai ba."


Catrina ta yi dariyar tana faɗin:

"Aw... kin gane ni daga farko? ke ce zaki iya dakatar dani? Ke da haskenki da bai iya ceton Nasreen ba? Ke da haskenki da bai hana Abul fadawa ruɗu ba? Kin san meye duhu? Ni ce duhu. Kuma ni ce zan rushe ku gaba ɗaya..."


Tasleem ta tsaya, ta ƙanƙame tafukan hannayenta, haske ya fara taruwa a cikinsu. Idonta ya koma fari kamar ƙarfen wuta. Sai furta da ƙarfi ta ce:

"Kin gurɓatar da jinin mu, kin cin amanar gidanmu, kin ɗauke mana Abeesh, kuma yanzu zaki zarge ni da rashin iya ceto? Duhu ba zai taba wuce haske ba... kuma yau... na zo daukar hakkina!"



Catrina ta zaro ido. Idonta ya sauya gaba ɗaya. Ya koma baƙi ƙirin kamar akwatin tsafi mai cike da ƙiyayya. Tana nufar Tasleem tana furta wani yare wanda ba wanda zai fahimta sai ƴan duhu ke amfani da shi....



Falon ya cika da wata iska mai nauyi, tagogi suka fara kaɗawa, fitilu suka fara tarwatse wa, ƙamshi mai ƙayatarwa na fitowa daga hasken Tasleem, yayin da wani ƙamshin ƙwari da dauɗa ke fita daga Catrina.

Sai kawai wata irin walƙiya ta sauka tsakanin su, kafin su kai juna hari.

Lokaci guda suka ɓace gaba ɗayan su...

A wani wuri suka sauƙa a cikin wata sahara da ba kowa, ba bishiya, ba tsuntsu. Wani tsarki na musamman ya rufe wurin – saharar tsakar tsafi wanda sai masu ƙarfin iko ne suke iya bayyana a wurin, wurin dandalin matsafa...

Suna sauƙa Catrina ta saki wata ƙara da sai aljanu ne ke iya fassara wa, Duk jikinta ya sauya. Idonta ya koma baƙaƙe, fuskarta ta koma kamar garwashi, cinyoyinta suka lankwashe kamar mahaukaciyar ƙuliya.

Ta rufo kan Tasleem da mahaukaciyar gudu tayi sufa cikin muryar ƙuliya ta yakushi fuskar Tasleem kamar zata....

Tasleem itama tɗaga hannunta tayi sama cikin nutsuwa, walƙiya ta tashi daga cikin tafin hannunta kamar gungumen wuta, ana ƙiran abun da Thunder, cikin fushi Tasleem take faɗin:


“Ina da haƙuri, amma ban zama mai shiru akan abun cutarwa ba...
Ina da zuciyar da tafi yarda da gaskiya, kuma ke – duhu – kece tsautsayin da ya hana ni kwana da zaman lafiya...
Yau zan fanshe rayuwar da kika ɓata!”


Thunder! Sai da haske ya sauƙa akan sa! Sannan ta buga Thunder akan Catrina, sai da ta nitse cikin ƙasa sannan ta fito daga cikin ƙasa da siffar babbar kuliya – baƙa kamar gabar dare!

Catrina ta ce:

"Kin manta ni ce nake kare duhu?!" Catrina cikin murya mai ɗauke da ƙara ta kuma furta

"Ni bana jin kunya, sannan bana kara kuma bani da tsoro....!"


Tasleem ta fasa dariya – dariyar girmamawa ga ikonta. Tana matso gaba, fuskarta ta koma haske, gashinta yana shawagi kamar zinariya a cikin ruwa, tana rufe da idonta tana miƙa hannu sama...

Wani abu kamar lu’ulu’un rana ya bayyana a cikinta. Daga cikin wannan hasken, sauti mai zurfi ya fito daga zuciyarta – kalmomin da suka girgiza saharar da babu kowa.

"Ina barin ƙauna idan na samu dama,
Ina barin gafara idan zuciyata bata cika ba,
Amma yau, bazan bar zafin zuciyar da kika haifar ba.
Soyayya ba sakacina bace, amma rashin adalci ke neman tara kaina.
Duhu! Ba za ki ci nasara ba!"



Catrina ta tashi sama da kafa huɗu, tana mirgina da zafi, tana fitar da hayaki daga cikin kunnuwanta da bakinta. Sannan ta harba wani jini mai zafi daga cikinta wanda ya zo kamar mashi ya nufi Tasleem – Tasleem ta kafa ƙafarta ƙasa sai wata garkuwa ta bayyana daga haske ta kare ta.....

A duk lokacin da Catrina ta fitar da duhu, Tasleem tana fitar da adalci da ƙarfi.

Suna cikin faɗan Catrina ta kifa kanta a ƙasa ta fashe da ihu sakamakon wani haske da ya bugeta wanda baza ta iya jurewa ba. Duk wata ƙarya da ta gina a zuciyarta tana narkewa.....

😳😳😳😳😳😳😳😳

MA SHA ALLAH!
ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFI NA ƊAYA, SAI MUN HAƊU A LITTAFI NA BIYU WANDA YA KASANCE NA KUƊI A FARASHI MAI SAUƘI NAIRA 300 KACAL👌👌

A CIKIN LITTAFI NA BIYU ZAN BAKU PAGE 1 TO 10 KYAUTA, NA MURNAR BIKINA CIKIN SATIN NAN, INA GODIYA SOSAI MASOYANA DA ADDU'O'IN KU TARE DA FATAN ALKHAIRI 🌹🌹🙏



*💋HASKEN RUHI💋*


*🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀*


It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person.

*WhatsApp 09065443871*


*🌹 ASMEETAH WRITER 🌹*


*BOOK TWO__________PAID_____₦300*


Page 1 to 2



Tasleem ta ɗaga hannunta sama, haske yana shawagi daga jikinta kamar rana da take haskawa, Duk da haka jikinta a gajiya yake, ba saboda ƙarancin iko ba, sai dan saboda zuciyarta da ke cike da bacin rai da takaici.

Catrina kuwa ta kasa kayar da Tasleem, sau uku tana faɗu wa ta tashi, amma hasken Tasleem yana cin galaba a kanta.

A karo na huɗu da Tasleem ta buge ta da haske, Catrina fasa ihu tayi kamar halittar da ta fito daga ɓoyayyen wuri. Sai kawai ta faɗi ƙasa tana numfashi kamar wacce za ta mutu.

Tasleem tana tafe tana faɗin:

"Karya zata ƙare yau, duhu zai durƙusa gaban haske.
Ba za ki ci nasarar kwace soyayya ba.
Kuma ba za ki sa ƴan’uwa na su lalace da tunanin ƙarya ba!"


Yayin da Tasleem ta ƙaraso dab da Catrina, sararin saharar ne ya canza launi. Rana ta ɓace. Wani duhu mai duhun gaske ya gangaro daga sama, iska na kaɗawa... Sannan ƙasa ta rabe biyu.

Daga cikin ramin asirai wata mummunar aljana ce ta fito.

Tana da ƙafafu huɗu, hannaye biyu, fuska mai idanu huɗu, gashinta kuwa kamar tsintsiya a tsatstsaye. Jikinta yana tafiya da Baƙin hayaƙi....

Cikin murya mai taushi wacce ke cike da haɗari, aljanar ta ce:

"Ni ce Bahrasha, uwargidan duhu uwa ga kowace mugunta.
Catrina ‘yata daga jini, na jiyo kiran ki... yanzu lokaci ya yi da zamu yaga sararin haske tare."


Tasleem ta ja baya da sauri, idonta yana haskawa, jikinta ne ya soma rawa saboda ƙarfinta yana raguwa.

Catrina ta miƙe daga ƙasa kamar halitta wacce aka rina da jini, ta ce:

"Hah! Kina tunanin ke kadai kike da gata daga haske?
Ni ma ina da nawa gata daga duhu.
Tasleem... yanzu faɗan ba tsakanin ki da ni kadai bane.
Yanzu Bahrasha ce zata koya miki yanda ake narkar da zuciya mai yawan gafara da ƙauna!"


A take Bahrasha ta miƙa hannunta zuwa cikin iska – sai wata zobe ta bayyana – zobe mai cike da jinin halittun da ba a san su ba. Ta miƙa wa Catrina, ta ce:

"Sa zoben jinin hauka domin ki jujjuya ki zama mace ba mutum ba
Ki zama Zarimar Duhu!"


Catrina ta amsa ta saka zoben, tana yin haka sai jikinta ya canza ta girma ta zama babbar halitta wacce jikinta ke huda sararin sahara da ƙura.

Tasleem kuwa ta dafe ƙirjinta, jikinta yana rawa, Haske yana ƙoƙarin ɓacewa, runtse ido tayi tana magana a cikin zuciyarta.

Ta ce cikin ranta:

"Haske ba iko kawai ba ne
Haske shi ne zuciyar da bata yarda da zalunci ba,
Shi ne idon da ke ganin mai laifi amma ya farka da addu’a...
Amma yau... Na yarda in tsaya domin kare aiki na ."


Haske ya sake ɓarkewa daga jikinta kamar wani tauraro da ya fashe a cikin duniya. Ta miƙa hannunta, ƙasa ta buɗe, wata garkuwar haske ta taso – tana fuskantar Bahrasha da Catrina.

Bayan Catrina ta sha zoben jinin hauka daga Bahrasha, ta canza zuwa wata baƙar halitta, gashinta ya tsawaita har zuwa ƙasa, fuskarta ta haɗu da wani irin tsufa da kwalliya mai ban tsoro.

Idonta huɗu ne yanzu – biyu masu jini, biyu kuma kamar hantsi a cikin duhu.

A bangaren Tasleem kuwa, bayan ta taso da hasken zuciyarta, ta miƙa hannu cikin iska ta furta da wata murya tana faɗin:

"Ya hasken ruhi,
ku buɗe ƙofofin ceto, ku aiko ma'abotan haske."


Sama ta tsage. Wata murya mai tsarki ta sauka daga sama:

"Anji kiran ki Sarauniyar Hasken Ruhi.
Kiyi maraba da ’Yan Agaji na Hasken Tabbas!"

Nan da nan haske ya fashe a sararin Sahara. Daga cikin hasken suka sauko:

Jundum – Wani babban halitta mai siffar mutum yana tafe da fuka-fuki masu walƙiya.

Rayyaa – Mace mai siffar haske gaba ɗaya, idanunta masu kukan adalci.

Sabeeh – Yaro ƙarami da jiki mai murɗaɗɗen haske, yana tafe da takobi wanda duk sanda ya buga shi ƙasa, ruhi mai kyau yana fita daga ƙasa.


Bahrasha da Catrina ganinsu yasa duk suka tsorata. Bahrasha ta furta:

"Toh, shima hasken yana da mabuƙata? Lallai yau sahara zata sha jini!"



Catrina kuwa ta ɗaga hannunta, ta saki wata ƙira kamar kukan dodo tana faɗin:

"Masu tarin duhu, ku fito daga ɓoyayyen duniya!
Ya ku halittun da na raya da kishi da tsoro, ku tsaya gaban haske yanzu!"


Wani irin ƙara ne ya sa ƙasa ta tsagei! Daga cikin ƙasa suka fito:

ZAKFURA – Halitta mai jikin maciji da fuskar mutum da wuya.

MAYURIN ZUCIYA – Wata halitta da ke ciyar da kanta da fushin mutane.

GALMASH – Halitta mai numfashi mai kone numfashin haske, tana rayuwa cikin kishi da munafunci.


FAƊA YA FARA CIKIN GASKIYA

Sabeeh ne ya ruga da gudu, takobinsa na walƙiya ya ɗaga sama tare da buga shi ƙasa ya haifar da rami mai kakkarfar haske ya bugi ZAKFURA a take ta faɗi haske na ƙone ta tana ihu...

Rayyaa kuwa wacce take fafatawa da Aljani Mayurin zuciya ta kifa fukafukanta ta fitar da murya mai ɗaukar ruhi mai duhu.
Mayurin Zuciya ya soma rawar jiki – yana ɓari – ya faɗi sumamme.

Jundum ya daka ƙara, ya bugi Bahrasha da wata garkuwa mai nisan haske, har sai da ta faɗi gefe tana tari jini.

Tasleem da Catrina sun sake haɗa ido. Catrina cikin murya mai ƙasƙantar zuciya da mugunta ta ce:

"Wannan ba faɗar ƙaramin iko bane.
Wannan faɗar zuciyarmu ce Tasleem.
Ki bani zuciyarki, mu raba haske da duhu...
Ki bani zuciyarki, in bar miki Abeesh..."


Tasleem ta amsa da karfi:

"Zuciyata tawa ce kuma na san darajarta, bana son in rasa abin da nake tsaye akai
Ina tsaye akan gaskiya, ƙauna da yanci!
Kuma a yau – ba za ku ƙara shan nasara ba!"



Cikin wannan lokaci ne wata ƙara ta buga daga nesa alamar cewa wani babban halitta daga haske ko duhu yana isowa...

Guguwar iska ta tashi cikin Sahara da hayaniya, lokacin da rana ta mai launin zinariya ta bayyana a sararin sama, wani haske ne mai sanyi da kwantar da zuciya ya sauka daga can…
Wannan ba kowa bace fa ce MIEMIE...

Miemie ce!

tana sauƙowa, gashinta na tafe kamar ruwa mai tsarki, fatar jikinta na haske kamar zinariyar dare. Idanuwanta sun cika da tausayi amma sukan ƙone dukkan duhun da suka kalle su da ƙyashi.

Kafin kowa ya ankara, ƙasa ta sake bugawa da ƙasa! Wani ƙaho na wuta ya huda sararin sama, zafi da hayaƙi da ƙamshin turaren ja suka mamaye saharar.

Madam Nablah ta bayyana.

Wuta tana tashi daga dukkan sassan jikinta. Hannunta biyu suna ci da harshen wuta, idanunta masu launin wuta sun cika da ƙarfi da ikirari.
Zuciyarta cike da mugunta domin tana ƙaunar 'ya'yanta, amma ba ta san tausayin duniya ba.


Lokacin da suka haɗa ido da Miemie, sahara ta girgiza....!

Miemie ta ce da murya mai taushi amma da nauyi kamar ruwa mai zurfi:

"Na zo ba domin ki ba, Nablah. Na zo domin kare gaskiya daga hallaka,
Amma yau zan tsaya gaban ki — domin ke da kanki kin zama hatsarin duniya."


Madam Nablah ta kalli Miemie da murmushi amma idonta na hura wuta ta ce:

"Kin zo ne domin kare gaskiya amma ki sani cewa wannan gaskiyar da kuke ƙoƙarin karewa jini na ne,
Ina da abin da ba ki da shi, Miemie. Ina da ƙiyayya da yaƙi.
Kuma yau zan nuna miki cewa wuta ba ruwa ba ce."


Nan faɗar ta ɓarke.


Miemie ta ɗaga hannu ta ƙira ruwan sama daga wani duniyar ruwa, ruwa mai daraja kamar lu'ulu'u ya sauƙo ya fara zagaye ta.

Madam Nablah kuwa ta fitar da harshen wuta daga zuciyarta, yana huda sanyi yana ƙone duk sanyin da ke kusa, a lokacin ta addasa zafi mai tsanani.. a yayin da sanyin ruwan Miemie ke ƙoƙarin kawar da zafin wuta....

Harshen wuta da ruwa ne suka haɗu ya fashe da wani irin ƙara wanda ya tarwatsa tsaunuka a gefe.
Tsuntsaye a sama suka fāɗi matattu. Rana ta dushe....


A gefe guda:
Tasleem tana fuskantar Catrina da Bahrasha.
Bahrasha ta fitar da kaho, tana ƙara tare da faɗin

"Na ɗauki zafi daga ruwan jini! Wani haske bazai iya kankare ni ba!"..

Tasleem kuwa ta kalli Bahrasha da dariya mai izza ta ce:

"Ke ne ake tsoro a cikin duhu? To, yau ki tsorata da hasken zuciyar wacce ku ke son cin amanarta!"


Ta fitar da wani garkuwa mai launin haske ta buga ta a ƙasa, wata walƙiya ta fito ta sare ƙafafun Catrina, tayi sama kafin ta faɗo ƙasi, Catrina ta zama gungume domin ƙafafun ta da hannayen ta ne duk suka watse gefe guda tana ihu domin ba ƙaramin raunana tayi ba....

Amma dake Aljana ce sai ta ƙara haɗe gaɓoɓin jikinta suka dawo normal...

Bahrasha ta ruga da gudu kamar giwa tana shirin yaƙar Tasleem, amma kafin ta iso yanda Tasleem ta ke, itama Tasleem ta yi tsalle tare da buga thunder hannunta ƙasa, har sai da Brahrasha ta tashi sama kamar guguwa ta faɗi gefe tsabar ƙafin haske...


ƘARFI DA ƘARFI: HASKE DA DUHU

A yanzu, halittun haske (Jundum, Rayyaa, Sabeeh da wasu sabbin) suna fafatawa da Galmarsh, Zakfura, da Mayurin Zuciya waɗanda suka farfaɗo da sabbin ƙarfi.


Faɗar da ba’a taɓa gani ba – faɗar da take canza nau’in duniya.

Sahara ta yi shiru.
Wuta da ruwa sun haɗu suka zama hayaƙi mai haske.
Madam Nablah da Miemie suna tsaye a sararin sama, jini da gumi na ratsawa jikinsu...

Tasleem tana ƙasa cikin kallo mai cike da mamaki — tana kallon Mahaifiyarta Madam Nablah, ba ta taɓa sanin cewa ikon mahaifiyarta ya kai wannan matakin ba.
A hankali take furta

"Shin wannan ita ce uwata wacce ta haifeni? Ita ce ta tsare ruhi da haske da duhu a jiki guda? Shin ita ce ta fi wuta zafi?..."

Zuciyar Tasleem na bugawa, yayin da hawaye suka cika idonta.

Kaff Aljanu da Jagororin hasken duk tsaya kallon faɗan manyan shuwagabannin suka yi,
Madam Nablah da Miemie...


Miemie cikin ƙarfin iko ta haɗa ruwa ta jefa Madam Nablah a ciki...

Tasleem har zata ruga da gudu wurin Madam Nablah ganin yanda aka jefa ta a ruwa mai yawan gaske, kafin ta motsa taji an riƙo hannun ta, tana juya wa ta haɗa ido da Miemie...

Miemie ta tsaya kusa da Tasleem, tana kallonta da idanuwanta masu launin ruwan sanyi.
Tasleem ta runtse ido, tana jin wani irin nutsuwa daga halittar da ba ta taɓa ganinta ba, amma zuciyarta ta yarda da ita gaba ɗaya.

A hankali ta furta

"Ke ba irin su bane... Ke haske ne..."


Miemie ta ɗora hannu a kan kafadar Tasleem, ta ce da murya mai sa hankali ya mutu:

"Haske bai faɗi ba. Amma idan haske da wuta suka ƙone juna, babu abinda zai rage sai ƙura. Don haka... sai a yi ƙoƙarin dakatar wa ta hanyar sadaukar da ɗaya.....


A gefe guda
Madam Nablah tana gefe, wanda fitowar ta kenan daga cikin ruwa tana huci da zufa, sai kuma ta fara nazarin ƴarta Tasleem, yanda zata ɗauke ta, ta rabata da ahalin haske gaba ɗaya....

Wata murya daga cikin zuciyarta ta ce:

"Zan rasa ƴaƴana gaba ɗaya idan na ci gaba da wannan yaƙi... Nasreen tana hannu na a killace..... Asmeen tana gida duk da nasan baza'a taɓa samun matsala daga ɓangaren ta ba domin yarinya ce marar wayo, so nake ta kasance da mijinta har su sama mun yaro wanda zai yi sanadiyyar ɗaukaka ta....sannan kuma Tasleem a yanzu zata faɗa tarkona....."


A can ɓangaren gida...

Amaar ya dawo gida cikin hanzari, tare da Asmeen da Shaprees da Abul.
Gidansu na cike da alhini, saboda duk sun tabbatar da cewa Abeesh ya ɓace.

Asmeen ta zauna cikin firgici, tana tunanin Tasleem da babu labarinta, itama basu san yanda ta je ba, ga samuwar rashin Nasreen...

Shaprees ya yi tagumi fuska a hargutse yana bin kowa da idanu masu ɗauke da mamaki, da jinjina lamarin da ke faruwa...

Abul kuwa, yana kuka a hankali, yana cewa:

"Na san wannan ƙaddara ce… amma a ina Abeesh yake? Wane ne zai iya ɗaukar shi daga asibiti har a ɓoye shi kamar iska?"


Amaar ya lumshe ido, yana jin wani abu ba daidai ba...


---


Yayinda Miemie ta fuskanci Madam Nablah bayan ta bayyana musu kamar iska, domin sun san ba zata taɓa mutuwa ba, su na so ne su kawo ƙarshen yaƙin

, ta ce:

"Nablah... Ƙiyayyarki ta cutar da duniya, amma so da kika ɓoye ya ceci ƴarki... Kuma zan baki zaɓi: ko ki daina, ko kuma ki rasa ta."


Madam Nablah ta ce da murya mai kaifi cike da izzah ta furta:

"Ba na jin tsoro... Amma ina jin zafin rasa ƴa... Idan hakan zai ceci Nasreen, Asmeen da Tasleem, zan tsayar."

Ta dakatar tare da jan yo Tasleem jikinta tana faɗin
"Wannan ƴata ce ta jini, bazan taɓa sadaukar da ƴata a gareku ba..."


MIEMIE ce take shirin yowa kan ta domin ƙwatar Tasleem, kafin ta motsa Madam Nablah ta kunna wutar tsafin ta mai ƙarfin gaske da tsananin zafi ya busa kowa dake wurin, tsabar tiririn wutar sai da Miemie tayi baya a gigice tare da faɗuwa ƙasi, duk babu wanda bai yi sama ya doku a ƙasi ba tsabar tiririn wuta..

A take Madam Nablah ta ɓace da Tasleem a cikin wannan wutar...


Catrina da Bahrasha ne suka kama kayuwansu tare da saki ƙara domin ƙwaƙwalwar baƙaƙen Aljanun ne suke tafarfasa tsabar tsananin zafin wuta su ma a take suka bace cikin duhu....


Halittun haske kuwa su ma ɓace wa suka yi cikin haske mai
End Ads