mata abun farin ciki bazata taɓa nuna wa ba, domin ba'a san farin cikin ta ba kullum sai baƙin ciki...
Madam Nablah ta cigaba da cewa "ita ɗin sam bata nuna farin cikin ta a kowa kullum a cikin wannan yanayin za kana ganin ta, Tasleem Kenam...."
Shapris jinjina kai yayi idonsa akan Tasleem sai yanzu ya gano ta....
Madam Nablah ta ce "Shapris na zaɓa maka ɗaya a ciki wato ita ce Aasmeen my lovely daughter...."
Cikin tsoro da fargaba Aasmeen ta ce "why Mommy?...."
Madam Nablah ta ce "Yes Aasmeen, bazan taɓa zaɓa miki abinda zai cutar da ke ba, saboda haka na ri ga da na yanke hukunci na, na mallaka wa Shaprees ke a matsayin matar sa ta Aure...."
Sannan ta maida idonta kan Shaprees ta ce "Shapris ga Aasmeen na mallaka maka ita, inaso ka riƙe mun ita amana, na baka amanar ɗiyata Aasmeen..."
Shapris ya ce "insha Allahu Madam zan riƙe ta kamar yanda kika umarta..."
Shapris har cikin zuciyarsa bazai taɓa haƙura da ɗaukar fansar matarsa Sophia ba, dole sai ya ɗau mummunan hukunci akan jinin Madam Nablah ko wacece kuma yayi alƙawarin bazai taɓa ƙyale wannan ahalin ba..."
Madam Nablah idonta akan Aasmeen ta ce "shi ɗin mutumin kirki ne, bazai taɓa cutar da ke ba..."
Aasmeen tana kuka ta ce "Mom wani abu yana faruwa da mu, kin kasa sauraron mu a duk lokacin da muka kawo miki kukan mu, duk wanda ya fara Soyayya da mu mutuwa yake, dan Allah kar ki jefa rayuwar sa cikin hatsari..."
Madam Nablah da Shaprees kallon juna suka yi domin Shapris yasan dole da hannun Madam Nablah akan abinda yake faruwa da ƴaƴanta, itama tasan ita take ai watar da hakan sai kawai ta wayance akan maganar tana faɗin "duk wanda kika ga ya mutu to lokacin mutuwar sa ne yayi, don haka ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru da Shapris..."
Madam Nablah ce ta kalli yanda Abeesh yake sannan ta ce "sai kuma Nasreen da Abeesh..."
Nasreen da Abeesh duk ɗago kansu suka yi suna kallon juna daga bisani suka mayar da kallon su kan Madam Nablah,
ta cigaba da cewa "na daɗe da tsara hakan a raina cewa Abeesh da Nasreen zasu zamo ma'aurata, don haka ya kamata ku ƙara fahimtar juna, na riga da na yanke hukunci na, hukunci na kuma shine dai dai, Nasreen da Abeesh ku fara tsara rayuwar ku kafin lokacin bikin ku..."
Daga nan Madam Nablah ta miƙe tsaye tana faɗin,
"Ke kuma Tasleem zan ji dake daga baya..."
"Aasmeen idan kun kammala fahimtar juna ke da Shaprees ki kaishi order part na musamman yanda zai zauna sannan daga yau ke zaki na masa gyaran room ki kai masa abinci part ɗinsa, gyaran gado da wanke toilet room duk ke ce, kar ki kuskura naga kin yi masa ba dai dai ba, sannan bana son ganin house worker a part ɗin Shaprees domin shi ɗin naki ne, babu macen da ta fi cancanta taje part ɗinsa in ba ke ba,
Wannan shi ake ƙira da training kafin Aure..."
Kema Nasreen daga yau ke za ki na gyara part ɗin Abeesh ba ƴar aiki ba, idan naga ba kiyi abinda nace ba haƙiƙa zaki ga ɓacin raina, kina ji ba..."
Nasreen gaba ɗaya ta ɗauke wuta domin bata taɓa tunanin zata Auri Abeesh ba, bata taɓa jin soyayyar sa ta Aure a cikin zuciyar sa ba, sai kuma tunanin Ayub ya faɗo mata a rai...
A tsawace Madam Nablah ta ce "kina jin abinda nake cewa ko Nasreen?..."
A firgice Nasreen ta amsa mata..
Madam Nablah bata tsaya ta ji daga bakin Abeesh ba kawai tayi tafiyar ta, kai tsaye upstairs yanda room ɗin ta yake ta nufa...
Abeesh kallon ta kawai yake gaba ɗaya ya rasa abin cewa, yanda kasan an sa masa kwaɗo ya gagara yin magana,. Shima a fizge ya miƙe gudu-gudu sauri'sauri ya bar falon, domin haɗa shi da Nasreen da akayi ba ƙaramin nauyin ta yake ji ba, har kunyar haɗa ido yake da ita samm bai so wannan haɗin ba.....
Tasleem ganin irin rainawa ƴan uwanta wayo da akayi ne yasa ta tashi cikin takaici ta haura saman upstairs zata shige room ɗin su,
Nasreen tana kuka itama haka ta tashi ta haura upstairs room ɗin su...
Aasmeen itama kuka take da sauri ta miƙe tare da shirin barin falon Shapris ya dakatar da ita yana faɗin "Amaryata shin baza ki kaini wurin mazaunina bane?..."
Asmeen tsayawa tayi idonta akansa yanda suka yi jawur domin haɗin yazo mata a bazata, tsoro da fargaba duk ya ratsa ta bugu da ƙari bata san shi ba, bata taɓa ganinsa ba lokaci guda ace an bayar ta a shi, abun yana ƙona mata rai......
NEXT NEXT NEXT
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 9 to 10
Shapris miƙe wa ya yi tare da tako wa har yanda Asmeen take a tsaye, a gaban ta ya tsaya yana ƙare fuskar ta da kallo a yayin da ita kuma take kallon ƙasi ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya ɗago da haɓarta a hankali ta sauƙe kyakkyawan idanuwanta akan fuskar sa tana bin sa da kallo daga bisani ta kawar da kanta gefe tare da faɗin "mu je na kai ka part ɗin ka...."
Sauƙe numfashi ya yi tare da bin bayan ta suka bar falon, sai dai suka fita can compound na gidan kafin suka hau wani beni mai hawa uku acan aka tanadar masa da tsararren part site ɗin sa,
Su na shiga falon suka tarar an tsara komai, komai da komai na rayuwar duniya an zuba a falon, ba abinda zai nema ya rasa, falon kaɗai ma abun kallo ne,
Murya ciki-ciki Asmeen ta furta "inaso zan koma part ɗin mu..."
Murmushi Shaprees ya sau tare da faɗin "baza ki rakani ciki ba ne?..."
A ruɗe ta furta "ciki kuma?..."
Ya ce "eh! ko baza ki iya ba? sai na ƙira Mommyn ku a waya tazo ta shigar dani ciki..."
Aasmeen kamar zata yi kuka ta ce "Shikenam! four bedrooms ne a site ɗin nan, ka zaɓi a wannan kake son zama?..."
Sai da ya baza eyes sannan ya ce "aina bedrooms ɗin suke?..."
Idonta na kallon gefe ta furta "duk su na upstairs, 2 su na hawa na biyu, 2 a hawa na uku..."
Goya hannayensa ya yi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa da alamun akwai abinda yake tsarawa a cikin ransa,
Ya ce "Ok mu je hawa na ukun, domin bana son zama a farko-farko, kinsan mijin ki matsoraci ne..."
Su na cikin wannan halin sai ga wasu security su biyu sun shigo da kayayyakin sa, daga nan ya sallame su, gyaran murya ya yi sannan ya ce "my Bride zaki iya taya ni ɗaukan jakakkunan nan?..."
Ba tare da ta furta komai ba tasa hannu ta ɗauki kaya biyu tabar masa sauran biyun ta haura saman upstairs,
Shima murmushi ya yi ya ɗauki sauran ya bi bayan ta....
Sai da suka hau saman upstairs ta uku sannan suka buɗe room ta ƙarshe suka shige, ga wantalelen gado da kujeru ata gefe guda har da plasman da ƙaramin frig, ta wani site guda dake cikin bedroom wardrobe ne da mirror and drowers, da kuma bathroom, su na shiga ta ajiye masa kayayyakin sa tayi saurin juyawa zata fice yayi saurin dakatar da ita, ba tare da ta juyo ba ta ce "na gama maka komai ai yanzu..."
Goya hannayen sa ya yi akan ƙirji tare da murtuƙe fuska kamar bai taɓa yin murmushi ba, zuciyar sa kawai take haurowa da zaran ya tuno da matar sa Sophia,
Cikin ɗaga murya ya furta "Keee!..."
Cike da mamaki Asmeen taji wannan kalma ya daki dodon kunnen ta, a firgice ta juyo tana kallon sa ganin ko shine domin taga yanayin sa kamar bazai iya cutar da mace ba...
Ya cigaba da cewa "Ke mallaki nane a yanzu, inada ikon da zan sa kiyi mun duk abinda nake so, saboda haka ki cire wannan jiji da kai naki ki fuskance ni da idon girmama wa...."
Asmeen lumshe idanuwanta tayi sai ga zafafan hawaye sun gangaro mata, murya a sanyaye take furta "ban kasance mai jiji da kai ba ya meri pati, ka mun afuwa domin fushin ka a gare ni tamkar wuta ne mai cin duk ilahirin jikina..."
Shapris cikin izzah ya furta "idan kuwa kina gudun ɓacin raina to kiyi duk abinda na umarce ki..."
Jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha Allahu Indai bai tsaba wa Ubangiji na ba..."
Ba tare da ya furta komai ba yasa hannu ya fara cire kayan jikin sa, Asmeen ganin haka yasa tayi saurin juya bayan ta jikinta har wani kakkarwa yake, ba ƙaramin tsorata tayi ba ganin ƙiran jikin sa,
Sai da ya kammala cire komai ya bar iya short pant a jikinsa sannan ya tako dab da Asmeen yasa hannu ya rungumeta ta baya yana faɗin
"Meri Bi-wi shin kina son kasance tare da ni?..."
Asmeen tsabar ta gama tsorata hatta muryar ta ma ƙakkafe wa yake, hawaye sun gagara tsayuwa, numfashin ta ne yake haurowa da ƙarfi-ƙarfi lokaci guda sai ji yayi ta faɗa jikin sa ba alamun motsi, ganin kamar a sume take yasa hankalin sa yayi matuƙar tashi, a ruɗe ya ɗago ta tare da kwantar da ita akan gado yana jijjiganta, ganin babu alamar zata farfaɗo yanzu yasa ya yi saurin zuwa wurin frig ya buɗe ya ɗauko ruwan sanyi sannan ya fara yayyafa mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo a ruɗe tana furta sunan "Mom! Mom!! Mom!!!..."
Cikin fusata ya wani darara mata wani irin mahaukacin tsawa yana zazzaro idanu waje, bata san lokacin da ta haɗiye kukan ba ga yanda idanuwanta suka yi jawur tsabar firgici da tashin hankalin da ta shiga,
Jawo ƙafafuwan ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado sannan ya ɗora ƙafarsa akan gadon dab da ita ya matso da fuskar sa kusa da nata yana mata kallon ƙurilla sannan ya ce "zan cigaba da dasa miki tsorona a cikin zukatan ki, sannan zan toshe duk wata kafar da zai sa ki raina ni Meri Bi-wi..."
Asmeen gaba ɗaya ta gagara gane manufarsa, zuciyar ta cike yake da tambayoyi, girgiza kai ta yi idonta akan sa ta ce "nasan akwai dalilin da yasa ka shiga jikin mahaifiyar mu, shin meye manufar ka akan mu har aka mallaka maka ni, shin cutar da ni zakayi ko kuma so kake kayi rayuwar aure dani tsakani da Allah?..."
Kafin ta lumshe ido bata ankara ba taji wasu zafafan mari har sau biyu akan kyakkyawar fuskar ta, a ruɗe ta kama fuskar ta cikin tsoro da firgici tana sakin ihu domin ba ƙaramin mari ya yi mata ba, har sai da ta fara ganin farfatsin wuta...
Cikin tsawatar wa ya ce "zan zubar miki haƙwara idan baki mun shiru ba, har ke zaki mun maganar cutar wa? cutar wa ya wuce wanda uwar ku ta mun..."
Tana kuka ta ce "tin kafin Aure?..."
"ko zaki janye ne?..."
Tana hawaye ta ce "idan ka cigaba da cutar dani zan janye..."
Murmushi yasau tare da faɗin "okay fine! ki janye sai na Auri mahaifiyarki ita ai zata iya zaman Aure dani tinda ba haramun bane, yanzu zan je na sanar mata cewa kin janye...."
Cikin kuka ta furta "Nooo! Dan Allah kayi haƙuri Meri pati, zan cigaba da zama da kai a duk halin da na tsinci kaina, wannan kalmar da ka furta ya mun muni, gwara ka ɗauki wuƙa kaita yankan naman jikina hakan zai fi..."
Sauƙe ƙafarsa yayi daga kan gadon ya nufi hanyar toilet yana faɗin "zan shiga wanka, ki shiga kitchen ki girka mun abinda zan ci..."