x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 172

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
A fusace ta miƙe daga kan kujerar tayi sama kamar mai furawa, bata taɓa taka ƙasi in har ta shigo fadar ta ba, komai a sama take yinsa ko tafiya take a sama take yin sa,
Shaprees bai ankara ba ya ji an ajiye masa wani cup mai ɗauke da jini a gaban sa tana daga bayan sa take faɗin "dama ta ƙarshe Shaprees! zan baka zaɓi biyu kuma a ciki dole kayi ɗaya a yanzu yanzun nan saboda haka na buƙaci a taru yau domin yau ba ranar meeting bane, a cikin zaɓin da zan baka dole kayi ɗaya Shaprees,
zaɓi na farko ka sha jinin nan ko ta halin ya ya ne, zaɓi na biyu ko kaban rayuwar matarka a yanzu..."

Shaprees wani irin bugun zuciya ya ji daman tsoron wannan ranar yake, ba shi da kowa sai matarsa shiyasa idon Madam Nablah yake kanta sannan jinin Sophia da Madam Nablah bai zo ɗaya ba shiyasa basa shiri, Sophia ta kasance mahaddaciyar Alkur'ani mai girma ne sannan tanada yawan ibada a koda yaushe, ta tsaya akan mijinta da addu'a shiyasa har yau Madam Nablah ta kasa cin galaba akan Shaprees, shiyasa take neman rayuwarta domin ta mallaki ruhin Shaprees wanda bazai taɓa bin umarnin kowa ba in ba nata ba....
___________________________________
Sophia tin lokacin fitar mijinta ta tashi zaune daman ba wani dogon bacci tayi ba, haka ta tashi ta ɗauro alwala ta fara jero salloli tana addu'a da nemawa mijinta tsari daga wurin Ubangiji, haka nan tana kan sallaya ba abinda take sai adduoi hakan yasa Shaprees ya kasa shan jinin da aka bashi, kullum a cikin haka ake.....

Ita kuwa Madam Nablah tasa Shaprees a gaba akan zaɓin da ta bashi,
yana matuƙar ƙaunar Matarsa shiyasa ya zaɓi shan jini amma kuma hakan ya gagara yu wa, da zaran ya ɗauki kofin jinin sai ya ɓarar da shi ƙasi shiyasa Madam ta zaɓa masa rasa matarsa domin a cewar ta hakan shine maslaha a tsakanin su, already tasan Sophia ce take taimaka masa shiyasa ta kasa cin galaba akan sa,
Shaprees haka yake kukan zuci yana tunanin matarsa Sophia,
Ita kuwa tana can sai karatun Alkur'ani mai girma take bayan ta kammala salloli da addu'o'i, Shaprees bashi da ƙarfin ikon da zai dakatar da faruwar haka domin Madam Nablah tana kwance akan gadonta zata iya kashe mutum daga can nisan duniya.

Wani irin murmushi tayi na mugunta sai yawo take ta mu su a saman kan su, tana yawo a sama tare da aiwatar da tsafinta tana maganganu...

Shaprees gaba ɗaya idanuwansa ne suka yi jawur tsabar tafasa da zuciyarsa ya ke yi, haka yake daure wa domin faɗan da yafi ƙarfinka sai ka mayar shi wasa...

Madam Nablah duk wani ƙoƙarin ta yana shirin fin ƙarfinta akan Sophia domin duk wani tsafin da ta tura wurin ta sai ya dawo mata, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba, hannu tasa ta ɗage hular kanta wanda ya rufe mata fuska tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Shaprees, tasau murmushi sannan ta ambaci sunansa "Shaprees..."

A taƙaice ya ce "Madam Nablah..."

Ta ce "Da hannunka nake so ka kawo mun Sophia nan wurin..."

Cikin takaici ya ce "impossible..."

Zaro manya manyan idanuwanta tayi waje a fusace ta ware tafin hannunta sai ga wani baƙin hayaƙi yana fito wa nan ta saita goshin Shaprees wannan hayaƙin ya shige shi nan danan tunaninsa ya juye sai abinda ta ce masa na lokaci ƙanƙani kafin ya dawo hayyacinsa,
A fusace ta ce "ina buƙatar ganin tsayinka..."
ba tare da ɓata lokaci ba ya miƙe tsaye fuska a rufe sannan ta ce "yanzu-yanzu kaje ka taho mun da Sophia now now..."

Ba tare da ya bata amsa ba ya yi gaggawar ɓace wa ɓatt, bai sauƙa a ko ina ba sai a bedroom ɗin matar sa Sophia,
Sophia ganin mutum a tsaye tsangamgam ko motsi babu yasa tayi saurin ɗagowa domin tasan sauƙar sa, hannu tasa ta rufe Kur'anin da take karanta wa daga bisani ta buɗe wardrobe ta ajiye tayo kan sa tana furta "Shaprees kaine a wannan yanayin? meyasa fuskarka a rufe nan fa ba wurin meeting ɗin ku bane, ka shigo gida ne..."

Hannu tasa ta buɗe fuskarsa lokaci guda tayi baya a tsorace tana binsa da kallo ganin yanda ƙwayar idanuwansa yake chanza colour yana fitar da farfatsin wuta,
Cikin sassanyar murya ta furta "Shaprees..."

Kafin ta ankara har ya damƙo hannunta suka ɓace a tare, basu sauƙa a ko ina ba sai a gaban Madam Nablah wacce take zaune a kan katafaren kujerar ta na sarauta wanda sai ka taka matakala kafin ka iso kan kujerar dake sama,
Madam Nablah ganinsu yasa ta tintsire da wata irin mahaukaciyar dariya..

Sophia idonta akan Madam Nablah ta ce "daman nasan aikin ki ne, shin lokacin rabani da rayuwata ce ya yi?..."

Madam Nablah girgiza kai tayi sannan ta ce "bazan barki kiyi mutuwar sauƙi ba, sai naga yanda Ruhinki zai wulaƙanta a cikin fada ta, sai na nuna miki yanda ƙarfin ikona yake, sai na shafe labarinki a doron ƙasar nan, zan ɓatar da gangan jikin ki yanda babu wanda ya isa ya san yanda kike, Ruhinki kuma haka zata rinƙa zagaye cikin hayaƙin uƙuba ta..."

Sophia cike da jarumta ta ce "haka kuma Ruhina saita hanaki sukuni, sai ta hanaki bacci, Ruhina da hannunta zata sheƙe ki, a shirye nake da ganin duk wani ƙalubalen ki Shaiɗaniyar Uwa..."

A fusace Madam Nablah ta fitar da wani haske daga cikin tafin hannunta tare da wurga mata shi, da wannan hasken Madam Nablah ta ɗago ta sama tana juyar da ita, sai da ta gama wahalar da ita kafin ta fara raba Ruhinta da gangan jikinta, daga sama gangan jikin Sophia ta faɗo ƙasi yaraf sai Ruhinta da Madam Nablah ta sauƙar da ita ƙasi da wannan hasken hannunta, Ruhi tana tsaye Madam Nablah ta ce "yau zan nuna miki cewa Devil Mom ba sa'ar kowa bace, ki biyo ni..."

Madam Nablah ce tayi gaba sai Ruhi da take binta a baya, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa a cikin fadar ta kafin ta buɗe wani ƙofa mai bala'in girma tana buɗewa sai ga wani irin iska mai ƙarfin gaske ya ɗauke Ruhin Sophia zuwa ciki, ciki kuwa wani irin haske ne ga hayaƙi kamar gajimare baka iya ganin abinda yake ciki tsabar tsafin da Madam Nablah tayi a wurin, ana shiga da Ruhin Sophia ƙofar ta rufu da kanta, murmushi kawai Madam Nablah tayi sannan ta juya...

Shaprees yana dawowa hayyacinsa ba abinda ya fara tarar wa sai gangan jikin Sophia dake yashe a ƙasi, a ruɗe ya yo kanta yana ƙiran sunan ta,
"Sophia! Sophia!! Sophia!!! ki tashi dan Allah kar ki mutu ki barni dan Allah..."

Madam Nablah ce ta bayyano lokaci guda tana faɗin "ka kwantar da hankalinka na kilacce maka matar ka, wannan gangar jikin ne babu amfanin da zata yi maka..."
tana kaiwa nan ta ɗauki jikin Sophia ta hanyar iska ba tare da tasa hannunta ba ta buɗe wani akwati ta jefata a ciki tare da rufe ta sannan ta tura ta cikin ƙasin ƙasin ruwa...

Shaprees haka yake kuka yana faɗin "Matata! Matata shin mezan ce wa iyayenta da suka bani amanar ta? na sanar musu cewa gobe Sophia zata koma Nigeria why?..."

Madam Nablah zama tayi akan kujerar ta tana faɗin "kai kana cikin Secret society Amma sam babu jarumta a tattare da kai, duk abinda na buƙata sai na same shi, saboda haka yasa hatta mijina ban bar shi ba, sai da jininsa ƙarfin ikona ya ƙara wanzuwa sannan tsafina ya ƙaru haka yasa na yi sadaukarwa da jinin mijina kuma na jure hakan, why you bazakayi hakan ba, daman matar ka ce matsalar ka yanzu babu ita zaka iya gudanar da aikin ka, yanzu inaso ka shanye mun jinin dake ajiye a gefenka Shaprees..."

Kamar yanda ta ce haka ya ɗauki cup zai kai bakinsa yaji kansa yayi wani irin sarawa lokaci guda ya yanki jiki ya faɗi, bai ƙara sanin halin da yake ciki ba...



NEXT NEXT NEXT....

New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

EP 3 to 4


Shaprees bai tsinci kansa a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa, farfaɗowarsa ke da wuya maimakon ya tarar da matar sa Sophia sai yayi ido huɗu da Madam Nablah zaune akan kujerar ɗakin tana jiran farfaɗowarsa, a zabure ya tashi zaune yana ambatar sunan Sophia, haka ya tashi a gurguje ya je gaban Madam Nablah yana faɗin "Please where is my wife? kar ki ce ta mutu dan Allah..."

Dogon numfashi Madam Nablah ta sauƙar tare da faɗin "So sorry Shaprees a wannan lokacin ka rasa matar ka domin ni ba'a ja dani kasan da haka, amma kar ka damu zan baka kyautar wacce zata maye maka gurbin Sophia, domin ina matuƙar ji da kai hakan yasa bana iya cutar da kai duk da tarin laifukan da kake mu, kyautar da zan baka shine abu mafi soyuwa a rayuwa ta, duk duniya babu abinda nake so sama da abinda zanyi maka kyautar sa..."

Shapris leɓɓensa na kakkarwa ya furta "wani abu ne?..."

Madam Nablah tasan murmushi sannan ta ce "Ɗaya daga cikin triplets daughter na, Ƴan mata uku sune ɓangarorin jikina, to na mallaka maka ɗaya daga cikin su duniya da lahira kuma zata haifa maka kyawawan ƴaƴan da kake so..."

Girgiza kai Shaprees ya yi sannan ya ce "a duniyan nan babu macen da zata kai Sophia a wuri na, kinyi kuskuren cutar mun da ita Devil Mom, domin ita ɗin rayuwata ce..."

Madam Nablah ta ce "ga shi lokaci guda na sauya rayuwarka Shaprees, yanzu sabuwar rayuwa zaka cigaba da gudanar wa..."

Tana kammalawa ta miƙe tare da faɗin "daga nan airport zan wuce domin a yau zan koma Nigeria..."

Bata jira wata amsa ba tayi ficewar ta,
Shaprees ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin yanda ake juyar da kwakwalwarsa, haka ya cije lips ɗinsa na ƙasi acikin ransa yake furta "Madam Nablah a yanzu wasan zai fara, idan kin san wani baki san wani ba, kin taɓo mun tabon da bazan taɓa warkewa ba, kin rusa mun farin cikina, kin rabani da rayuwata, bazan barki ba sai na ɗau fansa akan ɗiyarki da kika mallaka mun, zan nuna miki waye Shaprees Shattima...."

Haka ya gama maganganu a cikin zuciyarsa idanuwa duk sun yi jawurrr,
A lokacin ya ƙira waya ya sanar cewa yana buƙatar yin transfer zuwa Nigeria.
Domin yasan duk abinda Madam Nablah tasa a gaba sai ta kai ƙarshen shi, tinda har ya kasa ceto rayuwar Sophia to yasan ya rasa ta har abada kenam, shiyasa zai yanke hukuncin komawa Nigeria sai dai abu ɗaya yake shakka shine sanar wa iyayen Sophia cewa ya rasa ɗiyarsu...

Haka yake ta wannan tunanin...


*NIGERIA...*


Wasu maka-makan motoci ne guda biyar suka yi parking a harabar wani makeken gida mai upstairs hawa huɗu, bodyguards ne a tsatstsaye sun fi goma kowa yana riƙe da bindigar sa wanda ya kasance sune masu gadin gidan, wani daga ciki ne ya buɗe murfin mota wanda a ciki wata miskilalliyar mata ne mai ɗagun kai haɗe da girman kai, ƙafarta ɗaya ta soma sauƙo da shi wanda yake ɗauke da wani irin takalmi mai tsinin gaske, a hankali ta sauƙo gaba ɗaya a daidai lokacin da wasu ƴan mata su uku masu kamanni ɗaya suka nufo wurin parking, haka suka jeru tsayinsu ɗaya, kamanni kuwa kamar mutum ɗaya, kyau kamar su suka halicci kansu ga farin fata kamar ƴaƴan turawa, amma sai dai kowacce da kalar zuciyar ta.

Madam Nablah ce ta fito tana kallon su ɗaya bayan ɗaya daga bisani ta farkon tazo dab da Madam Nablah sannan ta rungume ta tana faɗin "your welcome Mom..."

Madam Nablah murmushi tasau tare da shafa gefen fuskarta ta ce "my big daughter Tasleem, god bless you...."

Jinjina kai Tasleem tayi sannan ta koma yanda take ta tsaya sai kuma ta biyu wato Nasreen itama rungumar mahaifiyarsu tayi sannan ta ce "your welcome Mom..."

Madam Nablah sumbatar ta tayi akan goshi sannan ta ce " I Appreciate you my lovely second daughter...."

Sai ga ta ukun itama ta zo ta rungumi mamanta tana faɗin "Mom I really missed you..."

Madam Nablah itama rungumar ta tayi sosai a jikinta tana faɗin "Ohhhh so sorry my heart partner Asmeen ..."

End Ads