Tasleem ta ɗora kanta akan cinyar Nasreen ta ce "Mommy bata mun komai ba.. "
Nasreen ta ce "to meyasa kike kuka domin nasan haka kawai babu abinda zai sanya ki kuka..."
Asmeen ta ce "tabbas domin sai abu ya kai abu kike kuka, bakya kuka akan ƙaramin matsala, shin me ya sa kika baro ɗakin mommy cikin dare?..."
Nasreen ta ce "kema dai Asmeen kin san Indai ta farfaɗo kam baza ta barta ta zauna mata a ɗaki ba, tin muna yara ƙanana mommy bata barin mu mu shiga mata ɗaki, yanzu haka ni ban san ya kalar ɗakin Mommy yake ba, ban taɓa shiga ba..."
Asmeen ta ce "nima ban taɓa shiga ba kuma itama Tasleem wannan ne karo na farko da ta shiga ɗakin mommy, ni nayi mamakin yanda mommy zata bar mutum har tsawon kwana uku a ɗakin ta, ni da na sani ai dana baki wayata kin yi mun video ɗakin Mom..."
Nasreen murmushi tayi tare da faɗin "ke fa kinada matsala..."
Tasleem abubuwa da yawa ne suke yawo mata a ƙwaƙwalwar ta, tana tunanin Abu Abeesh a yanayin yanda ta gan shi, sannan kayan tsafe-tsafen da ta gani a wardrobe ɗin momy wanda sai da jini yake buɗuwa, na uku shine baƙar kuliyar da ta gani amma wannan ba abun tashin hankali bane a wurin ta domin tasan mommynta ne tinda zaman ta a ɗakinta ta ga ta koma har macijiya sannan ta koma tsuntsuwa, duk da hakan bai sa tayi razanar da za'a gane ta farfaɗo ba, amma abinda ya fi ɗaga ma ta hankali shine jin itace tayi silar mutuwar Mahaifinsu, lokaci guda kuka ya ƙara yanko mata...
Cikin nuna damuwa Nasreen take faɗin "Haba Tasleem meyasa bakya jin rarrashi ne? ban saba ganin kina yawan kuka haka ba sai yau....".
Tasleem cikin kuka ta furta "Daddy..."
Asmeen ta ce "Daddy kuma?..."
Nasreen cike da mamaki ta ce "yau ɗin kewar Daddy ne ya motsa ?..."
Daƙer suka samu nasarar rarrashin ta kafin su ma suka yi sallah...
Misalin ƙarfe 7 na safe Tasleem da Nasreen tare da Asmeen duk hallaruwa suka yi a falo sunyi shirin makaranta, su na jiran fitowar mommynsu, can sai ga ta tana ɗaure da farin towel akan ƙirjinta, towel ya tsaya mata a iya gwiwa ta fito tana tajar gashin ta da mataji da haka ta fara sauƙo wa down stairs, Asmeen baki ta sake tana kallon mommy ta kasa furta komai, itama Nasreen cike da mamaki take kallon ta a cikin ranta ta furta "yau kuma Mommy, fitowa falo da ɗaurin ƙirji da ƙaramin towel?..."
Tasleem tana zaune haka take bin Mommy da kallo tin daga ƙasin ƙafarta wanda ko takalmi babu har saman ta, a tsakiyar falo Madam Nablah ta tsaya Tare da cigaba da tajar sumar gashin ta wanda yake har gadon baya ga shi baƙi ƙirin, jikin ta kuwa kamar na budurwar robot fari tass, ƙafar ta ko takalmi babu, bayan ta kammala tajar gashin kanta tsayawa tayi tana bin yaran da kallo ɗaya bayan ɗaya fuska ba annuri, ga goshinta wuri guda yayi jawur alamun ciwo taji a wurin, Asmeen idonta akan Madam Nablah ta ce "good morning Mom, meya sameki akan goshi ?..."
Nasreen ta ce "yau kuma ya kika fito haka? kuma alama daga wanka kika fito..."
Murmushi Madam Nablah ta sau idonta akan Tasleem ko sauraron su bata yi ba balle su sa ran zata basu amsa,
Tasleem gaba ɗaya ta tsargu da kallon da mommynta take mata, cikin wayince wa ta miƙe tsaye tare da nufan wurin Madam Nablah da murmushi akan fuskar ta ta ce "Mom good morning..." ta furta haka tare da rungumar ta, sannan ta sumbace ta a gefen fuskar ta...
Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi domin ba ƙaramin mamaki wannan al'amari ya basu ba, ganin Tasleem ta rungumi mommy tare da sumbatar ta.
Madam Nablah kallon Tasleem take tana wani irin tunani, maganar zuci take tana faɗin "me hakan yake nufi? kenam Tasleem bata san ko ni wacece ba har yanzu? duk da abinda ta gani a daren jiya?...."
tana cikin wannan tunanin Tasleem ta katse ta da cewa
"Mom! Mom!! jiya naga kuliya a ɗakin ki, shine dalilin da yasa na gudo room ɗin mu, kuma ban ganki ba, bayan tashi na nayi ta duba ki bakya nan, to nayi tunanin kina toilet ne shiyasa na buɗe wardrobe akan zan ɗauki riga nasa kuma sai na tarar da kayayyakin wasan yara a cikin wardrobe, daga baya sai ga kuliya, na tsorata sosai, Mom inadai kuliyar bata Miki komai ba?..."
Tasleem ta ƙarasa basajar ta idonta a cikin na Mom, kuma tasan wannan kuliyar itace domin ga tabon muciyar da ta kwaɗawa kuliyar ya bayyana akan goshin Mom.
Madam Nablah cike da mamaki take kallon Tasleem sai yanzu ta tabbatar cewa Tasleem bata san komai ba, itama wayince wa tayi tare da faɗin "kuliya kuma a cikin gidan nan? amma ban ga kuliyar ba shin tana ina?..."
Tasleem ta ce "Mom kamar fa ɓace wa tayi..."
Nasreen zaro ido waje tayi tare da faɗin "kuliya kuma ta ɓace?..."
Madam Nablah ta ce "what? anya kuwa ba mafarki kika yi ba Tasleem?..."
Tasleem ta ce "a'a ba mafarki bane..."
Asmeen ta ce "gaskiya azo a fitar mana da kuliyar nan, domin bazan iya bacci ba yau ..."
Madam Nablah ta ce "shikenam ku tafi makarantar ku, daga baya sai ku nemo wanda zai fitar muku da kuliyar..."
Daga nan Madam Nablah ta nemi wuri ta zauna akan kujera tare da ɗaukan kofin shayi tana kurɓa...
Nasreen ta ce "Mom yau zamu fara jarabawar gama makaranta a taya mu da addu'a..."
Jinjina kai kawai Madam Nablah tayi tana kurɓar shayi.....
Gaba ɗaya fita suka yi a tare, Tasleem da tunani ta fita daga gidan, tana tunanin ta yanda zata ɓullo wa wannan al'amarin, tana mai baƙin ciki a halin da ta tsinci mahaifiyar ta kuma tayi alƙawarin kawo karshen wannan al'amarin, har yanzu ta kasa yarda da zuciyar ta cewa mommyn su ce ta kashe Daddyn su...
Kamar yanda suka saba kullum ita take driving ɗin su a mota, har sun shiga zata ja motar sai ga Shaprees ya tsaya musu a gaban mota wanda basu san yana wurin ba, zuwa yayi wurin ya tsaya a wurin glass ta ɓangaren Tasleem yanda take jan motar, Nasreen ce ta fara yin magana tare da faɗin "Barka da safiya Ya Shaprees..."
Ya ce "yawwa sannun ki mai hankali..."
Asmeen gaba ɗaya ba fara'a akan fuskar ta kamar zata yi kuka ta ce "ina kwana meri pati..."
Tasleem ta gefen ido ta kalle ta ba tare da ta furta komai ba...
Amsa mata ya yi idonsa akan Tasleem, ganin ita bazata iya gaishe shi ba yasa shi faɗin "ke baki iya gaisuwa bane?..."
Tasleem ta ce "ban iya ba" a takaice..
Kama kuncin ta ya yi yana murzawa tare da faɗin "ke sakaliya ce ko?..."
Tasleem da sauri ta kawar da fuskar ta tana faɗin "You are bastard, jahilin bawa marar tunani, har kai waye da zaka taɓa fuska ta..."
Cikin ɓacin rai Shaprees ya buɗe murfin motar tare da ja wo hannun ta ya fito da ita sannan ya rungume ta yana faɗin "Ba ma iya taɓa fuskar ki zanyi ba har rungumar ki nayi, meye zaki yi..."
Tasleem da iya ƙarfinta ta fisge kanta daga gare shi a fusace ta zabga masa mari, yana ɗago da kansa ta ƙara zabga masa wani marin tana huci...
Nasreen da Asmeen su ma fito wa suka yi suna kallon ikon Allah, gaba ɗaya sun kasa gane meye dalilin faruwar haka..
Tasleem tana huci ta ce "kai baka kai namijin da zaka taɓa jikina ba, ba ka daga cikin tsarin namijin da nake so da alfahari da shi, kuma duk duniyan nan babu shi sai mutum ɗaya...."
Madam Nablah wacce take saman upstairs tana kallon duk halin da ake ciki, jin abinda Tasleem ta furta ne yasa ta ƙara saurara ta ji waye mutumin da yake cikin zuciyar ta.
Tasleem ta cigaba da cewa "ban san shi ba amma ina jinsa a raina, ban taɓa ganin sa ba amma makauniyar zuciyata tana tare dashi a koda yaushe, banza da kai maciyi Amana, duk wasu saƙonninka da kake turo mun ta wayata kafin na karanta sai na bawa ƴar uwata Asmeen sannan a gaban Nasreen ta karanta mun saƙon da ka turo mun, duk mun san kai ɗin munafiki ne, to ni nafi ƙarfin ka kuma duk wulaƙanci da kake wa Asmeen na sa ni, muna sane da kai amma zanyi maganin ka..."
Shapris idonsa ya sauƙar kan Asmeen wacce tin ɗazu sai kuka take ta sha, tana rungume a ƙirjin Nasreen....
Sannan ya kalli Tasleem ya ce "kin mare ni sannan kin zage ni kin wulaƙanta Ni amma ki sa ni taki lafula ne akan nawa, domin ni ɗin wuta ne, zan koya miki hankali, kina maganar ina turo miki saƙonni to ki tambayi mahaifiyar ku na sanar mata cewa zanyi chanji, don haka ke nake so ki zama baiwata..."
Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "lallai za'a bawa kura ajiyar nama kenam, to ka sa ni cewa ni ɗin kura ce wacce zata yi yaga-yaga da naman jikin ka, kuma ni ruwa ce wacce zata yo ambaliya ta kashe wutar dake tsakiyar kan ta, wawa kawai..."
Shapris ya buɗe baki zai yi magana kenam Madam Nablah tayi saurin dakatar da shi ta hanyar ƙiran sunansa,
duk ɗaga kayuwan su suka yi suna kallon sama, idonta akan Shapris ta ce "mun gama magana ai, meye abun faɗa kuma, na maka alƙawarin duk abinda ka tambaya a wurina zaka same shi don haka na sauya maka kamar yanda ka buƙaci haka, yanzu Tasleem ta zamo mallakin ka...."
Tasleem a ruɗe ta furta "what?..."
Madam Nablah ta ce "bana son yawan magana ku kama hanya ku tafi makaranta sai kun dawo..."
Tasleem buɗan baki tayi zata yi magana Asmeen ta tafo da gudu tare da kama hannun ta tana faɗin "dan Allah Tasleem ki amince, ki taimaka mun inaso daga yau kar na ƙara zuwa ɗakin sa, cutar dani yake Please, kin manta alƙawarin da kika mun?..."
Jinjina kai Tasleem tayi sannan tasa hannu tana goge hawayen Asmeen ta ce "mu tafi..."
motar su suka shiga a ɗari suka bar gidan...
Exam Hall
kowa ya hallaru ana rubuta examination, ko wani seat mutum ɗaya ne, Nasreen tana gaban seat ita kaɗai, Tasleem kuma a tsakiyar seat a yayin da Asmeen take can ƙarshen seat, sai sauran mutanen class babu mai motsi a cikin su, kowa abinda yake gaban sa yake, sai security masu zagaye su, wani mutumi ne ya shigo exam hall da sallamar sa tare da gabatar da kansa, shima ya buƙaci bawa student tsaro wurin gudanar da Exam, Nasreen ɗagowa tayi idonta suka sauƙa akan Amaar Junaid a cikin ranta ta furta "Major A.J..."
haɗa ido suka yi ya kanne mata ido ɗaya tare da sakin murmushi...
Itama murmushi tayi sannan ta cigaba da rubutun ta,
Itama Asmeen daga can seat back ganin sa yasa ta washe baki tana ƙoƙarin ɗaga masa hannu, ɗaya daga cikin security ne ya hango ta ya ce "ki maida hankali kafin na kore ki yanzu..."
Dasauri Asmeen ta sunkuyar da kanta ƙasi ta cigaba da rubutun ta,
Ita kuwa Tasleem ko ɗago wa bata yi ba daman bata san shi ba, tana cikin rubutun ta taji daga gefen ta an furta "ƴan mata zan iya taimaka miki?..."
Ɗago wa tayi tana masa wani irin kallo na rashin fahimta, sai gani tayi ya ajiye mata wata takarda akan booklet ɗin ta ya yi gaba, da sauri ta juya tana kallon sa, ganin ta juya bayanta ne yasa wasu security su biyu suka zo wurin da take, suna faɗin "ke a ɗakin exam kike juyawa?..."
Ɗaukan takardar gabanta suka yi suna faɗin "whattt! Cheating on an exam..."
A tsorace Tasleem ta zazzaro da manyan idanuwanta waje tana faɗin "ni mai zan yi da satar amsa, ku duba note ɗina ba iri ɗaya ba ne..."
Kowa juyowa ya yi yana kallon ta, Nasreen itama ba ƙaramin tsorita tayi ba ganin an kama Tasleem.
Ɗago ta suka yi tare da ƙoƙarin fitar da ita suna faɗin "kiyi waje bama son ƙara ganin ki a ɗakin jaraba again, kuma sunan ki zai tafi sama, za'ayi reporting ɗin ki as a cheater..."
Tasleem haka take kuka tana roƙon su amma sun ƙi haƙura sai ma yaga takardar exam ɗin ta da suka yi, dole tana kuka ta fita, kuma wannan exam shine final na gama school degree, daga baya shima Amaar aka gano babu wanda ya turo shi makarantar nan, kawai