da ita, ruwan da ba kowa zai iya hango ƙasarsa ba, balle ya fahimci a cikinsa akwai ɗaki mai rufin sirri. Tasleem tana zaune akan gadon alhurma mai hasken milk, cike da ƙamshi mai ɗaukar hankali, amma zuciyarta na cike da fargaba da duhu.
Idanunta sun kusan rikicewa saboda tsawon lokacin da ta ɗauka bata ga hasken rana ba. Amma hasken da ke fitowa daga jikinta ba ya mutuwa. A kowace rana, kifaye masu ban mamaki suna zagaya wajen ɗakin suna gadinta.
Sai dai a yau, wani nauyi na daban ya sauƙa a kirjinta. Ta furta cikin karamin murya:
“Ina ku ke! Ina ku ke Amaar! Nasreen!! Abul...!!!”
Zuciyarta na harbawa, ta tsare ruwan da ke zagaye da ita, tana jin wata murya a wajen ruwan ana furta:
“Ba za ki tsere ba, kar ki manta a ƙarƙashin ikon duhu kike...”
Amma bata ga wanda ya yi maganar ba, kamar dai akwai ɓoyayyen abinda yake tsare da ita...
★★★
Amaar yana zaune kusa da gadon Abul, yana sharar zufa, fuskarsa cike da damuwa. Dama ɗaya ya rage masa a zuciya, rayuwar su ta tsere daga hannunsa. Ya rasa Nasreen. Ya rasa Abeesh. Kuma yanzu Tasleem ta bace gaba ɗaya ya ce:
“Allah Ka dawo min da su… ko ɗaya ne a cikin su, kawai ɗaya...”
Sai yayi shiru. Ya kalli Abul, wanda idanunsa a rufe suke amma yana sauƙe numfashi cikin nauyi. Ya ɗauki hannunsa, ya riƙe shi yana faɗin:
“Zan riƙe ka. Zan kare ka daga komai, bazan taɓa barin a ɗauke mun kai ba Abul, shiyasa bana zuwa ko ina saboda kai…”
🖤
Catrina na tsaye a bayan wata bishiya cikin damuwa, ta rana ina zata sanya rayuwarta ta huta, tana tunanin Amaar da Abul daga nesa. Jikinta Gabadayanta rawa suke, zuciyarta na harbawa...cikin kuka ta ce
“Zan iya shigowa yanzu in ɗauki Abul… Amma idan Amaar ya gan ni...”
Ta taɓa kirjinta, inda zuciyarta ke bugawa sosai. Son da take yi wa Abeesh yana rikita ta. Amma umarnin Madam Nablah yana fasa mata kunnuwa yanda take faɗin cewa:
“Tafi ɗauko Abul ko ki kashe Abeesh da hannunki...”
Girgiza kai tayi tare da faɗin
“Bazan iya kashe shi ba… domin ina sonshi… amma idan na kasa ɗauko Abul fa?”
Ta juya baya, tana jin hawaye ya cika mata ido.
Sai murya daga cikin ganye ta fito – murya ce daga zuciyar tana maganar zuci:
“Catrina… duk wanda ya zaɓi ƙauna, baya tsoro. Amma duk wanda ya zaɓi biyayya ga sharri, ya rasa komai.”
🔥
A cikin wani tsauni mai duhu da yashi mai fitar da hayaki, Madam Nablah tana zaune, tana kallon cikin wata ƙwarya mai wuta. A ciki ne ta kulli Abeesh, cikin muryar tsafi ta zuba masa ruɓaɓɓen barci tana faɗin:
“Zan bar ka nan har sai ka farka ka manta da komai....”
Sai ta ɗago kai — ta ji Catrina na shigowa. Bayan gaisuwar tsoro da nauyin ido, Madam Nablah ta miƙa mata wuƙar zinariya wacce ke ci da wuta ta ce::
“Ko ki ɗauko Abul... ko ki kashe Abeesh yanzu nan. Babu hanya ta uku. In ba haka ba, ke kanki na fi karfin ki.”
Catrina ta kama wuƙar da hannunta, tana kallon Abeesh wanda ke fama da barcin sihiri. Sai ta furta cikin murya mai ɗauke da kuka:
“Bazan iya kashe shi ba. Ina jinsa kamar rabin raina. Ki kashe ni idan kina so... Amma kar ki ce in cutar da shi.”
Madam Nablah ta lumshe ido, zuciyarta na tafasa da wani abu da ba ta iya bayyanawa.
A zuciyarta ta furta:
“Abeesh... ɗana ne fiye da komai.”
Amma a fili, ta fitar da murmushi mai tsananin barazana da tausayi a lokaci ɗaya....
Madam Nablah ce ta karɓi wuƙan tare da saita zuciyar Abeesh tana faɗin
"Ok! tinda ke kin kasa saboda ƙauna, Ni zan kashe shi da hannuna..."
Catrina a ruɗe take faɗin "A'a dan Allah, Devil Mom please zan ɗauko Abul amma kar ki cutar da Abeesh...."
Madam Nablah ta ce "je ki to..."
Catrina ɓace wa tayi a hanzari ta koma duniyar mutane...
Kamar iska haka Catrina ta bayyana cikin dakin, tana tafiya da saurin takun da ke bayyanar da tsoro da ƙuduri a lokaci guda. Abul yana kwance akan gadon, yana ɗan fama da hawan jiki, amma idanunsa na bude suna hangen kowane motsi.
Da ya hango Catrina, sai ya miƙe da sauri yana ƙura mata ido.
Ya furta da mamaki da ƙiyayya:
“Ke? Me kika dawo yi gidan nan?! Ko kin manta irin abinda kika haddasa?!”
Catrina ta tsaya ba tare da ta motsa ba, tana kallonsa da ido mai taushi. Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce da murya mai rauni:
“An aiko ni ne… akan mu tafi tare.”
Abul ya matsa baya kadan, yana kallonta da shakku. Ya girgiza kansa yana furta:
“Waye ya aiko ki? Ina kike lokacin da komai ya rushe? Ina Abeesh? Ina Tasleem? Ina Nasreen?”
Catrina ta ɗauke kai gefe, ta lumshe idanu kamar mai ƙoƙarin ɓoye damuwa ta ce:
“Ban sani ba… wallahi ban san inda suke ba. Ni ma ban gan su ba tun lokacin.”
Abul ya fashe da dariyar takaici, yana girgiza kai tare da faɗin:
“Ke da kika fi kowa sanin shirin Madam Nablah, da kika fi kowa kusanci da ita, kina cewa baki san inda suke ba? Kar ki ɗauke ni sakarai, Catrina!”
Catrina ta matso gaba da sauri, idanunta cike da hawaye, tace:
“Wallahi ba na tare da sharrin da ke faruwa yanzu! Na zo ne domin… domin kawai in ɗauke ka mu bar nan kafin wani abu ya faru da kai.”
Abul ya ɗan ɗaga murya ya ce:
“To ki gaya min gaskiya! Abeesh fa? Ya ya yake? Ki ce min da bakinki! Ina Nasreen da Tasleem?”
Catrina ta durƙusa a gabansa, tana girgiza kai tana faɗin:
“Ban san inda suke ba. Ka yarda da ni... Abul, ban san komai ba game da su...”
Abul ya janye jikinsa, ya ce da ƙarfi:
“Bazan tafi dake ba, Koda kin faɗi gaskiya. Bazan yarda dake ba har sai Amaar ya dawo.”
Catrina ta ɗaure fuska hawaye na gangarowa daga fuskarta. Tayi ƙoƙarin kama hannunsa amma ya tureta da ƙarfi yana faɗin:
“Ki fita. Bana son ganin ki yanzu. Ki je ki bar ni.”
Catrina ta tsaya cak, zuciyarta na tafarfasa. Tayi juyi, ta juya za ta fita amma kafin ta kai ƙofa ta tsaya ta ce:
“Duk da baka yarda da ni ba… ina fatan wata rana zaka gane banason a cutar da ku. Kuma ni… ni bana so a cutar da Abeesh.”
Sai ta fice a hankali, ta bar ɗakin cike da damuwa, yayin da Abul ya bita da kallon shakku da tausayi a lokaci guda.
Bayan wasu ƴan mintuna sai ga
Amaar ya dawo daga waje ransa a cunkushe kamar dutse a ƙirji. Kusan kullum yana zaune kusa da mahaifinsa Abul, yana kulawa da shi cikin ladabi da biyayya. Duk da yawan tunani da bugawar zuciya Amaar bai taba barin mahaifinsa shi kaɗai na wani lokaci mai tsawo ba —sai yau.
Ya shigo ɗakin cikin hanzari, yana kallon yanda Abul yake a zaune yana faɗin:
“Abul, lafiya? Me yasa ka barni na ɗan fita? nasan tabbas Catrina ta shigo gidan nan...”
Abul ya dube shi da murmushin tausayi ya ce:
“Tana so ta tafi da ni… amma ban yarda na bita ba.”
Amaar ya ɗaure fuska, idanunsa suka ɗauke da barazana ya ce:
“Allah ya tsare, babu inda zaka je tare da ita. Catrina tana karkashin umarnin Madam Nablah. Kuma yanzu komai yana cikin hatsari.”
Yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya kuma cewa:
“Mun rasa Nasreen... har yanzu babu labarinta.
Abeesh ma ba’a san inda yake ba.
Tasleem kuma… bata dawo daga yanda taje ba.”
Hawaye ne suka cika a idanun Abul,
Abul ya kama hannunsa, yana ƙoƙarin ƙarfafa masa guiwa da cewa:
“Ka dage Amaar. Rayuwa fa gwagwarmaya ce. Sai jarumai ke cin nasara.”
Ɓangaren Tasleem!!
Idanunta sun cika da tambaya, zuciyarta na ƙuna da damuwa akoda yaushe a cikin tambayar
“Ina Nasreen? Ina Abeesh? Ya aka yi faɗa ya ƙare haka? Kuma… me yasa na kasa komawa gida?”
Kamar wata mai juyayyar ƙwaƙwalwa ta kasa fahimtar komai...
Tana ƙoƙarin tashi daga gadon, sai wani zafi ya shige jikinta, alamar an ɗaure ikon tafiyarta da tsafin ruwa.
A lokacin wani kifi ya zagayo kusa da gilashin ruwa dake kewayen ɗakin, yana jujjuya kai kamar yana kallonta.
Tasleem ta matso kusa da glass din ruwa, ta furta cikin siririyar murya:
“Ina nan… amma ba zan daɗe ba. Zuciyata tana tsaye ga gaskiya. Babu tsafi da zai iya hana haske dawowa...”
Yayin da Amaar ke ƙoƙarin nemo Tasleem da kuma laluɓo gaskiyar halin da ake ciki, Catrina ta dawo cikin gida amma zuciyarta a ɗaure take, Akwai wani sirrin da Madam Nablah ta ɓoye — kuma Tasleem tana cikin haɗari fiye da yadda kowa yake tunani.
Madam Nablah a yanzu tana shirye-shiryen ƙarshe:
Ko dai a rasa komai, ko kuma ta kafa mulkin duhu har abada.
Sai dai kuma... har yanzu Miemie bata ƙara bayyana ba. Kuma ikon haske yana ƙara ƙarfafa ne a cikin zukatan masu gaskiya.....
★★★★★
Nasreen tana kwance a cikin dogon baccin ta tayi wani irin mafarki mai razanar wa, a gigice ta farka daga bacci tana ambaton sunan Abeesh, tana sakin numfashi a tsorace domin tinda tayi hatsarin mota daga lokacin bata ƙara sanin yanda kanta yake ba sai yanzu, yanzun ma babu Madam Nablah ne yasa har tayi saurin farka wa amma itama Nasreen ba yanzu ake son ta farka ba.....
Nasreen haka take bin ɗakin da take da kallo, a fili ta ce:
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, kulli nafsin zaa'ikatul maut, ta tabbata da gaske na bar duniya kenam? domin nasan nan wurin da nake ba duniya bane, shikenam na bar wa Catrina Abeesh ɗina? Bai kamata na sadaukar da soyayyata wa shaiɗaniyar mace kamar ta ba, ga shi na mutu nabar mata shi, shin a wani hali Abeesh ɗina yake?...."
Lokaci guda ta fashe da kuka, zuciyarta ne ya yi wani irin bugawa a razane take furta
"Tasleem! kenam na bar ƴan uwana? Amma ina ji a zuciyata cewa babu kwanciyar hankali a tattare da ni, akwai abinda yake faruwa da gida, taya zan koma gida? Ina son komawa gida...."
Sauƙo wa daga kan gadon tayi tana ƙoƙarin fita daga ɗakin, abinda ta tarar da waje ne ya tayar mata da hankali, ganin ruwa yana zagaye da gidan da take, babu hanyar tafiya iya ɗakin da take ne kawai yake tsakiyar ruwa, ga ruwan ba'a ganin ƙarshen sa..... Nasreen fashe wa tayi da kuka ganin babu wata mafita...
Toshe bakin ta tayi da hannayenta tana jero addu'o'i, cikin ikon Allah idonunta suka sauƙa akan wani tsohon kole-kole wanda ba'a amfani da shi yanzu, da gudu ta isa wurin tana ƙoƙarin juya shi domin a kife yake.....
Daƙer ta samu ta tura kole-kolen cikin ruwan itama ta shiga cikin, tana sanye da wata ƴar doguwar riga marar kauri, wanda ya tsaya a iya gwiwa, Sumar gashin ta kuwa a fake anyi mata gyaran gashi, domin Madam Nablah kullum a cikin kula da ita take, tana tsabtace ta sosai duk da dogon baccin da tayi...
A firgice Nasreen ta shiga kole-kolen cikin ruwan da icen tuƙawa, haka take sauri zata bar wurin domin tsoro wurin yake bata, ko ɗan tsuntsu babu balle wani dabba ko mutum...
Madam Nablah kuwa tana can tana tsare da Abeesh bata san cewa Masreen ta farko ba har tana shirin guduwa,
Bayan awa guda Nasreen na cikin ruwa sai yanzu ta je tsakiyar ruwan, ba ƙaramin gajiya tayi ba sai haki take tayi, tayi tafiya mai nisan bala'i sosai amma duk da haka sai yanzu tayi rabin isa, ta tsaya tana hutawa har bacci ya ɗauke ta a cikin kole-kolen.....
Har ta fara nisa a cikin baccin kamar a mafarki ta fara jin ƙarar ruwa, ita har ta manta a cikin ruwa take, ruwan da ba'a san ƙarshen zurfinsa ba, a hankali take ƙoƙarin buɗe Idanunta kwatsam idanuwanta suka sauƙa akan wani ƙaton abu a cikin ruwa yana yowa kole-kolen ta, da ta lura dakyau ta ga shark 🦈 ne mai irin wasu hakwara masu kaifin masifa, Nasreen ganin yanda Shark yake gudu a cikin ruwan yana nufo ta yasa ta hanzarta ta ɗauki matuƙin kole-kolen ta fara tuƙawa tana sauri-sauri gudu-gudu tsabar ta gama tsorata bata iya tsere wa Shark ba, haka ya iskota ya kafa bakinsa akan kole-kolen tare da kifar da shi, wani irin ihu Nasreen ta yi ta kife ita da kole-kolen ta...
A ruɗe ta fara kokuwa da ruwa tana ƙoƙarin tsere wa Shark, tana gudu a cikin ruwa shima Shark yana bin ta da gudu, gudun shark ya ninka nata sosai nan danan Shark har ya iskota bata ankara ba, taji ya yi mata wani irin kyakkyawan cizo cinyarta wurin tsoka, wani irin gigitaccen ihu Nasreen tayi, kafin ta rufe baki har ya ƙara datsa mata hakwaransa har sai da ya kusan rabe mata ƙafa biyu ta wurin cinyarta, cikin ƙanƙanin lokaci ruwan har ya canza kalar jini, Nasreen ihu sau ɗaya ta ƙara daga nan ta sume a cikin ruwan, Shark har ya buɗe bakin sa zai datsa masa hakwara ta saitin wuyanta sai ga wata halitta ta bayyana mai jikin zinariya, kyanta ya wuce misali, tana sanye da kayan gold, sumar gashin ta kalar na gold, tana riƙe da dogon mashi mai baki uku, ta fito daga cikin ruwan tare da yin sama ruwa na bin jikinta sannan ta sauƙo kan ruwan tare da caka wa shark ɗin nan mashin kafin ya kai bakinsa saitin wuyanta, ta ɗago da shi sama tana tana zazzaro ido mai launin gold, cikin ɗaga murya take faɗin
"Kasa na hallaka ka saboda rashin imanin ka, Ni ce sarauniyar ruwa kuma dole duk wani halittan cikin ruwa ya bi umarni na, ita ɗin ba azzaluma ba ce, ka hargutsa mun ruwa da jinin haske, ruwa ba ya karɓan jinin da aka zalunta saboda haka zaka hallaka gaba ɗaya...."
Daga nan ta fitar da wani haske daga cikin ƙwayar Idanunta da shi ta tarwatsa Shark, babu ko burbuɗinsa...
Daga nan Miemie ta kai idonta kan Nasreen tare da ɗagota ta hanyar haske sannan ta ƙara nitsewa da ita cikin ruwa, a cikin ruwan ta nufi yankin kogin haske wanda babu bil adama da zai iya bayyana a wurin, kuma ruwan baya karɓan duk wani azzalumi......
*ASSALAMU ALAIKUM*
*BARKAN MU ƳAN UWANA, NA MANTA BAN SANAR MUKU AN KAI MINZALIN DA YA KAMATA ACE AN DAKATAR DA FREE BOOK BA, MUN SHIGA BOOK TWO DOMIN GEJIN BOOK ONE DAGA PAGE 50 NE, SAKAMAKON RASHIN SANAR MUKU YASA NA CIGABA DA BAKU PAID PAGE A MATSAYIN FREE, TOH INSHA ALLAHU ZUWA PAGE 10 ZAN TSAYAR DA FREE BOOK NA BOOK TWO*
*ƊARI UKU NE A YANZU KOWA ZAI IYA FARA TURO KUƊIN BOOK ƊINSA NA HASKEN RUHI....*
*NAGODE*
*💋HASKEN RUHI💋*
*🫀THE LIGHT OF THE SOUL🫀*
It conveys a deep and spiritual meaning referring to the inner light, truth, or purity within a person.
*WhatsApp 09065443871*
*🌹 ASMEETAH WRITER 🌹*
*BOOK TWO__________PAID_____₦300*
Page 5 to 6
✦ WURI A CIKIN TEKU — MASAUƘIN RUHI MAI GAGARA FAHIMTA
Da suka shiga cikin ruwan, sai abin mamaki ya bayyana. Ruwan da ya kamata ya jika su — sai ya buɗe kamar ƙofar, yana kai su cikin wani babban haske.
A cikin ƙasa, ba ruwa, ba laka. Wuri ne da ba a iya bayyana shi da kalmomi — wani ɗaki ne mai faɗi wanda yake a cikin zurfin teku amma ruwa baya shiga. Katangar ɗakin na lanƙwashe kamar gilashi, amma kana iya ganin kifaye suna yawo a waje.
Gado mai taushi, labulaye masu launin turquoise, hasken zinariya da yake fita daga saman bango, ga iska mai ƙamshi mai kwantar da hankali....
Duniyar Sarauniyar Ruwa! Nasreen kwanan ta ɗaya ta farfaɗo, tashin ta ke da wuya ta tsinci kanta a cikin wani yanayi mai daɗin gaske, ganin ta a çikin ɗaki wanda ruwa ne a zagaye a wurin ga kyawawan kifaye da suke yawo abun burgewa, ɗakin sai walwali yake yana shining, abinda ya ƙara bata mamaki shine ganin babu wani rauni a jikinta, wurin da Shark ya ciza babu tabon kamar babu abinda ya sameta a jikinta, ta tsinci kanta cikin ƙoshin lafiya, miƙe wa tayi tsaye taje jikin ruwan da baya samun damar ratsowa ciki tasa hannu tana shafan kifayen da suke jiki.... Tana cikin kallace-kallace taji sassanyar murya ta bayan ta, da sauri ta waiwaya tana kallon Miemie dake zaune a bakin wani tsararren gado na gold, sai wani shining take, kana ganin ta kasan ba bil adama bace domin duk matan duniyan nan babu wacce ta kaita kyau, in ba wani ikon Allah ba.....
MIEMIE ta ce...
"Triplets daughter, fatan kin tashi lafiya..."
Nasreen haka take kallonta cikin rashin sanin ko ita wacece...
Ta ce
"Wace ce ke!?..."
Murmushi Miemie ta yi daga bisani ta ce:
"Baki san komai game da ni ba, domin bakida alaƙa da yanda zaki sanni.....ita ƴar uwarki da ta kasance ɗaya daga cikin mu ta sanni domin tana ɗauke da littafin mu na hasken Ruhi, dole zata ji labari na ko da bata taɓa gani na ba, amma gani na ma sau ɗaya ta ganni domin ni mai iya ganina kai tsaye sai ikon Allah...."
Nasreen cike da mamaki take faɗin:
"Kina nufin ke ma Sarauniyar wata jinsi ce?..."
Miemie ta ce:
"Tabbas! Sarauniyar Ruwa..."
Nasreen bata san lokacin da ta tsinci kanta a cikin farin ciki ba, domin tasan ba wurin da zata sha wahala ta zo ba....
Miemie ta miƙa mata hannu ta kuma cewa:
"Na ganki kafin ki bar gida, Nasreen. Zuciyarki ta ƙira ni... yanzu lokaci ya yi da za ki huta."
Nasreen bata yi magana ba — ta ɗan girgiza kai kawai, hawaye na bin fuskarta...