x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - HASKEN RUHI BOOK 1

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 134606 words

Category: Horror Stories

Views 177

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
cikin motar zai nufi wurin Tasleem, ganin basa nan sai sojojin su da suke ƙoƙarin ta da mota tambayi wanda yayi treat ɗin Tasleem cewa ina suke?
Sojan ne ya bashi amsa da cewa "Ogah ai tin tinin na kammala, sun tafi..."

Da sauri ya tambaya cewa "ina suka yi?..."

Mutumin ya sanar masa cewa "Ɗaya daga cikin su ne taje ta kawo musu mota suka shiga, yanzu kam ko bayan motar su baza'a iya hangowa ba..."

Cikin takaici Amaar ya cusa yatsun sa cikin sumar kansa yana faɗin "Oh god! saboda su nasa aka dawo dani Nigeria, meyasa zaka bar su su tafi?..."

Sojan ya ce "sorry Ogah ai ban san kana neman su ba..."

Amaar cikin nuna damuwa ya ce "Please a duk yanda ka gan su ka sanar mun, ina buƙatar ɗaya daga cikin su, marar lafiyan nake so..."

Sojan cikin yaƙe yake faɗin "Oga ai sai dai kawai duk wacce na gani a ciki nayi maka magana amma ina zan iya gane mai lafiyar da marar lafiyar a cikinsu, kana ganin komai nasu iri ɗaya ne asalin ƴan uwa masu kama ɗaya..."


Amaar bai bi maganar sa ba haka ya shige mota suka tafi su ma......



Bayan isar su Tasleem gida a falo suka tarar da Momminsu da wani cikakken jarumin mutumi wanda kana ido huɗu da shi zai maka kwarjini, yanayin sa kamar irin mutanen da basa son rainin nan ne, fari kyakkyawa da shi.

Da sallama a bakin su suka ƙarasa cikin falon, Nasreen tana riƙe da hannun Tasleem wacce gaba ɗaya jikin ta ba ƙwari,
Madam Nablah tana ganin Tasleem ɗaure da bandeji a kan goshin ta yasa ta saurin miƙe wa tsaye tana faɗin "Meya same ki Tasleem?..."

Aasmeen ce ta buɗi baki ta ce "Mom Ɗaliban school....."

Nasreen tayi saurin katse ta da cewa "ta ɗan samu hatsari ne..."

Madam Nablah miƙewa tayi tana taku cikin ƙasaita tazo gaban Tasleem tana kallon cikin ƙwayar idanuwanta, duk abinda ya faru sai da ta kalla a cikin ƙwayar idon Tasleem ta hanyar ai watar da tsafin ta, murmushi kawai tayi sannan ta koma yanda take zaune before ba tare da ta furta komai ba domin tasan yaranta su na fuskantar wannan ƙalubale...

Shapris wanda idonsa yake kan su ya kasa ƙibta wa mamaki yake yanda Madam Nablah take da waɗannan zuga-zugan ƴan Uku masu kamanni ɗaya.
Su Nasreen har zasu haura upstairs suka ji Madam Nablah ta ƙira su, dakatawa suka yi tare da dawowa cikin falo su na amsa ƙiran Momminsu, cikin izzah Madam Nablah ta ce "tarbiyyar da na baku kenam?..."

Tasleem Nasreen Aasmeen duk kallon juna suka shiga yi ba tare da sun fahimci abinda take nufi ba,
Nasreen ce ta buɗi baki ta ce "Mom! me muka yi?..."

Madam Nablah ta ce "ku makafi ne? ko baku ga baƙo na ba? ko bai cancanci ku gaishe shi?..."

Nasreen ta ce "Sorry Mom a hargitse muke shiyasa..."

Nasreen ce ta fara durƙusawa a gaban Shapris tare da faɗin "Barka da zuwa, fatan mun same ka cikin ƙoshin lafiya..."

Shapris murmushi ya yi sannan ya amsa mata cikin kulawa.

Itama Asmeen durƙusawa tayi ta gaishe shi cikin nutsuwa, ya amsa mata itama cikin kulawa da kuma yabon su.

Tasleem dake tsaye wani irin juyar da ƙwayar idanuwanta tayi tare da furta "hajijiya nake ji ina buƙatar hutawa..."
Daga nan ta nufi upstairs, kafin ta haura Madam Nablah cikin fushi ta ƙira sunan ta "Tasleem ki zo nan ban sallame ki ba..."

Cikin nuna damuwa Tasleem ta ce "please Mom...."

Shapris idonsa akan Tasleem domin taurin kanta ya yi matuƙar burge shi, daman fatan sa shine a cikin ƴaƴan Madam Nablah ya samu mai taurin kai wacce zai sauƙe fushin sa akan ta...

Madam Nablah idon ta akan Tasleem ta ce "ki zo ki durƙusa a gaban baƙo na ki gaishe shi kamar yanda sauran ƴan uwan ki suka yi..."

Tasleem Sarkin zuciya lokaci guda zuciyar ta ya hauro ga manya-manyan idanuwanta yanda take zaro su ta ce "impossible Mom! bazan taɓa durƙusa gwigwowina a gaban halittar da muke matsayi ɗaya a wurin Ubangiji ba..."

Madam Nablah ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba cikin fushi ta miƙe tsaye tana faɗin "Tasleem idan bazaki bi umarni na ba zaki shiga uƙuba ta..."

Tasleem haka ta tanƙwashe ta ce "Mom no one like me haka zuciyata take bata tanƙwasuwa sai dai kawai kiyi haƙuri ki barni a yanda kika ganni, zuciyata ta dabance...."

A tsawa ce Madam Nablah ta furta sunan ta cikin fushi, har yanayin ta ya fara canzawa, ƙwayar idanuwanta sun canza launin green, kafin yaran sun ankara Shapris ya yi saurin miƙe wa tsaye ya nufi Madam Nablah yana bata haƙuri akan ta sauƙo, ya tare ta yanda yaran baza su ganta ba domin ya fahimci basu san halin da mahaifiyarsu take ciki ba,
Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta rufe idanuwanta sosai sai da ta koma normal kafin ta ratsa ta gefen Shapris ta je har yanda Tasleem take tsaye gira a haɗe, hannunta ta cabko tare da wurga ta saman kujera tana faɗin "ki nutsu ki saurare ni..."

Nasreen sarkin shiga damuwa tin tinin har hawaye sun fara zubo mata, ganin yanda mommy da Tasleem suke musayar yawu, ta rasa gane wannan matsalar har sun fara zargin cewa Tasleem ba lafiyar ta ƙalau ba...

Asmeen kuwa asalin matsoraciya kenan, yanda ta ji Momminsu tana darara tsawa kamar wata dodonniya yasa jikinta ɗaukar rawa, ga yanda ta rurrungumi Nasreen tsabar tsoro..

Madam Nablah juyo wa tayi tana kallon su Nasreen sannan su ma ta basu izinin zama, ba mu su haka suka zauna dab da Tasleem kowacce jikin ta kamar wacce aka watsawa ruwa ba ƙwari sai Tasleem da take ta huci idonta akan Shaprees tana jin haushin sa domin saboda shi ake tsawatar mata...

Shapris haƙuri yake ba wa Madam Nablah tare da faɗin "Sorry Madam control your self, ki daina biye wa yaran nan domin yarinta ke damun su..."

Madam Nablah sauƙe numfashi tayi sannan ta ce "okay Shikenam yanzu inaso nayi abinda ya tara mu anan..."

Su na cikin wannan halin sai ga Abeesh ya shigo da sallama a bakin sa, cikin nuna farin ciki Nasreen tayi saurin amsa masa tare da faɗin "your welcome my lovely bros..."

Murmushi ya sau mata tare da shafa sumar kanta yana faɗin "Allah ya miki albarka my gimbiya..."

Itama Asmeen masa sannu da dawowa tayi, ya amsa mata cikin kulawa tare da sanya mata albarka itama,
Idonsa ne ya sauƙa akan Tasleem wacce ko ɗagowa bata yi ba balle yasa ran zata gaishe shi, murmushi yayi domin tin tinin yasan halin ta haka take a ko ina ma, bai biye mata ba haka ya sa hannu ya shafa gefen fuskar ta yana faɗin "my juju..."

Itama hannu ta ɗora akan nasa tana jinjina masa kai amsuwar ta kenam, shirin barin falon yake ba tare da ya kalli yanda Madam Nablah take ba balle baƙon ta,
Madam Nablah ce tayi saurin ƙiran sunan sa "Abeesh ba kaga baƙona bane?..."

A slow Abeesh ya juyo yana kallon Shapris daga bisani ya ce "your welcome..."

Shapris ɗaga masa kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba,
Abeesh juyawa ya yi zai wuce Madam Nablah ta ƙara dakatar da shi tana faɗin "Abeesh ka zo ka zauna ina son yin magana da ku gaba ɗaya..."

Ko kallon ta bai yi ba ya ce "ba ki ga yanzu na dawo daga wurin aiki bane? ina buƙatar hutawa..."

Madam Nablah ganin zai iya tizgata a gaban Shapris wanda yake matuƙar jin maganar ta ne yasa ta sauƙar da muryar ta tana faɗin "Abeesh just two minutes please..."

Cije lips ɗinsa ya yi ta ƙasi sannan ya juyo cikin falon, samun kujera ɗaya yayi ya zauna shima....

Shapris abun mamaki ya bashi ganin Madam Nablah ta kasa control mutanen gidan ta hatta ƴar cikin ta amma sai tana bayyana tsoron ta da kwarjinin ta a mutanen waje, ya rasa gane dalilin haka, ta wani ɓangaren kuma yana tunanin har yanzu a cikin yaran gidan ta babu wanda yasan asalin wacece Madam Nablah ba, tana ɓoye musu kan ta shiyasa ta kasa hukunta su,
Haka yake ta wannan tunanin har Madam Nablah ta katse shi da wata iriyar tambaya da ya daki dodon kunnen sa,
Wannan tambaya ba shi kaɗai ba hatta sauran mutanen wurin tambayar ya girgiza su...

Nasreen da Aasmeen zaro ido waje suka yi suka kallon Momminsu, tunani suke ayya kuwa wannan tambayar daga bakin mahaifiyar su ta fito?...

Tasleem wacce take sunkuye da kanta ƙasi jin tambayar da mommy tayi ne yasa ta watso da gwala-gwalan idanuwanta kan Madam Nablah, idanu kamar zasu faɗo ƙasi domin duk ta fi sauran ƴan uwan nata manyan idanu sosai, sai take ƙara gwalalo su kamar wata aljana...

Madam Nablah ƙara maimaita tambayar tayi idonta akan Shaprees tana faɗin
"Shapris kai nake tambaya, shin a cikin waɗannan ƴan mata uku wacece ta fi burge ka? ina nufin ka zaɓi wacce tayi maka kamar yanda nayi maka alƙawarin zan baka ɗaya daga cikin triplets ɗina, to yanzu zaɓi nake baka domin ka cancanci haka...."

Shapris haka yake bin ko wacce da kallo gaba ɗaya ya kasa gane wa zai zaɓa a cikin su domin duk kamannin su ɗaya, ya so ya nuna Tasleem amma sai dai duk sun hargitse kayuwan su bazai iya gane ta ba domin fuskar ko waccen su ba annuri jin wannan batun sai fuskokin su ta zama kamar na mutum ɗaya,
Ganin bazai iya ware guda ɗaya a cikin su ba yasa shi kallon yanda Madam Nablah take yana girgiza kai ya ce "Madam kawai ki zaɓa mun da kan ki..."

Madam Nablah ta ce "okay tinda kai ka buƙaci haka zan zaɓa maka..."

Shapris ya ce "amma sai dai kiyi musu alamar shaida ta yanda zan rinƙa banbance su ..."

Girgiza kai Madam Nablah tayi sannan ta ce "babu wata alamar shaida da zan musu, kai da kan ka zaka rinƙa banbance su..."

Madam Nablah idonta ta sauƙar kan wacce take ƙarshen kujera ta furta "Aasmeen..."

Aasmeen wacce take last sopa sai dai ƙirjinta ya buga jin ta ambaci sunan ta tana tsoron kar ita ce zata yiwa kyauta...

Madam Nablah ta ce "inaso kiyi mun dariya yanzu..."

Asmeen kallon Nasreen tayi wacce take gefen ta daidai lokacin da itama Nasreen ta kalle ta suka haɗa ido su na kallon juna,
Lokaci guda Aasmeen ta fashe da kuka.

Madam Nablah ta ce "dariya nake so ki yi mun ba kuka ba, kar ki ɓata mun lokaci..."

Asmeen tsabar kuka ya ci ranta sosai kasa buɗe bakin tayi sai da Madam Nablah ta darara mata wata uwar tsawa tukun ta shiga taitayin ta ba shiri ta washe bakin ta tana dariyar dole...

Madam Nablah kallon Shapris tayi sannan ta ce kaga wancan ita gushiryar haƙorin sama gare ta, ita ce Aasmeen kuma rabin raina, ina matuƙar ji da ita..."

Shapris jinjina kai ya yi alamun ya gamsu.

Madam Nablah kallon Nasreen tayi sannan ta ce "ke kuma ki mun murmushi..."

Nasreen kallon mommy tayi sannan ta ce "Mom murmushi kuma?..."

Madam Nablah ta ce "ko baza kiyi bane?..."

Ta girgiza kai tare da faɗin "a'a Mom ban isa nayi jayayya dake ba..."

Saida Nasreen ta rufe idanuwanta sosai kafin ta sau wata iriyar murmushin dole mai kama da kuka...

Madam Nablah ta kalli Shapris sannan ta ce "ka ga wannan kuma dimple gare ta, ko magana take zaka ga kyawawan dimple su na lotse wa..."

Madam Nablah ɗagowar da zata yi ta kalli Tasleem sai karaf suka haɗa ido, har sai da gaban Madam Nablah ya yanke tsabar ta tsorata da irin kallon da Tasleem take mata ga fuska a murtuƙe ba annuri, da sauri Madam Nablah ta kawar da idonta tana faɗin
"Shapris ita kuma wannan ta hanyar idanuwanta masu firgitarwa zaka gane cewa Tasleem ce da kuma yawan fushi domin rabon da Tasleem tayi murmushi tin tana yarinya ƴar shekara 10 a duniya...."
Madam Nablah tuna lokacin da Tasleem ta daina murmushi a rayuwar ta tayi, tin lokacin da ta jefa Abokinta Amaar Junaid cikin ƙaton rafi wanda yake cike da ruwa daga lokacin aka daina ganin farin cikin Tasleem, da zaka kwana kana nuna
End Ads